Showing 27001 words to 30000 words out of 83936 words
dace ba? Anya Nafeesa kun yi karatun haƙƙin miji kuwa? Kin san ko ɗuwawuna kike lashewa kullun baki biyani ba?"
Na saki ja'irin murmushi ina hararar shi, yayin da ya ƙanne min ido ya juya min baya ya ce "Ko zaki gwada lashewa."
Na kai mashi dukan wasa ya goce yana dariya, nan da nan na washe, abinka da ban iya fushi da shi ba sam, dama kuma idan ka ji rai ya ɓaci to wani ɗan jakkar uban ne ya zo ya watsa mana farin ciki.
Da yake weekend ne, ya taimaka min muka gama komai, sannan ya ce bara ya je ya yi wanka, lokacin da na fito sai na taras da ashe har ya taimakawa su Airah sun shirya.
Suka bini da "Good Morning."
Na amsa fuska ta a sake, na samu guri na zauna bayan na zuba masu breakfast na tsare su da ido, Jiddo ce babbar, zata yi shekara 6, sai Airah da Safna basu wuce 4years ba, sai na ke ganin tsantsar kamar su da Sufyan har ta ɓaci.
A sanyaye na ce "Jiddo."
Ta amsa da "Naam Aunty."
"Ina Maman ku?"
"Tana Saudiyya."
"Suna tare da dadyn ku?"
Ta girgiza kai, kafin ta bani amsa Sufyan ya shigo sai zabga ƙamshi ya ke, fuskar nan ta yi fayau, sai na ga ya ƙara azababben ƙyau.
Ya samu gefena ya zauna, yana faɗin "Kin fara yadda da maganar ƙawar ki ko?"
Idona a kan shi ina murmushi na ce "Akan me?"
"Ta faɗa miki na yaudare ki, na cuce ki, na kawo miki ƴaƴana na cikina."
Na zunɓuri baki a shagwaɓe na ce "Ba fa haka bane?"
"To ya ne? Wannan tambayar duka ne menene to.?"
"Ni dai dan Allah mu bar maganar, kawai dai ina tambaya ne..."
"Hummm, to je ki ɗiyana ne, bara ki riƙe min su ba Nafeesa?" Ya langwaɓar da kai gefe ɗaya.
Na saki murmushin da iyakar shi laɓɓana na ce "Ƴaƴanka ai nawa ne."
"Good." Shi da kan shi ya janyo plate ya mana serving, a gaban su muka ciyar da juna cike da jin daɗi da annashuwa, sai nake jin ina ma da yarana na cikina muke tare, na ɗan muskuta na janyo kunnen shi na raɗa mashi "Am eager na haihu?"
Ya ƙanne min ido "Really?"
Na gyaɗa mashi kai ina murmushi, cikin kunnena ya raɗa min "Ai ke ce kika ja, da jiya na yi niyyar yi maki cikin..."
Na kai mashi dukan wasa ya goce muna dariya baki ɗaya.
Na kauda komai na gyara gurin, ina dawowa na iske duka sun miƙe, ya kalle ni ya ce "Zamu ɗan fita mu sha iska."
"Ai na ɗauka zamu je mu bawa Maama haƙuri."
"For?" Ya waro ido waje.
Da mamaki na ce "Abinda da ya faru jiya mana."
Ya lumshe ido "Ohh My God, na ɗauka tun jiya an gama da case ɗin, anyway ki shirya ki je, dan Allah ki bata haƙurin a madadina, i have alot da zan yi yau."
"Amma ka ce iska kawai zaku je sha, me zai hana idan mun dawo sai ku je."
"And so? Ba zaki iya wakilta ta a ko'ina ba? Na ɗauka idan kina guri babu buƙatar zuwana, na ɗauka ke ɗin kamar mirror na ce." Ya kamo hannuna ya damƙe cikin na shi "Ba ki fahimci abinda nake nufi ba ko Nafeesa? Da ni da ke duka ɗaya ne, na yadda da ke, ina son ki, zaki yi duk abinda ya dace, dan Allah ki bawa maman mu haƙuri a madadina kin ji ko Baby?"
Na murmusa, gaskiya ya faɗa, ni da shi duka ɗaya, kuma zan yi abinda ya dace.
