Showing 3001 words to 6000 words out of 83936 words

Chapter 2 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1696

ni ne Nafeesa?"

A hankali na girgiza kai ina toshe bakina.

"Kalle ni..! Ya furta cikin wata irin narkakkar murya.

Babu musu na juyo ina fuskantar shi, ya tsura min ido na ɗan lokaci kafin yw furzar da isa mai zafi daga bakin shi yana faɗin "Kina tunanin wannan abin zai datse mafarkin mu? Kina tunanin wannan abin ya isa ya zama hujjar da zamu raba zuciyoyin mu?"

Na girgiza kai a hankali ina hawaye.

"Nafeesa, bana jin aƙwai wani abu da zai datse alaƙata dake, ina son ki a duk yadda kike, kuma zamu rayu a tare insha Allahu, dan Allah ki daina kukan nan, kina karyar min da zuciya, kukan ki ya fi ɗaga min hankali a yanzu, kin san yadda muke ƙaunar juna, yanzu ne ya kamata mu nunawa juna zamu iya mutuwa a domin juna."

Lallashina ya gaba da yi, yayin da na samu ƙwarin guiwa daga gare shi, na tabbatar Sufyan masoyi ne na gaske, kuma ya kafa min hujjojin da zan rayu tare dashi har abada, yayin da muka ɗauki alƙawarin ƙare rayuwa a tare, sannan mu fuskanci duk abinda zai mana togiya da juna.

**********************

"Baba dan Allah ku barmu mu auri juna, ina son shi haka shima, mun shirya fuskantar rayuwa a duk yadda ta zo mana."

Bai ce min komai ba ya fice daga ɗakin, yayin da na kifa kaina jikin gado ina kuka kamar raina zai fita, ko da ya ke yadda nike ji a raina, gwara fitar ran da rabu wa da Sufyan, haka suka fice suka barni a ɗakin ni ɗaya.

How could i make them to understand my life without Sufyan is miserable? Da alamu kukana ba zai gamsar da su ba, na haɗiyi busassahen yawu tare da goge ƙwallan da suka ɓata min fuska, na miƙe jiri na ɗibata na fito daga ɗakin babu ko kallabi ina tangaɗi kamar ƴar maye, ganin na yi hanyar fita waje ya sa Aunty Haula ƙanwar Baba ta tare ni tana tambaya "Ina zaki fita haka Nafee?"

"Zan tafi in tari mota ta bige ni Aunty, rayuwa bata da amfani muddun ba'a barni na auri wanda ni ke so ba, Aunty Haula me yasa su baba ba zasu fahimci abinda muke ji ba? Anya sun san soyayya kuwa? Sun san irin ƙyaƙyƙyawar rayuwar da mukayi shirin ginawa da Sufyan? Dan Allah ki saka baki kar a fasa auren nan, Aunty shekarata ashirin da baƙwai ina gida, idan har na yadda Sufyan ya suɓuce min na shiga uku na lalace."

"Nafee Allah zai kawo maki wanda ya fishi, duk wannan abin anyi ne domin samawa ɗiyanku rayuwa mai albarka, idan kuka yi aure a haka bayan kun san makomar ɗiyan ku, to wallahi a ƙarshe sai kun tsani juna fiye da soyayyar ku."

"Aunty Haula Allah na iya canza tsari duk yadda ya so, babu wanda ke ta tabbacin lallai sai mum haifi ɗiya Sickler, Aunty Haula ko da zamu haifi sickler ɗin mun amince, zamu jure mu raine su kamar kowanne ɗa."

Muryar Ummi na ji a bayana tana faɗin "Ku barta ta tafi dan ubanta."



*UWAR SUKUM.*
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK.

*HASKE WRITER'S ASSO.*


*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm

  _Wannan littafin gaba ɗaya sadaukarwa ne ga NAFEESA MUHAMMAD SULE Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._


*003*


Duk yadda iyayen mu suka so, mu fahimci halin da zamu jefa ƴaƴan mu da rayuwar mu anan gaba, amma mun ƙi fahimta domin a daren ranar Sufyan a ƙofar gidan mu ya ƙwana, kuma tunda asuba ya tare baba da magiya, duk da jama'ar da ke cikin gidan.

