Showing 30001 words to 33000 words out of 83936 words

Chapter 11 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1710

tsakar bedroom ɗin yana tambayar "Mama ke auren ki? Mama ce ke baki iznin fita? Meyasa dan Allah ake son nuna mun ban isa ba? Wato sabida na ce ki je ki bata hakuri shine itama sai ta baki nata umarnin? Ok good kin ƙyauta."

Na kamo hannun shi da sauri tare da fashewa da kuka ina faɗin "To ni da me kake so na ji? Da dukan Teemah ko da faɗan ka? "

Kai tsaye ya ce "Dukan Teemah wannan Family issue ne, wannan kuma iyaka ta ake son nuna mun, kuma ba zan yadda ba. "

Ya fizge hannun shi ran shi a ɓace, har ya kai bakin ƙofa ya juyo yana faɗin "Ki fito ki nemawa waɗannan yaran abinci."

Ya fice fittttt.

*******************

Zamana da yaran babu daɗi sam don duk abinda na yi masu ban burge ba,  a haka suka gama hutun su suka tafi, sai dai abinda da ya ban mamaki ba su tafi da kayan su ba, ya ce duk hutun duniya anan zasu zo suyi shi, ni dai da ido na bi ni.

A ɗan tsakanin ne na fahimci ina da wani ciki, kuma na tabbatar bai kai wata ɗaya ba, don haka bayan na kauda kayan da muka gama cin abinci, na ƙwantar da kai na bisa cinyar shi, cikin Annashuwa na ce "Albishirin ka?"

"Goro."

"Ina da ciki fa."

"Ciki? Na cin abinci ko na me?"

Na ja hancin shi "Na haihuwa."

Sai na ga yanayin shi ya canza, ya tada ni zaune ya riƙe kafaɗuna "How sure are you?"

Na juya idanu na "Wallahi kuwa."

Ya furzar da iska daga bakin shi, kafin ya ƙaƙalo murmushi da bai wuce laɓɓan shi ba, ya lakuce min hanci sannan ya ce "Na kusa zama baba."

Na gyaɗa kai tare da rufe fuska ta da tafin hannu, ya janye hannun, ya rungume ni sosai "Am so happy gaskiya, kin san ko da yaushe maganar da Umma ke min kenan, sai dai problem ɗin issue na genotype ɗinnan shi ke tada min hankali, don wallahi crisis na sickle cell ɗinnan..

Na ɗaura yatsana bisa laɓɓan shi "Ƙhairan insha Allahu, kuma ka manta wannan lafiyayye ne? Dama ai kace na farkon ne zai zama sickler na biyu lafiya, so ka ƙwantar da hankalin ka."

"Yeah my love, na manta ashe an yi wani." Ya shafi marata "Idan Macace sunanki zan maida mata, idan kuma namiji ne sunana zai ci."

Na jefa mashi hararar wasa "Allah ba zaka sa mata sunan tsofaffi ba."

Ya ƙwashe da dariya "Kuma fa haka ne, Nahisa tun 19 no calender."

Na kai mashi dukan wasa ya goce, tun daga lokacin da kowa ya daina leƙo mu farin ciki ya wanzu a gidan mu, baka taɓa jin kanmu da Sufyan wallahi kullun cikin walwala da annashuwa, ni kaina hakan ba ƙaramin daɗi ya min ba, sai dai idan na yi missing gida na kira mu gaisa.

Ya miƙe ya ɗauki wayar shi ya fita, Ashe kiran Doctor yayi bayan sun gaisa Sufyan ya ce "Aƙwai matsala fa, tana da ciki, kuma wallahi ban shirya ɗaukar lalurar sickler ba, kai kasan crisis da suke da shi, kasan azabar da iyaye ke sha, kullun gantale hanyar asibiti, magani for life, jini, komi mutun ya tara sai ya ƙare a kan su, Doctor ina son Nafeesa amma ba zan iya yadda na sa kaina a matsala ba, ba zan yadda duk tattalin arziki ya tafi akan abinda zata haifa ba ƙarshe ma ya zo bai rayu ba, ina tunanin kamar ita bata san meye sickler ɗin ba."

