Showing 33001 words to 36000 words out of 83936 words

Chapter 12 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1713

ce "Kin san me kike faɗa kuwa?"

Na fizgi makulli ina faɗin "Ni dai dan Allah Inna unguwa zan je, ki fito zan rufe gidan, idan kuma in rufe ki a ciki to.."

Takaici ya hana ta ƙara min magana, ta ja ƙafafun ta kamar wadda ƙwai ya fashe wa a ciki muka fito, sai da na rufe gidan da key sannan na ce "Ki gaida gida, sauri na ke ko ruwa ban baki ba ki yi haƙuri."

Bata saurare ni ba ta kama gaban ta, yayin da na raka ta da harara, banda jaraba da rashin sirri da ga ka kira uwarka ka faɗa mata kana cikin damuwa sai ta kama gayawa nata ƴan uwan? Ni shaf na manta ma unguwa ɗaya muke da Inna, da ya ke da ita da Ummana uwar su ɗaya uban su ɗaya, kuma ni fa tunda na ga Sufyan baya so a zo mashi gidan sai na ɗauki wani karatu, ban taɓa taka gidan ta ba, don ina ce sai ka je sannan kaima zaa zo maka, kuma na ga kamar itama hakan ne, don bata taɓa zuwa gidan nawa ba tun kawo ni, amma yanzu gashi Maama na so ta janyo min ita da babbar bala'i.

Can wani lungu na maƙale sai na bar ganin ta sannan na juya na koma gida, dama babu inda zan je, don kawai ta fitar min gida yasa na mata ƙarya.

Na shige gidan kamar zan tashi sama, yayin da na janyo wayata dake maƙale tana chaji, na yi dialing number Mama, don wallahi dole na sanar da ita bana son yamiɗiɗi.

Ringing ɗaya ta ɗauka na gaishe ta sama sama, yayin da ta hau tambayar "Lafiya Nafisa? Sai kiran ki na ke baki ɗauka ba, bayan kin tayar min da hankali? Me ke faruwa?"

Ciki ciki na ce "Ni fa babu komai, dama ƴar matsala muka samu da Sufyan kamar kowanne ma'aurata kuma mun daidaita."

Ta yi jim kafin ta ce "To Alhamdulillahi."

"Amma Mama ban ji daɗin yadda kika faɗa ma Inna wannan maganar ba, na ɗauka idan na faɗa miki sirri babu wanda zai ji, amma shine kika ƙwashe kika faɗa ma Inna, yanzu fisabilillahi ni da uwata ba zan yi sirri da ita ba...

Rabon da na ji Maama ta auna min zagi wallahi har na manta, "Dake da sirrin kun ci ubanku Nafeesa, ni zaki maida sakara? Ko ni sa'ar ki ce da zaki riƙa min iskancin da kika ga dama? To bari ki ji kar ki kuma faɗa min abinda ya shafe ki ɗan ubanki, ki je can ki ƙara ta."

Ta yanke wayar ta, yayin da na zunɓuri baki ina faɗin dama wallahi ba ɗan ƙari, wannan ma ban san zaki ƙwashe ki faɗa ma ƴar uwar ki ba.

*************

Yinin ranar haka na wuni ina zunɓure zunɓure, ala dole so na ke Sufyan ya fahimci ban ji daɗin abinda Mamaa ta yi ba, a haka har ya dawo da la'asar ya iske ni ƙwance bisa doguwar kujera, sai zabga ƙamshi na ke.

Ya bini da kallo, yayin da ya tsayar da ƙwayar idon shi akan dukiyar Fulani na, da rabinta a waje ya ke, na kawar da kai gefe ɗaya ba tare da na ce komai ba.

"Hug da kisses ɗin yau duk ba zan samu ba?" Ya lakace min hanci tare da ɗosana ɗuwawun shi gefen kujerar.

Na gyaɗa kai tare da murguɗa baki "Uhmm.."

"Subhanallahi, zo ki faɗa min taɓa min Sweetie ta? Ko dai har yanzu baki huce ba?" Ya faɗa bayan ya rungumo ni jikin shi.