Ni kam wallahi na yi suma ya fi goma, domin gwaggunaye na a kaina suka ƙwana, wasu ma sun ɗauka bazan kai washe gari ba, sabida yadda suke iya hango bugun zuciyata, ga karkarwa da jikina ya ɗauka, ina fidda fararen ruwa daga bakina, bakina ya yi fari tas, tun Mama na ganin abun a iya shege har jikinta ya fara sanyi, ga bakin mutane da kowa ke tofa albarkacin bakin shi, wanda mafi yawanci sun goyi a barmu muyi auren tunda risk ɗin bai kai na AS da SS ba, ko ba komai ana sa ran mu haifi lafiyayyu, sannan daga ni har Sufyan ƴan boko ne mun san yadda zamuyi managing rayuwar mu.

Ganin abin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa ya sa aka ce ya kira waliyan shi, nima aka zauna da nawa da mu duk biyu, suka bamu baki, tare da shawarar mu yi haƙuri da juna Allah zai musanya mana mafi alheri, amma ina mun ƙwaɗaitu da son mallakar juna, wallahi ba zamu iya haƙura da juna ba, domin ni da Sufyan tamkar hanta da jini ne, ina da tabbacin an hallicine da haƙarƙarin shi, babu ta yadda zan iya rayuwa ba tare da shi ba, in gaya maku idonmu muka murje babu kunya muna roƙon a barmu mu rayu, don wallahi tashin hankalin da Sufyan ya ke ciki ya ma fi nawa, don shi har kusan sujada yake masu, sai da aka dakatar dashi, kuka kam kamar ƙaramin yaro, yana faɗin "Baba dan Allah kar ka hana min auren Nafeesa, wallahi idan har ban same ta ba, ba zan iya rayuwa ba, ko na rayu banda banbanci da katako, bazan iya rabuwa da ita ba har abada, dan Allah ka barni da ita, zan ɗauki responsibility na komai zai biyo baya, bana fata, amma ko da abunda kuke gudu ya faru, haka dama Allah ya ƙaddara, zamu zauna mu raini ɗiyan mu a tare ba tare da gajiyawa ba, dan Allah ku bar mu muna son juna, we are ready to sacrifice any thing for each other."

Tashin hankali fa, ƴan biki suka yi ta jimami tare da mamakin soyayyar da mukewa juna, a ƙarshe dai aka aminta za'a ɗaura mana aure amma duk abinda ya biyo baya mu kuka da kan mu, muka ce mun yadda, kuma insha Allahu babu abinda zai biyo baya, kai koma ya biyo zamu haɗe hannu mu fuskance shi ba tare da gajiyawa ba.

Wannan ƴar matsalar ce ta ɓata mana duk wani shiri da muka daɗe muna yi na bikin mu, ba kamu ba dinner, kai ba ba ɗin ta yi yawa, haka nan aka cigaba da shagali.

Ƙarfe 11am aka ɗaura auren NAFEESA da SUFYAN, auren da ya kafa tarihin da ba'a taɓa samu ba a unguwar mu, soyayyar mu ta shiga zukatan jama'a da yawa, har wasu da aka fasa auren su sabida genotype suka fahimci dama can ba son juna suke ba, yaudarar kawunan su suke, ganin yadda muka jajirce muka yaƙe shi, mu kam farin ciki gare mu ba'a magana, don ni sai daga baya ma na soma jin kunyar mutanen gidan, idan na tuna yadda na riƙa burgima ina soma duk akan ɗan namiji, don ina jin lokacin da wata innata ke faɗar wai Allah ya sa kar ya min irin halin su.

Wajen la'asar ina zaune Fannata na ɗaura min ƙallabi wayata ta hau vibrating, da ya ke sam bana iya saka ringing a waya, gani nake ƙarar zata zama takura ga na kusa da ni, lallausan murmushi na saki ganin Rabin rai ke kirana,domin tunda aka ɗaura auren na canza mishi suna zuwa rabin rai, kun ga idan shima rabin rai ya saka min a wayar shi kamar yadda na sa, idan aka haɗa da nawa ya zama cikakken rai ɗaya, na lumshe ido, na ɗauki kiran tare da kangawa a kunne ina murmushi sai ka ce wacce aka ma albishir da gidan aljanna.