Ya manna min kiss "Ki kula da kan ki." Ya cire 5k ya bani in hau abin hawa, sannan suka fice suna ɗaga min hannu.
Kasa tsayawa nayi a tsanake in shirya, don Allah Allah na ke na je na iske Teemah, sai na goge mata rainin da take tunanin ya shiga tsakanin mu, idan ma Maama ce ta bata fuskan haka wallahi sai na ji.
#UWAR SUKUM.
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: https://chat.whatsapp.com/DsVwJ3uucmG15H6Wk0JQgq
💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*017*
Ina shiga gidan na iske Teemah a tsakar gida tana wanke wanke, wani ƙalolon bakin ciki ya turnuƙe ni, sai na ji tamkar na yi tsalle na bugata cikin ƙwandon wanke wanken na bita da ruwan ɗaurayar, na samu da ƙyar na da ni zuciyata, yayin da ta bin da banzan kallo tare da ɗauke kai lokaci guda, ashe iskancin har da su Auta shima ta zuge shi don gani na yi ya sha mur ko irin ƴar ina ƙwannan ban samu ba, sai na ji raina yayi masifar ɓaci, ni tsorona ma ɗaya kar ace ta zuge mun Uwa, don da alamu banda baƙin ciki har da munafunci ta koyo, na yi ƙwafa.
Ganin dai da gaske Auta ba gaisheni zai yi ba, ni kuma ga ɗan iskan son girma, na watsa mashi harara "Dan ubanka baka iya gaisuwa ba ne? Ko baka ganni ba?" Na tambaye shi bayan na murɗe mashi kunne.
Ya saki ƴar ƙara murya ciki ciki ya ce "Ina ƙwana."
"Sakaran banza, har kaima ka iya rashin kunyar kenan, to wallahi dai dai nake da ku." Na ja tsaki na shige ɗaki kamar zan tashi sama.
Sam banga sauyin fuska ga Mamaa ba, sai dai ni da jikina yayi bala'in sanyi, ta kalle ni fuskar ta wasai tana faɗin "Lafiya tunda safe.?"
Na sadda kaina ƙasa "Uhm, ba komai zuwa na yi gaida ku, ina ƙwana."
"Lafiya lau Alhamdulillahi, ya gida?"
"Lafiya lau Mama, Su Sufyan na gaida ku." Na faɗa ina kallon yanayin ta.
Sai na ga tayi murmushi ta ce "Alhamdulillahi, muna amsawa."
Na yi shiru ina matsa mata ƙafa da ya ke tana zaune bisa kujera, sai na ga ta ɗan ƙara sakin jiki da alamu tana jin daɗin abinda na ke, don haka na ƙara ƙaimi wajen daddana mata ina faɗin "Baaba har ya fita?"
"Eh, kano ya tafi gaisuwar abokin su."
Na zaro ido waje "Wane ciki Maama?"
"Baki san shi ba, tare suka yi secondary."
Na rausayar da kai ina faɗin "Allah sarki, Allah ya ji ƙan shi, ya gafarta masa, yanzu mutuwa farat ɗaya take ɗauke mutun, dole sai ana yi ana yafiya." Ni wai irin ɗan wayon nan, don ta yafewa Sufyan farat ɗaya.
Ta murmusa "Amin."
Shiru na yi na ɗan lokaci ina tunanin ta inda zan fara, kusan minti biyar sannan na ce "Uhmm, Mama jiya kika bar mu cikin tashin hankali da fargaba."
Ta yi kamar bata ji ni ba, na ɗago na ga idonta ashe a lumshe ya ke, na maida kaina na cigaba da faɗin "Wallahi jiya ko bacci ba mu yi ba." Nan ma shiru kamar bata gurin, don haka na cigaba da faɗin "Shi kan shi Sufyan ɗin ƙwana yayi yana kuka, bai ji daɗin abinda ya faru ba, yau ma da zazzaɓi ya tashi shine ya ce in zo in baki haƙuri."
Nayi shiru ina jiran tace min wani abu amma shiru, don haka na cigaba da faɗin "Wallahi tunda nike ban taɓa ganin abinda ya sa Sufyan kuka ba sai jiya, ya yi nadama sosai har da zazzaɓi da ciwon kai ya....