"Ni fa babu komai." Na faɗa bayan na tabbatar da ba zai yadda da hakan ba.

Ilau ya hau naci "Ban yadda ba, aƙwai abinda ke damun ki, dan Allah ki faɗa min, ni ne na yi laifin ko wani ne daban?"

Ganin ya ƙagu da son sanin abinda ke damuna yasa na narke mashi ina faɗin "Maama ce mana, wai daga ɗazu na faɗa mata abinda ya faru shine har ta ƙwarmatawa ƴar uwar ta, ita kuma har da zuwa."

"Ina ta zo.?"

"Nan gidan mana."

"To me ta zo ta mana?" Ya faɗa bayan annurin fuskar shi ya ɓace.

Na taɓe baki na ce "Ina fa na sani."

Ya ja siririn tsaki "Maganin ki kenan wallahi baki da sirri Nafeesa, yanzu daga wancen ɗan abun har kin ƙwashe kin faɗa ma Maama, Allah kaɗai ya san inda abin zai je, Allah ya sa ma bata faɗa ma mijin ta ba." .


"Kamar ya?"

Ya taɓe baki "Eh mana, tunda har ta faɗa ma ƴar uwar ta ai kin san dole ta faɗa ma Teemah da baban ku, shima kuma baban naku ai ba zai rasa ɗan uwan da zai faɗa mawa ba, haka kurun kin ja min zagi da magana a cikin dangin ku, ni wallahi duk macen da bata da sirri ba matar da zaa zauna da ita ba ce. "

Gabana ya faɗi ras na bishi da kallo a tsorace, yayin da na tausasa murya na ce "Ya zaka ce haka, kasan dai lokacin raina a ɓace yake shiyasa na sanar mata."

"Ai ga ɓacin ran nan ni kina neman janyo min."

Ya miƙe zai tafi na yi saurin kamo hannun shi tare da lagwaɓe kai ina faɗin "Dan Allah ka yi hakuri, wallahi ban san bata da sirri ba sai yanzu."

Ya min banza amma ya dawo ya zauna, na ɗaura hannuna bisa cinyar shi ina yawo dashi a hankali ina faɗin "Please Habibiii na maka alƙawarin hakan ba zata sake faruwa ba, please Forgive me."

"Kin tabbata?" Ya kama min kunne ɗaya.

Na gyaɗa kai tare da jefa mashi lallausan murmushi na ce "Insha Allahu."

Ya lakaci hancina "Good girl, faɗa min ya kuka yi da ita."

Ban ɓoye mishi komai ba na zayyana mashi, har da wayon da na mata don ta bar gidan, ya ƙwashe da dariya yana faɗin "Nafeesata an fara hankali."

Na murmusa tare da ƙanne mashi ido na ce "Wanka ko abinci?"

"Wane kike so na fara?"

"Bath."

"An gama..." Muka jefawa juna murmushi sannan muka tashi a tare, yana riƙe da hannuna muka shige bedroom ɗin, na taimaka mishi ya rage kayan shi ya ɗaura towel ina zolayar shi "Zo ka bawa babyn ka abinci."

"Really?"

Na kanne mashi ido ɗaya, yayin da ya janyo ni muka faɗa saman gado muna dariya, daga wasa sai gashi abun ya girmama.

Bayan mun samu natsuwa a tare muka yi wankan, sannan muka fito falo na aje mana abinci, mun soma ci kenan wayar shi ta yi Ringing ya kai hannu ya ɗauka ya sata handsfree ya ɗaura a cinye shi fuskar shi cike da walwala yana faɗin "Umma ai yanzu nake ƙoƙarin kiran ki sai gashi kin kira. "

"Dama kira na yi in ji ta gama tsiyar ta?"

Ya kalle ni ya ƙwashe da dariya yana tambayar "Surukar ki kike nufi?"

"Eh.."

"Gashi har mun shirya." Ya kamo hannuna da hannun shi ɗaya

"Ya dai fi mata." Ta faɗa babu yabo ba fallasa.

"Ba ma ki san wani abu ba Umma, ai ina dawowa na iske ƙanwar Mamar ta zo wai sasanci, dama na faɗa miki lokacin da na mareta ta kira Mamar su akan zata taje gida, to shine ita maman ta sanar da ƴar uwar ta tazo ta ji ko lafiya."

