Showing 60001 words to 63000 words out of 83936 words
da ganina, sai na ga duk sun ja baya suna min wani irin kallo.
Maama ta daure da ƙyar da alamun mamaki a tattare da ita ta kira sunana "Nafeesa."
Na zunɓuri baki na ce "Naam.!" Irin dai yadda ake amsa rigista a islamiyya.
"Dama kina nan?"
Ban damu da yanayin da take ciki ba, kai tsaye na ce "Eh daga can gidan mijina na dawo, na san dai idan na koma gida bai zama dole ku barni na komo on time ba, kuna ma iya cewa sai ya zo da kan shi, kuma sai na ga ai ni naje da ƙafata, idan na dawo da ƙafata ba wani abu bane."
Ta haɗiyi yawu da ƙyar sannan ta ce "Amma da kin kira kun sanar mana ko."
Rai a ɓace na ce "To dan Allah da zan fita barina ku ka yi ne? Da idan na dawo sai na biya faɗa maku Mama? Daga ke fa har mijin ki zagina kuka riƙa yi, kuna neman hanani hanyar gyaro aure na, Alhalin ku zaune kuke lafiya lau, tunda kika haife ni ban taɓa ganin kin je gidan ku da sunan yaji ba, ba dai zaa ce bai taɓa miki laifi ba, amma ko bari mu sani baƙwa yi, sai ni banza don sau ɗaya na nuna an sake ni, shine kuke son kashe mun auren baki ɗaya, to ya mai da ni. "
Ta girgiza kai ta ce "Allah ya ƙyauta, mu je Fatima."
Teemah ina jin takaici ya hanata magana, sai wani huci ta ke sai ka ce mai shirin dambe, na san da gidan ubanta ne da yanzu ta ce zata kai mun hannu ko ta zage ni, amma da ya ke ta ga mijina a bayana munafukar sai ta yi shiru, don in toƙalota Sufyan ya laƙada mata dukkan tsiya sai cewa na yi "Ke kuma shegiya baki da abin faɗa ne kike ta mazurai kamar mayya.?
Maama ta kalle ta sai ta ƙi cewa komai, ina jin Sufyan na faɗin "Sweetie baki da kirki.."
Na zunɓuri baki na ce "Maama ga kuɗin wayar Baaba da kuɗin ku da a ranta sun samu, darajar fa aure kenan."
Ba dai ta kula ni ba, ta wuce, na bita da "Dan Allah idan kin ji ba daɗi ki yafe min."
Sufyan ya fizgo ni ya rufe gidan, yayin da yayi sama da ni yana faɗin "Sweetie an yi hankali."
"Amma duk da haka ban wuce ka maido Asiya ba." Na sake mishi maganar da tuni ta ke ci ni sabida in zunguri ruwan cikin shi in ji zai maido tan ko aa.
Ya ƙwashe da dariya "Maama fa ke so." Ya bani amsa kai tsaye.
"Kuma zaka maido da ita?"
"Idan ta ce a maido ta yadda zan yi ne Nafeesa.?
Na zuba mishi ido rai a ɓace ina faɗin "Sai ka maido ta? Ina alƙawarin da ka min?"
"Sabida na cika miki alƙawarin ki sai na ƙi bin umarnin mahaifiyata? Ko kin mance ita ta raine ni sannan kika ganni da haƙorana 32?" yadda ya yi maganar babu alamun wasa, sannan bai bani damar sake tofa albarkacin baki na ba, domin ya yi masifar tamke fuskar sa, sai ka ce bai taɓa dariya ba.
Sai na ji ya goge min hadda, yayin da na ƙara yadda da asirin su gaskiya ne wallahi, kuma dole in je gun Maaman Fannata ta taimaka min.
Tunanin mun yi faɗa da ƴarta ya faɗo min, na taɓe baki, yo ni ina ruwana? Ai ba da ita na yi faɗan ba, da Fannata na yi, kuma bata isa ta hanani zuwa gun uwar ta ba, don ba gidah ta bane, ta bari idan ta yi aure a aljanna sai ta hana, don na san a duniya bata da rabon aure, ni fa wallahi idan na yi faɗa da mutum dan uban shi ko abin hannun shi ya bani idan ina buƙata sai na ci, don ba da abin na yi faɗa ba.
