Showing 75001 words to 78000 words out of 163788 words

Chapter 26 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt

11 Jul 2024

32373

hakan ne yasa shi mikewa Zumbur, tareda cewa *Leemah* ta me yafaru meyasa meki waya taba mun ke?..duk alokaci daya yajero mata wayan nan tambayoyin, cikin kuka tace Hmm *Habeeb* kaga wannan mutumin daga ganina wai shi yana sona ance masa ni matar aure ce, yace"wai ai irina yake so dakarfi yace _what?? am coming right now_ yafadi tareda kashe wayar,




Nan ya sallami mutanen wanda tare suka fita escorts dinsa suna ganin shi suka tashi mota uku suka cika, cikin abinda baifi
30 minutes ba sukai sa school din.




Kiranta yayi ya tambaye ta Ina suke tafada masa saiga su dasauri ta'isa gurin *Habeeb* tana nuna mashi saurayin dake tsaye sanye da wata ko daddiyar riga saida tasha guga da'alama guy din me tsafta ne, sai wani wargajejen wandon shi dayayi as level, gawata hular sa hana sallah daya mayar da gaba baya,




*Habeeb* kam kallon saurayin yayi wanda bai fi ya dauke shi da hannu daya yafed'ar ba, tsaki yayi aikam take yaji wani irin tsanar shi yadarsu azuciyar shi tareda wani azababban kishi, Cikin kuka *Deeya* tace Hmm *Habeeb* shine nan, yace Ok" sannan ya kalli escorts din sa Cikin bacin rai yace...









*_Kuyi hakuri da wannan wlhy waya tace ke dan bani matsala shiyasa typing din yake yin kadan._*








Muje zuwa


A


*_KYAUTAR ALLAH CE_*
( Labarin Sadeeya)


Tareda


โœ๐Ÿพ


๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน
[7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ


_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_


๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ




4โƒฃ7โƒฃ




WRITTEN
By
๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ


OR


๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ




SADAUKARWA


*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*


___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~








โœ๐Ÿฝ






_*Bismillahirrahamanirraheem*_






_NOT EDITS_






"Me kuka tsaya jira?.. cikin rashin fahimta daya daga cikin su yace _"Sir what are we going to do?.._ Cikin tsawa yace beat him, aikam tuni suka rufe shi da duka wanda yasa hankali mutane yayo kan su yayinda yafara ihun nai man taimako, saida kuma babu wanda yakawo masa dauki,




*Deeya* kam tana rungume agefen kafadar sa still kukan take ahankali me cike da bacin rai abunda saurayin nan yai mata, Wanda itakan aganin ta yai mugun cutar ta sosai.




Saida *Habeeb* ya tabbatar _guy_ din nan yadaku sannan yace su kyale shi, Sannan yace da mutun guda ya dauko shi aikam dasauri daya daga cikin su yadauki _guy_ din yasaba aka fada, Cikin bacin rai yace oya _follow me yace "Ok "Sir_ Cike da isa da takama yake taku Wanda hakan yasake bayyanar da kwarjinin sa da haibar sa, hannun *Deeya* na cikin nashi *Feeya* kuma tana biye da shi yayinda su kuma escorts din suke biye dasu.




Basu tsaya ko'ina ba sai office din shugaban makarantar, tunda babu inda *Habeeb* bai sani ba acikin school din ba, Cikin sa'a kuwa suka iske shi zaune yana rubuce-rubuce, yana ganin *Habeeb* ya mike zumbur Cike da girmama wa, duk dacewa mutumin ya girmi *Habeeb* din amma hakan bai hana shi bashi girma a matsayin shi na senetor ba, Cikin girmama wa yace ah! yallabai ne?.. sannu da zuwa yafadi yana nuna masa kujera, Bismillah! yallabai zauna mana ga kujere nan,




fuska murtuk *Habeeb* zauna tareda dora *Deeya* akan cinyar sa.




*_Nikam danake gefe ina dauko maku rahoto, ido nazaro cike da mamaki Habeeb tofa su BB kenan wato dai ita Leemah nan ba'a hadata dakowa ba lol._*




*Deeya* kam sarkin sanjiki kwantar da kanta tayi akan faffaden kirjinsa tana sauke ajiyar zuciyan kukan datayi, bayan shugaban makaran ta yakoma ya zauna sai yamika wa *Habeeb* hannu fuska murtuk ya mika masa nasa hannun suka gaisa, cikin girmamawa mutumin yace yallabai meke tafe dakai?...




