Showing 15001 words to 18000 words out of 163788 words

Chapter 6 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt

11 Jul 2024

34795

dariya yace toh" ai da aljani da maye ko'ina kaje cikin duniya sai sunbika,


harara *Habeeb* ya Watsa masa yace au hakane..?.yace tabbas yace toh" shikenan duk aljanin da mayen da ya'isa ya biyo ni U.K idan banyi kasa-kasa dashi acan ba,


yace dalla nidai ka taso mutafi nagaji da maganar wannan aljanar yarinyar, yafadi tareda nufar kofa zaya fita yayinda *Harees* yabi bayanshi yana cewa hhhh! Yaro zakasha mamaki domin tabbas sai sun bika har U.K.


Washegari Jumma'a jirginsu *Habeeb* yatashi zuwa U.K.


*********
Akwana atashi ba wuya agurin Allah kwana kin sun tafi har zuwa shekaru, tun dasu *Habeeb* suka tafi basuzo hutu KO" sau daya ba, saidai waya kawai sukeyi da mutanan gida,


Haka zalika komai yafaru agida sai anfada masu har da minister da shugaban kasa yana Abba saida aka fada masu, tunda alokacin ya sauka daga kujere governor Wanda mutane Sam basu so ya sauka ba saboda adalcinsa agaresu,


A haka dai tafiya ta tafi har su *Habeeb* suka gama karatunsu, suka dawo cike da nasaran abinda sukaje nema,


sun zama cikakkun samari kwawa masu cike da kwarjini, sun iskesu su *Sadeeya* sunyi girma sosai inda suka koma *Deeya* da *Feeya* saboda yawan kallon India films Da sukeyi, anan ne sukaji sunan sai sukace wai ai sunan sune a kayan ke don haka suma deeya da feeya zasu ringa kiran junansu,


sun Fara zama yan mata tunda lokacin suna jss1 har sun mafara kirgen dangi,๐Ÿ˜œ mamaki sosai *Harees* yayi da ganin yadda suka girma, saifaman washe baki yake yana fadin gaskiya kannaina kunyi sauri girma me Hajiyarmu da lnna suke baku kunaci haka ne...?


dariya sukayi ba tareda sun ce komai ba, shima *Habeeb* mamaki yayi amma dai bece komai ba saidai kawai yatabe baki, ganin saifaman wani rawar kai sukeyi ko" don sunga yan wannan kushashin dasuka fara fito masu ne Oho!๐Ÿ˜‚kuji *Habeeb* fa.




**********
Bayan Wata daya da dawowar su sukafara aiki akamfani da Abba ya gina, cikin kwanciyar hankali suke gudanar da aikinsu, ranan wata alhamis sunfito cikin shirinsu nazuwa gurin aiki kamar yadda suka saba,


Cikin nutsuwa suke tafiya suna fira abunsu gwani sha'awa, har suka isa gurin ajiye motoci sai *Habeeb* yami kawa *Harees* key motar da zasu shiga, harara shi yayi tareda cewa wato kana nufin yauma nizanyi driving dimu..?Kai *Habeeb* ya gyada alamar "eh *Harees* yace toh" bazan yiba,


cikin sanyi murya yace haba nawa yi hakuri mana, *Harees* yace naki wayon *Habeeb* yace banajin dadi ne shiyasa kasan Allah ko" office dinma dole zanjeshi saboda takardun jiya daka kawo mun banga ma cika suba,


yace kuma saika cikasu ba murmushi yayi tareda cewa dolema, yanzu dai karbi kaja mutafi karban key yayi tareda cewa toh" wai meke damun kane...?


Maimakon yayi magana sai yasaki wata kara tareda rike ciki, saikuma yafadi kasa dasauri *Harees* yanufeshi saidai koda ya dagashi baya numfashi, cikin matsanancin tashin hankali yace...?








Muje zuwa






A






*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)








Tareda






โœ๐Ÿฝ






๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน
[7/2, 11:28 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ


_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_


๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ


1โƒฃ1โƒฃ




WRITTEN
By
๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ


OR


๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ




SADAUKARWA


*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*


___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~








โœ๐Ÿฝ




_*Bismillahirrahamanirraheem*_






Ba *MUTUM* bace toh" wacece...? yace aljanace ido ta zaro๐Ÿ˜ณ tareda cewa aljana kuma...? yace "eh Hajiya bakiga tsananin kyan datake dashi bane...? ajiyar zuciya tayi tareda sakin murmushi tace naganta tun dazu tabbas ita din kam kyakkyawa ce sosai tubarakallah masha'allah, saidai kuma ni banga wani Kaman datayi da'aljanu ba,


