Showing 48001 words to 51000 words out of 83936 words

Chapter 17 - KUSKUREN SO Book Complete by Feedohm.txt

Feedoms   

21 Sep 2025

1698

yi miki dan Allah, daga magana sai ki mare ni? Ba ma zaki rungume ni ba ki taya ni jimamin an asirce min miji ya sake ni, kamar ba ke kika haife ni ba?"

Ta daka min gigitattar tsawa "Na fi kowa farin ciki da sakin da ya miki wallahi, sannan ki juya ki fice min daga ɗaki, idan na kuma jin kin sake min maganar sai na ci mutuncin ki, mutuniyar banza, sakara mara hankali, wallahi sai na yi maganin ki, dan ubanki kan ki farau miji?"

To me yayi zafi? Na tambayi kaina, yayin da hawaye ke ambaliya a fuskanta, sam ban ji daɗin kalaman Maama ba, ni fa ƴar ta ce? Kuma ta ke faɗin ta ji daɗin sakin da aka min, anya ta san darajar aure kuwa? Anya ta san girman saki? Wallahi da ace ba uwa ba ce, da yau na ƙwana ina mata addu'ar a sake ta ta ji yadda na ke ji, ko da ya ke ma zata fini jin zafi, don ni nasan mijina baa hayyacin shi ya sake ni ba.

"Fice tun kafin in ci mutuncin ki."

Daga inda Teemah ke ƙwance na ji tana "Sa Si So Su Se." Sam ban fahimci me ta ke nufi ba, sai dai harara da na danƙara mata cikin duhu, shegiyar yarinya daga yin aure na tana neman ta zama abokiyar gaba ta, kuma wallahi na san sai ta fi kowa jin daɗin wannan sakin, kuma tana zaune mijina zai zo ya ɗauke ni.

Jiki babu ƙwari na ja jikkar na fita, ban zame ko ina ba sai ɗakin mu, na zaro wayata na kunna, na tabbatar izuwa yanzu Sufyan ya kirani ya fi sau 100 ya ji a kashe, kuma zai bar mishi message na ban haƙuri, mamaki ya kashe ni ganin har tsawon lokaci babu message ko ɗaya da ya shigo wayata, na shiga gurin message ɗin da tunanin idan har bai turo ba, to tabbas ba ƙaramin baƙin asiri aka mishi ba.

Ilau bai turo ba, hankalina ya ƙara tashi, na miƙe zunbur na ɗauro alwala, don wallahi zama bai ganni ba, dole in roƙi Allah sannan na nemi magani.

******************

Tun da na yi asuba ban koma ba, idona ƙuri ga wayata, wajen 6:30am na gama shiryawa na zunbula hijabi na fito, don na gama yankewa ba zan iya jiran har Maama ta huce nan da gobe ba, ƙara kawai in je ga Fannata idan aƙwai wanda ta sani mai karya asiri ta min hanyar shi.

Da ya ke ana makaranta, suna tsakar gida ita da Teemah suna ƙoƙarin sheƙa ƙunu, kallo ɗaya ta min ta ɗauke kai, ko a tunanin ta zan shiga bayi ne, na zunɓuri baki ciki ciki na ce "Ina ƙwana."

Bata amsa ni ba, nima kuma ban damu ba, na murguɗa baki na ce "Ni na tafi."

Ta yi watsi da ni, har sai da ta ga da gaske ni ke gidan zan bari sannan ta miƙe tsam ta daka min tsawa ta hanyar tambayar "Gidan uban wa za ki je?"

"Gidan su Fannata mana."

Kafin ta bani amsa Teemah ta amshe da "To ko iya darajar auren kaɗai Yaya ta sani? Bata san idan miji ya ɗanƙara maka Sa Si So Su Se baa fita ko ina ba sai an gama idda...."



#UWAR SUKUM.
[5/25, 8:49 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*

   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm


  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._


*029*



Auta ya ƙwashe da dariya yana tambayar Teemah "Yaya Fati menene Sa Si So Su Se.?"