"To yanzu me kake so ayi.?

"A zubar da cikin, if possible ma a dakatar mata da haihuwa."

"Amma Sufyan duka kasan da wannan ka yadda kuka yi aure?

"Yes, sabida ina son ta, sannan idan ma yara ta ke so, zan iya ɗauko mata su Airah su dawo gunta baki ɗaya."

Dr ya ja numfashi sannan ya yanke wayar, suna gamawa kiran Umma ya shigo, ko gaisuwar shi bata amsa ba, ta soma da masifa "Ni fa wallahi na gaji da jiran banzan, idan yarinyar nan ba zata haihu ba, to ka maido Asiya.....




Ku yi manage dan Allah, kar ku ce na gantale.



UWAR SUKUM.
[5/17, 8:20 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*

   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm



  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._


*019*

Sai da Sufyan yayi jim tukun ya ce "Umma dan Allah ki bar maganar Asiyar nan, wallahi bana jin zan iya maido da ita, kin fi kowa sanin rashin mutuncin da ta yi min kafin mu rabu, kuma idan yaran kike so, ai sai na amso na gurinta su dawo hannuna tunda dama ba ita ce ke da haƙƙin kula da su ba, na bar mata ne kafin na sake wani auren.."

Gunjin kukana da ya ji a bayan shi yasa ya maido hankalin shi gare ni, na ƙara sautin kukana, yayin da jikina ke rawa sai ka ce mazari, zuciyata ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi, a zatona zai razana ganin na ji me ya ke faɗa amma sai na ga sam ba haka ba ne, hasalima sai ya maida wayar shi a kunne yana faɗin "Umma zan kira ki anjima, Nafeesa ce ke jin rigima."

Ya yanke wayar, sannan ya tako kusa dani fuskar shi ɗauke da murmushi yana faɗin "Idan Umma ta jiyo kukan ki fa? Me kike so na faɗa mata." Irin yadda ya maze kamar bai san dalilin kukan nawa ba, ko dai bai yi tunanin na ji maganar fidda ciki bane da maganar wacce ya kira Asiya.

Ya kai hannu da niyyar dafa kafaɗata, na buge hannun ina faɗin "Wacece Asiya?" Don maganar ta tafi tayar min da hankali fiye da zubda ciki, shi ko ba komai na ji kalmar yana sona.

Ya ƙwashe da dariya yana faɗin "Wai dama ko da wasa ban taɓa baki labarin Asiya ba? Zo mu je falo sai na faɗa miki acan."

A tsawan ce na ce "Babu inda zanje sai ka faɗa min wacece ita?"

"Tsohuwar Matata ce." Ya faɗa kai tsaye tare da maƙe kafaɗa

Wallahi sai na ji tamkar an buga mun duguma a ƙirjina, na yi tangal tangal zan faɗi na dafe bango da ƙyar ina fidda numfashi sama sama.

Cikin halin ko in kula na tsinkaye shi yana faɗin "Bi a hankali kar ki faɗi mana Sweetie."

Na ɗago na kafa mashi ido, ina jin muguwar tsanar shi da takaici shi lokaci guda, wallahi ko da wasa ban taɓa tunanin Sufyan maƙaryaci bane sai yanzu a tunani duk kalmar da ta fito daga bakin shi gaskiya ce, da ƙyar na buɗ baki na ce "Dama kana da mata? Ka taɓa aure Sufyan?"

Ya murmuwa "Ke ya zaki maida abu babba Sweetie, duka fa auren bai kai 10years ba muka rabu, please dan Allah zo mu je in ji yadda za'ayi da cikin nan, na san kin ji bana son shi ko? Kuma za ki yi komai domin ki faranta min."

Ya kama hannuna na buge shi da ƙarfi ina aika mashi da mummunan kallo mai cike da takaici, wani irin azababben kishi nake ji duk da basa a tare, ina jin sam bai cancanci Sufyan ya ɓoye min wannan sirrin ba, idona cike da ƙwalla na kafe shi da su, cikin rawar murya na ce "Ban yi tunanin kai maƙaryaci bane ba Sufyan, wallahi ka ci amana ta ka yaudare ni, me yasa tun kafin mu yi aure baka faɗa min ka taɓa aure ba? Me yasa ka yaudare ni akan kai saurayi ne?"

