Showing 162001 words to 163788 words out of 163788 words

Chapter 55 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt

11 Jul 2024

32376

hakur... dasauri Abba yace "a ah Alh Sani kar kace haka dama can Allah ya kaddari hakan sai yafaru, Baffa yace haka ne nan yai tayi ma baba nasiha




kai ya girgiza yace shikenan na gode mlm yusufa kai kuma Alh *Habeebu* Allah yaimaka albarka yanda ka rufa mata asiri Allah yarufa maka da zuri'ar ka baki daya, Alh mun gode sosai Allah ya'albarkaci zuri'ar ka gaba daya falon aka ce ameen sannan yamike yace to mu zamu koma su Baffa sukace to a sauka lafiya,




Da sauri yafita rai bace yayida ahalinsa suka tashi suka bishi *Jana* kam fuska duk ta kumbure dakyar take tafiya sai wai-wayen bayan ta, take tana kallon *Habeeb* Wanda bema san Allah yayi ruwan tsiyar taba.




Suna fita falon yakaure da hayaniya adda mamu tace Oh! daza'a hada mana zuri'a da bara gurbi, adda Rahma tace hum kedai bari *Feeya* tace ai aunty *"Jana* tayi asara arayuwar wlhy Kai Allah yasa Lilin Daddy bata nan,




sosai suke fadin albarkacin bakin su su hajiya da lnna suma suna ta tattaunawa akan wannan al'amari, tsawa Abba yadaka masu shiyasa sukai shuru, ita kam *Deeya* ba tace komai ba asalima hankalin ta yana kan *Habeeb.*




Ahankali yadaga Kai suka hada ido yasa kar mata lallausan murmushi ajiyar zuciya tayi tareda mayar mashi martani, dai-dai lokacin da abba yace kodai mene yari ga yafaru saidai muroki Allah yai mana tsari da shigowar irin su cikin zuri'ar mu,




sannan Allah ya shirya su da'aikata wannan mugun aikin mu kuma Allah yatsare Mu da'aika tashi arayuwar mu, suka ce ameen yace yauwa Baffan *Hafeez* ayi ma addu'a mu tashi yace to.




*_Bayan kwana biyu_*
*****
*Jana* taji sauki daga dukan data sha gurin jafaru yayinda gaba daya kuma baba da dija sun fita sha'anin ta, abinci ne kawai yazama dole abata gashi yanzu sosai ruwa dake fita agaban ta me wari yakaru harta kai inta zauna kusada mutun yanajin warin,




gawasu kuraje dake fito mata a jiki kome ya kwabe mata domin yanzu batada abokin shawara dama Shafa ce abokiryar shawaran ta da badala, to tun wani lokaci da mijin shafar yaka masu suna aikata madigo aikam yaima su dukan tsiya musamman ita Shafan sannan yasake ta ita kuma *Janar* yace idan takara zuwa gidan shi sai yasa yan'sanda sun kamata,




don haka sukayi fada da Shafa kaca-kaa domin tace ita ne ta kashe mata aure, don haka rayuwar yai mata tsanani kuma gashi bata daina wannan mugun mafarin ba yanzu har da Junior take mafarki yana kuka yana kiran sunan ta.




Kamar yanzu kwance take adakin ta ita kadai bacci take me cike da wahala firgigit ta farka sai gumi take tana zaran ido, takurarran hijab dinta tasa tafita batareda kowa ya saniba bata tsaya ko'ina ba sai gidan yari akafa don haka tayi mugun gajiya kasan cewar da ga unguwar su zuwa gidan yari danisa sosai,
sannan dakyar daroko suka fito mata da ado.




Yana ganin ta yace Kai shegiya tawajena haka kika koma meyasa me ki haka?.. ban zatayi dashi sai harara datake zuba mashi, dasauri yatoshe yace hum! *Jana* tusaki kayi haka?.. cike da haushi tace kashi nayi baki yatabe yace amma dai bakida lafiya ne ko?.. tace "eh yace ayya kema kin kusa mutuwa kenan,




kamar yanda nayi mafarki da kaka ta kusan mutuwa cabbb, kuna nufin tun yanzu zaku mutu?..lallai aiki yaganku nikam ba yanzu zan mutu ba wlhy kuttt! idan na mutu yanzu ai banyi wa kaina adalci ba domin zuciyata cike takeda abubuwa masu yawa, musamman daukar fansa kuma ba makawa sai na dauki fansa




