Showing 45001 words to 48000 words out of 83936 words
wanke kawai, sai dai wani ɓangare na zuciyata ya ƙwaɓe ni da yin haka, ƙara in tsaya komai zai faru kawai ya faru, don ba zan yadda da wannan ƙasƙancin ba, na yi shiru gabana na tsananin faɗuwa, yayin da ni ke jera addu'o'in neman tsari daga Umma.
"Nafeesa.." Daga yadda ya kira sunan ka san ba cikin yanayin daɗi ya ke ba.
Da ƙyar na amsa da "Naam."
"Me na faɗa miki jiya?"
Na tashi zaune ina yatsina fuska kamar irin ta mara lafiyar nan a hankali na ce "Akan me?
"Akan Umma. "
Na yi shiru ban ce komai ba, ya tako har kusa da katifar yana kallo na fuskar nan murtuk kamar bai taɓa dariya ba, a tsawan ce ya ce "Tashi ki je ki yi abinda Umma ta sa ki."
Kafin na bashi amsa Umma ta cafe "Ta ya zata yi tunda ban isa da ita ba, yanzu dan Allah Sufyan banda mugun hali da ƙyashi ko baa ce ta wanke kayan Asiya ba, bata da hankalin da zata ɗauka ta wanke? Ɗazu fa ta yi nata? Banda baƙin hali me ya hana tace a kawo na Asiyar ta haɗa tayi ? Yarinya abin tausayi, ta rasa yara uku ace ba zaa riritata ba? To wallahi muddun na isa da kai, matar ka ta tashi ta wanke kayan can yanzun nan."
Ya sake harzuƙa ya ce "Kin isa da ni Umma." Ya juyo gare ni "Tashi ki wanke su tun kafin ranki yayi mummunan ɓaci wallahi."
Na ɗaga kai zan yi magana na ji daga bakin ƙofa ana faɗin "Umma a bani zan yi abina."
Ai da sauri na maida kallona gare ta, tana tsaye sanye da doguwar riga bubu, ta cikin ɗan hasken ɗakin na ƙare mata kallo yayin da gabana ke dakan uku uku, har ga Allah ƙyaƙyƙyawar gaske ce, don ban fita ba, sai dai mu goga, sannan tana da haske mai ɗaukar ido, kuma bana bleaching ba, ga alamun hutu da ƙwanciyar hankali da kuma gogewa ta duniya a tattare da ita.
Na maida kallona ga Sufyan da ya juya fuskar shi a sake yana faɗin "A'a, zaa miki."
Kutmar uban can, na faɗa a zuciyata, anan fa gidan duk rashin kunyata a zuci kawai na ke iya yin ta, a fili kuma sai da yaƙe da kuka yadda zuciyata ke ta farfasa ina jin wallahi ko da sakina zai yi ba zan taɓa wanke kayan nan ba, wato abin ma ya zo da ƙasƙanci, har ta san ni ce aka ba wankin kayan ta.
"Ki tashi Nafeesa tun kafin ranki ya ɓaci." Ya daka min tsawa.
"Ni fa ba zan yi mata wanki ba wallahi, kaina ciwo ya ke Sufyan, Haba dan Allah." Na ƙarashe maganar murya ta na rawa.
Umma ta ce "Ƙarya ta ke wallahi babu wani ciwon kai, ni zaki ma rashin kunya Nafeesa?"
"Ban miki rashin kunya ba Umma, wallahi kaina ke ciwo. "Idanuna suka ciko da ƙwalla.
Asiyar ta matso fuska a ɗaure zata janye bokitin sai na ga har rige rigen dafe shi ake da Sufyan da Umma, wani tuƙuƙin baƙin ciki ya turnuƙo min, na haɗiyi yawu mai zafi lokacin da Sufyan ya ke faɗin " Idan ba zata yi ba, ni sai na yi mata Umma."
Na yi tsalle na diro daga gadon ina faɗin "Wallahi ba zaka yi ba."
Wata bangaza Umma ta min tana tambayar "Ke a uban wa? Wacece ke Nafeesa?
