Showing 6001 words to 9000 words out of 163788 words
Chapter 3 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt
siyaya ne wanda yai suna sosai acikin ta kuma ya kasan ce mutun ne mai matukar tausayin talakawa, gashi da kyauta don haka mutane suke matukar son shi domin yanayi masu yadda suke so, shiyasa ma duk kujerar daya nema sai yasamu don haka yarike matsayi iri-iri da ban, da ban harda governor yayi matarsa daya me suna Haj Rabi'atu amma ita yar nan cikin garin Bauchi ne.
Haj Rabi'atu takasa ce mace kyakkyawa me kyan hali wanda halinta yazama iri daya da mijinta, domin kuwa macece mai matukar hakuri tanada kirki sosai, bata kyamar talaka, sannan abin duniya bai rufe mata ido ba, ya'ya'nsu biyar maza biyu mata uku *Habeeb* shine babba wanda ya kasan ce mutun mai hakuri yanada kyauta sosai, halinsa sak irin na iyayansa,
Saidai yanada matukar zurfin ciki wanda duk yanda kaso kagane cikinsa Sam bazaka gane ba, amma duk da haka wani lokaci mahaifiyarsa tana gane cikinsa, sai me binsa Maryam wacce taci sunan mahaifiyar Abban su amma suna kiranta Adda mamu itama halinta irin na mahaifanta, sai Rahma sai Hafiz sannan auta *Safeeya*.
***********
_*Shekaru masu yawa dasuka wuce*_
A wani kauye mesuna *GUDUM FULANI* ayin wani attajirin bafulance mesuna Alh Isyaku yanada shanu sosai yanada mata biyu uwargida wadda suke kiranta lnna Rakiya tanada ya'ya' uku duk mata, Lanti da Harira da Mari sai amarya lnna Halima tanada d'a namiji daya mai suna yusufa wanda Lanti ce kawai ta girmi yusufa don awance lokaci anyi mata aure amma da Harira da Mari duk yusufa ya girmesu amma dayake matane alokacin suma ansa ranan aurensu dukkansu kasan cewar girmansu daya,
Inna Rakiya ta kasan ce masifaffiyar mata yayinda lnna Halima ta kasan ce mace mai hakuri, lnna Rakiya tana bala'in jin haushin lnna Halima da d'anta yusufa musamman dataga Alh isyaku yana matukar son yusufa, shiyasa take jin kamar ta kashe shi, tabi malamai da bokaye don ta raba Inna Halima da Alh isyaku amma takasa.
Don haka kullum gidan Alh isyaku cikin fada da tashin hankali yake, wanda kuma lnna Rakiya ce mai tada fadar duk dacewa ita Inna Halima bata biye mata amma kullum cikin masifa take, wanda abin yana matukar damun Alh isyaku saidai kuma ba yadda ya'iya da'ita domin itadin irin matan nan ne dasuke zama jaraba ga miji Kai! harda al'uma wanda bamai iyayin maganin su saidai Allah,
Haka dai akayi rayuwa agidan Alh isyaku da dadi ba dadi Kwatsam Wata ranan juma'a sai akawayi gari lnna Halima ta mutu, mutuwar data girgiza mutane musaman mijinta da d'anta domin lafiya lau aka kwanta, da'ita saidai kawai aka bude daki aka iske rai yayi alinsa, haka akayi jana'izarta akaita gidan ta na gaskiya. saidai kuma wani abin al'ajabi shine ranan da lnna Halima tayi kwana uku da rasuwa,
"toh aranan ne kuma Alh isyaku shima yarasu Allahu Akbar Allah mai ikon,
Aranan kam yusufu kamar zayayi hauka saboda tsabar tashin hankalin daya shiga Na rashin iyayansa alokacin daya, saidai kuma babu yadda ya'iya da abinda Allah ya kaddara masa sai hakuri, haka shima Alh isyaku aka kaisa gidan sa na gaskiya. Saidai kuma tun bayan mutuwar Alh isyaku da Inna Halima yusufa yake fuskar matsala agurin Inna Rakiya sannu ahankali tamai dashi tamkar bawa, duk wani aiki shita kesawa, harda aikin da ya kamata su Harira suyi amma saita nasashi yayi dayayi magana sai tace aure zasuyi kuma idan suka tafi shi zaya cigaba dayi don haka dole sa yayi, kiyo kuma dama shikeyinsa.
