Showing 9001 words to 12000 words out of 163788 words
Chapter 4 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt
Ina kuma mutanan nan suka tsaya?..(kasan cewar Haka yake kiran *Habeeb* din) cikin ladabi *Habeeb* yace Abba ai can waje suka tsaya, yace Allah sarki toh" jekace sushigo mana yace toh" tareda fita.
Dai-dai lokacin da Hajiya ta zauna kusa da Abba tana cewa Alh munyi baki ne?..yace "eh nan yafara fada mata abunda yafaru dasuka fita zuwa sallah.
*Habeeb* yana gaba suYusufa suna biye dashi abaya, cikin sakin fuska Abba yace a ah mlm Yusufa shine kuma kuka tsaya awaje, baku shigoba?.. Yusufa yace Alh ai malamina yasha fadamun cewa bamu kyau mutun yashiga guri ba tareda anyi masa izini ba, Murmushi Abba yayi tareda cewa mlm Yusufa kenan wannan haka yake, toh" yanzu nabaku izini kushigo ga kuma gurin nan Ku zauna.
Zama sukayi yayida Yusufa yake cewa toh" Alh mun gode sannan yace Hajiya wayan nan sune bakin, tace Allah sarki sannun Ku dazuwa sukace yauwa, sannan Abba yace sunan shi mlm Yusufa matar shi kuma lndo da sauri Yusufa yace Alh kanata kirana mlm alhalin kuma nidin Almajirine yafadi cikida ladabi da biyayya, murmushi Abba yayi yace Hajiya kikai ta tayi sallah, tace toh" tareda tashi tana cewa mushiga ciki sai kiyi sallar lndo tace toh" tareda tashi tabi bayan ta.
Dai-dai lokacin da su Mamu suka fito hannunu wansu dauke da al'qur'ani *Habeeb* yakarbi nashi sannan suka fita zuwa gurin daukar karatu.
Ahankali Abba yamaida kallon sa ga Yusufa Wanda kansa kekasa, sannan yace mlm Yusufa inasan kabani Labarin ka cikin nutsuwa Yusufa yace toh" tareda fadawa Abba komai tun dagakan mutuwar "iyayensa har kawowa Auren sa da "lndo da irin kuntatawar da "Inna Rakiya takeyi masu saida yafada masa.
Aciyar zuciya Abba sauke yayinda zuciyar shi tacika da tausayinsu Yusufa, _kasan cewar shi mutun mai matukar tausayi_ don haka sai yaji tsanar "Inna Rakiya ya darsu aransa. cikin bacin rai yace tabbas "Inna Rakiya ta zalinceka ta kuma gwada rashin imani akanka da matarka.
kamar yadda kafada mun labarin ka nima bari nabaka Labarin Na, nan dai Abba yafada masa koshi wane inda yakarashe fadi dacewa yanzu haka nid'an majalisa ne kuma nadauki alkawairn zan karewa mutane mutuncin su, haka zalika nasha alwashin duk wanda aka tauye masa hakkin sa insha'allah saina kwato masa abunsa don haka dole "lnna Rakiya ta fusakanci mummunan hukunci akan abunda ta aikai- agareka.
Dasauri Yusufa yace a ah Alh akyaleta nikam tuni nayafe mata abunda taimun cikin matsanancin mamaki Abba yace..
_*Washhhh! ๐คฆ๐ฝโโdon Allah kuyi hakuri da wannan wlhy Ina cikin typing din duk sai naji nagaji๐, lah๐ kilan dan Na kwana biyu banyi bane shiyasa, koda yake dama ai typing dinma is not easy walla am๐ amma dai karku damu next page zanyi kokari nayi maku read moreeeeeeeeee.๐*_
Muje zuwa
A
_*KYAUTAR ALLAH CE*_(Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นLufhat๐น
[7/2, 11:27 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
8โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirrahim*_
Kace me?..yace nayafe mata Kai Abba yajinjina sannan yace toh" shi kuma hakkin kafa?..yace Alh wannan kam ban yafe mata ba, domin kuwa Annabinmu ma yace kabi hakkinka saidai idan ba'a baka ba toh" kabar mutun da Allah, Abba kam jiyayi zuciyarsa tacika da kaunar Yusufa haryana fadi aransa tabbas wannan da'alama zayayi rukon amana, cikin sanyi murya Abba yace wanna haka yake. Yusufa yace toh" don haka kaga inada da damar da zanbi hakkina saidai kuma Alh bazan iyaba, da sauri Abba yace saboda me?.. yace bayaga ubangijina bawani dan Adam din danake tsoro aduniya irin lnna Rakiya Alh Ina matukar tsoronta don haka nibazan iya tunkaranta akan tabani hakkina ba,
Cikin tsanani tausayin sa Abba yace indan wannan ne karka damu ni Zan karbar maka hakkin ka insha'allahu, yace toh" Alh nagode sosai, saidai don Allah Alh karkace nakoma kauyan nan dan nikam yanzu banajin zan'iya komawa gudun fulani domin naji kauyan yafita araina.