Da safe na ce ma Sufyan zan je ANC, kuma fa ƙarya ni ke, so nike na je gun Maman Fannata na ji ta inda zamu ɓullowa al'amarin.
"Mu je tare." Ya faɗa tare da rungumo ni jikin shi.
Na shagwaɓe fuska na ce "Mata da sun fi 50, baa barin maza su shiga."
"Ok to."
Ya ciro 10k ya bani, na shirya ya aje ni asibitin sannan ya wuce aikin shi, yana aje ni na hau machine sai gidan su Fannata, wai shashashar yarinyar tana ganina sai ta ɗaure, ko ta ɗauka haƙuri na zo bata ne oho, nima kam na ɗaure tawa fuskar na hau hura hanci ina buɗewa.
Ganin ina niyyar shiga ɗakin Maman su ya sa ta sha gabana tana tambayar "Me ya kawo ki gidah mu.?"
Sabida tsabar ƙarfin hali sai na ce "Ai gidan ku kika ce ba gidan ki ba, ki bari idan kin yi na ki gidan na je sai ki mun wannan tambayar, yanzu ɓangaren Maama na zo."
Ta girgiza kai cike da takaici ta ce "Bikki da kunya Nafeesa, wallahi bikki da kunya."
"Sai ki samman ta ki."
"Fita, tun kafin na ci mutuncin ki wallahi."
Maaman su ta fito da sauri tare da taka mata birki "Ke Fannata bana son rashin wayau.."
Ta fashe da kuka tana faɗin "Maama uban me ta zo yi gidan mu, bayan ta gama kirana da baƙar ƙaddara."
Na ja tsaki ina faɗin "To ƙarya na yi? Kuma sauƙin ma gurin ki na zo ba."
Maman su ta kalle ni da sauri sannan ta nunawa Fannata ɗaki tare da daka mata tsawa "Wuce tun kafin na ɓata miki rai." Fannata ta wuce tana kuka ƙasa ƙasa.
Ni kam na taɓe baki na yi ƙasa da kai na ce "Maama ina ƙwana."
"Lafiya lau Alhamdulillahi Nafeesa, ina kika shiga jiya ake ta neman ki Nafeesa, kun tayar da hankalin kowa?"
Kai tsaye na ce "Wallahi gidan mijina na koma Maama."
"Madalla, amma ai da kin faɗa ko?"
Na riƙe haɓa "In faɗa su hanani su kashe mun aure, ƴar so na gaban su?"
"Bangane ba."
Na saki murmushin takaici ina faɗin "Hmm, wallahi basa son na koma gidan mijina Maama.".
"Subhanallahi, mu shiga ciki Nafeesa."
Na bi bayan ta a sanyaye, yayin da muka baje falo, na hau zayyana mata duk abubuwan da ke faruwa na asirin da aka ma Sufyan da sakin da ya min, da kuma mai do Asiya da uwar shi ke son yi, sai da na kai aya sannan ta saki ɗan siririn murmushi tana faɗin "Lallai kam an mishi asiri."
Sai na ji wani sanyi ya ratsa ni, ko ba komai na samu mutun ɗaya da ya yadda da maganata, na samu mutun ɗaya da ya yadda da asiri aka ma Sufyan ɗina, na murmusa ina kallon ta cike da shauƙi, da soyayya da ma ace ita ɗin ta haife ni, lokacin da ta miƙe ta shiga ɗaki, mintuna kaɗan sai gata da ƙaramin littafin addu'o'i ta zauna gabana ta ɗaura mun shi a cinya, sannan ta riƙo hannayena cikin nata, cikin ƙwantar da murya ta ce "Wannan kike buƙata Nafeesa, shine maganin duk wani asiri."
Na zuba mishi ido sannan na kafe ta da ido, shin uban wa ya faɗa mata ban san da shi ba.....
#UWAR SUKUM..