Ta ce "Allah ya sawaƙe."
Na murmusa na cigaba da faɗin "Bawan Allah kamar ya mutu Maama sabida takaici, wallahi jikin shi rinkim da zazzaɓi, idanun nan jawur, haka na yi ta bashi haƙuri da yau da asuba ma asibiti..
Ta katse ni tana zabga min mugun kallon ta tare da janye ƙafar ta tana faɗin "Ke bani son sakarci da surutan banza."
Na marairaice murya "Dan Allah ki yi haƙuri Maama wallahi ba surutu ba ne gaskiya na faɗa yayi nadama, wallahi tunda asuba ya ce in baki haƙuri shi kunya yake ji, ni ce na dage sai da safe..."
"Ba yace mantawa yayi ba Nafeesa?"
Na gyaɗa kai na ce "Eh wallahi, kuma dama yana da yawan mantuwa, haka ya ke ko kuɗi ya aje wani sa'in sai dai ni ke tuna mashi inda suke, rannan ma haka ya manto wayar shi office."
"Tunda bai taɓa manto uwar shi a motorpark ba ai da sauƙi." Teemah ta amshe da shigowar ta kenan falon tana tsane hannun ta da ƙwalle.
Dama da cikin ta, don haka ban san lokacin da na yi tsalle na isa gabanta ba, na kashe ta da mari ina hushi sannan na haɗe ta da bango ina faɗin "Ni sa'ar ki ce dan uwar ki? Koko mijina sa'ar ki ne da zaki nemi zagin shi?"
Mama ta daka min tsawa "Sakarta Nafeesa."
Na fashe da kuka ina faɗin "Mama baki ji me ta faɗa ba akan Sufyan? Sannan baki ga messages da ta turo min ba jiya?"
"Ki sake ta." Ta sake umurtata
Cikin kuka na cigaba da faɗin "Sai yarinya ta zage ni sannan a hanani ɗaukar mataki? Har fa mijina take neman zagi a gaban ki yanzu.?
Teemah ta ce "Au dama ban zage shin ba? To Sufyan ɗin ya karci hancin uwar sa."
Wani mahaukacin duka na kai mata ina ihu "Har kin isa ki zagi mijina ki ƙwana lafiya dan uwar ki? Sabida ba ki samu mijin ba kika yi aure shiyasa baki san darajar shi ba, wallahi sai na lahanta ki."
Duk zatona zan daki Teemah ba tare da ta rama ba kamar yadda nake mata kafin aure, kuma ma ance idan mutun yayi aure wata daraja yake samu ta musamman, don haka na sake ta na yi tsalle na fizgo wata wayar wuta dake gefe don gani nake laifin ta ya fi ƙarfin bugu da hannu, Mama na faɗin "Ki bari Nafeesa, ki rabu da ita na ce."
Kai tsaye na ce "Wallahi ban ƙyale ta, duk wani iskancin ta sai na cire mata shi, idan ma ɗaurin gindi ta samu sai in gani."
Na ɗaga laftawa Teemah wannan wayar tsakiyar kan ta, kafin na sake yunƙurin lafta mata wallahi yarinyar nan mai zubin Maguzawa ta amshe wayar daga hannuna ta shiga lafta mun ita ta ko'ina, tun ina ƙoƙarin amshewa har na soma ƙoƙarin karewa ina kallon Mama da ban san dalilin da ya sa ta ƙi tasowa ta rabamu ba.
Can azaba ta ishe ni na ce "Mama kina gani fa?" Na faɗa cikin kuka
Sai a lokacin ta daka ma Teemah tsawa, sannan ta rabu dani ta yadda bulalar itama cikin kuka take faɗin "Kin ɗauka zaki daki banza? Wallahi tun daga lokacin da kika nuna ma mijinki uwar ki bata da daraja nima...
Ban san lokacin da Mama ta iso gurin ba, sai dai saukar marin da na ji a fuskar Teemah, ta nuna mata ƙofa "Fita anan..."
Nima ta jeho min jikkata da hijabina a jiki tana faɗin "Daga nan ki wuce gidan su Fannata ki gyara KUSKUREN ki."