"SUFNAH.! Ya faɗa cike da annashuwa.

"Sufnah?" Na maimaita domin ban san inda aka samu sunan ba.

Daga muryar shi zaka fahimci tsantsar farin cikin da ya ke ciki ya ce "Yes, we become one, sunan ma dole ya haɗe, ko sai na ce Mrs Sufyan zaki fi fahimta?"

Na lumshe ido, sai yanzu na fahimci sunana da nashi ne ya haɗe, a raina na maimaita sunan domin ba ƙaramin daɗi ya mini ba, a fili kuma cikin halin ko in kula na tambaye shi "Wai har an ɗaura auren ne?"

"Au b ma ki sani ba?"

Kai tsaye na ce "Ina gida ya za'ayi in sani."

Ya ƙwashe da dariyar farinciki yana faɗin "Humm ba wani nan, yadda ki ka yi ma su Baba bori a jiya, Allah na tabbatar ba za'a ɗaura auren baki sani ba, may be kina lafe ƙofar gida har aka shafa fatiha, kina jin kamar ki rungumo ni."

Kunya ta lulluɓeni da na tuna yadda ni ke ihu haɗi da roƙan a barni na aure shi kuma a gaban sa, na zunɓuri baki kamar yana kallona, shine ma har na zama abun zolaya gare shi, lallai ma Sufyan.

Kafin in bashi amsa na tsinkaye shi "Dan Allah mama ki taimaka, i cant live without Sufyan, Allah ina son shi, wayyo na suma, zan mutu, mamar mu, Sufyan ɗina, ni nasan me nake gani a tattare da Sufyan." Ya faɗa yana noƙe murya irin ta wa yana dariya.

Kamar zan yi kuka na ce  "Kai ko?"

Ya ƙwashe da dariya "Ba'ayi ba? Yauwa Babyna, ni faɗa min me kika gani a gurina? Ai mun zama ɗaya ko?"

Na zunɓuri baki tare da yanke wayar na danƙwafar bisa mirror, ni wallahi ban ma san na ce haka ba, ɗan siririn tsaki na ja ina jin haushin kai na, lokaci guda kuma na ƙwashe da dariya kamar mahaukaciya ina kallon Fannata da ta zuba min ido tana murmushi, da alamu salon soyayyar mu na burge ta.

"Hey! Ya dai?" Na katse ta, ganin kallon ya ƙi ƙarewa.

Ta girgiza kai tana murmushi "Da yanzu kin yi asara babba."

"Why?"

Sai da lumshe ido sannan ta ce "Kin gan shi ɗazu Nafee? Hmm wallahi ba za ki taɓa samun gaye irin shi ba, kin ga madarar ƙyau? Ai ban taɓa sanin haka yake ba sai yau da ya sa wani arnen voile fari? Ya ilahi Nafee."

Na murmusa, ni kaina na san Sufyan ya haɗu, duk da ba dan ƙyau na aure shi ba, na sauke ajiyar zuciya na ce "Ke dai bari kawai Fannata, thank you for gwarin guiwa, Allah ke ma ya baki miji na gari soon."

"Ƙyaƙyƙyawa Nafee." Ta ƙarashe min.

Na ƙwashe da dariya "To nagari Ƙyaƙyƙyawa Fannata."

"Amin Nafee, yanzu ki kai full du'a'i."

Sai da ta gama ɗaura min kallabi sannan muka fita falon cikin friend ɗina ana maida yadda aka yi, inda suke faɗar wai sai ka aurar da ƙawa sai ta watsar da kai, ana ta dariyar wai ƙawar A'i ta yi aure, lokacin bikin A'in ta sha wahala da ita akai komai, amma wai ko ta kirata bayan bikin ta mata ya gajiya, shine da A'in ta ji shiru ta kira amaryar amma sai mijin ya ɗauka ya ce wai kar ta kuma kiran matar shi, shi yanzu duk ya rabata da su. Muka ƙwashe da dariya baki ɗaya, Biba na faɗin "Hala mai kuɗi ta aure?"