Ya waro ido waje cike da mamaki ya ce "Dama na taɓa faɗa miki ban taɓa aure ba?"

"To me yasa baka faɗa ba?" Na tambaya a tsawance.

"Sabida ke ma inda a ce ba budurwa ba ce ba zaki faɗa min ba, sai dai ki shiga bagaruwa a lulluɓeki a kawo min, so ban ga amfani....

Na katse shi "Ƙarya kake ni ba zan yaudare ka ba, munafuki....

Ɓacin rai ya bayyana ƙarara a fuskar shi, ya nuna ni da yatsa "Ya isa haka, me na maki da zaki riƙa zagina haka? Ko kin ɗauka nima sakaran namiji ne da zaki faɗa min abinda kika ga dama? Au ashe rashin ɗa'ar ba ga Fatima kaɗai ya tsaya ba, dukkan ku ne baku samu tarbiyya ba, to bari ki ji, wallahil azim zan mugun saɓa miki, sakara da bata san darajar miji ba...

Duk a cikin kalaman shi kalmar sakara ta fi baƙanta min rai, wato a dake ka a hana ka kuka? Na lashi laɓɓana tare da ɗauke hawayena da babban yatsana, na zuba mishi ido ina faɗin "Ni ce sakara?"

Ya gyaɗa kai "Eh, banda kina sakara, dabba iyayen ki basu baku tarbiyya ba, ta ya zaki ta sa miji a gaba kina faɗa mishi waɗannan wayayyen maganganun.

Sam bana jin ina cikin jerin matayen da miji zai zaga in yi shiru, wata baƙar zuciya ta ƙwashe ni, ban san lokacin da na ce "Kai ne dabba sakarai Sufyan, kuma tarbiyya da kake magana kaine ka rasa ta a gidan uban ka.....

Falll na ga walƙiya a fuskata, wani azababben zafi ya ratsa kuncina na dama, na dafe bango ina maida numfashin tare da ƙoƙarin saito duniyar da nike, sai da nayi minti uku tukun na fahimci zafin mari ne, na ɗago da ƙyar na zuba mishi ido yana tsaye ƙiƙam ranshi a dagule, kafin in yi wata magana na tsinkaye shi yana faɗin "Ko da wasa, kar na kuma jin kalmar iyayena a bakin ki, don wallahi ban haɗa su da kowa ba, idan kuma ba haka ba wallahi abinda zan maki sai ya fi haka..."

Ya juya a fusace ya shige ciki, yayin da na zube bisa guiwa ta na fashe da wani irin mahaukacin kuka, abubuwa goma da ashirin suka haɗe min, na fi minti talatin a gurin, sannan na miƙe jiki babu ƙwari na koma ciki, na gifta shi zaune a falo yana karkaɗa ƙafafu, kai tsaye bedroom na shige, na ɗauko babbar jikkata na soma loda kaya, ina jin har abada na gama auren Sufyan, domin duk namijin da zai ɗaga hannu ya daki matar shi wallahi ba abin zama da shi ba ne, bayan kuma shine da laifi, shi ya yaudare ni, ina zubawa ina kuka, sai da na ɗauki duk abin buƙata sannan na rufe ta gam na ɗauki hijabina, sam barka wayata ta yi ƙara na kai hannu da niyyar ya ke ta sai na ga kiran Mamaa ne, don haka na ɗauka da sauri ina ƙara sautin kuka na, cikin tashin hankali Mama ke tambayar "Lafiya, me ya faru.?

"Sufyan ne. " Na faɗa cikin kuka.

"Me ya samu Sufyan ɗin?"

"Ashe yana taɓa aure bai faɗa min ba? Wallahi gida zan taho, na gama auren shi."