Na yayibi hijabin ina faɗin "Ai ban faɗa mashi ba, kuma wallahi baki daki banza ba, har ma kin isa."
Wani banzan kallon da Maama ta watsa min sai da na ji tankar itama bulalar zata sa min, don haka kafin ta yi magana na yakici hijabina na fice da sauri sai ma a ƙofar gida na sashi.
Tafiya nake ina kuka tare da takaicin abinda Teemah ta yi min, sai ma nake jin tamkar da gayya Mama ta bari sai da Teemah ta make ni sannan ta hana ta a matsayina na matar aure, sam baa ƙyautatawa auren ba, wallahi na yi zaton na fi ƙarfin bugu ga kowa bare ma waccen yarinyar da kafin na yi auren nake mata dukan tsiya ba tare da ta rama, amma yanzu da yake baƙin ciki take da aurena shine ta amshe bulalar ta bugeni, na kasa tsaida ƙwallana, sai na ke ganin idan Teemah ta yi min haka ne sabida abinda Sufyan yayi ma Maama ai bata fini jin zafin abin ba, nima ai mahaifiyata ce kuma ina son ta.
Kamar ba zan wuce gidan su Fannata ba, sai kuma wata zuciyar ta ce kawai na bi umarnin Maama, idan na koma sai na fara faɗa ma Sufyan dukan da Teemah ta mun sannan na faɗa mashi na je gidan su Fannata, na san zafi maida hankali ga dukan ba ma zai damu da gidan su Fannata da naje ba, da wannan tunanin na tsaida abin hawa na nufi gidan su Fannata.
A zatona zata watsar dani ta wulaƙanta ni kamar yadda na yi mata, don haka na tamke fuska tamau lokacin da na iskesu falo suna fira da ƙannen ta.
Ta washe baki cike da mamakin ganina kafin ta miƙe ta iso gareni kamar tun kafin nayi aure ta rungume ni tana faɗin "Ƙawata masu aure ne yau a gidan maga zawarawa?"
Na yatsina fuska don na san magana ta yaɓa min, ƙannen ta suka gaisa ni sannan suka fice, da yake na san mamar su malamar asibiti ce kuma tunda har ban ganta ba nasan bata gidan, don haka ban tambaye ta ba na samu guri na zauna ina cika da batsewa.
Ta kawo min lemu da cake ta aje, sannan ta zauna gefena tana tambayar "Amma ɓatan hanya kika yi?"
Na girgiza kai ba tare da nace komai ba, ina ƙoƙarin sakin raina ganin bata nuna min komai ba.
"Ki ce Allah yau ya ci da ni?"
Na ce "Uhmm."
"To ya jikin? Hope kin warware?"
Na ce "Da sauƙi."
"Allah ya ƙara sauƙi."
"Amin."
Ta kai min duka tana faɗin "Dama anjima kaɗan nake niyyar zuwa gidan ku wallahi in kaima Maama saƙo"
"Saƙo?"
"Eh, First Salary, shine na sai mata atampha ta sa mana albarka." Ta ƙanne min ido.
Da mamaki na bita "Yaushe kika fara aikin?"
Ta kai min duka a cinya "Tsaya nan dai."
"Hmm, Amma ko ki faɗa min?"
Ta ƙwashe da dariya "Ba na je zan faɗa miki ba kika min eh ya ne."
Sai na ji wata kunya ta lulluɓe ni, ban san wace irin abokiya Allah ya haɗani da ita ba, ban san wane irin so da uzuri Fannata ke min ba, na sadda kai ƙasa na ce "Allah yasa alheri, ina nawa kason.?"
"Ke ma ai kin san dole ne." Ta miƙe ta shiga ɗakin su, sai gata ta fito da handbag mai ɗan karen ƙyau cikin ƙwalin ta ta miƙo min " Dama hanyar kai maki ita nake nema wallahi."
A sanyaye na ce "Duk wannan abin ba kiyi fushi dani ba Fannata."
Ta watsa min harara "Uban wa ya faɗa maki? Wallahi na yi fushi da ke sosai, amma ai kin san ni ban iya riƙe mutun ba ko.?