Da sauri yace gaskiya Hajiya yarinyar nan aljanace domin kyantan yayi yawa, da dai taga zaya cigaba da zuba mata wauta irin wacce kana ji zakasan cewa "eh shidin *D'AN FARI NE*, don haka saita daure fuska tareda cewa don kyanta yayi yawa shine zakace ita din aljana ce..? Cikin sanyi murya daganin yadda taba rai yace toh" Hajiya ai naji ance sune keda tsananin kyau fiyeda mutane,


tace kaga nifa banason wautan banza idan bazaka tayasu murna da *KYAUTAR* da ALLAH yabasu ba, toh" karka sake alakanta masu 'ya da aljana, shin wai kamanta tsawon shekarun da sukaiyi suna neman haihuwar ne...? yace a ah Hajiya toh" amma ita wannan din kamar ba mutun ba wlhy dana kalle ta saida naji tsoro, 'kura masa ido tayi na tsawon wani lokaci sannan tace hmm...toh" KO" mutun ce ita KO" ba mutun bace suna sonta haka tunda itadin *KYAUTAR ALLAH CE* da yabasu,


Daga haka kuma batasa ke cewa komai ba saidai kawai ta tashi ta'ajie jaririyar saman gado sannan tashige bayi,
shikam *Habeeb* da sauri yaje yadauki jaririyar da Hajiya ta ajiye shuru yayi nadan wani lokaci yana kallonta can kuma sai yace wannan dinma kyakkyawa ce sosai, saidai waccan tafita kyau,


toh"๐Ÿค” amma kuma meyasa ke banji irin abunda naji agurin waccan ba...? baki yatabe tareda ajiye jaririyar yanufi shashin shi.


************
Ranan suna jaririyar lnna taci suna *Haleematus Sadeeya* wanda Abba ne yai mata huduba da sunan wato sunan mahaifiyar Baffa wanda hakan ba karamin dadi yaima Baffan ba, ita kuma jaririyar Hajiya taci suna *Safeeya* wanda Abba ne yaba Baffa Yusufa umarni yasa mata sunan da duk yakeso toh" shine yasa mata *Safeeya* domin yana son sunan sosai shiyasa yasa mata, hakan nan dai aka gama suna cikin kwanciyar hankali, yayinda suka cigaba da rainon yaran su cikin kwanciyar hankali.




*_Bayan wata uku_*
Dayin suna Hajiya tana zaune saiga Inna tashiga da sallama tana rungume da *Sadeeya*, Hajiyar ta amsa sallamar fuskarta daukeda fara'a tace ah! Innan *Hafeez* kinshigo...? tace "eh zan shiga wanka ne shine nace bari na kawota, Hajiya tace toh" kawota idan kin fito sai nashiga tace toh" tareda mika mata *Sadeeya* dake ta sharan bacci abunta sannan Inna tafita, *KYAUTAR ALLAH* kenan hakanan Baffa yake cewa itama lnna saboda alkunya *KYAUTAR* take kiranta.



*Habeeb* ne shida *Harees* suka shiga falon Hajiya tsaye suka isketa tana jijjiga *Sadeeya* dake tafaman kuka ga kuma *Safeeya* kwance itama sai faman kukan take, da sauri *Harees* yanufi gurin *Safeeya* ya dauke ta tareda cewa Kai! yaran nan duk kun gigita mana Uwa, tace hmm! kadai Bari tun dazu kuke kukan nan nayi lallashi har nagani amma basuyi shuru ba, ga kukan nasu dazaran daya yafara sai kuma daya shima yafara, tafadi ne tareda mikawa *Habeeb* *Sadeeya* tareda cewa karbi *KYAUTA* kaita nasan yanzu lnnan tafito wanka,


jiyayi gaban shin yafadi sakamakon tunawa da abunda yaji lokacin da yafara daukar ta, kasan cewa tun ranan be sake daukar ta ba sai yau don haka cikin fargaba ya karbeta aikam tuni yaji irin abunda yaji din lokacin daya fara daukar ta, ahankali yace yah! ilahi! dai-dai lokacin da Hajiya takarbi *Safeeya* daga hannun *Harees* inda shikuma yace ma *Habeeb* muje daga can sai mutafi KO...? Kai kawai *Habeeb* ya gyada domin wani irin yakeji ajikinsa, aranshi kam fadi yake meyasa duk lokacin da yadauki *Sadeeya* saiyaji wani irin Abu nayawo acikin ajikinsa,
toh" wai *MEYE HAKA NE*...?