Cikin bacin rai *Habeeb* yace wannan matata ce sannan yanuna *Feeya* dake tsaye yace wannan kuma kanwata Ce matar "dan'uwana ce, yau suka Fara zuwa school din nan shine wani _stupid guy_ yace" wai yanason matata kuma anfada masa matar aure Ce, shine yace wai ai irin ta yakeso Kai kaji fa?..dasauri yace subhalallahi! wanene shi?.. kallon escort din dasuka shi office din shiyayi, yace yaje yakira su,




Ai kam Dasauri escort din yafita zuwa kiran su kasan cewar dazasu shiga sai *Habeeb* yace su tsaya awajen office din.




Can sai gasu sun shigo dasauri *Habeeb* yace gashi nan don haka inason ajamasa kunne hawainiyar sa takiyayi ramata, KO" kallon matata yasakeyi zaya fuskaci mummunan hukunci daga kareni eheee.




Shikam shugaban makarantar sai Kallon _guy_ din yake wanda yaci duka sai numfashi yake fitarwa Da kyar, cikin harshen turanci yace da _guy_ din wani department yake?.. shuru bai amsa ba sai nishin wahala yake, Cikin tsawa yace badakai nake magana ba?.. cikin tsananin galabaita yace yallabai niban san abinda kake nufiba,




Cike da mamaki yake kallon shi cikin hausa yace bakajin turanci ne?..Kai _guy_ din yadaga, alamar "eh bai iya ba mamaki ne yasake kamashi don haka sai yace nace ne awani shahi kake karatu?.. yace yallabai niba dan makaranta bane, Dasauri yace _what_?.. cikin mamaki *Habeeb* yadoka masa tsawa tareda cewa to uban me kazoyi ciki makarantar?..




yace yallabai akwai samarin dasuke shigowa saboda wasu mata auren dasuke daukar su haya don subiya masu bukatar "su tahanyar kwanciya da su, sai subashi kudi to nima Ina daya daga cikin samarin.




Dasauri *Habeeb* da shugaban makarantar sukace a'uzubillahi!.




*_Wa'eyazubillahi! wannan wace irin masiface" ZINA da AURE ya elahi, wai meke damun wasu mata auren ne?...haba YAR'UWA duk bukatar ki da mijinki yake biya maki bai isheki ba?..har saikin sake BIYAN KUDIN KI don abiya maki wata bukatar, wacce take tattareda MASIFA da BALA'I, ya Allah kai mana tsari da aikata ZINA musamman ma da aure, wayan da kuma sukeyi Allah kashiryasu Ameen_*.




Cikin bacin rai *Habeeb* yace ya ilahee matar aure da ZINA?... _shame,_ shugaban school din yace kadai bari yallabai babban abin kunya ma kuwa, *Habeeb* yace yakamata ku dauki tsatsauran mataki akan irin wayan mutanan, yace kwarai kuwa kuma yau din nan zamu fara dauka *Habeeb* yace lallaikam,




yace don haka kayi hakuri kuma Insha'allah hakan bazaya sake faduwa ba, domin zamu dauki mataki akan su sosai kiyi hakuri kinji madan yafadi yana kallon *Deeya* dai-dai lokacin da *Habeeb* yatashi yana me rungume ta aka fadarsa, ahankali tace bakomai sannan sukai mai sallama suka fita.




Suna tafiya *Habeeb* ya nafada dacewa ai saida nace nahada kuda escort kikace "a ah saboda bakinjin magana ta ko?..to aiga irin tanan, cikin sanyi murya tace to kayi hakuri fuska had'e yace bazan yi ba, tace pls yace nakiya dai-dai lokacin da suka karasa gurin motocin su, tace pls now yace no cike da shagwaba tafara bubbuga kafa tana fadin nisai kayi hakuri,




shi dariya mata bashi yayinda yake jin *SONTA* yana fisgar shi jawota yayi ya rungume ba tareda shakkar komai ba, yace kai *Leemah* ta idan kina irin wannan abin zakisa na rigayin _hug_ dinki a gaban kowa fa, tace to bakai bane nace kayi hakuri kace ba zakayi ba, yace to zanyi amma da sharadin zan bar maku escort hudu tukun,




Dasauri tace kai Hmm *Habeeb* har hudu?..yace "eh idan kuma baki yadda ba to bazan hakura ba, baki ta tabe tareda kallon manya-manya escort din dake can gefe tsaye fuska murtuk, tace to na yadda amma dai ba motar mu zasu shiga bako?.. yace "aah waccan zasu shiga tace to shikenan yace yauwa *Leema* ta yafadi tareda yimata kiss agoshi, sannan yakira mutun hudu yace su kula dasu *Deeya* sannan ya sallame su yatafi.




