Showing 87001 words to 90000 words out of 163788 words

Chapter 30 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt

11 Jul 2024

32378

tareda cewa a ah *Habeebu* ne?..yace "eh Baffa ni ne mun same ku lafiya?.. yafadi yana zama lnna tace lafiya lau, cikin girmama wa ya gaida su suka amsa tareda tambayar shi ya aiki?..yace lafiya lau, nan ma saida Baffa yai masa nasiha, bai dade ba yafita.




Saida ya tsaya yadauki wayoyin sa da ledar maganin da yabari a mota sannan yanufi part din *Harees.*


A falon kasa ya'iske su *Feeya* kwance akan cinyar *Harees* sallamar *Habeeb* din ce yasata tashi cike da kunya, ta gaida shi bayan ya amsa sai tace Hmm *Habeeb*
Awani part my sweet *"Deeya* take?..yace tana part din Hajiyarmu, mikewa tayi tareda cewa yauwa to bari naje dasauri suka hada baki sukace ina zaki?..ahankali tace gurin my sweet *"Deeya,* hararan ta *Habeeb* yayi tareda cewa baki da hankali ne kina dauke da baby shine zaki fita yanzu da daren nan?..




*Harees* mikewa yayi tareda cewa yi hakuri me Darajata ki taimake ni kibari saida safe, koki kirata a waya ma kawai sai kuyi magana kinji?..tace to ai nakira wayar "ta akashe, *Habeeb* yace kira layin "Hajiyar mu ta hadaki da "ita kice nace" tabude wayar ta idan nata so zan kiranta, tace to tareda daukar wayar ta dake kan table tanufi sama.




Zama sukayi lokaci daya *Harees* yana cewa dan'uwa ya'akayi ne?.. *Habeeb* yace dai-dai, yace to ya zazzabi?..ko dayake "Queen of beauty ta kori zazzabin ko?..ya kareshe fadi yana dariya, murmushi *Habeeb* yayi me kayatar wa tareda cewa hmm aikam in fada maka koran kyau *"Leemah* ta tayi wa zazzabi nan, shiyasa nima nazo kayi mun bayanin yadda zanyi amfani da magungunan don nakori wannan ciwon da aka lakamani da wuri ko nasamu damar cin amarcina,




Kai! dan'uwa *"Jana* ta zalunce ni dayawa fa ko kasan hutun one month na dauko don nazo naci amarcina da kyau, amma sai wannan azzalumar "ta lakamun ciwo wanda zaya hanani cin amarcina kamar yadda nayi buri.




Kafadar shi *Harees* yafada
yace kayi hakuri dan'uwa, *"Jana* Kanta a ta zalunta ba kai ba amarci kuma zakaci yadda ka keso kaidai kayi amfani da magungunan nan insha'allahu bazaka wuce two week ba karabu da ciwon kaji?..Kai *Habeeb* ya gyada masa, sannan yayi mashi bayanin yadda zayai amfani da magungunan,
bayan yagama fada masa.




Sai *Habeeb* yace kai Dan'uwa kasan abunda *"Jana* tace" a gaban "Abba kuwa?. yace a ah,yace hmm wai shiya kiramu yayi yai mana fada kawai sai tace.. nan dai yafada masa abunda yafaru,




Murmushi yayi tareda cewa su *"Jana* manya
yanzu itafa atunanin ta bakasan abunda
ta'aikata ba ko?..
yace "eh dayake itadin sha sha sha ce bashi yasa har take maganar
raba kwana, batasan dazuta mugun kaini bango bane shiyasa nashaki wuyan ta inba dan haka ba ai ko yatsarta bana fatan sake taba wa, balle har na sake had'a jiki da'ita wancan da Allah ya kaddare ni nayi ya'isa.




*Harees* yace hakane to Allah ya kyauta to kai yanzu idan kwanan yaza gayo "kanta yaza kayi?..tsaki yayi mtww yace sai nace bana ra'ayin yi idan kuma za'a saniyi dole ne to saina gani, dariya *Harees* yayi tareda cewa dan'uwa baka da kyaufa amma dai zaka horata, yace batta kawai ai saina gasa "mata gyada ahannu kafin iddarta yacika nan dai suka cigaba da tattaunawa.