Suna fita dasauri ya mikawa *Harees* ita tareda cewa karbeta shikam *Harees* karbanta yayi ba tareda tunanin komai ba, *Habeeb* yace da kadauketa me kaji..? yace banji komai dasauri yace da gaske bakaji komai ajikinka ba..? yace "eh dasauri yasake karban *Sadeeyar* wacce har tayi shuru, amma saboda karban ta da *Habeeb* din yayi daga hannun *Harees* dasauri yasata saki kuka wanda hakan yanuna taji tsoro
ne,


shikam *Habeeb* abunda yake gudu shi yaji don haka jiki asanyaye yasake mika ta gurin *Harees* aran shi ko fadi yake wato shi kadai yake jin hakan kenan, kallon shi *Harees* din yayi tareda cewa menene...? cikin sanyi murya yace ba komai don Allah jeka kaita gurin lnnan kadawo mu tafi yace toh" bayan *Harees* din yakaita yafito sannan suka nufi shashin su yayinda jikinta *Habeeb* asanyaye.




*******
Sannu ahankali *Sadeeya* da *Safeeya* suka girma inda suka taso gwani sha'awa kamar tagwaye kasan cewar komai iri guda ake yi masu, Abba ma tagwayen Hajiya yake kiran su domin idan ka kallesu farar daya sai kaga kamar suna kama saidai *Sadeeya* tafi *Safeeya* kyau sosai, sun taso cikin tarbiyya me tsafta takowani bangare daga gurin lnna har gurin Hajiya wacce suke kira da Hajiyarmu, gawani irin kauna dasuke yiwa junansu naban mamaki gasu da dan kare wayo komai tare sukeyi, kasan cewar halayyarsu kusan daya saidai sun dan ban-banta tawasu gurare kadan,


kamar *Sadeeya* tanada matukar tsoro kamar farar kura ga d'an karen tsokana, sabanin *Safeeya* da batada tsoro kuma batada tsokana amma zama da *Sadeeya* yasa ta'iya sosai saidai kuma batada karfi amma tanada juriya, ita kuma *Sadeeya* tanada karfi saidai batada juriya domin abu kad'an sai yasata kuka, gasuda d'an karen shagwaba musamman ma *Sadeeya* wanda ita shgawabar a jininta yake.

Abangaren *Habeeb* kuma bai daina jin abunda yakeji ga me da *Sadeeya* ba muddun yaganta sai yaji faduwar gaba idan kuma har yai kuskure yadauke ta sai yaji wannan abu nabin jikinsa wanda yarasa dalilin dayasa yakejin hakan, tunda yagane haka sai yake gujema ganinta musamman ma kwayar idonun ta dasuke bashe tsoro toh" balle kuma daukar ta shikam tuni yadaina,


shekaran su *Sadeeya* biyar *Habeeb* da *Harees* suka gama degreen suna farko akan business administration wanda Abba yasa suka karanshi, toh"bayan sun gama ne sai ya shirya masu zuwa U.K don suyo degree su nabiyu akan ra'ayinsu inda *Habeeb* zaya karanci fannin siyasa shi kuma *Harees* zaya karanci fannin lafiya.


Lokacin ana gobe zasu tafi *Habeeb* yana dakinshi tsaye gaban madubi yana kum din kanshi yayinda *Harees* ke wance saman gado yana kallon shi, can sai *Harees* din yayi murmushi me cike da zolaya yace nidai don Allah mlm mu tafi haka nan tun dazufa kake faman wannan k'ak'ale-ka'ka'le saikace mace, hararan shi *Habeeb* yayi zayayi magana kenan saiga *Sadeeya* tashiga dakin da gudu ta rungume *Habeeb* ta baya tareda cewa Hamman *Harees* kaga Hamman *Hafeez* zaya dukeni ko,


_azaton ta *Harees* din ne_ domin shiyana sakar masu fuska sosai sabanin *Habeeb* da ko" kadan ba yasakar masu fuska, dasauri kuma cikeda tsoro tasaki *Habeeb* din sakamakon hango *Harees* din datayi tacikin madobi yana zaune saman gado yanata murmushi domin dai yasan yau akwai dirama tsakanin *Sadeeya* da *Habeeb*,


Wanda tuni yasaki kum din hannun shi dai-dai lokacin *Hafeez* ya biyota da gudu ran shi bace har zaya shiga dakin sai yafasa ya tsaya bakin kofa, saboda wani irin kallo da *Habeeb* yaimashi, cikin bacin rai yace ita cefa ta bata mun littafina shine ta gudo nan, yarinya aizaki fito ne sai nayi maki duka kuma ance *_KYAUTAR 'BERA_* ๐Ÿ˜œsannan yajuya yatafi, aikam tuni tafara bubbuga kafa yayinda hawaye yafara gangaro wa akan beauty fice dinta,