Umma ta ja tsaki tana faɗin" To meye abin zuwa daga samun ɗan saɓani."

"Wallahi kuwa Umma, dan ma Nafeesa ta fahimci basu ƙyauta ba, shiyasa ma da ta zo ta ce mata fita zata yi don ta tafi."

"Ya dai fi, amma dai yanzu lafiya lau ko?

"Eh Umma lafiya lau, ita fa tsoron ta ɗaya kar na dawo da Asiya. "

"Yo Sufyanu idan ka tashi maido da Asiyar ta isa ta hana ne? Ita ɗin banza zata rabaka da uwar ƴaƴan ka? Bayan ita ta kasa haifa maka?"

Ya katse ta yana satar kallona "Umma na faɗa miki ciki gare ta."

"Ciki? Ba ance sikila zata haifa ba? Ka gwammace a haifa maka wahala fiye da ka maido lafiyayya? Sufyanu Asiyar da ka sani da ba ita bace ta yanzu, wallahi ta canza kullun sai ta kirani ta gaishe ni, ni kam ina so ka maidata......



#UWAR SUKUM

[5/17, 8:21 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*


*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm




_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._




*021*



Da sauri ya yanke wayar yana kallona, i zuwa lokacin idanuwana sun cika da ƙwalla, tambayoyi ne fal a zuciyata, yayin da maganarta ta dake ni kuma ta ɓata min rai, wallahi da ace Maama ce faɗa ma Sufyan haka na tabbata sai na yi tsalle na faɗa mata ban ji daɗi, amma shi sam baya son ganin laifin ta. Ni ban ma san wa ya faɗa ma Ummar Sufyan haihuwar sikila ta wa ce ni kaɗai? Ko ta manta da ni da ɗanta duka lalurar mu ɗaya, kuma a haka muka dage muka yi aure don muna son juna?

Ya kamo hannuna cikin na shi, a tausashe ya ce "Why are you crying? Don ta ce na maido Asiya ko? To ai Nafeesa laifin ki ne, ke ce sai ki yi 3days baki kira Ummana ba, kuma a haka sai na takura miki, sannan irin wannan ƙyautatawar ta uwar duka baƙya yi."

Hawaye na ya ƙara yawa na zuba mishi idanu, wato ni ce mai laifi? Duka maganganun da ta faɗa daidai ne? Shi tunda muka yi aure sau nawa ya je gidan mu? Ina ce sau ɗaya ne lokacin da ya kai ƙarar Teema, sannan maganar kira da ya ke, wallahi na tabbatar ko number Baaba da Mamar baya da su, tunda muka yi aure ya goge, don ƙwanaki da zan kira Mama sai da na sa number ta, ƙara ni bana week ba tare da na kira uwar shi ba, kuma a haka ma faɗa ya ke, idan yadda yake so ne kullun na kira ta safe da rana

Ya katse min tunani na ta hanyar janyo ni jikin shi yana faɗin "Stop crying please, ban ce zan maido ta ba ai."

A hankali na ce "Ashe ba ni kaɗai ba ce bana da sirrin.?"

"As in how?" Ya tambaya idon shi a waje.

Na lumshe idona ba tare da na amsa mishi tambayar ba, na cigaba da faɗin "Baka faɗa ma Umma ba ni da kai duka AS ne? Idan na haifi sikila laifin namu ne mu biyu? Sabida mun sani muka dage sai mun yi aure?"

"Me kike faɗa haka Nafeesa? Dan Allah mu bar maganar, ita Umma ba zata fahimci haka ba, tunda har na samu normal tare da Asiya."

"Ai da sai ka faɗa mata nima idan na auri AA normal yaran zan haifa ai . "

Ya tsuke fuskar shi tamau kamar bai taɓa dariya ba, ya zuba min ido, na gyaɗa kai na ce "Haka ya kamata ka faɗa mata."

"Mahaifiyata ce."

"Nima ina da mahaifiyar."

"Wannan mai surutun tsiyar?"

Lumshe ido na yi na ce "Masu surutun tsiya dai."