Bayan anyi auren su Harira sai aiki yakaru sosai saida kuma ahaka yake samun lokaci yana zuwa makaranta allo, ba tareda Inna Rakiya tasani ba ahaka har yasauke al'qur'ani, aranan dataji tayi masifa sosai tace wai ya munafurce ta tunda har yasauke al'qur'ani ba tareda tasani ba shidai baice komai ba, domin shi bama'aboci magana bane.
hakan yasata takarajin tsanarsa a zuciyarta domin tarasa yadda zatayi dashi duk hanyar datasan zatabi don taga bayansa tabi, amma abunya agagara don haka ta karaninka masa azabar wahalar aiki fiyeda Wanda yakeyi, ahaka rayuwa tamika duk sa'anninsa sunyi aure amma ban dashi duk yarinyar dayaje neman auren ta, sai taje gidansu yarinyar tace karsu kuskura suba shege yar'su domin shidin shege ne da cikinsa Halima tashiga gidan Alh Isyaku, abun mamaki shine babu Wanda ya karya ta wannan sharri da Inna Rakiya tayiwa Yusufa.
Haka Yusufa yacigaba da rayuwa cikin wahala yayinda yadaina Neman auren gaba daya, mlm Babuga wani bafullace ne yanada ya' maisuna lndo kyakkyawa ce mahaifiyarta tarasu "toh matar daya aura mai suna Larai saitana bata wahala shi kuma yarasa yadda zayayi da'ita domin itama halinta irin na lnna Rakiya ne, Wata rana yusufa yadawo kiyo saiya hadu da mlm Babuga sai yatsugun'na ya gaidashi cikin farin ciki ya amsa tareda cewa yusufa dama inason ganin ka,
Yusufa yace "toh Baffa gani Allah daiyasa lafiya? yace lafiya lau yusufa, nidai nayaba da hankalinka da kuma nutsuwar ka, don haka nayanke shawara daura maka auren ya'ta lndo, Yusufa yai shuru.
Mlm Babuga yace Yusufa naji kayi shuru kodai baka sonta ne?..dasauri yusufa yace wlhy Baffa Ina son ta saidai banida halin yin aure kuma kasan anceni din shegene, taya zaka aurawa yar'ka wanda bayada uba?.dasauri mlm Babuga yace kul! nasake jin kakira kanka shegene, waye bai sanan cewa Alh isyaku ne mahaifika bane?..saidai kawai a kifada saboda masifa Rakiya,
Don haka nidai nariga nabaka Indo kuma bana bukatar "KO sisinka dama dai sadaki shine aure ko?..yusufa yace "eh, yace "toh nizan baka gobe in Allah yakaimu kazo kofar gidan mai gari za'a daura auranka da "Indo kuma kar ka kuskura kafadawa Rakiya kabarta kawai saidai taganka da matar ka kaji ko?..,yace "toh Baffa nagode aranan yusufa kamar zayayi kuka saboda farin ciki don haka yaita zubawa mlm Babuga godiya.
Washegari juma'a aka daura auren Yusufa da Indo ba tareda anyi shela ba kuma Larai da Rakiya basu saniba, domin maigari yahana a fada masu, bayan angama daurin auren sai mlm Babuga yace da Yusufa yaje yagyara daki anjima yazo yadauki matar, yace Baffa ai dama dakin bawani gyara daza'ai masa yace "toh madallah anjima saikazo kadauki matarka kayanda zatayi aiki kuma zan kawo mata suda kaina, yace "toh Baffa nagode Allah yasa kasa alkhairi yace babu komai tashi katafi.
Bayan sallah isha'i Yusufa yaje yadauki matarsa lndo suka nufo gida, lnna Rakiya tana zaune atsakiyar gida tana cin abincin, suka shiga da sallama bata amsaba yusufa badamu ba domin yasan itadin bama'abuciya amsa sallama bace, don haka sai kawai suka nufi dakin shi cikin matsanancin mamaki tace kai! Yusufa,
Tsaya yayi tareda cewa na'ama Inna, tace "eh lallai abinda ake fada da gaske ne domin kuwa yau gashi har gidana za'ayi nagani, "toh wlhy baka'isaba kayi kad'a, gani inda zancenta yadosa yasa dasauri yace lnna Rakiya wlhy bana neman mata, cikin masifa tace Kai kaniyarka ga karuwa kashigo mun da'ita cikin gidana amma kace mun kai baka neman, mata..
yace lnna wlhy ba karuwa bace, duk da cikin duhu ne hakan bai hanata zagba masa harara ba tareda cewa, "Oho wato ita wannan din uwar kace "Halima tafifo daga kabari tabiyo kako?..cikin sanyi murya yace lnna Rakiya lndo ce yar'gurin Baffa Babuga dazu aka daura mana aure, cikin matsanancin bala'i da tashin hankali tamike tanufi gurinsa hartana kokarin faduwa tace..