A'i ta ce "Wani iskanci ai sai malamin makaranta, ina mai kuɗi da lokacin wannan sakarcin? Ka ga mace da ƙawayenta shekara da shekaru lokaci guda ka raba su."

Muka ƙara ƙwashewa da dariya Fannata na tambayar "Amma kin rabu da ƴar is ko?"

A'i ta ce "Ai ku baku sani ba, da marece na wanki ƙafa na tafi gidan wai ni in nunawa ƙawata yadda na ji ba daɗi, ta tareni tana yatsina fuska, ban damu ba, sabida har da alkaki ya kaini, in gaya maku muka zauna a falo na fara karanta mata, ai ba'a haka, kar ta yadda miji ya rabata da ƙawayenta tun na yarinta, zai iya rabuwa da ita, ashe ƴar is mijin na ɗaka sheme yana saurarena, sai da na gama sannan ya fito da chajar waya, ban aune ba sai ji nayi ana lafta ta, na miƙe ina tambayar lafiya? Kai ɗan mutumin nan ya cigaba da tsula min wai zan hurewa matar shi kunne, in gaya maku da gudun masifa na bar gidan, in gaya maku shekaranjiya sai gata ƴar is gidan mu, take faɗa min wai ya sake ta, na ture kallabi gaba na ce Aiyo, zuwa tayi mu gaisa, shine na ce ta tashi ta tafi, ba zan yadda jawara ta huren kunne ba."

Mu duka muka ƙwashe da dariya ana tafawa, kun san yadda zama yake cikin friends, yayin da Biba ta ɗauka "Ki ce kin sha tsula, nima fa na taɓa zuwa gidan ƙawata, na iske mijin ya kawo masu taliya da kayan miya, na zaƙalƙale na yi ta masifa, ta ya taliya ɗaya zata ishe su har da yara biyu, kuma rana da daddare, ƴar is ashe mijin itama yana ɗaki ƙwance maimakon ta taɓoni sai ta bar ni, sai da na gama ina shirin fita sai gashi ya fito, nayi tsuru tsuru ya gifta mu, ɗan shegiya ya rufe mu ta baya ta ƙwaɗo ya kama gaban shi, ai in gaya maku bai dawo ba sai 12 dare, duk kiran da aka mishi ya ƙi ɗauka, ga gida sai kirana ake, na yi gwalo gwalo, kuma shegen da ya dawo ya ce idan na ci taliyar na tashi na bar mashi gida, haka na tattara takalma a hannu na falla da gudu, ga karnuka unguwa, kai da ƙyar dai na kai gida, ai gulma gidan mai aure ba ta yi ba, wallahi ƴan is basa faɗar maigida na nan ka yi ma bakin ka linzami, itama fa daga nan mijin ya ce kar ta kuma kula ni, dama ni ma na yanke haihata haihata."

Dariya sosai muke, wanda dama idan muka haɗu bama barin juna da ƙunci, childhood friends ne, duk da ƴan is ne basa ji, amma muna ƙaunar juna, Biba ta kalle ni ta ce "Ke ma Allah yasa kar dai ki yadda mu, kin san yanzu da an yi aure sai a watsar da ƙawayen gida, bare ke da zaki gidan daɗi.."

Na watsa mata harara "Rufan asiri dan Allah, Allah ya ƙyauta min."

"Amin."

Aunty Amina ta shigo da cup a hannun ta, zata ja ni ɗaki suka ɗauki ihun "Kayan mata ne! Muma ai matan ne."

Suka ɗauki dariya, ta girgiza kai "Allah ya shirya ku."

"Amin Aunty.."

Ta dube ni ta miƙo min "Ƙarba ki sha."

Na yatsina fuska "Menene?" Nima na sani sarai ba zai wuce kayan matan ba kamar yadda suka ce.

Illau ɗin su ne, domin kankana ne da madara da kanumfari da minannas da coconut aka markaɗe, babu musu na karɓa na shanye, yo tun fa kafin a bani na ke siye nake sha, ina jin tun saura 5month na fara da maganin sanyin ROYAL EQUISITE 0803 064 4073, shine na san babu ha'inci ga kuma inganci, sannan fa na riƙa siye wajen su a ɓoye ina sha, kuma wallahi ni kaina na ji a jikina, domin da an fasa auren nan da na shiga uku na lalace.

