Showing 42001 words to 45000 words out of 163788 words
Chapter 15 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt
taba rike mata hannu to balle kuma rungumeta ta hakan yasa jikinta sake daukar rawa, tareda wani irin tsoro saka makon tunawa da maganar Hajiya don kaka sai kawai ta fashe da kuka me cike da tsoro.
tareda cewa wayyo Allah na don Allah Hmm *Habeeb* kayi hakuri kasa keni ka daina tabani kaga"Hajiyar mu tace" idan muka bari namiji ya tabamu zamuyi ciki, tafadi tareda kokarin tureshi daga jikinta ido ya rintse saka makon jin kukan ta har cikin zuciyar shi, don haka saiya sake rungumeta sosai cikin sanyi murya yace *Leemah* ta kiyi shuru babu abunda zai faru, "Hajiyar mu tana nufin namijin da ba muharramin kinba, ni kuma kinga mijinki ne don haka babu komai.
Sannan *Leemah* ta "amatsayin ki na matata bazaki zokice mun Allah ya tsare hanya ba sai ance kizo kice mun umm?..batace komai ba sai mutsumutsu da takeyi wanda so take kawai ta kwace kanta daga gare shi, domin ita bawai ta yadda Da abunda yafada bane, saidai kuma takasa don haka sai tayi tamo tana sauka ajiyar zuciya tareda shakar daddad'an tura ranshi, Sannan kuma kirjinta bai daina bugawa ba haka kuma jikinta bai daina rawan dayake ba.
*Habeeb* kam yana jinta amma yakasa sakinta din kamar yadda tabu kata, asalima sake rungumeta yayi sosai domin yanayin dasu ke ciki yai masa dadi matuka, shi bai kima ace su dauwama haka ba,
ahankali yace *Leemah* ta bakice komai ba wato hakan yana nufin da gaske baki *SONA* KO?.. Cikin rawar murya tace to ainima baka *SONTA,* Dasauri yadago kanta tare da zutsura ma kyakkyawar fuskar ta ido, yace waya fada maki banason ki?.. dukar dakai tayi cike da shagwaba tace to bakai bane sai kaita yimun tsawa da zare ido da rankwashi, har da matse mun baki kuma fa akwai zafi ta kareshe fadi cike da yanayin tana shagwaba.
Murmushi yayi tareda cewa to kiyi hakuri kiyafe mun, amma nidai nasan ina sonki sosai irin son da bayaga "Hajiyarmu babu wata mace dana kema irin shi matsayayin ki acikin zuciyata me girma ne *Leemah ta*, dasauri tadago kaita kalle shi cike da mamaki! murmushi yayi yace kina mamaki! jin haka ne?..kaita gyada alamar "eh, yace *Leemah ta* kenan karkiyi mamaki! da lamarin ubangiji, domin ni tun ranan da'aka haifeki *ZUCIYATA* taka mu da kaunar ki,
ido๐ณtazaro cike da matsananci mamaki! yace tabbas abunda nafada maki ba karya bane kuma ki tambayi *"Harees,* kuka tafashe dashi, cikin gigita yajata ya rungume tareda cewa me yafaru *Leemah ta??* cike da shagwaba tace to ba kai bane kace tun ranan da'aka haifeni ka kesona amma kuma sai, kayita yimun zalu,
yace to kiyi hakuri kodama karfin hali nakeyi kuma daga yau bazan sake ba kinji?.. batace komai ba sai mamakin shi daya darsu cikin zuciyar ta, har tana fadi aranta wai yau ita ce Hmm *Habeeb* yakece ma yana son har da bata hakuri akan abubuwan da yai mata, tab! lallai yau za'ai ruwa da kankara.