"Abunda ake ma masu aure su koma ƙananan jawarawa..."

Mamata ta tamke Fuska tana hararar ta, ni kam a lokacin na gama ƙuluwa, ko ba a faɗa ba nasan Teemah na cikin masu farin ciki da wannan sakin, kuma wallahi babu mai laifi sai Baaba da mata, don ni fa banga ma dalilin da zai sa a faɗa mata ba an sake ni ba, idan suna da sirri don Allah ba sai su ce hutu na zo yi ba in koma? Amma da yake shegen ɗumi ne da su, har ita ƙanwata ta san an sake ni.

"Koma ciki." Na ji umarnin Mamaa.

Na juyar da kai gefe ɗaya na ce "Yanzu fa zan dawo, kuma ai ba wani guri na ce zan je ba, gidan su Fannata ne."

"Wallahi idan ƙafar ki ta fita daga gidan nan sai na ci mutuncin ki fiye da zaton ki." Ta cigaba da aikin ta.

Kuka ya taho min na ce "To idan ba zaki barni na je ba, dan Allah ke ki je ki ji ko aƙwai inda ake karya sihiri, wallahi ni da mijina muna son juna."

Teemah ta amshe "Ashsha Ja Ji Jo Ju Je."

Maimakon Mamaa ta gaura mata mari sai ta yi kamar ba ta ji ta ba, ta maka min harara tana faɗin "Idan bai sake ki ba ai bai ƙyauta min ba, ina amfanin zama da sakara? Wato uwar shi ta ce ya rabu da ke, shine kike tunanin yadda ke baki ji maganar ta ki iyayen ba, shima kar ya ji ta su? To ai ba kowa bane sakarai irin ki ba."

Na kalle ta a hasale na ce "Wallahi tallahi asiri ne."

"Na Ni No Nu Ne." Auta ya faɗa kamar yadda ya ji Teemah na yi.

Ban san lokacin da na rufe shi da duka ba ina faɗin "Ni zaku maida ƴar iska mahaukaciya, wallahi ba ku isa ba, sai in illa ta ka." Da ya ke shi zai bugu, amma Teemah ba zata bugu ba, don ina tuna ɗan iskan dukan da na sha gurin ta, abin daɗi Mamaa bata min maganar na daina dukan shi ba, har sai da na mishi lis shima Baaba ya fito ya tambayi "Me ya maki."

A hasale na ce "Iskanci."

Teemah ta kalle ni da sauri, na maka mata harara na nunata da yatsa "Hadda waccen dan ubanda ya haife ta."

Ya girgiza kai tare da bina da kallo yana faɗin "Allah ya sawaƙe."

Na amsa da "Amin." Sannan na tausasa murya ina faɗin "In shigo mu yi maganar yanzu.?

Bai ce da ni komai ba, ya shige toilet ɗin waje, na koma bakin ɗaki na zauna tare da rafka tagumi.

*************

Abu kamar wasa na tun ina jiran Sufyan ya kira ni, har na soma kiran wayar kamar mahaukaciya, yayin da duk lokacin da zan kira sai dai na ji wai the number you have try to call does not exist, please check the number and try again.

Hankali ya yi masifar tashi, gashi daga Maama har Baban babu wanda ya kira ni akan maganar Sufyan hasalima neman maida ni ƙaramar bazawara suke, sauƙin ma ciki ne da ni, kuma ba zan fita idda ba har sai ranar da na haihu, a lokacin na shiga tashin hankali duk na fige na fita hayyacina.

Yau kam tunda safe na nufi ɗakin Babaa na samu ma ya koma bacci bai kai ga farkawa ba,wato ni ina ƙwana ido biyu amma su har wani baccin safe suke, na ja siririn tsaki, bana jin zan iya haƙurin jiran shi har ya fito, don haka ƙarasa uwar ɗakar kaina a tsaye, sai dai daga bakin ƙofar na ja burki, ganin Maama da Babaa ƙwance suna bacci a jikin juna.

Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, har ya tayar da su firgigi, yayin da Baaba ya daka min gigitattar tsawa yana tambayar "Baƙi da hankali ne? Me ya kawo ki nan babu sallama? Fita ki bani guri tun kafin in saɓa miki..

Cikin kuka na ce" Dole ka ce in fita mana, kai kana tare da matar ka ni ga banza, yau ƙwana hudu da dawowa ta gida babu wanda ya kira mijina bare ya ji ya akai, babu wanda ya fara shirin neman karya sihiri da aka mishi bare har na koma gidana. "

Kamar ruwa ya ɗauke su haka suka zuba min ido suna kallona daga bisa gadon da suke ƙwance, yayin da na dafe ƙofar ɗakin da hannu ɗaya na cigaba da faɗin" To wallahi na gaji, muddun ba zaku nemi Sufyan ba, ku mishi magani ni zan fita na neme shi da kaina babu ruwana da wata idda, don ban saku ba, babu kuma ubanda ya isa ya ce na saku, ina ji ina gani ba zan yadda ku taimaka gurin lalacewar aure na ba, Alhalin ku shekarar ku nawa da auren ku.?

Ban yi aune ba sai jin saukar ƙarfen labule na yi a bayana, na zabura ina kallon Maama da ranta ya gama masifa ɓaci, kafin na tambayi baasin bugun na ji ta rufe ni baki ɗaya, ta shiga narka min dukkan ta ko'ina a jiki sai ka ce ta samu jaka.

Zafi ya sa na hau ihu ina faɗin "Dan Allah ki yi haƙuri, amma wallahi ina son Sufyan ku kira shi ku nemar mashi magani na koma gidana."

"Ke ce ke buƙatar magani ba shi ba. "

Baaba ya riƙe ta gam yana faɗin "Bar dukan ta haka, baki ganin juna biyu ne tare da ita."

"Dan Allah ka barni nayi mata magani yanzu,duk wani iskancin ta ganin ana ƙyale ta ne."

Sai da yayi da gaske tukun Maama ta rabu da ni, ta fice daga ɗakin da ƴan ƙananan ƙwalla a idon ta, yayin da ta barni durƙushe bakin ƙofar.

"Nafeesa. " Ya ƙwala min kira bayan ya koma falon shi ya zauna.

Na taso jikina babu ƙwari na zube gaban shi ina kuka mai cike da ƙunar zuci, abu goma da ashirin ya haɗe min, sai yau na tabbatar da ana zaɓen ƴa ƴa, tunda gashi Maama ta zaɓi sauran ƴaƴan ta a kaina.

"Shin gidan Sufyan kike son komawa.?"

Na shiga kai "Ba a hayyacin shi ya sake ni ba, asiri aka mishi, wallahi ina son mijina Baaba, ina son shi kamar yadda kake son matar ka."

"Tashi ki tafi." Ya nuna min ƙofa.

"Ina zan tafi bayan ba ka kira shi ka fara cuku cukun neman mashi maganin asiri ba.."

Kai tsaye ya ce "Sabida na lura baki da hankali, kin fi buƙatar maganin fiye da Sufyan ɗin, kuma ki sani ba zan nemi Sufyan domin ya maida ki ba, idan kina buƙatar komawa gare shi, ki neme shi da kan ki.."

"Ai wayar shi ma an asirce ta." Na faɗa cikin rawar murya.

"Tashi ki bani guri."

"Zan iya zuwa gidan shi? Na san yanzu ya dawo, ina da addu'o'in da zan karanta mishi."

Bai ce min komai ba, ya tsallake ni ya fita, da alamun shima rashi ya yi matuƙar ɓaci.

Tsawon minti ashirin ban fito ba, har sai da na ji Teemah na faɗin "Da Di Do Du De, Sa Si So Su Se." Sannan na yi tsalle na fito ina auna mata zagi, da ya ke Maama ta hanata kulani bata ce min komai ba, sai ta cigaba da iya shegen ta, da ke masifar ƙona min rai.