Cikin daki Hajiya da *Deeya* suka kule inda take sakeyi mata huduba data rike mijinta da kyau tayi masa biyayya, ta kula da duk abunda yake so takuma kiyaye wanda bayaso, domin "shi me hakuri ne saidai idan aka kureshi to fa sai ahankali do haka ta kula da hakan, sanna ta kula da cikin "shi domin shidin acici ne baya wasa da cikin sa dariya *Deeya* tayi tareda cewa kai Hajiyar mu "Hmm din nawa ne acici?..




tace "eh aikin san haka don haka sai ki kula sosai, sai shinfid'ar sa shima ki kula dashi da kyau, tace to Hajiyar mu ai zan din ga gyara masa kamar yadda nake gyara maki naki ko?..murmushi tayi domin ta fahimci *Deeya* bata gane inda tado saba, "eh kawai tace domin tasa nan gaba kad'an zata gane sannan ta cigaba da fada mata abubuwa masu mahimmanci da zata kula dasu agidan auren ta, bayan tagama sai ta tashi taje ta dauko mata wani hadadden tsumi acikin cup ta bata, fuska taya mutsa tareda karban cup din a zaton ta magani ne me d'aci




dariya Hajiya tayi tareda cewa sanye ki bani cup, ahankali ta kafa cup din a baki tareda rintse ido sannan tafara sha, dadin dataji ne yasata waro ido tareda sake bude d'an mitsitsin bakin ta, ta nasha sosai wanda saida ta shanye tas sannan ta cire cup din tana lasan baki tareda lumshe ido,




Tace umh dadi idan akwai akara mun, dariya Hajiya tayi tace yana nan dayawa nata nade shi domin ke do haka duk lokacin daki ka tashi kizo ki sha, tace yauwa Hajiya ta nagode daga nan suka cigaba da fira.




Can saiga kiran *Feeya* ta wayar Hajiya murmushi Hajiyar tayi tareda cewa *Deeya* dauki wayar nan Auta ce nasan dake take san magana, dasauri tadauka tareda cewa Oh! my sweet *Feeya* am so sorry kinji waya ta akashe KO?.. tace wlhy to ya'akayi ne?.. tace dai-dai daga nan suka fara fira, wanda sun dauki tsawan lokaci suna yi saida Hajiya tayi masu magana sannan suka kashe wayoyi,




bayan tafada mata Hmm *Habeeb* yace" ta kun na waya zaya kiran ta,




Key Hajiya tabata tareda cewa ga makullin dakin ki nan don haka tashi kitafi Allah yatashe mu lafiya, tace to tareda kar batayi mata saida safe sannan tafita.




part dinsu ta nufa alokacin 11:30pm dai-dai na dare, DA sallama tashiga falon dai-dai lokacin su Baffa suka mike zasu shiga bacci, ganin ta yasa suka tsaya cikin mamaki Baffa yace *KYAUTAR ALLAH* daga ina kika fito haka?.. tace part din "Hajiyarmu, yace me ki kazoyi nan din?..ido tazaro cike da tsoron jin abunda Baffa yace" sai kuma tayi shuru tana kallon shi, domin wani irin kwarjini Baffa yai mata wanda yasa takasa cewa komai ahankali tadukar dakai tana wasa daya tsunta.




Saida yasake tambayar ta sannan ta dago kai tareda turo baki tace ayya Baffana nazo ganin kune fa, yace dayake mudin bakine agurin ki ko?.. cikin kwantar da murya yace haba *KYAUTA* yanzu fa karfe 11 :30pm amma sai yawo kike ba tareda kin zauna dakin kiba to idan "mijinki yazo bai'iske kiba fa?, cikin sanyi murya tace to ai Hmm *Habeeb* din ba yana nan,




Dasauri lnna tace tunda bayana nan sai akace kiyi ta yawon bi shiya-shiya KO?.. tace to ai yace" idan yadawo zaya kirani, lnna tace to kije dakin ki ki zauna ya'iske ki acan ba sai yadawo yana kiran kiba har zatayi magana, Baffa yace jeki dakin ki *KYAUTA* Allah yatashi mu lafiya karki sake fitowa a irin wannan lokacin kinji ko?..




ahankali tace to saida safen ku lnna tace Allah yatashi mu lafiya
kuma karki sake shigo mana shiya ba tareda izinin "mijinki ba kinjiko?...tace to tareda fita.




Ahankali take tafiya tamkar kazar da kwai yafashe wa aciki, tunani take aranta yanzu shikenan ta daina kwana part dinsu Dana Hajiyarmu, sai ana Hmm *Habeeb* hawaye ne suka zubo mata.