Na ɗauke kai ina kallon Sufyan idanuna na fitar da wasu irin ƙwalla masu ɗumin gaske, ture min hannu ya yi daga jikin shi, yana faɗin" Ta saki ba ki yi ba, ke kin isa ki hana ɗanta yi ne?"
Na zuba mishi ido ina fitar da ƙwalla masu ɗumin gaske, ji na ke kamar na yi tsalle na shaƙare Asiyar nan, don wallahi na yi masifar tsanar ta, ina ganin ya ɗauki bokitin ta saki murmushi yayin da Umma ta gyaɗa kai ta cije laɓɓa alamun isa, ban san lokacin da na yi tsalle na dire gaban shi ba ina faɗin "Wallahi muddun ka yi wannan wankin sai ka sake ni Sufyan, wallahi na gama auren ka, kar ka maida ni banza jaka wacce bata san ciwon kan ta ba mana? Ta ya zaka ɗauki kayan baligar mace da babu aure tsakanin ku ka wanke a gabana?"
"To sai uban menene don ya sake ki? Ke har wata mace ce?" Umma ta faɗa tana min kallon ƙasƙanci tare da nuna ni da yatsa.
Ban ko kalli inda ta ke ba, na zuba mishi ido ina ganin yadda jikin shi ya yi masifar sanyi, cike da baƙin ciki na ce "Kuma wallahi tallahi na gama auren ka har abada, ba zan sake zama da kai ba..."
Ya saki bokitin yana kallona, yayin da jikin shi yayi masifar sanyi, Umma ta rarumi bokitin ta danƙa mashi a hannu tana faɗin "Sakar ta, dama wace bura ubar zata tsinana maka? Banda jaraba da wahala."
Ban dai kalle ta ba, sai Asiyar da ta murmusa tana kallon Sufyan ɗin, da ƙosuwar jin abinda zai fito daga bakin shi.
Umma ta janyo kafaɗar shi baya tana faɗin "Tunda ba gindin gold gare ta ba, ka sake ta mana Sufyan."
Cikin rawar murya ya ce "Umma.."
"Ka sake ta, ba ita ta ce ba? Ka sake ta na ce, ina ce tun kafin ka aure ta, Asiyar ka fara aure, sai da ta haifa maka ɗiya uku sannan ƙaddara ta gifta ka rabu da ita ka ƙwaso ta, don haka sake ta."
"Umma dan Allah ki yi haƙuri. "
"Ni me na ce? Ai ita ta nema."
Yayi shiru yana kallona, ni wallahi na san duk runtsi Sufyan ba zai iya sakina ba har abada, sai dai idan asiri suka mashi, na kalli Ummana sheƙeƙe nima na ɗauke kai na sama, ba dai zan mata rashin kunya ba, bare har na tunzura shi.
Asiya ta kuma kai hannu ta ɗauki bokitin da gayya, yayin da Umma ta cafke ta miƙa mishi taba faɗin "Da ban saka wankin ba, amma yanzu na ce ka ɗauka ka je kayi shi Sufyanu."
Na riƙe bokitin ina faɗin" Wallahi sai dai Jamila ta yi shi, amma Muddun Sufyan ya mata wanki na barshi har abada." Ina da tabbacin Sufyan ba zai iya rabuwa da ni ba wallahi, dole ya nemi wata mafita, domin na fi uwar shi haƙƙi a kan shi, ni aure na ya ke, mutuncina da komai yana ƙarƙashin tsaron shi...
Umma ta riƙe baki "Au da ni zaki ja kenan? To sake ta, ka je ka yi wanki idan har na isa da kai.."
"Na sake ki saki ɗaya...."
Kamar saukar aradu haka na ji kalaman Sufyan na yawo a ƙwalwata, lokaci guda juwa ta ɗauke ni, da ƙyar na dafe bango na kalle shi ina tambayar "Ka sake ni?"