Cikin sanyi murya yace *Leemah ta* kinyi shuru kodai baki yafemun bane?... Cikin cool voice din ta tace nayafe maka amma kar kasake, dariya yayi tareda cewa to nagode kuma bazan sake ba insha'allahu to amma kefa; yanzu kina sona?.. tace nima bansani ba,
murmushi yayi tareda cewa to shikenan ni Zantafi amma inason kiyi mun Addu'a kinji?.. ba tareda tadago Kai ba ahankali tace Allah yasa tsare hanya, yace yauwa *Leemah ta* ameen amma pls kibarni naga kyakkyawar fuskarta ki, yafada tareda sa hannun yatallabo fuskarta dasauri ta lumshe ido,
Kuri yayi yana kallon tsantsar kyau irin na *Deeyar* *Feeya*, *KYAUTAR* lnna da Baffa hali dubun Hajiya๐,
"Ahankali yace *Leemah ta* bake son ganin fuskata ne?.. cike da shagwaba tace to ni idonka tsoro yake bani, baki yabude tareda yin dariya yace Kai *Leemah ta* idon nawane yake baki tsoro?.. tace "eh, yace to bude idon ki ki kalli kwayar idona idan kikayi haka shikenan bazaki sake jin tsoro ba, "ahankali ta bude idon tareda tsura mashi Su, shidin ma ita yake kallo zuciyar shi cikeda matsanancin kaunar ta,
tsawon lokaci suna haka can saita dukar dakai ba tareda tace komai ba,
Shikam ajiyar zuciya yayi tareda cewa to *Leemah ta* zantafi meki keso nasiyo maki idan Zan dawo?.. tace ba bukomai, yace Kai *Leemah ta* bakison komai fa kikace?..
tace "eh yace to shikenan amma ni idan nadawo zakiyi mun jagwalgwalon nan me dadi?.. dasauri tarufe fuska tana dariya, shima dariyar yayi tareda sake rungumota jikinshi yace Allah akwai dadi jagwalgwalon nan umm umm Ina sunan shi yauwa natuna alalan kwai KO?..yafadi tareda kashe mata ido daya,
murmushi tayi tareda daga Kai alamar "eh.
yace yauwa to zakiyi mun idan nadawo?.. tace "eh yace nagode to bude ido muyi sallama, tana budewa yasake ta tareda yi mata kiss agoshi sannan yace byeeee!, tareda wucewa tagefen ta, baki tabude cike da mamaki aranta tace oh๐คwai dama haka Hmm *Habeeb* yake very simple amma sai yai tayiwa mutane masifa, tana tsaye har yashiga part din Hajiya Sannan tashiga falon.
Mamaki ne Yakama lnna da Baffa ganin yadda tashgo fuskarta dauke da farin ciki sabani yadda tafita, kamar ba'ita ne taci muka ba, fuska sake tace Baffa Hmm *"Habeeb* yatafi Baffa yace to madallah yanzu zonan ki zauna kiji yafadi tareda muna mata gurin data tashi,
Bamu su taje ta zauna cikin hikima irin tasu ta manyan mlm yaimata nasiya me kashe jiki, dangane da auren *Habeeb* dake kanta, Sannan ta tashi tafita zuwa part din Hajiya.
*******
Bayan *Habeeb* yashiga ya sallami Hajiya Sannan yafito yanufi part din shi, saidai wani abun takaici shine koda yashiga bai'iske *Jana* ba sai me aiki dasu juinor, dagudu sukazo sukai mashi oyoyo, lili mama yadauka tareda Shafa kam Junior, yace Ina momin ku take?..
Junior yace tafi unguwa lili mama kam baki ta tabe tareda cewa Dad shine kuma bataje dani ba, yace Sorry bari nakira ta koda yakira layinta akashe, tsaki yayi tareda cewa my lili wayar ba tashiga yanzu dai kunci abinci?..suka ce "eh,
Yace to ni zanshiga wanka amma idan nafito zan tafi abuja so kuje part din Hajiyar mu idan zan dawo me zan siyo maku?.. dauri sukace yeee! Dad sweet and ice cream zaka ciyo mana inji cewar lili mama; Junior yace Dad har da biscuit, yace to tareda sauke lili maman suka fita da gudu.
Dakin sa yashiga ba tareda bata lokaci ba yashiga wanka, bayan yafito ya shirya cikin hadadd'en suit blue yai masa kyau sosai Sannan yadauki wata yar karamar jaka baka tareda wata babba itama baka cewadda da'alama kayan sawan shine acikin,
sannan yadauki wayoyin sa yafita.
Direban sa yana ganin shi yafito yai sauri yakarbi jakar kayan yabude but yasaka, sannan yasaka karamar jakar abaya tareda bude masa mota yashiga, masu tsoron shima suka shiga ta su motar Sannan sukaja suka fitada dudu ZUCIYAR *Habeeb* cike da KAUNAR *LEEMAR* shi.