Karar wayar ta ne yakatse mata tunanin datake tareda tsaya wa, ahankali ta bude jaka taciro wayar
Hmm dina ne ya bayyana akan wayar, cikin kuka tadaga tace Hmm dina kadawo ne?..gaban shine yafadi jin tana kuka don haka da saurin yace *Leemah* ta kuka kike mesa meki wane ya taba mun ke?... Duk alokaci daya yajero mata wayan nan tambayoye yin tareda kokarin shi
gowa harabar gidan,




Tafiya ta farayi ahankali still wayar tana kunna cikin kuka zata fara yi masa ba yani, dasauri yace gani nan zuwa *Leemah* ta juyoma kiganni;
Ahankali ta juyo tundaga ne sayake sakar mata kyakkyawa murmushi, cikin takun kasaita yanufe ta tareda bud'e hannu wan shi alamar taje gareshi aikam cikin sassarfa tafad'a faffad'an kirjinshi tareda sakin kuka me cike da shagwab'a.




Ajiyar zuciya yayi tareda yarintse ido domin jin kukan ta yayi har cikin ranshi.




Ahankali yace Oh! my Lovely *Leemah* me yafaru wanene yasa mun ke kuka
yi shuru ki fadamun kinji?..cike da shagwaba tace to ba "Baffana da lnnata bace daga nashiga ganin su "KO zama banyi ba shine suka koroni, murmushi yayi sai kuma yace Kai!Kai!!Kai!! yanzu Baffa da Inna ne suka koroki?..tace "eh,




yace to saboda me?.tace wai dare yayi na tafi dakina, yace ayya *Leemah* ta to kiyi hakuri kibari da safe sai kije kinga su ko?.. yafadi tareda da go kanta daga kirjin shi, yana me share mata hawaye tareda kallon kwayar idon ta yana jin SONTA yana bin jinin shi, baki ta turo tareda cewa to ai "lnna tace" karna sake shiga part dinsu" ba tareda izini ka ba,




yace karki damu *Leemah* ta indai nine tona lamunce maki duk lokacin daki
ka tashi ki shiga duk part din daki keso ko'i na nan ko bana nan kinji ko?.. Cike da farin ciki tace to har da part dinsu my sweet *"Feeya?..* yace "eh amma ban yadda kiringa zuwa da dare ba,




Cike da murna tace yauwa hmm Dina nagode yace to muje mu kwanta yafadi tareda daga ta sama yanufi part dinsu, dariya ta kyalkyace dashi tareda kwakume shi cike da shagwaba tace wayyo Hmm Dina zan fadi dariya shima yayi tareda cewa ba zaki fadi *Leemah* ta
Dai-dai lokacin da suka shiga falon.




Dasauri
*Jana* dake zaune tamike ta tari gaban su, sanye take da wata yar figigiyar riga bacci iya guiwa kanta yarbatsai-yarbatsai, kallon ta *Habeeb* yayi
sama da kasa yayinda *Deeya* mata ke bintada kallo fuska daure yace lafiya kika tare mana hanya?.. tace dama ku nakejira da tun dazu, cike da mamakin ta yace...








Muje zuwa






A




*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)




Tareda




โœ๐Ÿพ




๐ŸŒนMeenat๐ŸŒน
[7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ


_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_


๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ




5โƒฃ4โƒฃ




WRITTEN
By
๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ


OR


๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ




SADAUKARWA


*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*


___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~








โœ๐Ÿฝ






_*Bismillahirrahamanirraheem*_






_NOT EDITS_




Kamar ya mu kike jira tace "eh kuna kejira, yace to gamu saiki fadi abunda za muyi maki dakike zaman jiranmu tun dazu kinji ko?..tace "eh saboda gaskiya niban yadda sai kayi kwana bakwai adakin ta ba sannan kaje dakina, yace to sai me don baki yadda ba?..tayi shuru cikin tsawa yasake cewa nace to sai me don baki yadda ba eyeee?... Dasauri ta dan matsa baya kadan tareda cewa atoba sai abar shi akwana biyu-biyu ba, inba dai so ake aci amana taba yaza'ai ace sai ka kwana bakwai adakin ta sannan kazo dakina gaskiya bazan yadda ba ehee, Cikin bacin rai yace to kar Allah yasaki yadda kinji KO?..waima angaya maki Ina neman yaddar kine?..to bari kiji nagaya maki koki yadda ko karki yadda babu abunda ya dameni kinji ko?..domin ke baki isa kiyi jayayya da fadin Allah ba haka kuma baki isaki haramta mun abunda Allah ya halasta mun ba kinji KO?