don haka kinga mutuwa yanzu batawa bace ko?.. itakam bata iya ce masa komai ba sbd tsabar mamakin jin abinda yake fadi, yace haka ne KO?..Kai ta gyada domin lamarin shi tsoro yake bata yace yauwa kuda ku kashirya mutuwa yanzu sai kuyi ta mutuwa, amma kafin na kike gurin "kakata domin naji ajikina ita ce zata fara shurawa don haka kije unguwar jahun layi na biyu ki tambayi gidan "kaka Ladi masifaffiya,




tabaki D'ana kikai shigurin "dija ta'ajiye munshi kafin nafito nan da sati biyu na karbe shi tunda kema mutuwa zakiyi, idan kuma ki kai kuskuren kai shi gurin shegen *"BB* nan na rantse idan nafito sai na kashe duk azuri'ar ku na kashe *"BB* sannan na dauko D'ana, ido tazaro cike da tsoro dariyar mugun ta yasaki tareda juyawa yakoma.




Dasauri tafito tanufi unguwar jahun akafa kai aranan *Jana* ta wahala irin wanda bata taba yi arayuwar ta ba,




Kamar yanda ado yace haka tayi abin mamaki ce mata akai yau tarasu yanzu ma aka dawo kaita, cike da tsoro ta shiga gidan Junior yana ganin ta yazo dagudu ya rungumeta bayan ta zauna sun gaisa dayan kalilan mutan dake zaman makokin, sannan tafada masu itane maman Junior dama tazo daukar shine makociya iyalle tace Allah sarki *Jana* ba tadade bata karbi kayan Junior suka tafi,




Still akafa suka isa unguwarsu sun gaji sosai junior har da kuka yayi sbd tsabar gajiya suna shiga gida *Jana* tazube kasa sume, nan dija tayi kanta da gudu cikin tashi hankali ta dagota tana kiran sunan ta dai-dai lokacin da Jafaru yashigo dasauri, yadebo ruwa aka zuba mata amma bata farfado ba don haka suka dauke ta zuwa asibiti.




Asibiti ikitoci sunyi nasara ta farfado, saidai cikin wani masuyacin hali, domin kuwa wani irin ihu take tana fisgan naman jikinta musamman gaban ta sai surutu take barkatai da likitoci suka ga haka sai sukayi mata allura bacci.




*_Bayan sati biyu_*
*****
Ayau asabar ne aka saki su ado yabito xuciyar shi cike farin ciki da kuma kudirin daukar fansa, saidai kuma baikaga daukar fansan ba rai yayi halinsa,




domin kuwa yazo sallake titin dake gefen gidan yarn kenan sai wata babban tankin motar maita ta, takeshi murus sai tattara naman shi akai sannan akai mashi sallah aka kai shi gidan sa na gaskiya wanda yace be shirya zuwa yanzu ba, sai gashi yatafi bazato
hum yaruwa kenan,




kanataka allah natashi na Allah kuma shi ne gaskiya to Allah yasa muyi kyakkawan karshe amin,




Koda labari ya'iske su baba hankalin su yatashi sosai to yaza'ayi haka rayuwata ke,




*_su ado dai kam anzo duniya abanza ankoma awofi to Allah yai mana tsari da iri wann rayuwa._*




A banga ranan *Jana* kam ba sauki sai agurin Allah hauka tubura, likitoci sunyi bakin kokarisu don ganin tasamu lafiya tunda sungano tana dauke da cutar HIV,


sai suka dorata akan maganishi saidai kuma batashan maganin sbd fisge-fisgen datake, kwanata goma sha biyu asibiti suka sallame ta sukace suje suyina gargajiya.




Kwanan su biyar da komawa gida tarasu rasuwa me cike da tsoro da al'ajabi domin rainta be fitaba, saida taringa ihu tana fisgan gaban ta tareda fadi duk abin da tayi arayuwa sannan taroki iyayenta gafara da yan'uwanta sannan tace ace *BB* da *Deeya* suyafe mata abinda tayi masu sannan ta cika.