************************



*UWAR SUKUM 08036953516.*
[5/17, 8:18 PM] RN Feedohm: 💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK.




*HASKE WRITER'S ASSO.*


*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm


  _Wannan littafin gaba ɗaya sadaukarwa ne ga NAFEESA MUHAMMAD SULE Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._



*004*


Bayan kowa ya watse na samu damar ƙarewa gidan kallo, tabbas Sufyan yayi matuƙar ƙoƙari domin wallahi ƙaton gida ne na ji da gani, sannan ya zuba abubuwan more rayuwa a ciki da ƙyale ƙyale, sannan su ma iyayena sun mini ƙoƙari matuƙa sun fidda ni kunya, banda abinda zan ce masu sai Allah ya saka masu da gidan aljanna.

Ina zaune gefen gado Sufyan ya shigo, na yi saurin maida kai ƙasa tare da jan mayafi na rufe fuskata domin wata irin tsantsar kunyar shi nike ji, bare ma idan na tuna borin da nayi.

Kusa dani ya zauna yayin da sanyayyen ƙamshin turaren shi ya daki hancina, na lumshe ido, ya saka hannu a hankali ya ɗage mayafin da ya rufe mani fuska, ya zuba min ido kamar wanda bai taɓa gani ba, fuskar shi ɗauke lallausan murmushi.

Ganin kallon ya ƙi ƙarewa yasa na kasa haƙuri na ɗago na jefa mishi hararar ƙauna haɗe da zunɓurar baki na kauda kai gefe ɗaya ina kallon ƙasan tiles.

Murmushi ya yi mai sauti ya ja hancina yana faɗar "Tubarkallah masha Allahu, godiya ta tabbata ga ubangijin da ya hallaci wannan zankaɗeɗiyar yarinyar."

Ɗan murmushi na yi ina kallon ƙasa, ya saka lallausan hannun shi ya ɗago haɓata tare da sumbatar goshina yana faɗin "Tashi mu je ku gaisa da abokai na.'

Na maƙe ƙafaɗa alamun a'a, don har ga Allah bana sha'awar yadda abokan amarya da angwaye suke haɗuwa ai ta surutai na rashin aji da sunan siyen baki, shiyasa ma na kore su.

"Me yasa?" Ya tambaye ni idanun shi na kaina.

A shagwaɓe na ce "Ni dai bana son zuwa kunya nike ji."

"Ok to, bara na sallame su, nima dama bana buƙatar a kalle min ƴar mata." Ya kanne min ido ɗaya yana kallon gaban rigata da ya ɗan buɗe, ai kam nan da nan na ja na rufe ina hararar shi, yayin da ya saki murmushi ya shafi gefen fuskar shi ba tare da ya ce komai ba.

Daga haka ta fice yana waige na, mintuna kaɗan ya dawo yana dariya riƙe da leda a hannun shi yana faɗin "Kin san me suka cewa?"

Na girgiza kai ina kallon shi.

"Wai kin sa na kore su, don haka zasu sa na yo ƙari nan da 2month wacce...

Hararar da na dalla mashi yasa ya guntse bakin shi, domin ko da wasa bana ƙaunar maganar kishiya, sannan shi kan shi Sufyan ɗin ne ya ƙara ƙarfafa min guiwa, domin na sha jin yana faɗar ba zai iya rayuwa da mace biyu ba, shi fa idan za'a raba mace ɗaya ma a bashi rabi sai ya fi farin ciki.

"Sorry, ai kin san wasa ni ke ko?" Ya katse ni tare da kama kunnen shi ɗaya.

Ban ce komai ba, har ya zo ya zauna kusa dani ya na lallashi na wai na saki raina suma wasa suke, ta ya amarya sukutum zaa yadda ta ɓata ran ta, sai da ya ga ina murmushi sannan ya umurce ni in tsshi in yi alwala mu yi nafila, babu musu na miƙe da yake na san ana yi, yayin da ya bini da kallo yana murmushi, har na kusa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login