Yar rainin hankali kawai me yasa acan gaban su" Abba bakice baki yadda ba sai nan saboda kin raina niko?..to kisani ni *Habeeb* nafi karfin raini agurin ki wlhy kuma baza'a barshi akwana biyu-biyun ba sai nayi kwana bakwan yar bakin ciki inyaso duk abunda zakiyi sai kiyi kuma na rantse da sarkin daya busamun numfashi idan ki kasake kirana da maciyi amana zakisha mamaki, zaki bani guri na wuce KO sai nayi ball dake agurin nan eyeee?..
ya kareshe fadi da karfi.




Aikam da sauri ta masa gefe yanufi dakin shi rungume da *Deeya* wacce tasake kwa'k'ume shi saboda tsoron tsawar da ya bugawa *Jana,* ltakam *Jana* bin bayan su tayi da kallo zuciyarta Cike da mamakin abubuwan da *Habeeb* yake mata tareda tambayar kanta wai shin meyasa *BB* tan yake mata haka ne?..to kodon yaga yayi sabon aure ne?..Oho! mashi kwaf tayi tareda hawa sama tana fadin aiza kagama kwana bakwan ne zakazo kasa meni.



*Habeeb* kam bai dire *Deeya* ko'ina ba sai bedroom dinsa akan katafaran gadon shi tareda yimata runfa, dariya yake mata sosai ganin yadda ta k'wak'ume shi kamar wacce akace za'akama, gaba daya hannu wanta ta zagaye bayan shi dasu yayinda ta tura fuskar ta afaffad'an kirjin shi sai sauke ajiyar zuciya take tareda shakar dadd'adan kamshin turanan shi, ahankali yazare hijab din ta.




Cike da shaukin kaunar ta yace Kai! *Leemah* ta kin cika tsoro dayawa yanzu d'an wannan tsawar danayi ma *"Jana* shiya baki tsoro?..Cike da shagwaba tace Hmm dina ni banason tsawa tsoro take bani, ahankali yake goga sajen sa afuskarta yanajin wani irin sonta da sha'awarta suna bin sassan jikin shi, cikin cool voice yace am so sorry *Leemah* ta zan kiyaye yinta a gaban ki tunda bakiso kinji?.. idon ta lumshe tace to.




"Ahankali ya cigaba da goga mata sajen shi afuskar ta yayinda yasa hannun daya yazame ribbon dinta tareda cusa hannun shin cikin lallausan suman kanta yana, ya mustawa yanajin wani irin ma tsanancin feeling dinta har gangar jikinshi yana bukatar ya kusance ta" saidai kuma aranshi yanajin bazaya iya kusantar *Leemarsa* ba alhalin yana dauke da wannan ciwon wanda dazaran ya kusance to itama zata dauka ne shikuma ba zayaso haka ba.




Sannu ahankali yahad'e bakin su yafara tsotsa, wanda yake ganin haka ne kadai zaya rage mashi abunda yakeji game da'ita, saida yadauki tsawon wani lokacin sannan yacire bakin shi daga nata yana sauke numfashi da sauri da sauri. ahankali, tace Hmm Dina inajin bacci cikin wata rikitacciyar murya yace to *Leemah* ta, bari nayi wanka sai narakaki dakin ki ki kwanta amma kema zakiyi wankan KO?...tace "eh yace to bari nashiga nafito sai kema kishiga ko?..tace to,




Ahankali yatashi tareda dagata yana gyara mata sumanta datuni ya wargaza shi saida yasa ribbon din yadaure mata sannan yashiga toilet. Be dade ba yafito daure da towel yace tashiga itama bata dade ba tafito daureda towel, tsaye ta'iske shi jikin mirror yana saye da rigar bacci irin me igiyar nan ta gefe, yana kum din kanshi sai kamshi yake zubawa murmushi yasakar mata ta mirror, itama murmushi tayi Cike da kunya tareda dukar dakai kasa, ajiye kum din yayi tareda juyawa yanufe ta yana fadin *Leemah* ta kinfito? ahankali tace "eh, yace OK" to muje narakaki ki kasa kayan baccin sai ki kwanta yafadi tareda daukar hijab din ta, tace to tareda daukar jakarta suka nufi dakin ta.