[6/7, 9:42 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*036*
Na zame hannun tare da ɗaukar littafin na hau jujjuya wa a hannuna, na buɗe jiki babu ƙwari raina a dagule, ayoyin alƙur'ani ne a ciki, kafin na ce wani abu ta cigaba da faɗin "Babu abinda ke saurin ƙaryar da asiri sama da ayoyin alƙur'ani, ki lazumce su Nafeesa."
Babu yabo ba fallasa na ce "Banda wannan fa?"
"Shi kaɗai gare ni, domin shi ke tattare da kowacce irin matsala.." Ta faɗa a sanyaye.
Na kafeta da ido "Babu wani ɗan malami da kika sani Maama?"
"Ga malamin ki a hannun ki Nafeesa me kuma kike buƙata." Ta Nuna littafin.
"Wanda zai karya asirin nan da nan." Na faɗa rai a dagule.
Ta murmusa "Shine dai wannan."
Duk yadda na so ta fahimce ni ƙi ta yi, ta dage lallai na riƙe wannan littafin addu'o'in, ni kuma Allah ya sani sam ba haka nake nufi ba, so na ke ta kaini gun malamin da zai karya mashi asiri nan da nan, idan da hali nima a mallake mun shi, na girgiza kai ina binta da ido, wallahi da fari kamar mutuniyar arziƙi mai son cigabana, amma yanzu kam kamar ba haka ba, na dai sani wallahi bata isa ta ce bata zuwa gun malami ba, sabida na ga yadda suke juya mazajen su da Maman mu, kawai dai babu wanda zai min hanya ne..
Na miƙe bayan ta ƙara jaddada mun maganar ta, na dungure mata littafin ta a cinya ina faɗin "Idan ba zaki taimaka min ba to ki je kawai." Na fice a fusace.
"Nafeesa.." Ta ƙwala min kira.
Yo uban me zan Mata? Na ja dogon tsaki, insha Allahu ni da su haihata haihata.
A ƙofar gidan na tsaya cak ganin mota hilux a ƙofar gidan, da wata irin wargajejiyar mota gefe ɗaya, ana ƙoƙarin sauko da uwayen kayan da ke bayan motar, na kasa haƙuri, na matsa kusa da wani ɗan saurayi da na gani gefe ɗaya ina tambayar "Nan gidan ne kuma?" don fa kayan su min kama da na lefe.
Ya kalle ni sheƙeƙe ya ce "Ba nan ba ne gidan su Fannata?"
Nq gyaɗa kai da sauri ina faɗin "Eh ya akai.?"
"Kayan sa ranar ta ne muka kawo, ke wacece.?"
Gabana yayi masifar faɗuwa, kayan sa ranar Fannata kuma? Fannata fa? Kuma a hilux? Cike haka? Na hau girgiza kai, sannan na ƙara zunguro shi na ce "Fannata baƙa fa?"
Ya maka min harara, ya cigaba da abinda ya ke, ni kam wallahi mamaki ya cika ni, wai kayan Fannata fa ya ce? To yaushe ne ta samu mijin da har aka sa rana? Hmm sai yanzu ma na fahimci komai, wato ita zata yi aure ni banza ta ke so na kashe nawa, na ja ƙafa na soma tafiya da tarin abubuwa bila adadin a zuciyata.
Bayan na koma gida na soma kiciniyar dafa abinci, sai na ke jin jikin nawa sam babu ƙwari, da ƙyar na dafa mana jallop rice da wake, na yi wanka na tsantsara ƙwalliya sannan na koma falo na hakince yayin da tunanin Fannata ya addabi rayuwata, ba wai ina mata baƙin ciki ba ne, aa ina mamakin tarin kayan sa ranar da aka kawo mata, shi kam wannan wane irin kuɗi ne dashi haka? Allah dai shi sa ba ƙarya ya mata ba, sam ban san Sufyan ya shigo ba, sai da ya hura mun sanyayyar iskar bakin shi yana tambayar "Tunanin me kike?"
Na murmusa tare da lumshe idanu na ce "Kai, ina da abin tunani da ya wuce Mijina?"
"Kamar gaske.." Ya lakace min hanci.
"Wallahi kuwa.."
"Na yadda." Ya zauna gefena tare da ɗaura hannun shi bisa kafaɗata ya saƙalo shi yana faɗin "Me kika dafa mana?"