Ƙwabbbb ya buge min baki tare da ture ni kusa dashi yana faɗin "Umman kike faɗawa haka don baki da kunya? To wallahi baki isa ba, ni na san darajar uwata, sai da nayi 1000days ina rayuwa a jikin ta, tun daga ciki har yaye, daga jikin ta nake samun abinci."

A fusace na ce "Ni kuma a Ghana must gon uwata na rayu ba a cikin ta?"

"What ever dai, ki kiyayi furucin ki akan Ummana."

"Nima haka, ni ga sakara ka faɗi abinda kake so ga uwata sai ta ka ce mutun, bayan ita ce ma bata ƙyautawa." Na murguɗa baki.

"Dan ubanki Umman ce bata ƙyautawa?" Ya faɗa a harzuƙe.

"Kar ka sake zagina, wannan ne na biyu, idan ka kuma na uku wallahi sai na rama."

Wani banzan mari ya sauke min a kumatu, na dafe ina kallon shi, yayin da zuciyata ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi, ba tare da na ce mishi komai ba na shige ɗaki na finciko hijabina, duk soyayyata da Sufyan ace sau biyu kenan yana marina, idan na cigaba da zama gidan shi wallahi wata rana dukana zai yi da bulala ƙara tun wuri in tafi gida a ɗauki mataki, domin duk makauniyar soyayyar da nike mishi wallahi ba zan zauna namiji na duka ba.

"Ina zaki je?" Ya faɗa daga kan doguwar kujera yana karkaɗa ƙafa.

Ban ce mishi komai ba na fice a fusace, ina jin yana "Kar ki fita, idan kika fita ba da yawuna ba, kuma kin sani sarai duk takon ƙafar ki mala'iku na tsine maki."

Na ja tsaki hawaye na bin idanu na, ni ban ma san idan zaka yi yaji kana buƙatar iznin miji ba, a haka ba tsaida napep, sai da na shiga na zauna sannan gabana ya fara faɗuwa, ina fargabar abinda zan iske a gida, ga dai rashin kunya na walwalawa Maama gashi kuma banda gurin zuwan da ya wuce gidanmu.

Bayan na biya mai napep din na sauka, na ƙara sautin kukana sannan na shiga gidan, na iske Fannata ta zo, suna cin ɗan wake da Teemah yayin da Mamaa ke zaune ta miƙe ƙafa tana sakuce da tsinke.

A tunanina duka zasu taso a ruɗe suna tambayar menene, amma sai na ga daga Teemah har Maman sun watsar dani, sai Fannata da ta rungume ni tana faɗin "Me ya faru? Wani abu ya same ki?"

Na saci kallon Maama da Teemah sannan na kuma fashewa da kuka ina faɗin "Sufyan ne?"

"Wani abu ya same shi?"

Har zan ce marina yayi sai kuma na tuna tsinannen surutu irin na Maama, wata ƙyil ma ta ce ba zan koma ba, ni kuma wallahi ban zo don su kashe min aure ba, zuwa na yi su ɗan ja mishi kunne.

"Ki faɗa min wani abu ya miki?" Fannata ta faɗa a kasalance.

"Matsala muka samu."

Mama ta yi wuf ta miƙe ta nuna min ƙofar gida a fusace tana faɗin "Matsalar uban ki, zo ki koma tun kafin na ƙwaɗe ki wallahi, ban shirya tallata ki ba.."

Fannata ta marairaice "Mama dan Allah ki yi haƙuri, tunda kika ganta wallahi da babban dalili."

"Dalilin banza da wofi, ta koma can ko kashe ta zai yi na yafe wallahi."

Teemah ta tsame hannun ta tana faɗin "Wallahi kuwa."

Na watsa ma Teemah harara ina faɗin "Ke kuma uban wa ya saka da ke?"

Cikin tsiwa ta ce "Duk abinda ya shigo gidan ubana ya shafe ni."

Kamar Fannata zata yi kuka ta ce "Dan Allah Maama ki yi haƙuri, idan ba ta zo nan ba ina zata je?"