Muje zuwa
A
_*KYAUTAR ALLAH CE*_(Labarin Sadeeya)
Tareda Alkalamin
โ๐ฝ
๐นLufhat ce๐น
[7/2, 11:26 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
6โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*ga SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
_*Wannan nan page gaba dayan sa nakine my sister Shafa'at, kiyi yadda kikeso dashi nagode sosai da kulawarki agareni inayinki irin over din nan fa*_๐
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
Kace me?..yace an daura mana aure dazu, cikin masifa tace kan uban can nizaka munafurta shine kayi aure ba tareda sani naba wato shanu na kadauka ka siyar kayi aure KO?.. "toh wlhy baka isaba sai kabiyani shanu na kuma bazaka zauna agidan nan ba...dasauri yace wlhy Inna ban daukar maki shanu ba KO daya ba, tace "toh ubanwa yabaka kudi kayi aure?.. yace wlhy Baffa Babuga yabani auren lndo ba tareda kosisi naba, tace "toh yayi kyau kutashi kufita mun agida.
Da sauri ya tsugun'na tareda cewa don Allah Inna kiyi hakuri, kirufa mun asiri kibarni Na zauna da matata kinsan cewa banida gidan daya wuce wannan, shewa tayi tareda cewa Allah sarki ai yanzu kam kanada gidan dayafi wannan, don haka kadauki matar taka kutafi can gidan ubanta daya baka aurenta Ku zauna agidansa amma banan ba, rokon ta yake akan tabarsa yazauna amma takiya, sai mafa man yimasa masifa take.
Aikam nan da nan gida yacika da mutane, ana tambayar meya faru Yusufa yafadi, nan akaita bata hakuri akan tabarshi ya zauna da matarsa amma tace Sam saidai yakoma can gurin "mlm Babuga kamar yadda yabasa mata "toh yabasa gurin zama, amma banan gidan taba.
Wasa-wasa saida aka Kai ruwa rana da lnna Rakiya sannan tabari suka shiga dakin, koshi saida maigari yazo yace idan bata kyalesu ba sai yafitar da ita daga garin sannan tabarsu.
Acan kuma gidan mlm Babuga Inna Larai tasashi gaba da masifa wai ya munafurce ta ya aurar da yar'sa ba tareda saninta ba, sai yace mata ai lokacin daya samu diyar bata sani ba don haka "KO aurar da'ita bai zama dole tasani ba, aiko tace Ina wuta tasa kashi saboda tsabar masifa shidai yace "Oho yarsace kuma ya aurar da'ita ga wanda yakeso.
Tunda misalin karfe hudu na asuba lnna Rakiya tadinga bugawa su Yusufa kofa su tashi, koda yabude kofa tana tsaye tana girgiza jiki cikin sanyi murya yace Inna lafiya?..harara ta zuba masa tareda cewa "toh ubana aisai kafito katafi kiyo KO?..da sauri yace haba Inna "KO sallafa ba ayiba tace "eh ainasani, zaya sakeyin magana tace shin zaka fito kosai nacimaka mutunci hakan yafito badan ranshi nasoba, yakora shanu zuwa kiwo, ita kuma lndo tace tafito tayi aikin gida.
Dagari ya waye mlm Babuga ya kawoma lndo kayanta tareda masu jera mata, inda lnna Rakiya take ta zuba ruwan masifa da bala'i sudai masu Jere basu tanka ba domin kowa tsoron ta yake bayan sungama sannan suka tafi.
Sannu ahankali lnna Rakiya tamaida Yusufa da lndo bayinta, shi wahalar kiyo ita kuma wahalar aikin gida da kuma tallar nono tun karfe hudu take tadasu barci su tatsi nonon shanu da lndo kezuwa talla, bayan sun gama shi yatafi kiyo ga shanun suna da yawa sosai wanda ya kamata ace akwai wani dake tayashi, ga kuma tumaki suma da yawa amma hakanan yake korasu zuwa kiyo.
Sannan ita kuma tayi aikin gida bayan tagama sai ta tafi talla, gashi bata basu wani abincin kirki duk sun rame sunyi baki su KO" dan kyan'nan da amarya da ango keyi su basu yi ba, yayinda ita kuma lnna Larai tazo taimasu rashin mutunci ta tafi.