Na yatsina fuska "Rice and beans."
"Ki ce zamu ci daɗi."
Na sani shine fave food ɗin shi, shiyasa ma na sa wake, na miƙe a sanyaye na jero mishi komai a ƙaton tray, na dawo ina faɗin "Kasan Fannata aure zata yi."
Ya taɓe baki "Ya fi mata wannan yawon gantalin gidajen ƙawaye
"Kuma fa mai kuɗi." Na ƙura mishi ido da spoon a hannuna.
Ya ƙwashe da dariya "Ita ta faɗa miki? Wai ma tukun ina kuka haɗu.?
Na maida idona ƙasa na ce "Wata ƙawarmu ce muka haɗu da ita asibiti shine take sanar mun."
"Ok.." Ya ja plate ɗin ya soma cin abincin shi hankali ƙwance yana bani a baki, wayar shi da ta yi ringing ya kai hannu cikin aljihu ya ɗauko yana satar kallo na, sai na ga ya miƙe ya shige bedroom yana faɗin "Cigaba da ci ina zuwa."
Nayi sukuti na bishi da kallon mamaki, wato don zai yi waya da uwar shi shine har sai ya shige bedroom, wannan wane irin sabon salon iskanci ne, sai na ji raina ya ɓaci, ina nan zaune zuciyata na azalzala yayin da gaba ɗaya hankalina na gare shi, kusan minti ashiri sannan ya dawo yana faɗin "Wai ba ki ci abincin ba?"
"Idan zaka yi waya da Umma har sai ka shiga bedroom." Na kasa haƙuri na tambaye shi.
Ya watsa min harara ba tare da ya ce min komai ba, sannan ya ja plate ɗin abincin shi ya cigaba da ci bai kuma kulani ba..
************************
Wayar Maama na kira amma shiru baa ɗauka ba, ban sani ba ko har yanzu fishi ta ke da ni, tunda dama tun daga lokacin idan na kira sai an ga dama ake ɗauka, na cije laɓɓana tare da gyara zamana ina kallon Sufyan da ke danna waya hankali ƙwance.
"Basu ɗauka ba." Na faɗa a wahale.
"Ki sake kiran su mana, kin ga dai ba zan zauna asibiti ba har agama miki komai."
Sai na ji hawaye na bin kumatuna, wato fa kamar bai damu da rasa babyn mu da muka yi, kamar ni ce rashin ya shafa ba shi ba? Na sa hannu na ɗauke hawayen ina jin wani iri a raina, shin ko dama baya son babyn kamar yadda ya faɗa? Kuma fa yaron har an gama halittar shi, namiji da shi? Na lumshe ido ina jin yadda gabana ke zugi, a hankali na ce "Baka ji komai ba Sufyan?"
Ya kalle ni ya watsar sannan ya ce "Me zan ji? Yara uku fa na rasa na yi haƙuri bare wannan da ko haihuwar shi baa yi ba."
"Shima fa mutun ne? An gama halittar shi."
Ya min banza yana latsar wayar shi, takaici ya sa na cigaba da kuka ƙasa ƙasa, a zatona zai rungume ni ya lallashe ni, amma sai ya daka min tsawa yana faɗin "Malama kar ki sa min ciwon kai da Allah, ki rufe min baki, baa kan ki aka fara ɓari ba."
"Ni fa ba ɓari na yi ba, fidda shi aka yi."
"Amma ai kin ji me likitan ya ce miki? Da Allah ki kira wanda zai zo ya kula dake, don wallahi ba zan tsaya ba."
Na zuba mishi ido cike da mamakin shi, ni Sufyan ke faɗa ma ba zai zauna ya kula da ni ba zuwa 10pm a sallame mu, to dan Allah wa yake so na kira? Bayan Maama ta ƙi ɗaga wayar, kuma Teemah idan na kira na san ba zata ɗauka ba.
Muma nan zaune likitan ya shigo round, ya duba ni sannan ya janyo wata ƴar ƙaramar kujera ya zauna yana fuskantar mu, a nutse ya ce "Amma kafin ku yi aure kun san Genotype ɗin ku.?