**********
*Jana* kam lokacin data hau sama tana kiran layin shafa kawarta bai jeba, don haka sai kawai tadauki gyale da key mota tafita bata tsaya ko'ina ba Unguwar su Shafa inda take aure, ahar gitse tashiga gidan shafa nagani ta tace lafiya naganki haka?..
zama tayi jagwaf tamkar kayan wanki tareda cewa hmm! kedai bari inafa lafiya ke kinji irin masifa data sameni rana tsaka kuwa?..ido shafata zaro cike da tsoro tace ke! meyasa me ki?..tace kishiya wani uban asharar Shafa ta yanko tareda cewa BABBAN masifa kuwa "shi *BB* ne yai aure kuma yaushe?..
Nan tafada mata komai aikam cikin masifa tace aibe'isa ba wlhy wannan aicin amana ne, don haka tashi muje nakaiki gurin wani hatsabibin mlm sunan shi mlm dare me abun mamaki, bamusu *Jana* ta tashi yayinda Shafa ta dauki gyale ba tareda Neman izinin mijinta ba suka fita.
Saida sukayi tafiya sosai kamar zasu fita cikin garin Bauchi tukun sannan suka shiga cikin wani daji, shima saida sukayi tafiya me nisa sannan suka tsaya nesa dawata bukka me lullubeda ganyayyaki sannan suka fito suka rufe mota suka karasa gurin bukkar da kafa.
Shafa tace da *Jana* karki ga gurin babu mutane shi baifaye aiki da rana ba saida daddare, amma idan irin na gaggawa ne to yanayi da rana tace nagane, dai-dai lokacin da suka isagurin bukkar Shafa tarera kirari sannan suka shiga cikin bukkar.
Bakine mutumin wul yana sanye da bakin kaya zaune a saman bakin buzu, gaba daya tarkacen dake gaban shi bakake ne babu fariko daya, ya kalli Shafa yace kinzomun darana tsaka kuma kinsan bana aikin rana, tace ayi hakuri mlm dare a taimaka kawata ce take da matsala, yace meke tace da'ita?..
Nan take *Jana* ta koro masa bayani ba tareda bata lokaci ba yai yansur kullen shi, sannan takalli *Jana* tareda cewa kinyi sake domin kuwa son wannan yarinyar yayi matukar tasiri acikin ZUCIYAR shi, wanda bayan son uwarshi babu na wata ya'mace acikin ranshi, ke bari nafada maki gaskiya niko d'igon kwayar zarrar SONKI ban gani acikin ranshi ba,
Dasauri tace wlhy mlm karya kake "mijina yana sona kuma babu wata mace data keda tasiri a ZUCIYAR shi idan bani ba.
Cikin bacin rai yakalli shafa yace shafa'atu tunda nake aiki ba'ataba karya tani ba sai yau, wacece wannan ita har ta'isa nayi magana ta karya tani?...
Cikin rawar jiki Shafa tace don bakin aljani mlm kayi hakuri, yace kingama magana domin kin hadani da masoyina amma badan haka ba da tabbas yau saina koya ma kawarki darasi me muni,
Shafa tace bakin aljani yahuci zuciyar ka, Shafa tace da *Jana* ki bashi hakuri, tace Allah ya baka hakuri Shafa tace ke! cewa zakiyi bakin aljanu yahuci zuciyar ka, nan dai tafadi sannan yace tafadi abunda takesan ayi mata".
Da sauri *Jana* tace mlm kashe "ta nake son ayi, yace bazata kasu agareni ba domin addu'o'in dake jikinta sunfi karfina da aljanuna idan kuma nace zan kashe "ta dakarfi to saidai aljanuna sukone ni dake kuma mu mutu, ido ๐ณ *Jana* tazaro cike da tsoro tace....
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_*(Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นMeenart๐น
[7/2, 11:48 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
2โฃ9โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
Mutuwa kuma mlm?.. yace tabbas idan har mukace zamu kashe "ta mutuwa zamuyi, domin tsarin dake jikin "ta yanada matukar karfi sanna "ita kanta bata wasa da lbada, don haka yima irinsu" asiri yakamau nan take to sai anrasa rai nikuma banyi shirin mutuwa yanzu ba gaskiya.
Cikin rawar murya tace nima gaski ban shiryawa mutuwa yanzu mlm yace to kingani, tace to mlm ka kyaleta kar akashe ta" amma kuma na tsaneta fa mlm banason "ta ko kad'an, don haka inason kayi "mata abunda zata zama da'ita da banza duk daya acikin gidan, Ina nufi kadasa tsana atsakan "su yaji "ya tsaneta sosai yaji aran shi bayason ganin ta kusa dashi.