"Eh ya sake ki." Umma ta bani amsa
Na kalle shi na tabbatar da maganar dai daga gare shi ta ke, sai na ji komai ya tsaya min, komai fa, mamaki da tashin hankali suka min dirar mikiya, mamakin wai yau ni ce Sufyan ya saka sabida mahaifiyar shi ta ce? Mamakin wai yau ni ce Sufyan ya saka sabida ya wanke kayan wacce ba muharramar shi ba, sabida mahaifiyar shi ta ce? Ina soyayyar? Ina alƙawarin? Na runtse ido na gam ina jin yadda jinina ke tafarfasa, na zuba mishi ido a lokacin da ya ɗauki kayan ya fice Umma, Asiya da Jamila suka mara mishi baya ba tare da sun ƙara kulani ba, a take na sulale ƙasa na dafa ƙasa da hannaye na biyu biyu ina fitar da wani irin numfashi mai wutar gaske.
Saki! Saki! Ni Sufyan ya saka? Dama uwa har darajar uwa ta kai ta sa ka aikata kuskure ga matar da kake aure? Dama uwa ta fi aure daraja? Sai ga hawaye masu ɗumin gaske na bin kumatuna, kamar wacce aka tsinkara na miƙe zumbur na janyo jikkata da kayana da ke zube bisa gadon na hau lodawa a ciki ba tare da na liƙe ba, sannan na zura hijabina na ɗauki wayata, ina jin komai dare ba zan iya cigaba da zama a gidan su ba, wallahi ko a tasha ne ƙara ma ƙwana.
Anya kuwa? Anya yana cikin hankalin shi? Na girgiza kai, lokacin da zuciyata ta tabbatar min da Sufyan ba zai taɓa aikata hakan a cikin hankalin shi ba, sai dai ko Asiya ko Umma wani ya mishi asiri, ko kuma sun haɗa sun yi a tare, wallahi asiri ne, asiri suka mishi. Wallahi sai na ji tausayin shi ya kamani, tausayin halin da zai shiga idan ya dawo hankalin shi ya fahimci ƙwaɓar da ya aikata, na cigaba da goge hawaye akai akai.
A lokacin da na fita tsakar gidan, yana zaune a kujera yana wanke kayan, yayin da Jamila ke mishi ɗauraya, a tunanina tunda sakin sashi akai, kum wallahi asiri aka mishi, don cikin hayyacin shi ba zai iya sakina ba, zai biyo ni ya roƙeni yafiya sannan ya maida auren mu, mu je ya kama ni hotel kafin safe mu wuce, amma sai na ga ya sadda kan shi ƙasa ya cigaba da wankin shi kamar bai ji zan fita ba, a take na ƙara tabbatar da aikin asiri ne...
Ina jin lokacin da Jamila ta ce "Ki bari da safe ki wuce, hanya babu ƙyau fa."
Na watsa mata uwar harara, na ja jikkata na wuce zuciya ta kamar zara fito waje, yayin da tausayin Sufyan ke shawagi a wani ɓangaren na zuciyata, sam ban taɓa tunanin zaa haɗa baki da uwa a cuci ɗa ba sai yanzu, anya ma kuwa ita kanta Umma ba asirin Asiya ke tasiri a kan ta ba? Na ja jikkata na yi gaba....
A ɓangare ɗaya kuma ina tunanin yadda zamu ƙare da Ummana, fatana dai Allah ya sa ta taimake ni mu nemarwa Sufyan maganin karyewar sihiri, don na san ɗan laifin da na mata ina zuwa zata yafe min, sai da Sufyan ɗin ne na ke jin kamar ba zata bani haɗin kai domin dawo dashi hayyacin shi ba....
#UWAR SUKUM
[5/25, 8:49 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*028*
Da ƙyar na ƙaraso bakin titi na samu abun hawa, yayin da idanu na suka bushe baki ɗaya sai dai tuƙuƙi da tafarfasar da zuciyata ke yi, Allah ya taimake ni ina da kuɗi a jikkata don haka kai tsaye tasha na nufa sabida bana da wani ɗan uwa ko dangi da zan je gurin shi na ƙwana, kuma yadda na ke ji a raina wallahi ba ma zan iya ƙwana a garin ba, kuma fa kar ku ce ina jin haushin sakin da Sufyan ɗin ya min, aa na sani aikin asiri ne, kuma ina da tabbacin zai biyo ni yana kuka da ban haƙuri, na shafi gudan jinin shi da ke rayuwa a jikina, sai na ji ƙwallan ta fito, na lumshe ido dai dai lokacin da muka isa tashar.