"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, kar ki sake ki taho Nafeesa, ki zauna a gidan ki, wannan bai zama hujjar da zaki baro gidan ki ba." Ta faɗa cikin sanyin murya.

"Wallahi tahowa zan yi Mama ba zan zauna ba." Na yanke wayata.

Ina ganin ta cigaba da kirana amma sam na ƙi ɗaga wayar, don bana jin aƙwai abinda zai hana ni barin gidan Sufyan yanzu.

Ina ƙoƙarin fita na ci karo da shi, ko kallon inda yake ban yi ba na zagaye shi zan wuce, sai na ji yayi saurin cafko hannuna ya zube ƙasa, na soma ƙoƙarin ƙwace hannuna amma sai ya rungume ƙafafuna yana faɗin "Dan Allah kar ki tafi Nafeesa, wallahi ba zan iya rayuwa babu ke ba, ki yafe min ki min duk hukuncin da kike gani ya dace, amma banda tafiya Nafeesa, kar ki tafi ki barni..."

"Wallahi sai na tafi, na gama auren ka tunda har ka saka hannu ka dake ni." Na faɗa cikin kuka.

"Wallahi sharrin shaiɗan ne, ban san na dake ki ba Nafeesa dan Allah ki yafe min, wallahi ba zan taɓa rayuwa babu ke ba, idan har kika tafi dai dai yake da kin tafi da rayuwa, ki tausaya min Nafeesa, ki yafe min, ina son ki, ina ƙaunar ki, my life is incomplete, ki tausaya min.... " Ya janyo ni da ƙarfi ya rungume, ina jin yadda ya ke fidda kuka tamkar ƙaramin yaro.

Nan da nan sai na ji zuciyata ta yi sanyi, domin duk namijin da zai zubda maka hawaye wallahi ba ƙaramin ƙaunar ka ya ke ba.

"Forgive me Nafeesa, Dan Allah ki yafe min, idan kin tafi wallahi na shiga uku, ke ce rayuwata, ke ce farin cikina..."

Ban san haka nake da power ba a zuciyar Sufyan sai yau, na zunɓuri baki domin wani sashe na zuciyata na tafarfasa akan lamarin Asiya, a hankali na ce "Ka yi alƙawarin ba zaka ƙara duka na ba?"

Ya gyaɗa kai "Wallahi na maki alƙawari."

Na kauda kai gefe ɗaya "To Meyasa baka taɓa faɗi min ka yi aure ba kun rabu da matar?"

Ya sa hannu ya juyo da fuskata gefen shi, yayin da ya haɗe ta da shi, cikin rauni da hawaye ya ce "Sabida bana so ki rabu da ni, ina tsoron rasa ki Nafeesa."

Na lumshe ido, sai na ji wani irin tausayin shi ya kama ni, ashe har na kai haka a rayuwar shi? Wani farin ciki ya lulluɓeni, na lashi laɓɓana na ce "Su Aira ɗiyan ka ne?"

Ya yi jim yana kallona lokaci guda kuma ya sadda kan shi ƙasa yana faɗin "Zan iya yafe su muddun zaki zauna da ni Nafeesa...

"Haba Sufyan, ɗiyan ka fa ne, dan Allah kar daina faɗin haka, ba zan rabu da kai ba, suma ba zaka yafe su ba, ina son ka, dole in so su, kawai dai na ji ba daɗi da baka faɗa gaskiya ba, amma yanzu komai ya wuce, babu inda zan tafi in barka...."

Ya ƙara rungume ni gam tare da sumbatar goshina yana faɗin "Dan Allah ki yafe min."

"Ya wuce."

"I love you." Ya ɗaga ni, ya kama hannuna ya zaunar dani gefen gado, sannan ya ɗauki ƙafata ya ɗaura ya ƙwantar dani yana faɗin "Nagode Nafeesa, maganar cikin kuma ina son shi, mu haifi abin mu, zan iya komai domin ki."

Na gyaɗa kai ina bin shi da kallo, yayin da na ji zuciyata ta yi wasai kamar babu abinda ya faru, ya sake sumbatata a karo na ba adadi sannan ya miƙe yana faɗin "Ki ƙwanta ki huta bara in je in dawo kin ji ko? And please ki min alƙawarin ko na tafi babu inda zaki je."