Murmushi Abba yayi yace mlm Yusufa kenan bazance ka koma gudun fulani yanzu ba, saidai kuma kasani dole zakaje wata rana domin bukatar zuwan naka zayazo, yace toh" shikenan Alh nagode sannan kuma don Allah ina naiman wani taimako agurin ka, Abba yace mlm Yusufa kafadi bukatar ka indai baifi karfina ba toh" insha'allahu zanyi maka, yace Alh dama sonake kataimaka mun da gurin zama nadan wani lokaci sannan kuma kanema mun dan wani aikin dazan rike iyalina dashi.
Abba yace kar kadamu zan taimaka maka Insha'allah yace toh" nagode kwarai Allah yasaka da alkhairi, Abba yace bakomai idan dawata bukatar kafada nikuma zan biya maka ita muddun baifi karfina ba, Yusufa yace "eh toh" akwai saura saidai kuma kar nadora maka nauyi dayawa, dariya Abba yayi yace Mlm Yusufa kenan babu komai, nidai burina nataimaki wanda baya dashi fatana kuma wanda nataimaka shima wata rana yataimaki wani, don haka fadamun menene yaisaura?..
yace "eh toh" dama damuka gama sallah sainaga yawancin mutane sun kewaye liman din kowane da al'qur'ani mai girma harda wasu littafan addini zasu dauki karatu sai abun yaburgeni toh" shine nakeso nima narika zuwa daukar karatun domin burina arayuwa nasamu ilimin Addini mai zurfi.
Abba kam ajiyar zuciya yayi domin kuwa gaba daya zuciyar shi tagama yadda da Yusufa mutumin kirkine, don haka yace kar kadamu Insha'allahu zakasamu abunda kakeso. yace toh" nagode sosai, dai-dai lokacin da su Hajiya suka fito itada lndo, Abba yace tayi sallah nan?..Hajiya tace eh yace yauwa toh" akira Kulu takaisu shashin baki suyi wanka su huta idan angama karin kumallo sai akai masu, inafata dai shahin agyare yake?..tace "eh Alh aikasan bamu rabuwa da mutanan arziki don haka koda yaushe cikin gyarashi ake, yace yauwa ai hakan yanada kyau, kai mlm Yusufa tashi muje gurin mlm Liman nafada masa zakaringa zuwa daukan karatu, yace toh" Alh aini yauma zanfara dauka dama da Qu'rani na nake tafe kaganshi nan ma, yafadi yana nunawa Alh qur'ani dake cikin jakar datake rataye akafadarsa yayinda fuskarshi ke dauke da matsanancin farinciki,
Murmushi Abba yayi tareda mikewa yana cewa a ah mlm Yusufa bayau zakafara daukar karatun ba, sai Allah yakaimu gobe domin yau sonake Ku huta sosai kaji KO?..yace toh" Alh yadda kace haka za'ayi dai-dai lokacin da suka fita.
_*GUDUM FULANI*_
Inna Rakiya kam dama tasaba bata tashi daga barci sai Rana tafito kwal sannan tafito ta bubbuga sallah, cikin masifa ta turo kofar dama haka takeyi tsaye tayi tana mika ba tareda salati ba yayinda hamma yabiyo baya cak! ta tsaya baki hankade sakamakon ganin gida kaca-kaca gakuma shanu d'add'aure, wani uban ashar tayi tareda cewa su wayan nan yan'iska yau me suke nufi?..cike da masifa tanufi dakinsu Yusufa, tana cewa kai isuhu.
_domin ita bata kiransa Yusufa_
Dakarfi take bugamasu kofa tana cewa dan'ubanshi yau ba zayakai shanu kiwo ba ne ita kuma Indo bazata fito tayi aikin gida bane?..sanna yau bazataje tallar nonon bane?.. shuru ba amsa don haka dakarfi tasa kafa tabanki kofar aikam sauran kad'an tafadi ๐yayinda kafarta daya tana waje daya kuma tana cikin dakin, dasauri tadafa bakin kofar dakin Wanda yake wayam bakowa sai Yar tabarmar dasuke kwana.