**************

Abu kamar wasa sai na yi wata biyu babu Sufyan babu dalilin shi, babu kira babu saƙo, na fige na lalace na yi baƙi, ga shi ba wani ɗaɗin zaman gidan na ke ji ba, don wallahi Maama ko kulani bata yi, haka Teemah ma, idan ka ji ina magana da wani to Auta ne, shima sama sama.

Wani salon iskancin da Teemah ta ɗauka shine maƙe murya tana min ɗan kira "Ja Ji Jo Ju Je, Jawaris..."

Yau kam zuwan Fannata ne ma ya sa na ji sauƙi a raina, cike da tausayin halin da ni ke ciki ta ce "Dan Allah ki ƙwantar da hankalin, idan Sufyan alheri ne da kan shi zai dawo gare ki.

"Alheri ne Fannata, kawai dai sun juyar mashi da hankali."

"Babu fa wani asiri Nafeesa, idan iskancin namiji ya motsa bai da maraba da shaiɗan, wannan fa mutumin idan yana son ki ya san inda kike, kuma ba zai ɗauki tsawon lokaci bai zo ba."

Na watsa mata harara "Allah ya haɗa ki da shaiɗan Fannata, da kike maganar zuwa, ta ya zai zo bayan asirin da suka mishi bai kare ba.?

Ta taɓe baki tana faɗin "Allah ya baki haƙuri."

"Ameen."

Muka ɗan yi shiru na ƴan mintina, kafin na ƙwantar da murya na ce "Ya maganar maganin da na miki.?

"Kin san dai ban ga ana zuwa gun malamai ba a gidajen mu ko.?

"Ai ba asiri na ce ba." Na zuba mata ido ina kallon ta, amma sai ta ɗauke kai, don haka na cigaba da faɗin "Mu bar maganar, dan Allah ki taimaka ki je ki gano min ko lafiya ya ke, ni wallahi gani na ke ma kamar ciwon zuciyar shi ya motsa."

"Ai kam wallahi babu gidan ubanda zan je."

Na buɗe baki da niyyar yi mata magana na ji sautin kirana, sautin da mutun ɗaya kaɗai ya mallake shi a, wayata, kamar wacce aka fizga na yi gun wayar idona da baki na a buɗe, ina jin yadda zuciyata ke bugawa fat fat fat......


#UWAR SUKUM.
[5/31, 8:22 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*

FREE BOOK

*HASKE WRITER'S ASSO.*

   *FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm

  _Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._

_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._

*030*

Jikina ya soma rawa, yayin da hawaye ya fara sunturi a saman fuskata, hawayen farin cikin da na shafe wata biyu da ƙwanaki ba tare da sun fito daga idona ba, tsabar farin ciki ya saka na kasa ɗaukar wayar har sai da kiran ya katse, yayin da na ɗaura hannuna bisa baki na gudun kar na kurma ihun da zai janyo hankalin ƴan bakin cikina..

"Sufyan Fannata, Sufyan ne ya kira ni." Na faɗa cikin rawar murya har lokaci hawayen farin ciki bai daina fita daga idona ba, wallahi sai na ke jin tamkar an zunduma ni aljanna.

Ta taɓe baki tana faɗin "To sai me? Shine kike wannan rawar jikin sai ka ce wata tsiya ce a kiran na ki?"

Na zaro ido cike da mamaki ina tambayar "Bangane ba?"

"Eh, abin jin daɗi ne don ya kira ki bayan shafe wata biyu bai neme ki ba?"

Na girgiza kai tare da cije laɓɓana ina ƙoƙarin danne abinda na yi niyyar faɗa mata, kafin na bata amsa kiran na shi ya sake shigowa, na wani ja numfashi na sauke ina godiya ga Allah da ya karya asirin ba tare da taimakon wasu ba, na ɗauke hawayen da suka sake zubo min da babban yatsana, sannan na kanga wayar a kunne yayin da bugun zuciyata ya ƙaru linkin ba linkin.