*****
Saida karfe 4:30pm sannan su *Deeya* suka dawo gida har zata shiga part dinsu, sai Baffa yace mata ai lnna bata nan taje gidan goggon ta Lanti don haka sai tanufi part din Hajiya, wanka tashiga.




Tana fitowa gada toilet shikuma *Habeeb* yana shiga dakin, lallausan murmushi suka sakar ma juna yace student kun dawo?. tace "eh yace to ya studies din?..tace alhamdulillahi yace to masha'allah sai amaida hankali sannan duk wanda ku kaga zayai maku iskanci kuhada shida escort din nan suci ubansa ni nace,




Cike da farin ciki tace to Hmm *Habeeb* Allah na tsani irin mutanan nan, yace konima wlhy ai wawaye ne kazamai kawai, inban da kazanta meke cikin zina?.. ke! *Leemah* ta _we close this stupid chapter_ kinji?..tace gaskiya kam babu ko dadi firar, yace inafa.




Yauwa *Leemah* ta ina tason na tambaye ki amma dazaran mun hadu sai shaukin *SONKI* yasa na manta, yakara she fadi tareda kashi mata ido daya dariya tayi tareda cewa me zaka tambaye ni?..yace wayar ki fa?.. bakita turo tace tun yaushe ta bace a, abuja yace Oh! *Leemah* ta shine baki fadamun ba?..rai adan bace tace to aiba ka bani damar hakan ba, tafadi tana kokarin isa gurin dressing mirror.




Hannun ta yariko ahankali ta juyo suka hada ido wani irin kallo yake mata me cike da tsantsar *SONTA* DA sha'awarta, cikin sanyi murya yace sorry *Leemah* ta shirya muje na siya maki wata ke! ko guda nawa kike so zan siya maki kinji?.. dasauri tace really?.. yace yeap my *Leemah,* wani irin tsallan murna tayi tareda rungume shi aikam tuni yaimata masauki afaffadan kirjinshi
suna dariya sai kuma yafara yimata chakulkuli,




hakan yasa dariyar ta yakaru tana ta zillewa shikuma yana cigaba dayi mata chakulkulin, sunata dariya har suka fada kan bed sai kuma yafara sumbatar ta tako'ina cikin shaukin sonta, ahankali wasan ya chanja salo cikin wani irin yanayi yake aika mata da zafafan sakonni, Wanda yasa gaba daya kwakwalwar ta takasa dauka hakan ne yasa jikinsu yadauki rawa _especially_ ma ita aikam tuni tasaki kuka me cikeda tsoro da kuma rashin sabo,




ahankali yabar abunda yakeyi tareda da gokai cikin wata rikitacciyar murya yace menene *Leemah* ta?..murya tana rawa tace ni banason wannan abunda kakeyi mun, murmushi yayi yace to nabari kiyi shuru kibar kukan yafadi tareda koma wa gefe yana sauke numfashi,




Dasauri taja bedsheet ta rufe jikinta kasan cewar tuni yara batada towel din jikinta, cikin mutuwar jiki yamike yace ki shirya nima zan jena shirya kinji?...
kaita gyada sannan yafita baki ta turo tareda jawo towel ta daura sannan tashi tafara shiryawa.




****
Wani hadadden shop complex sukaje aikam suna shiga kallo ya koma kan su kasan cewar sunyi shiri kusan iri daya, *Deeya* tana sanye da wata roba gown blue ta dan Kama jikinta kadan sai tayi rolling Da bakin gyale tasa bakin glass tayi kyau sosai, shikuma *Habeeb* yana sanye da bakin wando da blue T-shirt sai yasa bakin glass, shima yayi kyau sosai, wata hadaddiya kuma tsadaddiyar waya ya siya mata saikuma ya siya masu laptops itada *Feeya* tareda wasu siyayya sannan suka dawo gida.