_tunda dama tuni sun siyar da kayan dakin sunci abinci_
Cikin matsanancin tsoro tazaro!๐ณtareda kunduma uban zagi sai kuma tafito cikin masifa take fadin su wayan yan'iskan Ina suka tafi?..ba'amsa dayake ita din masifaffiyace don haka saitafara masifa tareda zage-zage aikam nan da nan aka ciki gidan ana tambayar ta meya faru?.. nan take tafadi bataga su" Yusufa ne, cikin takaici mutanan suka fara fita suna gun-guni fadi su "Yusufa kam aiba kananan yara bane daza ta daga hankalin ta don bata gansu ba duk inda sukaje aizasu dawo, duk mutanan suka fita suka barta tana masifa sai wata makociyarta me suna Kulu ta tsaya.
_wacce ita kam sam bata tsoron lnna Rakiya,sabani yawanci mutanan dake masifar tsoron ta_
Tsaki tayi tareda cewa don baki ga su" yusufa shine duk saiki tayarwa da mutane hankali, cikin masifa tace ya bazan tada hankali ba tare da "sufa muka kwanta amma yanzu kuma gari yawaye bangansu ba,
hararanta Kulu tayi tareda cewa "eh kuma fa hakane dole kitayar da hankali saboda kina tsoron idan "suka kufce maki bazaki sake samun bayi kamarsu" ba KO?...,hararanta lnna Rakiya tayi tareda cewa ban gane ba?..baki Kulu ta tabe tareda cewa ai zakigane toh" bari nafada maki abunda baki sani ba," Yusufa da "Indo sun gudu saboda sungaji da azabtar dasu" daki keyi bakar azzaluma kawai kinsamu marayun Allah sai azabtar dasu" kikeyi, ke bakiko tsoron haduwarki Da Ubangiji, don haka kisani "Yusufa da "lndo bazasu taba dawowa gareki ba, indai dasunan "su cigaba dayi maki bautane toh" har abada bazaki sake ganinsu" ba saboda haka saiki nemi wasu bayin tafadi tareda juyawa zata wuce abunta.
Cikin masifa lnna Rakiya tajawo rigar kulu tana cewa aidama tunda naga kina yimun katsalanda acikin al'amurana, dama nasan Wata Rana sai haka tafaru don haka bazaki fita gidan nan ba sai kin fadamun gidan uban dakika turasu" domin na tabbatar keki kasa suka gudu, itakam Kulu kamar dama tanajira Inna Rakiya aikam cikin masifa tajuwo tace tace "eh ninasa suka gudu don haka sainaji kamshi mutuwa sannan Zan fada maki inda suke kinji KO?..
kafin kace me tuni dambe yakaure tsakaninsu aikam tuni Kulu ta turmushe lnna Rakiya tana ta jubga saikace Allah ya'aikota, Kai! da'alama lnna Rakiyan madai batada karfi๐ domin kuwa sai ihu take zubawa๐ฉ tana fadi ataimake ta zata kulu zata kashe ta, saidai kuma ina babu Wanda yaleko balle yataima keta, yayinda itakam Kulu sai kirbarta take kamar tasamu fura๐ saida taimata shegen duka wanda ko iya tashi batayi sannan tafita daga gidan.
_Nikam nace alhaki marayun Allah ne_
***********
A bangaren su Yusufa kuma shashin da'aka kaisu maikyau kuma akwai komai ciki, bayan sunyi wanka sai sukasa sabon kayan da'aka basu sunyi fesss abunsu gwanin sha'awa, sannan aka kawo masu karin kumallo sukayi bayan sungama sai suka fara firarsu Abba da Hajiya, suna mefadin kirkirnsu tareda jin-jina karamci irin nasu har bacci yadauka su me nauyi, Wanda rabon dasuyi irin sa harsun mata rana Allah sarki bayin Allah, har sun bani tausayi ๐ kuhuta kunji marayun Allah.
_*Bayan kwana biyu*_
Sai Abba yakira Yusufa yasanar dashi cewa ya yanke shawaran zaya hadashi da wani amintatcen yaronsa me suna Al-mustafa suringa kulamasa da gidan gonansa,
_kasan cewar yanada wani tabkeken gidan gona da ake masa noman Rani da DA muna domin yatallafawa al'umma,idan ancire amfanin gonan sai yaraba kashi biyu daya yana raba masu kyauta daya kuma yana siyarwa cikin sauki domin shidin mutun ne mai matukar tausayi Al'umma._
Yusufa yayi na'am da aikin da Abba yace zaya ringayi shida Al-mustafa, don haka cikin lokaci kan-kani suka cigaba da aikin kulada gidan gonar yadda yaka mata, ahaka kuma Yusufa yake daukar karatu kamar yadda ya bukata.