Mlm dare yace wannan abune me sauki yanzu aikin takanshi" zaya koma kenan?.., tace "eh mlm yakoma takan shi din domin yaci amanata, yace to bari mugani ta'ina zamu fara domin shima naga a tsaye yaka da ibada.
Bayan yayi yan surkullen shi sannan yace inason kikawo mun gashin ganshi, KO rigarsa ke ko hular shice ki kawo mun, tace to mlm saidai akwai matsala yace menene matsalar?..tace yaune zaya tafi Abuja kilama yanzu yawuce, sannan maganar gaskiya mlm baya bari nashiga dakin "shi, saidai shi yashigo dakina idan yanada bukata ta, bayan yagama sai yafita sannan kuma baya barin komai nashi adakin nawa.
"Wata mahaukaciyar dariya mlm dare yayi tareda cewa aina fadamaki kinyi sake yanzu kar kidamu Zan baki wani ruwan magani, ki ajiyeshi duk ranan daya dawo kizuba shi ta'inda zayabi yawuce Ina nufi ya tsallaka wannan maganin to shikenan magana takare daga ranan zaya tsaneta sosai dazaran yaganta zayaji ranshi yabaci sannan yadinga yimata masifa ke Bari kiji daga karshe mantawa dawata wacece ma kikace sunan "ta?..
tace *"Sadeeya* ana kiranta *KYAUTA* yace ba *KYAUTA* ba ko *SAMU CE* daga ranan zakiga abunda zaya faru tsab zaya manta da'ita", arayuwar shi kilama sai ya tambaye ki wacece ita" ke kuma zaya soki feye da kowace mace kilama harda uwarsa, amma da sharadi....tace mlm menene sharadin?.. yace daga ranan wata ma'amala ta'auratayya bazaya sake shiga tsakanin kuba, tace mlm ban game ba?..
yace zaya'iya rungumar ki da sumbatar ki amma kuma bazaya kusance ki ba, Dasauri tace kan uba mlm tayaya hakan zata kasan Ce Ina matsayin matarshi amma bazaya ringa saduwa dani ba gaskiya mlm bazan iyaba, saboda inada tsananin bukata.
Dasauri Shafa ta dungure ta tareda yimata rad'a akunne, tace dalla gafar ke banza ce don be saduwa dake sai me?.. baga adonki ba sannan idan kina bukaran wasu mazan saina nemo maki, tace kin fasan idan "yadawo wani sati tare zamu tafi "Abujan tace shegiya shikenan sai kici karanki babu babba ka, tace "eh kuma fa haka ne.
to mlm na yarda saidai fa shima yanada tsanani bukata, yace karki damu zamu dauke mashi bukatar shi zayaji bayaji sha'awa, tace yauwa shikenan ma nan dai yabude wata kwarya yadebo wani bakin ruwa yai wani siddabaru acikin sannan yazuba cikin wata bakar kwalba sannan ya mika mata.
tareda cewa ki tabbatar dakin zubashi gurin da zaya tsallaka, akarba tareda cewa to mlm nagode yace kinsan makarin wannan sihirin?..tace a ah yace duk ranan daki kabari jikinshi Dana waccen "yarinyar yahadu to daga ranan asirin zaya karye, wlhy zaya so ta feyeda da ke! nafada maki gaskiya zai mata wani irin mahaukacin so ne wanda zaya zarce yi tunanin me tunani, domin alokacin zaya'iya aikata komai akan *SONTA"* don haka sai ki kula da kyau.
tace Ina mlm aibazan taba yadda yaganta bama ba talle yata" yace to shikenan, sannan taciro kudi ajakarta masu yawa tabashi sannan suka fito suka tafi, saidai *Jana* ta maida Shafa gida. sannan itama tanufi gida koda ta tambayi me aikinta Ina *Habeeb* tace mata aiya tafi Abuja baki ta tabe tareda hawa sama, boyan kyau tayima kwalban maganin da mlm dare ya bata sannan tafito tazo zaman falo.
*******
*Deeya* kam fuska sake takoma part din Hajiya har saidai Mamaki yakama *Feeya* tace my sweet *Deeya* me yafaru?..
Dariya tayi sannan tabata labarin abunda yafaru tsakanin ta da *"Habeeb,* (amma kuma bata fadimata cewa ya rungume ta ba har yayi mata kiss agoshi) ita kam *Feeya* ido zaro cike da matsanancin mamaki wai Hmmm *Habeeb* ne yakeson *Deeyar* ta tun ranan da aka haifeta tab! lallai ma Hmm *Habeeb* din nan.