*_Bayan sati biyu_*
*******
Tuni *Habeeb* yakoma gurin aikin sa ya cigaba da gudanar da aikinsa, yayinda su *Deeya* ma suka cigaba dazuwa school din su cikin kwanciyar hankali Da escorts dinsu, agefe daya kuma Adda Mamu da Adda Rahma suna ta gyara ta harda Hajiya ma ba'a bar ta abaya ba gurin gyara hali dubun ta, shiwa waya kusan kullun sunayi itada *Habeeb* sosai suke soyawa ta waya especially ta video call Wanda tana gama kwalliya saita nuna masa sannan ta tafi school.




"Abangaren *Jana* kam tana ta holewar tada Ado yanzu ta dai zuwa gurinsa, saidai shine yake zuwa gurinta da irin shigar da yake ta bakaken kaya.




"Ayau Jumma'a kuma yaune akesa ran zuwan *Habeeb* kasan cewar bai samu zuwa satin da yawuce ba saboda ayyuka da sukai masa waya, kuma yau ne *Deeya* zata koma dakinta anyi mata gyara sosai tayi kyau har tagaji.




Misalin karfe 2:30pm *Habeeb*
ya'iso Bauchi yaso yafara shiga part din Hajiya, to amma hakan bai samu ba saboda mutane da ya'iske suna jiranshi, don haka sai daya sallama su tukun sannan yashiga suka gaisa da Hajiya sannan yake tambayar ta
*Deeya* tace ta part dinsu,tashi yayi yafita kamar zaya shiga part dinsu *Deeyar* sai kuma yafasa saka makon wani irin nauyin su Baffan dayaji yakama sa murmushi yayi tareda nufar part dinsa.




Yana shiga falon yaji wani irin faduwar gaba, ahankali yake takawa zuwa sama direct dakin *Jana* yanufa da ya hango sa abude, tun kafin yakara sa yafara jiyo wani irin sautin nishi me dauke da wasu surutai, ahankali yakara sa bakin kofar abinda idonsa yaganar masa ne yasashi juyawa dasauri, cikin wani irin azababben tsoro me dauke da tsanani tashin hankali yace...














*_Yeeeee๐Ÿ’ƒ๐Ÿป readers anzo gurin fa so ku bani buhuhunan comments, idan ba haka ba kuma nafasa eheeeee๐Ÿ˜‰._*








*_Barkanmu da Jumma'a_*






Muje zuwa




A


*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)




Tareda




โœ๐Ÿพ




๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน
[7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ


_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_


๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ


4โƒฃ8โƒฃ




WRITTEN
By
๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ


OR


๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ




SADAUKARWA


*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*


___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~








โœ๐Ÿฝ






_*Bismillahirrahamanirraheem*_






_NOT EDITS_






"A'uzubillahi! yah ilahee yau me zan gani agida na haka ni *Habeebullahi?..* wani irin rawa jikinsa yake har wayar dake hannushi takusa faduwa saboda tsantsan tashin hankali saka makon abinda idon sa ya gani, wato *Jana* da Ado tsirara akan gado suna aikana fasikancin su tsabar shakin masifa yasa sun manta basu rufe kofa ba,


Dagani ma sun da deyin nisa dabarin duniyar mutane suntafi duniyar kazamai marasa tsoron Allah sai nishi suke, tareda surutan banza wanda kanaji zaka fahimci basa cikin hayyacin su saboda tsabar masifa da bala'i dasuka sa kansu ciki.


*_Wa'eyazubillahiayya matan auren da kuke aikata ZINA da aure kunyi makan Ku adalci tareda mazajan Ku kuwa???..., nasan tabbas idan har ba'asa SON ZUCIYA ba to amsar itace A A lallai yar'uwa bakiyi makanki adalci ba,sanna bakiywa MIJIN Kl adalci ba, sannan kisani kece maciya AMANA ta farko A DUNIYA, domin cin Amana DA YAWA kinga yar'uwa da farko kinci AMANAR ALLAH mahaliccin ki, kinci Amanar AURE sunnar Annabi (S W A), kinci Amanar MUSULUNCI kinci Amanar IYAYANKI domin ba'irin TARBIYAR dasu baki bake nan and than kinci Amanar MIJIN KI Uban yayanki, kin gurb'ata masa zuri'a kin hada mas tsaftatattu da kazantattu, sannan suma yayanki kinci Amanar su domin kinbar masu abun fade da gori ga al'umma, kuma kisani duk dakin kasance UWA agaresu daga ranan dasuka san ke "mazinaciyace tofa daga ranan zasu" tsaneki har masuji dama bakeki ka HAIFE suba, don haka yake yar'uwa Ina me baki shawara dakiyi gaggawar daina ZINA domin itadin MASIFA CE BALA'I CE_* *_Hmm yar'uwa ZINA babbar BALA'I Ce wacce take TARWATSA Al'umma wlhy yar'uwa inda kinsan BALA'IN DA ZINA take dauke dashi na rantse da SARKIN daya busamun NUMFASHI dabaki aikata ZINA ba Allah ka tsaremu daga aikata ZINA masu aikata wa kuma ka shirya su ALFARMAN BIJAHI SAYYADIL WARA ameen._*