Akwana atashi bawuya agurin Allah su Yusufa watansu Uku agidan Alh Hashim, sunyi kyau abinsu kamar basu ba don haka basuda wata matsalar komai daga abinci har suturar sawa, Indo kuma tana shiga shashin Hajiya Rabi'atu ta tayata aiki, yayinda Yusufa yake cigaba da aikinsa tareda karatun al'qur'ani dama wasu littafai addi'ni duk yayi nisa acikin karatun su, domin shi mutun ne me matukar hazaka.
kuma acikin watannin uku nan Abba yagane Yusufa mutumin karkine kuma shi me amana ne, shiyasa yajashi jikinsa sosai don haka sha kuwa mai karfi hade da kauna da yarda tashiga tsakanin Abba da Yusufa harda iyalinsa ma inda su *Habeeb* suke kiran Yusufa Baffa lndo kuma lnna tun Abban su yace Yusufa dan yan'uwansa ne.
Ranan Wata Jumma'a da milasalin 4: 30 Pm Abba da Yusufa da Al-mustafa suna zaune aharabar gidan kan babbar dadduma, kallo daya zakai masu ka fahimci akwai aminci me karfi atsakaninsu wanda bazaka taba cewa mai gida ne da yaran shi ba, saidai kace wayan nan aminan juna ne tun bayan dasuka sufito sallar la'asar suke ta fira abunsu gwanin sha'awa,
_kasan cewar ranan Jumma'a basa zuwa gona_
Abba yace mlm Yusufa nagama shirya komai gobe in Allah yakaimu zamuje gudun fulani, cikin girmamawa yace toh" Alh Allah yakai mana rai lafiya Abba da Al-mjstafa sukace ameen, yayinda Abba yace ai harda su Hajiya da Al-mustafa zamu tafi yace toh" shikenan Alh yadda kace haka za'ayi nan dai suka cigaba da fira har lokacin magrib yayi suka tashi suka nufi masallaci.
Washegari koda 10:00Am tayi sun gama shirinsu tsaf mato biyu suka cika daya Hajiya Rabi'atu Indo *Hamman Habeeb* Adda Mamu Adda Rahma sai direba, daya motar kuma Abba Yusufa Al-mustafa dan'sanda sai direba suka nufi.
_*Gudum fulani*_
Kwance take saman katifa nishitake da kyar kallo daya zakayi mata kafahimci tana matukar jin jiki, bakowa bace illa Inna Rakiya wacce ciwon shanyewar barin jiki yaima dirar mikiya acikin watanni uku kacal tazama bata'iya yima kanta komai sai anyi mata kashi da fitsari duk a kwance takeyi, gefenta Lanti Ce keyi mata fiffita da mafici yayinda take tazuba mata ruwan sannu, duk tasan cewa lnna Rakiya ba amsawa zatayi ba tunda batayin magana, amma haka Lanti keta jera mata sannu.
Wata yarinyace Yar kimani shekara goma sha biyu me suna mairo, mairo diyar makotan lnna Rakiya ce mairo suna matukar shiri daYusufa, yayinda take matukar jin haushi lnna Rakiya akan abunda takewa Hamman Yusufan ta da Adda lndo, don hakane ma take kiranta masifaffiya, tafito gidansu kenan saitaga Yusufa yafito daga mota,
don haka da murnarta tanufi cikin gidansu Yusufan da gudu tashiga dakin lnna Rakiya tana cewa lnna masifaffiya, Ga Hamman Yusufa can yazo acikin mator yan birni harda yan'sanda sunzo sutafi dake birni suyita baki wahala, kuma suki baki abinci kamar yadda kike yiwa Hamman Yusufa da Adda lndo, dama kin kusa mutuwa shikenan idan kika mutu sai ajefaki ashara sai tsutsotsi su cinye naman jikinki kinga shikenan kowa yahuta da masifarki takarashe fadi tareda yimata๐dai-dai lokacin da Lanti tajefa mata mafici tana cewa toh" shegiya me mugun fata bakin ki yasari danyan kashi, saidai ina bata same taba domin tuni mairo tafalla da gudu, yayinda lnna Rakiya ta daga kai dakarfi cikin matsanancin tashin hankali da karka tattacce bakinta dake tafaman zubar da miyau tace.....