Duk da magriba ta yi a haka na samu motar da zata maido ni katsina, kuma cikin hukuncin Allah mutum ɗaya ake jira, don haka ina shiga aka tashi motar muka ɗau hanya.
Sai da iskar mota ya fara kaɗani sannan na kiɗa kaina bisa cinyoyina na fara rera kuka kamar yanzu abin ya faru, kafin na ɗago na janyo wayata na kira number Mamaa domin na sanar mata da abinda ya faru amma matar nan sam taƙi ɗaukan kirana, kuma wallahi na san tana ganin kiran, kai ko da wayar bata hannun ta babu makawa ta na hannun Teemah, ganin na yi kira har biyar ba a ɗauka ba, ya sa na canza tasha na kira Babaa, shima bawan Allah nan sai da na mishi kira biyu sannan ya ɗauka haɗe da sallama.
Ban amsa sallamar shi ba, sai da ƙara farashin kukana ina faɗin "Baaba Sufyan ya sake ni."
A tare da ƴan cikin motar suka ɗauki salati, sannan ya tambaye ni "Saki kuma Nafeesa? Garin yaya? Me kika aikata mashi?
"Wallahi tallahi asiri aka mishi, kawai daga...
Ya katse ni "Kina ina yanzu da na ji ƙarar iska."
Kai tsaye na ce "Gashi nan zan dawo gida."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, kar ki taho Nafeesa, ki zauna gidan ki yi idda."
"Uwar shi ta koro ni." Na faɗa lokacin da wani mulmulen baƙin ciki ya tokare ƙirjina
"Subhanallahi, garin yaya Nafeesa?Koma menene ki bari gobe da safe ki taho."
"Na ri ga na taho."
Duk yadda ya so na koma gidan in ƙwana acan na ƙi wallahi na ƙi, ƙarshe ma yanke wayata na yi tare da kashe ta na jefa jikka na cigaba da kukana ƙasa ƙasa, da ya ke aƙwai mace a cikin motar ta soma jajanta min, tana faɗa min haka maza suke basu da amana, duk tsawon shekarun da zaka ɗauka tare da su baka fi ƙarfin su saje ka ba a duk lokacin da rashin mutuncin su ya motsa.
Na maka mata harara, ko uban wa ya faɗa mata laifin shi ne, na yi watsi da ita har sai da na ji ta cigaba da sukar mijina sannan na tsagaita kukan na ce "Baiwar Allah Uwar shi da tsohuwar matar shi suka haɗu suka mishi asiri wallahi, amma Sufyan ba zai taɓa sakina ba muddun yana cikin hayyacin shi."
Matar ta jinjina da alamu itama da takaicin namijin a tattare da ita, sannan ta ce "Kayya dai, ba wani asiri sai iskanci, kin ganni nan? Na auri mijina tun bashi da wando, ni ke aikin wahala na ci da mu safe, rana dare, ban taɓa nuna mashi gazawar shi ba, wallahi babu irin wahalar da ban yi ba, ƙarshe ubana ya rasu aka raba mana gado na bashi ya ja jari, ya yi aure da kuɗin, ban damu ba na cigaba da rayuwa da shi a wahale, in ci da shi, matar shi sauƙi na ma ban taɓa haihuwa ba, a wannan wahalar Allah ya rufa mishi asiri ya fara sanya wando, sannan ya bawa amaryar ciki, wallahi ranar suna ya danƙara min saki uku reras, ba zai iya zama da juya ba."
"Mijin ki daban nawa daban." Na bata amsa a sanyaye.
"Duk fa halin su ɗaya, haka mijin ƙanwata ya..."
Na katse ta ta hanyar taɓo kujerar driver ina faɗin "Dan Allah tsaya zan canza guri."
Ta murmusa "Aa ƙanwata, abin bai kai haka ba." Sai ta saki maganar ta cigaba da ƙwantar min da hankali tare da bani magunguna da zan iya haɗawa da kaina da kuma addu'o'in karya sihiri kowanne iri ne.