********
A haka rayuwa tamika shekaru sunja don alokacin shekaran su biyar dayin aure, kuma alokacin tuni mlm Babuga yadade da rasuwa saka makon rashin lafiya dayayi Na tsawon shekara biyu, shiyasa suka sake shiga cikin kunci tunda dama shike taimaka masu dayan wasu abubuwa, kuma har wannan lokacin lndo ko batan wata bata tabayi ba domin lnna Rakiya tasha tace masu suda haihuwa saidai sugani anayi amma badaisu suyi ba, gori da habaici kuwa kusan kullum yimasu take musamman idan jikokinta sunzo wato ya'yansu Lanti, ba dama lndo tayi masu magana idan sunyi marna saita lnna Rakiya hautada masifa da ba'ai.
Da abin bai damu lndo ba amma gani lokaci yaja bata haihu ba, sai abin yafara damunta ita kuma tafara damun Yusufa, Saidai yace mata kiyi hakuri lndo kibar damuwa da'abunda lnna Rakiya take fadin akan mu, tabbas nasan inda lnna Rakiya ke bada haihuwa toh saidai muyi hakuri domin nasan bazata taba bamu ba, "toh sai kuma akayi sa'a ba'ita ke bayarwa ba Allah ke bayarwa don haka kisa aranki muma wata rana Allah yaza bamu kinji?..sai tace "toh.
haka rayuwa ta tafi ranan wata laraba cikin dare misalin karfe uku sai yusufa yatashi yayi sallah kamar yadda malamin sa yakoyar dashi, bayan ya'idar sai ya zauna yana kuka wanda sautin kukansa ne yatada lndo daga barci cikin sanyi murya ta tambaye shi lafiya yake kuka?..
yace mata yatuna iyayansa ne saitace "toh kayi masu addu'a mana yace nayi masu" sannan ina kuka ne akan irin wahalar da Inna take baki, nikam nariga nasaba amma kefa?..tace nima yanzu nasa ba yace hakane saidai nikuma hakuri na yagaza akan wahalar datake baki, don haka kitashi kihada mana kayan mu mubar kauyan gudun fulani, wadda tazamo mahaifarmu saidai kuma yau zamu barta kuma bari na har'abada domin banajin zamu dawo kauyan nan, tace "toh yanzu Ina zamuje?..
yace kar kidamu Allah yasani kedai tashi kihada mana kayan mu, tace "toh tareda tashi ta hada kayan ta kullesu adan kwalinta, dama ba komai dakin sai katifar su kasan cewar lnna Larai da Inna Rakiya duk sun kwashe kayan, don haka kayan sawarsu kawai suka dauka suka fita abinsu ba tareda lnna Rakiya tasani ba.
Sai kusan asuba suka isa cikin garin Bauchi lokacin anata kiraye-kirayen sallah, wata anguwa mai kyau suka fada akofar wani gida mai kyan gaske suka tsugun'na suna huta gajiyar tafiyar dasuka yi domin ba karamin tafiya sukayi ba, basu dade da tsugun'nawa ba sai gawani kyakkyawan mutun managarci yafito daga wannan gidan tareda wani d'an kyakkyawan saurayi, bakowa bane wannan mutumin face.
Alh Hashim soro bayan shi kuma *Habeeb* ne alokacin duk baifi shekara goma sha biyu zuwa sha uku ba, da'alama masallaci zasuje.
har zasu wuce su domin shi Alh Hashim soro Sam ba kula da mutane agurin ba, *Habeeb* ne yagansu yace Abba kaga wasu mutane anan, da sauri Abba yajuya aikam sai yaga mutane rakube jikin bango.
ahankali ya karasa kusada su yace bayin lafiya daga Ina kuke da'asubar fari haka?..Yusufa ne cikin gur'batacciyar hausarshi domin bawai ya'iyata sosai bane, yace Alh mu baki ne daga kauyen gudum fulani muke fito, yace Allah sarki sannun ku da hanya, yace yauwa Alh sannu yace "toh meke tafeda Ku?..yace Alh Labarin mu yanada tsawo, Abba yace Allah sarki zanso naji labarin ku "toh amma yanzu lokacin sallah ya gabato, don haka kazo muje muyi sallah idan mundawo sai mushiga gida matarka tayi sallah kai kuma saika bani Labarin ku KO?..