Cikin muryar shi da ke ƙara rikita ni, da rura wutar ƙaunar shi a zuciyata ya kira sunana "Nafeesa....."

Na fashe da kuka mai ƙarfi hannuna na rawa, wata biyu fa kenan cikin ƙunci da kewar abinda zuciyata ke so, sai na ke jin tamkar na yi shekara dubu biyu ba tare da shi ba.

"Ko na kashe wayar idan kin gama kukan sai na ke kira..." Ya furta a kasalance.

Na hau girgiza kai, ni kaina na san yadda kuka na ke ɗaga mishi hankali, don ya sha faɗa min ƙara a ɗiga mishi dalma da ya ji sautin kukana.

Cikin shashshekar kuka na ce "Idan ban kuka ba me kake so na yi Sufyan? Sakina fa aka sa ka yi, sannan baka neme ni ba tsawon wata biyu, kullun cikin tsumayen ka nake, ina jiranka, babu kai Sufyan, idan na kira wayar ka baya shiga, na shiga tashin hankali, na shiga ƙunci, ya zan yi......

Kai tsaye ya ce" Duka laifin ki ne Nafeesa.."

"Laifina?"

Ya jijjiga kai, da alamu shima yana jin radaɗi fiye da ni, don wallahi ko ban ganshi ba, na san ba ƙaramar rama da baƙi ya yi ba.

"Me na yi?" Na furta jikina na rawa, don da alamu har yanzu asirin su na tasiri akan mijina

Ban yi tsammani ba sai tsinkayar shi na yi yana tambayar  "Me yasa ba ki kira mahaifiyata ba kin bata haƙuri akan abinda ya faru Nafeesa?

Kamar wacce ruwa ya cinye haka na yi difff da wayar a kunnena hannuna na rawa, Lallai sai yanzu na ƙara tabbatar da asiri aka na Sufyan wallahi, wai ni ce zan kira uwar shi na bata haƙuri? To wai ma uban me na mata?

"Wannan shine son da kike min Nafeesa? Shine alƙawarin da kika min zamu rayu mu mutu a tare? Shin baƙya tunanin halin da zan shiga idan  na rasa ki? Ba ki taɓa tunanin daga ribs ɗina aka halicce ki ba? Ba ki yi tunanin idan babu ke ba zan iya rayuwa ba? Why Nafeesa, me yasa kike azabtar da mu.?

Cikin rawar murya na kira sunan shi "Sufyan....

Ya katse ni "Bana son jin komai daga bakin ki Nafeesata, almost 2 month baƙya tare da ni, amma ba kiyi tunanin gyara kuskuren ki ba, am highly disapppointed on you wallahi, ki sani idan na mutu ke ce kika kashe ni..."

Ƙitt ya yanke wayar shi, hankali ya ƙara masifar tashi fiye da wanda ni ke ciki, mutuwa fa? Sufyan? Lallai na tafka KUSKURE, sai heart attack ɗin da ya samu lokacin da na dawo gida ya dawo min, zuciyata ta buga da ƙarfin tsiya, a ruɗe na cigaba da bin wayar da kira kamar mahaukaciya, amma sai aka ce mun wai sam sam number ma baa daidai ta ke ba, na yi check na gyara na sake kira.

Na fashe da mahaukacin kuka, tare da kifa kaina bisa cinyar Fannata ina faɗin "Na shiga uku na lalace Fannata, Na shiga uku, Wayyo Allah, na bani, ban ga amfanin rayuwata ba muddun babu Sufyan, Na bani na lalace." Na hau jujjuya kaina tare da kifewa na yi goho.

Cikin tashin hankali ta ke tambayar "Me ya faru Nafeesa? Ya ƙarasa sakin ki ne.?"

Na ɗago a firgice, wato har kullun Fannata fatan saki ta ke min, wato yadda ba ta yi aure ba, nima so ta ke na dawo na zauna muna yawo a gari, saki ɗayan bai ishe ta ba, uku ta ke so a min baki ɗaya, wallahi da ace ba ita ba ce, da yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login