Sannan kuma ta bata Labarin yace" idan yadawo zatayi masa jagwalgwalon nan dasu kayi ya cinye masu aikam nan sukai ta dariya, har Hajiya ta'iske su Wanda hakan ba karamin dadi yai mata ba ganin yadda *Deeya* tasaki jiki, kamar ba 'itace tayi kuka dazu ba tason *Habeeb* ba.
Cikin farin ciki ta tambaye su abunda sukema dariya?.. nan suka fada mata itama dariyar tayi tareda cewa Oh! yaran nan Allah ya shirya munku sannan tafita tabar suna firar su gawani sha'awa.
*_Bayan kwana biyu_*
*******
Su *Deeya* basufita ko'ina dama can suba masu yawon banza bane, kuma *Deeya* tasaki jiki abunta sosai tama manta da wai akwai aure akan ta; sai sha'anin su sukeyi itada *Feeya,* saidai kuma takasa mantawa da "abunda *Hmm Habeeb* yaimata abun ya tsaya mata arai tana yawan tunawa sai tayi murmushi,
Ganin tasaki jiki sosai ne yasa Hajiya tafara gyarasu cikin hikima, haka itama lnna sannan su Adda Mamu suma suna yin nasu gyaran nasu na musamman, gefe kuma gasu goggo Lanti suma suna yin nasu kai abunda ba'acewa komai.
Inna ce zaune adakin su *Deeya* yayinda suma suke zaune a gabanta "KO wacce hannun ta rikeda cup din glass wani, hadin magani ne tayi masu shine ta tsare su sai sun shanye,
*Feeya* takusa shanye nata amma *Deeya* ko rabin cup ba tayi ba.
Cikin yanayin tana shagwaba tareda yamutse fuska, tace don Allah lnnan Mu kiyi hakuri anjima zan sha kinji?..hararan ta lnna tayi tareda cewa ba zanyi ba saikin shanye shi tas! yanzu kinbani Kofi, ga yar'uwan kinan takusa shanye nata amma ke kin tsaya shiriri ta.
tace to zansha amma ki karbi wannan kibani najiya din nan yafi dadi ko sweet *Feeya*?..Kai ka wai ta gyada batayi magana ba domin gaba daya baurin maganin yahade mata baki,
Inna tace to sarkin kwadayi babu irin shi kun shenye tun jiya, don haka ku shenye yanzu ku bani Kofi na haka nan, dai suka shanye badan sun soba sannan tadauki kofunan ta tafita.
"Ajiyar zuciya *Deeya* tayi tareda kwanta wa kan kafe tayi rigingine tana kallon sili tace don Allah sweet *Feeya* tashi mu gudu daga part din nan, idan ba haka ba anjima ma sake bamu zatayi tsaki tayi tareda cewa to aiko muje can part din itama Hajiya mu maganin zata bamu Cikin sanyi murya tace "eh kuma fa haka ne suma su Adda Mamu duk kanwar jace yanzu tashi muje gidan Hajiyar su Hmm *Harees* mu boye, bamusu *Feeya* ta tashi suka fita.
*_Nikam nace a ah su Feeya ba'ajin kunyar sarakuwa_๐*
Zasu shiga part din Hajiya shikuma *Harees* yana shigowa da motar shi yagan su" amma su basu gashi ba, murmushi yayi tareda cewa hmm! su me Darajata kenan duk yadda akayi sunzo 'boyewa ne, bayan yaifakin sannan yafito yanufi part din shi.
zaune suka iske Hajiya a falon kasa bayan sun gaida ita ta amsa ciki farin ciki, tace yasu Hajiya sukace lafiya, Hajiya zamu kwanta idan azo Neman mu kice munyi bacci inji cewar *Deeya,*
Dariya tayi tareda cewa to amma banda Hmm Ku KO?..dariya sukayi sannan suka haye sama dakin ta suka shige suka kudindine akan faffadan gadon ta *Feeya* tace ke nifa bacin gaske zanyi *Deeya* tace nima ai dai-dai lokacin da sukaji murya *Harees* yana cewa two brads, wato amare biyu dariya sukayi domin sunan na dasu yake.
Dasauri *Feeya* tarufe da bargo tana dariya dai-dai lokacin da