_Domin ta tsani bera arayuwar ta tun wani rana da Hajiya zataje store debo abinci sai *Sadeeyar* tabita, toh" shine beran yafad'a ajikinta saboda tsanani tsoro saida numfashi ta yadauke na wucin gadi, sannan tasaki kuka tareda cakume Hajiya to shine tundaga ranan take mugun tsoron beran,_


Cikin kuka tace Hamma *Harees*
kag.....kasa karasawa tayi saboda wani irin tsawa da *Habeeb* yadoka cikin matsanancin bacin rai yace....?








Muje zuwa




A


*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Sadeeya)






Tareda




โœ๐Ÿฝ


๐ŸŒนMeenart๐ŸŒน[7/2, 11:28 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ


_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_


๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ


1โƒฃ3โƒฃ




WRITTEN
By
๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ


OR


๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ




SADAUKARWA


*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*


___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~








โœ๐Ÿฝ






_*Bismillahirrahamanirraheem*_






Subhalallahee! *BB* meyasa meka..? da karfi yake kiran sunan shi tareda girgizashi saidai ina ko kadan *Habeeb* bai motsa ba, cikin tashin hankali *Harees* yatashi yabude mota dai-dai lokacin da Musa drive yanufo gurin dasuri, _kasan cewar yana hango duk abunda yake faruwa_ yace subhalallahi! yalla'bai *Hareesu* meyasa meshi..?


Cikin tashin hankali yace bashi da lafiya taimaka mun musashi cikin mota, suna kokarin sa shi amota saiga su *Safeeya* sunfito zasu tafi school _Dama su musa drive kejira_ don haka dasuri suka nufi gurin,


Cikin tsoro suke tambayar meyami Hamman *Habeeb*..?, nan *Harees* yafada masu" yace su shiga gida sufada
dasauri yashiga motar yatayar yanufi asibiti da *Habeeb*.




Dasauri *Sadeeya* tanufi part dinsu tafadi itama *Safeeya* ta nufi part dinsu ta fadi, kusan alokacin daya Abba da Baffa suka fito cikin tashin hankali, Baffa yace Alh ashe *"Habeebullah* baiji dadi ba..? Abba yace nima yanzu nan *Safeeya* tashiga take fada mana waima harma *Hareesu* yatafi dashi asibiti, yace "eh haka *KYAUTA* tace mun,


Musa dake tsaye gefe cike da jimami yace gaskiya yallabai *Habeebu* bashida lafiya sosai don ko motsi bayayi, cikin tashin hankali Baffa yace subhalallahi! toh" Alh mutafi asibitin mana, Abba yace toh" musa mutafi yace toh" Alh nan da nan suka shiga mota harda su *Sadeeya* da jikinsu yai sanyi ganin yadda aka dauki *Habeeb* baya numfashi.




Cikin sanyi murya *Safeeya* tace Abba muma za muje mu gaida Hamman *Habeeb* din, yace a ah yan'biyun Hajiya banda rigima kuda zaku tafi makaranta, gashima kun kusan makara kubari idan Ku tashi makaranta saikuje Kunji KO..? suka ce toh" dai-dai lokacin da Musa yashiga school din su wato alfurqan, banyan ya sauke su sannan ya nufi asibiti.


*****
Su Abba suna'isa asibiti anafito dashi kasan cewar koda *Harees* ya'isa dashi dakin taimakon gaggawa akaishi, wanda sun dan sauki lokacin kafin su samu numfashi sa yadawo dai-dai, baya ankai shi dakin Hutu sai Likita yanemi ganinsu Abba don yasanar dasu abinda yake damun shi,


Inda yafada masu cewa *Habeeb* yana daya daga cikin mutanan dake da karfin sha'awa, sai kuma yake shan magunguna don su rage masa karfin sha'awar, saidai kuma saka makon shansu dayake sosai shine sukai masa yawa har suka haifar masa da matsanancin ciwon mara, kasan cewar maganin sun daina yimasa amfani,


Idan kuma har bai daina shansu ba zuwa gaba zasu'iya haifar masa da mummunan matsala, dasauri Baffa yace subhalallahi likita Insha'allah hakan baza yafaru yace "eh bamu fatan hakan yafaru, shidai Abba bai Ce komai ba, sai
Baffa ne yasake cewa toh" yanzu Likita wani irin magani ne zaya ringa amfani dasu wayan da bazasu haifar Masada matsala ba..?