*Habeeb* ne ya ciro mata wasu riga da wando iya guiwa cike da kunya takesa kayan baccin, kasan cewar *Habeeb* yana zaune gefen gado yana kallon ta tunda har zata shiga toilet yace saidai ta tsaya tasa agaban shi dole ta tsaya ba dan ta so ba , Ahankali yamike yanufi gurin ta jawota ya rungume tareda cewa *Leemah* ta kinyi kyau sosai to ki kwanta saida safe kinji, tace to saidai ya kwantar da'ita tareda yimata addu'a sannan yarufa mata bargo yai kiss dinta agoshi sannan yamike zaya tafi,




Dasauri tarike masa hannu tace Hmm dina yanzu ni kada'ai zan kwana a daki?...yace"eh *Leemah* ta to ai bakomai, cike da shagwaba tace Aa Hmm Dina gaskiya nidai tsoro nakeji, dasauri yakoma ya zauna tareda cewa to *Leemah* ta ko zamuje dakina mu kwanta?.. ido tazaro tace kai! Hmm dina tareda kai zamu kwanta kenan fa?..




yace "eh mana to meye nifa mijinki ne ke kuma matata, shuru tayi batare da tace komai ba, yace to tashi muje mu kwanta can dakina kinji *Leemah* ta ahankali tace to amma kar kabari "Hajiyarmu tasani idan tasan tare muka kwana fada zatayi Mu kaji?.., dariya ce taku sa kwace masa amma sai ya dan ne yace kai! *Leemah* ta ai bazan bari tasani ba, tace to har da "Baffa da "lnna suma kar su sani kaji Hmm dina?..ta kareshe fadi tareda langab'ar dakai murmshi yayi tareda dagata ya rungume ahankali yace karki damu *Leemah* ta babu wanda zaya sani kinji?, tace to sannan suka fito yarufe kofar suka koma dakin shi suka haye faffad'en bed dinshi bayan yaimasu addu'a sannan ya rungume ta tsam ajikinsa tareda jan bargo ya rufe su, to asuba tagari *Habee-Leemat.*




****
Ado kam koda su Saminu suka fito dashi saida suka wuce unguwan ni biyar tsakanin fadaman madan sannan suka jefar dashi gefen wani bola suka tafi abun su, misalin karfe daya na dare wasu gayu su hudu sun dawo shar holiyar su suna tafiya suna wakokin su, na mashaya zasu wuce ta gefen bolar sai suka ji nishi kamar mutun dasauri daya daga cikin su yace kai! gayu baku jinishin mutun tagurin nan ba?..daya yace yaji dukkan su sukace sunji, nan daya ya kunna touch wayar sa suka haska aikam suka ga ado, duk daya sha duka ligis hakan bai hana daya daga cikin su yaga ne ado ba domin kuwa dasauri yace kai! wannan ai Oga adonjana ne _haka suke kiran shi_ suka rufu akanshi kokarin sance shi suke saidai duk sun kasa kasan cewar babu wani me sauran karfi acikin su, sai daya daga cikin su ne yaciro wuka acikin aljihun sa ya yake sauri wani irin ajiyar zuciya ya sauke na tsantsar wahala,




tambayar shi suke wanene yayi masa haka?.. amma tsabar azabar dayakeji yasashi kasa magana don haka sai suka dauke shi suka nufi gida dashi, inda biyu suka kama kafafu biyu kuma suka kama hannuwa suna tafiya suna faduwa kasan cewar duk abuge suke ahaka har suka isa gidan sa, suka jefar dashi suka b'ingire da bacci abinsu shikam ado be iyayin bacci ba domin yadda yaga rana haka yaga dare.




*_Bayan sati daya_*
******
A cikin sati dayan nan kuwa wani irin shakuwa ne yashiga tsakanin *Habeeb* da *Leemarsa* duk da cewa babu wani abunda yashiga tsanani su tafan ni auratayya, saidai hakan be hanasu jin kamar su cinye junan su ba dan so da kauna kasan cewar komai tare sukeyi bacce ne cin abinci ne, shiga kichin kai! har da wanka saida *Habeeb* yasan yadda suka koma yi tare tun tana jin kunya har ta daina,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login