_*Washhhhhh! ๐คฆ๐ฝโโnagaji saidai kuma yaseen naji zaki๐tunda nacika alkawari so*_
Muje zuwa
A
_*KYAUTAR ALLAH CE* (Labarin Sadeeya)_
Tareda
โ๐ฝ
๐นLufhat๐น
[7/2, 11:27 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
9โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*Ga SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
*_WANNAN_* page nakike ke kadai nabawa *_KYAUTAR shi my Aunty JIDDA BALA_* kiyi yadda kikeso dashi kisani inayinki irin babu din nan fa๐.
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
E....e.....eeeeeh......nahhh....isuhun yake?????.. dasauri Lanti ta matsa kusa da ita sosai fuskarta dauke da fara'a tace Alhamdulillahi yau lnna tayi magana sannu lnna yajiki..?
Bata amsa sannun ba saidai cikin gurbatacciyar murya tace nace ina isuhun" yake...? Lanti tace lnna ki kyale waccan yar banza yarinyar me kama da kazar mayu, karya take ba Yusufa bane, cikin masifa tace ba karya "take ba naji'ajikina cewa "shine don haka tashi ki kiramani shi na nemi gafararsa" tunkafin na mutu domin wannan ciwo bazaya barni ba,
Cikin sanyi murya Lanti tace toh" lnna amma kibar fadin haka ai cuta ba mutuwa bace, tace kayya kedai tashi kidubo shi kar yatafi ban roki gafarar shi ba, jiki asanyaye tamike tareda cewa toh" Inna, tana fita tsakar gida saitaji sallama don haka sai ta tsaya.
Da sallama Yusufa yashiga gidan lndon nabiye dashi yayinda su Alh ke biye dasu a baya, Lantin kam mamaki ne yakamata naganin da gaske ashe Yusufan din ne abunda batayi zato ba,
Don haka dasauri takoma daki tana cewa lnna ashe mairo da gaske take ga Yusufa nan yadawo, kokarin tashi lnna Rakiyan takeyi tana cewa ina yake isuhu..? dasauri Lanti ta matsa gurinta tareda dagata tasa mata filo a bayanta yadda zataji dadin jingina tana cewa gashi nan waje bari nace sushigo,
Shi kam Yusufa tsaye yayi cak! yana kallon garken shunu wayanda basufi guda goma ba, juyawa yayi fuskarshi dauke da matsanancin mamaki ya kalli lndo wacce itama fuskarta daukeda mamaki take kallon shi, harzayayi magana sai ga Lanti tafito fuskarta daukeda farinciki tana cewa sannun ku dazuwa Yusufa ku karaso mana bari na dauko shinfida, dasauri yace toh" Adda Lanti Alh ku karaso, sukace toh" tareda karasa shiga daga ciki dai-dai lokacin da Lanti tadauko babbar tabarma,
_Lanti kam tayi haka ne domin dakin babu abunda yakeyi sai tashin wari da tsami, wanda bakowa ne zaya iya shiga dakin ba_
tashin fida masu, tana tayi masu sannu dazuwa bayan sun zazzauna sai takawo masu ruwa suka sha sannan tazauna suka gaisa
Bayan sun gama gaisawa, sai Yusufa ya gabarar da Alh da iyalain, sannan yace Adda Lanti lnna Rakiya banganta ba sannan kuma meya faru naga duk shanu sun kare...? Kuka Lanti tafashe dashi tareda cewa Yusufa maganar shanu labari ne me tsawo,
Sannan lnna kuma tana cikin daki batada lafiya tsawon wata uku kema bata iyafita ko'ina don haka kashiga kaga yadda Allah yamaida ita, wanda kuma nasan alhakin Kane ya kamata harma damu gaba daya,
Jiki asanyaye Yusufa yamike tareda cewa Alh kushigo bamusu suka shiga dakin saidai kuma tuni suka fara toshe hanci saboda wari, da sauri *Habeeb* yajuya yafita daga daki hannun sa toshe da hancinsa yayinda yan'uwansa suka rufa masa baya, domin shi mutun ne da yatsani wari arayuwar sa, suna fita tsakar gidan *Habeeb* yasaki ajiyar zuciya, dariya Rahma tayi harara yawatsa mata aikam tuni ta tohe bakinta domin tasan shi baya son raini,
Suma su Abba Bayan sun gaida lnna sai suka fito don da alama bazasu jure shakar wannan warin ba.
Shi kam Yusufa ya tsorata dagani yadda lnna Rakiya takoma cikin watanni