yace mace ne maganin matsalar sa, Baffa yace Likita ban gane bafa...? Abba kam murmushi yayi domin tuni yagane abunda Likita yake nufi, shima likitan murmushi yayi, yayinda *Harees* ya dukar dakai kasa cike da kunya yana faman sosa keya alamar tuni yagane abunda Likita yake nufi, likita yace ina nufin aure ne abunda yaka mata yayi domin shine maganin matsalar shi dazaran ya kusanci matar toh" shikenan babu wani sauran matsala,


Baffa yace "Oho nagane toh" amman dai yanzu babu wata matsala zaya farfado lafiya lau KO...?, yace "eh ba matsala mun bashi taimakon dayaka mata kuma insha'allahu zaya barfado normal zaku'iya ma tafiya dashi, Baffa yace toh" madallah mungode sosai, sannan suka fito.


Suka nufi dakin Da aka kwantar da *Habeeb* din har lokacin bai farka ba, Abba ya kalli *Harees* sai yai murmushi Cikin zolaya yace mlm Yusufa nikam yau abun nan yaban mamaki yace meke nan fa Alh..? yace toh" muda muke da likita sukutun agida amma kuma saigamu acikin asibiti toh" wai ya'kayi haka..?
Murmushi Baffa yayi tareda cewa gaskiya kam,


Cikin murmushi *Harees* yace Abba aini yau tsabar rikicewa mantawa nayi ni likitane, Abba yace toh" shikenan mu zamu tafi kaga Abbanka bai saniba, ni kuma zanje nashirya natafi office so aibabu wani abu KO..? yace "eh Abba yace to shikenan tunda litikitan ma yace bawata matsala idan yafarfado kaga sai kutaho , yace toh" shikenan Abba sannan suka fita.




Cikin sanyi murya Baffa yace Alh shin har sai yaushe ne za'a ba bam....dasauri Abba yakatse shi da cewa lokaci na nan zuwa in Allah ya yadda, yace toh" shikenan Allah yanuna mana lokaci Abba yace Ameen, suna tafe suna fira har suka isa gida yayinda kowa yanufi part dinsa.




*ASIBITI*
**********
Su Abba ba su dade da fita basai *Habeeb* yafarka, *Harees* yace masa sannu ya amsa da yauwa ina ne nan...? *Harees* yace asibiti, yace waya kawoni..? yace ni yanzu masu Abba suka tafi gida cikin mamaki yace meya faru dani..?


Cikin kosawa da tambayoyin *Harees* yace kai kam aidama karatun jarida kayi, haba wannan irin tambaya haka nan dai yafada masa duk abunda yafaru harda abunda Likita yace.


tsaki *Habeeb* yayi tareda saukowa daga saman gadon, yana kokarin saka takalmi sannan yace toh" nagode da tona mun asirin dakayi saika tashi kamai dani gida, cikin mamaki *Harees* yace" don nakawoka asibiti shine natona maka asiri...?


yace "eh dai-dai lokacin da yabude kofa zaya fita yana cigaba dacewa saboda baka tsaya gida kayi mun taimakon da kasa ba bani a U.K ba, sannan kuma aikasan magunguna kala-kala basaika siyomun ba amma duk baka yiba, saika wani daukoni ka kawo asibiti gashi nan yanzu kowa zayasan abinda keda muna ,


*Harees* dake biye dashi a baya yace shin wai Kai bakaji abunda nace maka Likita yafada bane..? kafin haka nima banasha fada maka cewa ka rage shan magunguna ba...? saboda zasu iya haifar maka da matsala, dai-dai lokacin da suka higa mota *Harees* yatayar suka tafi, yana cigaba dacewa
sannan kuma ni banga abun bata raiba, don ansan halinda ka ke ciki wanda hakan shi zayaba da damar asamo maka mafita cikin sauki,




Dan dai yanzu na tabbatar za'ace kafito da mata aimaka aure, toh"๐Ÿค” yanzu kaida baka kula yan mata idan akace kafito da mata ya zakayi kenan...? yafadi yana kashe masa ido๐Ÿ˜‰, hararanshi *Habeeb* yayi tareda cewa ban saniba kajiko..? yace ai zaka sani ne idan akace ka fito da mata nan da sati biyu๐Ÿ˜.




Koda suka'isa gida part din su Hajiya suka shiga sunyi ake lnna da Hajiyar su *Harees,* sun shiga gaida shi Cikin jin kunya *Habeeb* ya amsa gaisuwar sannan suka tashi suka nufi part din su, suna shaga *Harees* yace ka kwanta kahuta nizan tafi office.




*Bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login