Ido yarintse cikin wata irin rikitacciyar murya yafurta yah ilahee kasa mafarki nake yi, Ina kuma rokon ka dakata Dani daga wannan mummunan mafarki, sai kuma yayi shuru nadan wani lokacin da'alama yanajiran ubangiji yafarkar dashi daga _bad dream_ din ne, saidai kuma me?..




sound din dayaji yana cigaba da moving shine ya tabbatar masa bafa mafarki yake ba is really, don haka ne yasake rintse idon shi domin baya fatan yasake ganin wannan mummunan kazanta, ahankali yafara tafiya zaya sauko.




Murya Lili mama Ce tadoki dodon kunnan shi hakan ne yasashi saurin bude idon shi dasuka rikid'e suka koma jajir tsabar tashin hankali daya shiga, hangota yayi sanye da riga ja me hannun shimi tanada hoton Tom and Jerry da wando baki iya kwauri kanta sanye da hula baka irin me tuntu taga ba tayi kyau sosai kamar furen fulawa, Cike da farin ciki take tako upstairs din tareda fadin Dady oyoyo bayan ta kuma Junior ne biye da ita,




gaban shine yafadi gani cewa zasu haune kuma idan har suka hauwo to tabbas zasuga abinda yagani, Wanda shi kuma baya fatan suga wannan kazantar musamman ma Lili data kacen me dan karan wayo da surutu, don haka da sauri yai wani irin mahaukacin juyawa idon shi rufe yakai hannu yajawo kofar ya rufe dai-dai lokacin da suka karasa hawowa.




Dasauri ta rungume shi cike da farin ciki tace Dady kadawo?..cikin wani irin murya yace nadawo Lilin Dady yafadi tareda shafa kanta Junior yace Dady sannu da dawowa, shima kan shiya shafa tareda daga mai kai alamar "eh Lili tace Dady Ina Aunty *"Jana* tafadi tana kokarin isa bakin kofa,




Dasauri *Habeeb* yariketa tareda cewa ayya Aunty *"Jana* kanta yana ciwo ta sha magani ta kwanta, fuska tabata alamar tausayawa ga maman ta ahankali tace Dady anyi mata alluna ne?..yace "eh mujen ku falon kasa Mu zauna KO?..suka ce "eh dom haka yasaka su gaba suka sauka kasa.




Suna zama lili tahaye kan cinyar sa tana wasa tareda daba shi labarin abinda Aunty *"Deeya* tayi mata, wai ita Ce takira meyin lalle fulawa tayi mata a hannu da kafa sannan ku tayi mata kicho kalli Dady tacire hulan aikam saiga yan kanana kitso masu kyau sun sha kalolin beat, mikewa yayi zumbur tareda zaunar da Lilin kan kushi sannan yashafa kan nata ba tareda ya kalla ba kamar yadda ta bukata saidai yace nice, domin gaba daya hankalin sa yana sama, aran shi kuma addu'a yake Allah yasa karsu fito su Lili sugan su,




can sai tace Dady me kacuyo mana kacuyo mana ice cream da sweet da chocolate? shuru bai amsa ba sai safa da marwa yake yana kallon saman benen, yayinda kallo daya Zakai masa ka fahimci yana cikin matsanancin tashin hankali duk sanyi ac falon hakan bai hana matsanacin gumi tsatsufo masa ta ko'ina ajikin saba, musamman ta wuyan rigan shaddar dayasa sky blue duk tajike da gumi yayinda yaketa share na goshin sa da hand kerchief, sai magana suke amma bayajin su da'alama yana tunanin yadda zaiyi ne kar su Lili suga su *Jana* da kuma irin hukunci daza yayima *Janar* da kwarton tane.




"Junior ne yai magana da dan karfi yace Dady kasiyo mana sweet?..Dasauri yace "eyeee Junior meka ce?..yace Dady kasiyo mana sweet ne?..yace Oh! Sorry Junior na manta amma ga kudi kuje uncle *"Hafeez*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login