Daƙyar Fannata ta lallaɓi Mama ta barni na shiga tsohon ɗakin mu na zauna bisa katifa ina kuka, yayin da Fannata ta biyo ni ta zauna gefena tare da dafa kafaɗata tana faɗin "Dan Allah ki yi shiru ki bar wannan kukan insha Allahu komai zai wuce."

Na cigaba da kukana, ta sake marairaice murya ta ce "Haba Nafeesa sai ki tayar mana da hankali, ko dai sakin ki yayi?"

A razane na ɗago ina kallon ta, wallahi ban yi zaton Fannata bata ƙauna ta ba sai yanzu, tunda har ta buɗe baki tana ja min saki, kamar na luƙa mata zagi sai kuma na danne zuciyata da ƙyar ganin ƙananan hawaye a fuskar ta, na maida kaina ƙasa ina faɗin "Sakin kike min fata Fannata?"

Ta hau girgiza kai da sauri "Subhanallahi, ta ya zan miki fatan saki ƙawata? Na ga kukan yayi yawa ne, dan Allah ki yi haƙuri haka nan."

Ban ce komai ba na koma na ƙwanta, itama bata sake tambayar dalilin da ya sa na taho ba, ta miƙe ta min banƙwana ta fita, ina jin tana roƙon Mama akan kar ta kore ni, yadda na ke son Sufyan tunda har suka ga na baro gidan wallahi da dalili babba, su dai bincika sosai.

Na taɓe baki na gyara ƙwanciyata, message da ya shigo wayata ya sa na kai hannu na ɗauka ina dubawa, ashe har da missed call 12 da messages 5 daga Sufyan, na zunɓuri baki na soma karantawa don ba zan iya tsallake su ba, kuma ni ai ba messages na shi nake fushi ba da shi kan shi ne.

_“Ashe zaki iya tafiya ki bar ni Mata ta? Ashe aƙwai ranar da zaki taka ƙafarki ki fita daga gidan Sufyan ɗin ki da sunan ya miki laifi? Am disappointed Baby na.”_

_“Gidana is in complete idan babu ke, ina son ki, ba zan iya rayuwa babu ke ba, please ki dawo Nafeesata, na karɓi laifina, zan kuma amshi duka hukuncin da zaki yanke min.”_

_“Idan na mutu ki yafe min, zuciyana ciwo ya ke Nafeesata, ke ce ke haska duniyata.”_

Na zabura na dafe ƙirji zuciyata na bugawa da ƙarfi da ƙarfi, yayin da hankalina ya yi masifar tashi, mutuwa fa? Ta ya ma zan iya rayuwa babu Sufyan? Ai ban san lokacin da na yafe mishi komai ba, na san ƴan group ɗin kuskuren so zasu ce ban ƙyauta ba, to ku je don kan ku, wallahi baku son da darajar aure ba, na janyo wayata na yi dialing number shi.

Ringing ɗaya ya ɗauka "Nafeesataaaaaaaaaahhhhhh." Ya ja sunan cikin wata irin sigar da sai da tsigar jikina ta tashi yarrr.

"Me ya same ka?" Na faɗa cikin rawar murya jin da ƙyar ya ke magana.

"Zuciyata Nafeesa, ba zan jure rashin ki ba, zuciyata zata fashe, uhmmmmmmmm, idan na mutu ki yafe mun." Ya kuma faɗa da ƙyar.

Jikina ya soma rawa "Na shiga uku Sufyan, dan Allah kar ka mutu, wallahi yanzu zan dawo, nima ba zan iya rayuwa babu kai ba."

"Kin tabbata zaki dawo yanzu."

"Wallahi kuwa." Na finciki hijabina na fice daga ɗakin da gudu na, yayin da Mama ta sha gabana tana jefa min wani mugun kallo.

"Gidan uban wa zaki je?"

Cikin rawar murya na ce "Gidana zan je, Sufyan ne daga tahowata ya samu attack a zuciya."

Teemah ta ƙwashe da dariya "A tafawa attack..."

Na watsa mata harara, sannan na kalli Maama na marairaice na ce "Dan Allah ki barni in tafi, kar wani abu ya same shi."

"Babu gidan ubanda zaki je, yadda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login