Na lumshe ido alamun na yi, sannan ya fice jikin shi na rawa, wallahi sai na ji tausayin shi na ratsa dukkanin saƙo da lungu na zuciyata, samun miji mai tsoronka ba ƙaramin abu ba ne, sai yanzu nake ganin wautar matan da ke ɓata kuɗin su don su mallaki namiji, ni gashi babu ko sisina amma tsoron na rabu dashi na ke, na gyara ƙwanciyata wani ɓangare na zuciyata na azalzalar son sanin wacece Asiyar nan, yayin da ɗayan ɓangaren ke tunasar dani babu buƙatar hakan, sabida ko ba komai na tabbatar da Sufyan ya barta har abada...

Sallamar da na ji a falo ce ta sa na fita da sauri, a tsakiyar falon na yi katari da.



_Bazan dinga typing weekend ba, dan Allah a yi haƙuri sai Monday, ina da uzuri._




*UWAR SUKUM.*
[5/17, 8:21 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*


FREE BOOK



*HASKE WRITER'S ASSO.*


*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm




_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._





*020*



Na bita da kallon ba'a maraba da ke anan, tare da dafe kaina gefe ɗaya, ina addu'ar kar Allah ya maido Sufyan yanzu, na samu mun shirya sai ga wata matsalar na neman kunno kai? Har ga Allah ban ji daɗin zuwan ta, kaina ya kulle yayin da nake tambayar kaina shin me ya kawo ta gidan ma a daidai wannan lokacin banda jaraba? Me yasa mutane ba zasu gane yawon banza ba abin yi bane? Wallahi da ƙasar turawa muke da tuni an yi ram da dangina, haka kawai ba biki ba suna ku yi ta gantalin zuwa gidan mutane ba tare da an gayyace ku ba, shin ko dai bata san mijina baya so ana zuwar mashi gida ba? Na ja siririn tsaki ta yadda ba zata jiyo ni ba, da ƙyar na saita kaina, ina yatsina fuska na ce "Au su Inna na?"

"Eh mu ne, ki ce ma lafiya lau ku ke." Ta faɗa tana ƙoƙarin zama ɗaya daga cikin kujerun falon.

"Ko uban wa ma ya ce mata ta zauna?" Na faɗa a raina, yayin da zahiri na watsa mata harara ƙasa ƙasa ina faɗin "Ce miki aka yi babu lafiya ne Inna?"

Kai tsaye ta ce "Eh, ai maman ku ce ta kirani hankali tashe ta ce in leƙo mata ke in ji me ke faruwa, wai kin kira ta kina kuka hankalin ta ya ƙi ƙwanciya."

Wani mugun takaici ya lulluɓe ni, raina a ɓace na ce "Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un, yanzu har ta fara yaɗawa?"

Kamar bata fahimci me na ke nufi ba ta ce "Matsalar tsakanin ki ne da mijin? Idan yana gidan kira min shi."

Na kalle ta sheƙeƙe na ce "Wai dan Allah wa ya faɗa miki ina da matsala ne?"

"Maman ku mana."

Kasa danne zuciyata na yi na cigaba da faɗin "Sai dai idan ita ke neman janyo min matsalar yanzu, haka kurun daga faɗi mata magana sai ta hau tallata ni kamar mai jira? Ina ce ciki ba dan abinci kawai aka yi shi ba."

Ta kalle ni dososo alamun mamaki a fuskar ta, yayin da na shige ciki fuuuu sai kace wacce zata tashi sama, na finciko hijabina da jikka na fito ina faɗin "Inna fita zan yi."

"Nafeesa lafiyar ki kuwa?"

A zafafe na ce "Ni dai dan Allah lafiya ta lau, kawai don na kira ta na faɗa mata damuwata sai ta hau yaɗani? Shikenan mace ba zata yi kuka gidan miji ba? Ni wallahi bani son rashin sirri, ko da ya ke laifine da na faɗa mata.. "

Cike da mamaki ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login