A lokacin da na isa gida kusan 11pm, ina knocking Baaba na buɗewa da alamu dama yana jirana, cikin tashin hankali ya ke tambayar "Sai da kika taho Nafeesa? Ina wayar ki?"
Na fashe da kuka ba tare da na ce mishi komai ba, ina kallon cikin gidan da tunanin zan ga su Maama, auta, da Teemah cirko cirko suna tsumayen jiran a kamar yadda na ga Baaba ya yi, domin su taya ni jaje da kukan abinda aka min amma wayam babu su babu alamun su.
"Garin yaya haka ta faru Nafeesa? Me kika aikata mashi da har ya kasa haƙurin safiya ta yi ya sake ki.? Ya katse ni cikin jimami
Cikin kuka na ce "Wallahi ban yi komai ba Baaba, asiri suka mishi ya sake ni."
"Subhanallahi, su wa?" Ya faɗa da alamun ɗaurewar kai a tattare da shi.
"Uwar shi da tsohuwar matar shi.." Na bashi amsa kai katse.
Ya yi jim na ƴan mintoci, sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana kallona, can ƙasan maƙoshi da alamun tashin hankali a tattare da shi ya ce "Je ki ciki, zuwa safe zamu tattauna."
Har na ja jikkata na fara tafiya na juyo jiki a mace ina wuni tambayar shi "Malan liman yana karya asiri ko?"
Ya kalle ni cike da tausayawa ya girgiza kai ya ce "Je ki ƙwanta kin ji ko, zuwa safe duk zamu yi wannan maganar."
Na cigaba da tafiya kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, na ƙarasa ɗakin Mamaa, wai abin takaici sai na iske ta shememe tana bacci sai ka ce bata san ƴar ta aka ma asiri aka saki ba, wallahi na ɗauka ina shigowa zan ga ruwan rubutu na sha da shafawa a jiki, takaicin haka ya sa na fashe da kuka, na kalli Teemah da auta kowannen su sai bacci ya ke hankali ƙwance, kowanne shege ma ya kawo su ɗakin Mamaa? Hala suna gulmana bacci ya ƙwashe su, na jefa jikkar gefe ɗaya na hau taɓa ƙafafun Mamaar ina kiranta cikin ɓacin rai "Maama, Maama."
Cikin bacci ta ce" Wai waye?
A ƙule na ce "Nafeesa."
Ta gyara ƙwanciyar ta, sannan ta ce "Wace Nafeesa?
Kamar zan ce ta Sufyan sai kuma na fasa, na fashe da kuka na ce "Nafeesa fa.
Ta murtsuka idanun ta da hannu biyu biyu tana tambayar "Har an iso.?
Wato dama ta san da zuwa a shine har da su bacci, na ƙara sautin kukana ina faɗin "Eh dama ashe kin san ina hanya shine kike bacci har da salaɓe?"
Ta min banza kamar bata ji me na faɗa ba, a take raina ya ƙara ɓaci, na ɗauke ƙwallana da hannu ɗaya ciki ciki na ce "Maama saki na fa Sufyan ya yi."
Cikin halin ko in kula tayi hamma ta sa hannu ta kare sannan ta ce "Ashsha, abu bai yi daɗi ba, haka na ji baban ku na faɗa."
"Shine kuma kike bacci kamar baki san girman saki ba? Haba dan Allah, wannan ai ba adalci ba ne, ko don ke baa taɓa sakin ki ba ne?"
Walau na ji tafin hannun ta a kuncina , ban ma san lokacin da ta miƙe daga ƙwance da take ba, na dafe kuncin ina kallon ta, ta nuna ni da yatsa "Idan ban yi bacci ba uban ki zan tsaya na miki? Ka ji mara kunyar yarinya dan uban ki, ni zaki riƙa gasawa magana kamar ke kika haife ni? To ban san girman sakin ba, dan ubanki sake ni yanzu idan kin isa."
Na ja baya na buga ƙafa ƙasa ina kuka, cikin ɗaga murya na ce "Na shiga uku, kamar kina jira na, me na