Sosai mutuwar *Jana* yataba iyayenta dasu *Habeeb Deeya* kam harda kuka tayi na tausayi ta, sunje gaisuwa baba yake fadawa *Habeeb* sakon *"Jana* yace shi aituni ya yafe mata allah yajikanta sannan yace yayi alkawari daukar nauyin karatun Junior,




tunda ga primary har university, su baba sunji dadi sosai suna tasa mashi albarka, bayan ya cika su da kudi da abinci sannan suka tafi zuciyoyin su cike jimami mutuwar *Jana.*




*_Hmm su Jana kam ayima duniya shigan zomo kasuwa, wato shiga da gudu fita da gudu batare da guzirin komai ba to Allah ya kyauta, yabamu ikon guziri na alkhairi amee._*






*_Bayan shekara daya_*
****
Haka rayuwa tamika tsakanin *Deeya* da *Habeeb* kwanciya hankali nutsuwa yawanzu a gares, sosai suke kaunar junan su tareda gudanar da soyayya su cikin aminci da yardan juna,




batare da tunani sake faruwar wani abin duk dacewa ana samu yan wasu kalubale akan siyasar *Habeeb* din, saidai addu'ar iyaye data su had'e data al'umma dasu ke matukar taimako tana tasiri sosai akan su,




*Haleem* da *Haneef* kam tuni aka yayesu kasan cewar da kansu suka daina shan nono, sbd sudi yarane masu kazar-kazar sunada kwarjini sosai da shigaran mutun tuni suke tafiyar su ko'ina basu cika zama part din suba,




saina *Feeya* wacce sukayi matukar sabawa da'ita, sai kuma part din hajiya dana lnna.




Ranan wata juma'a da misalin karfe
5:30pm, *Deeya* da *Feeya* ne zaune a falon *Deeyar* tun Bayan da suka gama tattaunawa akan business dinsu dasuke sanna sufara fira, kasan cewar yara suna part din Hajiya su kuma mazajen su sun tafi soro da gujun fulani kamar yanda su kasa ba,


Sosai suke fira cike da kaunar juna da aminci sanye suke da wani aren fakista me tsada dakyau, riga da wandon pencil kala royal blue da ratsin yellow sai sukayi rolling da gyalen sunyi kyau sosai.




*Habeeb* ne yashiga dai-dai lokacin da *Feeya* tace sweet *Deeya* mu kiyi family planning dakarfi yace what?..dasauri suka mike tareda fadin la! sannu da dawowa, harara yawatsa masu yace no wonder aketa kiran wayoyinku baku dagaba ashe kuna nan kuna shirya yanda zakuyi wa mutane illah ko?.




Dasauri ko wacce ta dauki wayarta dake cikin silent taduba aikam miss calls dayawa,baki suka bude tareda zaro ido hararan *Feeya* yayi yace bar part din nan kona fasa maki kai har sai likitan mijinki yai maki dinki, aika dagudu tafita tana dariya.




Wani irin kallo yaima *Deeya* sanna yajuya yanufi dakinshi cikin sassarfa Yake taka steps din, aikam da gudu tabishi cike da kwarewa take take steps din yana steps nakarshe ita tana steps na uku don haka tayi tsalle ta haye baya shi,




abuga tsayayyan namiji ko gezau beyiba asalima ajiyar zuciya yasaki sbd jinta ajikinsa, sannan ya gyara mata zama a bayan nashi sannan yashiga dakin har ya'isa bedroom ba tareda yace mata komai ba, cike da shagwaba tace Oh! oh! yau zakayi fushi da honey ka ne?..




yace umh ai har nayi tunda ba nason family planning shine ita zatayi so daga yau ni ba ruwa na da'ita, tace ayya sorry sweet hmm na ba zanyi bafa tunda baka so,kwantar da'ita yayi yai mata runfa sannan yace yauwa my honey karki kinji?..




tace to yace promise me tareda mika mata yar yatsa, itama yatsarta bashi tace yes I promise u dariya yayi yace yauwa tawan, to d'an taimaka mun nayiwa *Leem da Neef* kannai da trimple kinji? ido tazaro cike da tsoro tace wayyo sweet Hmm na yan uku fa?.




yace yeap tareda kashe mata ido daya pls taimaka mu kila Allah yabani sa'a na bugosu yau, baki ta turo cike da shagwaba zata sake magana yai dariya tareda had'e bakin su.






_To hmm *Habeeb* Allah yabada sa'a abugo yan'uku_😀








*_Alhamdulillahi a nan na kawo karshen Labarin KYAUTAR ALLAH CE inda nayi dai-dai allah yabamu lada nida masu karatu, inda kuma nayi kuskure Allah yayafe mana amee nagode sai mun had'e a sabon littafi na me suna ZAUJEE-MAJNUN_*


🌹Meenat Lufhat ce🌹

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login