"Dan Allah ki yi haƙuri." Na marairaice.
Ta dakatar da ni "Share dan Allah."
Na bita da ido, tausayin ta da kunyar ta suka dirar mun, yayin da maganganun da na faɗa mata suka riƙa dawomin.
"Dan Allah ki yi haƙuri.
"To."
Mun ɗan taɓa fira sannan na ce zan tafi, da yake ta daban ce, bayan jikkar kuma ta san ina da abubuwan lefe amma sai da ta shiga ta ƙaro min kayan ƙwalliya da turaruka ta bani, kunsan Allah Baban su Fannata ya fi Sufyan kuɗi, gida mai ƙyau ne kadai Sufyan zai nuna masu, sabida su irin tsarin da ne, ta raka ni har na hau abin hawa sannan ta juya cike da annashuwa da alamu ta yi farincikin zuwan nawa sosai.
Ni kam Allah Allah nake na je gida na faɗa ma Sufyan ɗibar albarka da Teemah ta yi min, don bana buƙatar ta ci banza, kuma na san ba zai bar ta haka ba, sai dai wani ɓangare na zuciyata na rawa, ina tsoron ran shi ya ɓaci maganar zuwa gidan su Fannata, ga kuma tulin kayan da ta bani.
#UWAR SUKUM.
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*018*
Bayan na koma gida naɗewa na yi bisa gado na ƙi ko da dafa abinci, don wallahi na shirya haɗa na Teemah gurmin da ba zata iya fidda kan ta ba, don bana tausayin ta, sai na tabbatar mata da banbancin gatan da ke tsakanin matar aure da wacce bata da aure..
Wajen azahar na ji ƙarar motar Sufyan, na janyo bargo da sauri rufawa kaina, nan da nan na hau rawar sanyi ina jijjiga, ina jin yana ƙwala min kira na yi shiru, ya shigo bedroom ɗin, ganina a ƙwance ya sa yayo kaina da sauri ya yaye bargon yana tambayar "Baby lafiya?"
Na fashe da kuka "Bana jin daɗi ne."
Ya kai hannu ya shafi wuyana tare da zama gefen gadon ya ɗago ni yana faɗin "Me ke damun ki? Ba dai ciwon cikin ba ne?"
A shagwaɓe na ce "Jikina ke ciwo."
"Subhanallahi, garin ya a ƙafa kika je ne?"
Na fashe da kuka "Da na je gida Teemah ce ta dake ni da wayar wuta."
Ya ƙanƙance ido "Pardon me please?"
Na soma rera kuka ƙasa ƙasa tare da ɗaura kaina a cinyar shi, ya ɗaura hannun shi a goshi na cikin rashin fahimta ya sake tambaya ta "Bangane ba, wane irin duka ki ke nufi Nafeesa."
Na sake narke murya ina shashsheka "Rashin kunya ta min shine na ɗauki bulala zan daketa ta amshe ta hau lafta min, don kawai ina ƙoƙarin kare martabar mijina."
"You are kidding."
"Wallahi kuwa."
"Ahhhh, wai da gaske? Fateema dai ƙanwar ki? To ina mutanen gidan? Rashin tarbiyyar ta har ya kai ta amshe bulala ta bugar min mata? Ahhhh, i will deal with her, Ina zuwa." Ya miƙe tsaye.
"Baaba na gidan?" Ya tambaye ni ranshi a ɓace.
Kafin na bashi amsa hankalin shi ya kai ga ledar da na aje kai hannu ya ɗauko ya duba "Na waya aje wannan abin?"
A raunane na ce "Fannata ce ta bani."
Yanayin shi yayi bala'in canza wa, cikin ƙunar rai ya ce "Fannata? Ban hana ki mu'amula da ita ba?Ina ma kuka haɗu? Nan ta zo? Shine ta kawo miki sabida ni na kasa siyar maki ko?"
Na ɗauka abinda Teemah ta yi min zai sa ya ƙi maida hankali akan lamarin Fannata amma sai na ga ba haka ba, cikin sanyin jiki na ce "Maama ta ce in je gidan su in bata haƙurin abinda na yi mata."
Ya dafe kan shi tare da juyi