Yakarashe fadi fuskarta daukeda murmushi, shima yusufa murmushi yai tareda cewa "toh Alh mungode, sai Yusufa ya kalli lndo cikin harshen fullanci yace mata tafa zauna karta Kara matsawa ko'ina, tace "toh amma tanajin tsoro Yusufa zayai magana sai Abba yai sauri cikin harshen fullanci yace karki damu babu abinda zaya same ki insha'allahu, cikin matsanancin mamaki Yusufa yace....
Muje zuwa
A
_*KYAUTAR ALLAH CE*_(Labarin Sadeeya)
Tareda Alkalamin
โ๐ฝ
๐นLufhat๐น
[7/2, 11:27 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
7โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
_*ASSALAMU'ALAIKUM YAN'UWANA KUMA MASOYANA, DAFATAN KUNA CIKIN KOSHIN LAFIYA TAREDA IYALANKU ALLAH YASA HAKA AMEEN, MASOYA ALHAMDULILLAHI ANYIMUN OPERATION LAFIYA ANCIRE MUN CIWON DAKE DAMUNA, YANZU HAKA NASAMU SAUKI SOSAI WANDA HAR ALLAH YABANI IKON MIKA GODIYA TA AGAREKU AKAN IRIN ADDU'O'IN, DA KUKAITA KWARARA MUN, GASKIYA MASOYA SUNA DA MATUKAR DADI๐๐ฟ KAI! NI AMEENA UMAR FARUQ NAGA RUWAN MASOYA, KIRA AWAYA NE, TEXT NE ZUWA ASIBITI NE ZUWA GIDA NE KAI! BABU WANDA BANGANI BA, DON HAKA NAGODE KWARAI DA KULA WARKU AGARENI ALLAH YASAKA DA ALKHAIRI YABAR KAUNA DA ZUMUNCI MAI DOREWA, YAKUMA KARA MANA LAFIYA DA IMANI AMEEN.๐YAH ALLAH๐ INASAKE ROKONKA KA KARA BANI LAFIYA TARE DA DUKKAN WAYAN DABASU DA' LAFIYA WAYAN DA KUMA SUKE DA LAFIYAR ALLAH KA KARAMASU LAFIYA MAI INGANCI ALFARMAN ANNABIN RAHMA AMEEN YAH RABBI.*_๐๐๐
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirrahim*!_
Yace Alh ko kaima dai fulfulde ne?..murmushi Abba yayi tareda cewa tabbas nima bafullace ne gaba da baya, daga kauyan soro nazo neman ilimi sa kuma Allah ya kaddara mun nayi zama na acikin birni, saidai ina zuwa soro. cike da farin ciki Yusufa yace Allah nagode maka daka hadani da d'an'uwana bafullace.
murmushi Abba yayi tareda cewa ya sunan mlm din?..yace sunana Yusufa matata lndo Abba yace Allah sarki toh mlm Yusufa muje muyi sallah idan mun dawo saika bani Labarin ka" nima saina baka labairna KO?..yace toh Alh sannan suka nufi masallaci.
_Assalamu'alaikum_ Abba yai sallama acikin kayatattace falon nasu, yayinda Hajiya Rabi'atu ta amsa da _wa'alaikassamu_ dai-dai lokacin da tamike,
Ahankali take ninke abun sallah bayan ta kuma kyawawan yan' mata ne guda biyu yayinda yar karamar ke ninke abun sallah wacce shekarunta bai wuce shida ba, bakowa bace illa "Adda Rahma wacce ayanzu haka tana zaune a Tambari estate da mijinta babban soja da yaranta hudu mata biyu maza biyu Walida da Salma sai Salim da Walid, sai kuma babbar yar shekara takwas bakowa bace ita illa Maryam wato Adda mamu yanzu haka itama tana zaune a G R A da mijinta wanda yake babban alkali ne, da yaranta biyar maza biyu Hassan DA Hussain sai mata uku Husna Hafiza da Adawiyya sai tsohon ciki datake daukeda shi.
Hajiya tace kun dawo?.. Abba yace eh" muntashi lafiya tace lafiya lau *Habeeb* ma yace mun tashi lafiya tace lafiya lau, mamu ta matsa kusa da Abba tsugun na tareda cewa antashi Abba, kanta yadafa tareda cewa lafiya lau uwata. sannan tace *Hamman Habeeb* antashi lafiya?.. yace lafiya itama Rahma ta tsugun Na ta gaida Abba da *Habeeb* bayan ya amsa sai yace ku dauko Qur'ani muje afada mana karatu kafin lokacin makaranta yayi sukace toh" tareda nufar hanyar daki.
Zama Abba yayi adaya daga cikin kushin din falon yana cewa a ah *Na ALLAH*