Sufyan ya ce "Eh, dukkan mu AS ne."
Ya lumfasa ya ce "Duk da haka kuka yadda kuka yi auren a haka?"
Muka kalli juna a sanyaye, sannan Sufyan ya gyaɗa kai har lokacin idon shi na cikin nawa.
"Ok, amma kun san abinda ya rasu ku ne kuka kashe shi? Sannan za ku cigaba da kashe ɗiyan ku ko da yaushe."
Kamar haɗin baki muka tambaya "Kamar ya?"
"Yes, rashin jini ya kashe abinda ke cikin ta."
Na zaro ido waje a tsorace ina tambayar "Dama za'a iya samun rashin jini a abinda ba'a haifa ba.?"
Likitan ya ce "Gashi a jikin ki."
A tare muka kalli juna, yayin da likitan ya hau mana mana faɗa, wai ta ya zamu yadda mu yi aure bayan mun san Genotype ɗin, kai tsaye na ce sabida muna son juna, ya kau ƙara hawa, wai su abinda zamu haifa bama tausayin su? Ba mu san zamu tsaya gaban Allah mu amsa tambayoyi ba? Ba mu idan har suka rasu sanadin sikila mune muka kashe su ba?
"Me ye solution." Sufyan ya tambaya a sanyaye.
"Ko dai ku dakatar da haihuwa, ko kuma ku rabu, idan ba haka ba, zaku cuci ɗiyan ku, sannan kuma ba zaku taɓa samun ƙwanciyar hankali ba."
Na kalli Sufyan da sauri ina jiran ya bashi amsar zamu yadda mu rayu a haka har abada, ba zamu taɓa rabuwa da juna ba, kamar yadda muka ma juna alƙawari a baya, idan da hali ma ya ƙwaɗe likitan da mari da ya ke son kashe mana auren mu, amma sai na ga ya miƙe a sanyaye ya fita waje, na bishi da kallo, kafin na yi magana likitan ya fice shima, suka barni zuciyata na bugawa da ƙarfi.
Kusan minti Ashirin sannan Sufyan ɗin ya dawo, daga bakin ƙofa ya tsaya yana tambayata "Kin ji me likita ya Faɗa?"
Na gyaɗa kai "Ai dama an mana wannan bayanin tun kafin mu yi aure, kuma muka yadda."
"Na manta, na yanzu na ke magana.."
"Amma ai muna son juna, sannan mun yi alƙawarin zamu rayu mu mutu a tare."
"Ina maganar yanzu ne." Ya faɗa babu yabo ba fallasa.
A firgice na ce "Bangane ba?"
Ya tako har kusa da gadon da nike zaune, ya dafa ƙarafan gadon yana faɗin "Gaskiya ya faɗa." Ya ɗago ya zuba min ido sannan ya cigaba da faɗin "Zaɓi ya rage gare ki, ko dai ki tsayar da haihuwa na maido Asiya, mu rayu har abada, ko kuma mu rabu Nafeesa....!
#UWAR SUKUM..
.
[6/13, 9:14 PM] RN Feedohm: 💧💧 *KUSKUREN SO.*
FREE BOOK
*HASKE WRITER'S ASSO.*
*FEEDOHM*
Wattpad@Feedohm
_Ga ba ɗaya littafin nan sadaukarwa ne ga NAFEESA Muhammad SULE, maman jinjiri, Alherin Allah ya kai maki a duk inda kike._
_Ina kike Aunty Zainab Abubakar Kotorkoshi? Ke ma ina maki fatan alheri._
*037*
Ƙwana da yawa? Kun ji shiru ba? Ayi haƙuri dan Allah, kun san dai mun san darajar aure? Suna mu ka sha...
Jikina ya fara karkarwa yayin da zufa ta fara keto mani a dukkanin ilahirin jikina, duk da kuwa sanyin Ac da ya gaurayen ɗaki, lokaci guda na mance da ciwon da ke jikina na yi tsalle na diro daga bisa gadon ina tambayar "Anya kuwa Sufyan ɗina ne? Anya kasan me kake faɗa kuwa? Rabuwa fa kace? Ko kuma ka maido da