Showing 159001 words to 162000 words out of 163788 words

Chapter 54 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt

11 Jul 2024

34808

masu tsaran su suhana ta zuwa,




don haka hankalin ta yai mugun tashi domin batason kowa yasan Junior ba dan *Habeeb* bane, tunda ado yace mata karya ne be fada mashi cewa Junior badan shi bane, haka ne yasa duk tafita hayyacin ta,




dataga sun hanata shiga sai takoma basu kudi suna barin ta ganin shi saidai kuma tayi rokon tayi masifa tayi lallashi be fada matan ba, sannan beyi sakin ba kamar yanda takeso don haka duk yan kudin ta yakare gashi yanzu Alh Barau yace ta daina zuwa gurin shi, kasan cewar Jafaru yaje har gidan shi yamai gargadin ya rabuda ita kosu kaishi kara kotu,




don haka komai yakwabe mata domin yanzu babu me kwasarta saboda wani al'amari da yasame ta, wato idan ta tsugunna tayi fitsari sai wani irin ruwa yana fitowa ta gaban ta me masifar wari, gawani mugun mafarki da takeyi wani koton mutun baki yana binta da gudu hannunsa rike da sharbebiyar wuka zaya caka mata,




idan tana gudu sai taga zata fad'a wani katon rami yana ci da wuta, gashi kusan kullun sai yaya Jafaru yazo yaima fadan akan saita karbo Junior tunda shida kansa yaje gurin adon don yafadi inda yakai Junior sai cewa yayi atambaye ta tasan inda yake, shiyasa
abubuwa sukai mata yawa ta koma kamar mahaukaciya.




*****
Aban garen kaka da Junior kuwa abin gwanin tausayi domin suna cikin wani hali yayinda sosai jikinta yatsanan ta, danma makociyar ta na kula da'ita ba tareda gajiyawa ba yanzu kam ko abinci bata iyaci balle magana,




sannan bata gane mutane abin sosai yadami matar kasan cewar batasan kowa nata ba, tsoron ta daya ma karta mutu ta barta da Junior Allah sarki wanda yanzu ya dangana darashi su Lili,




bawon Allah saidai yakan zauna yayita kuka, wata rana sai matar nan me suna iyale ta lallashi tukun.




*******
Aban garen su *Deeya* kam komai yana tafiya yanda yakamata, sosai suke gudanar da rayuwar su hankali kwance
yayinda suka tsanan ta addu'ar neman tsari,




ga makiya da dukkan wani abinki hakan ma iyayensu sosai sukeyi masu addu'a, don haka yanzu sunaji babu wani abinda zaya same su saidai kaddaran ubangiji wanda babu wani mahalukin daya'isa ya kauche mata.




Yau juma'a tunda *Deeya* tadawo daga school bata zauna ba, saida ta tabbatar ta gama hadama *Habeeb* kalolin lafiyayyun abinci masu jida lafiya tareda abin sha Bayan ta shirya komai akan dinning table, sannan tashiga,




wanka bayan tayi kwalliyar ta me tsari sannan ta shirya cikin wata bakar abaya me asalin kyau da tsada, Sannan tayi rolling kanta da gyalan abayar bayan ta feshe jikinta da turaruka masu asalin kamshi sannan tafita tanufi part din Hajiya.




Tana shiga ta'iske hajiya na jijjiga *Haleem* dayake ta kuka, kallon ta hajiya tayi me dauke da harara fuskar hade ta tace...








*_Second to the last page Insha'allah nagode sosai ,da kaunar ku gareni ALLAH yabar zumunci ameen๐Ÿ‘๐Ÿฝ_*






Muje zuwa


A


*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)


Tareda


โœ๐Ÿพ


๐ŸŒนMeenat Lufhat๐ŸŒน
[11/9, 10:19 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ


8โƒฃ6โƒฃ


WRITTEN
By
๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ


OR


๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ


_DAGA MARUBUCIYAR_
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_(Labarin na)_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
*_(Labarin Sadeeya)_*


SADAUKARWA


*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
__________________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
__________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~




โœ๐Ÿฝ




_*Bismillahirrahamanirraheem!!!*_




_NOT EDITS_




Yanzu saboda Allah hali dubu na tun dazu kuka dawo amma kika gagara shigowa kibasu nono su sha ko?...wai meyasa kikeyin haka ne umuh?.. kodan kinga suna da hakuri shiyasa ko?..,




hum to bari kiji nafada maki ranan da duk kika cikasu, suka ture maki zaki sani ne ke bakisan halin tagwaye ba ko?..dasauri ta'isa gurinta cike da tsoro tace wayyo Hajiya ta me sukeyi?..,




hararan ta tayi tareda cewa bansani ba nidai karbeshi kibashi yasha, tun dazu yake tafaman kuka karban shi tayi tareda turo baki sannan ta zauna yayida Hajiya fuskar ta had'e, taduka tadauki *Haneef* dake kwance akan dan keken shina jarirai yanata butsul-butsul da hannun dakafa da'alama shima nonon yakeso.




Cikin wantar da murya *Deeya* tace eyya yi hakuri hajiya ta karkiyi fushi dani, kinga ko muna kan hanyar dawowa ne sai "sweet Hmm na yakirani yace" gashinan zuwa shine nashga na hada masa abinci, saida ta zauna sannan tace hum sarki me sweet hmm to Allah yakawo su lafiya,




murmushi tayi tace ameen Hajiyar mu dai-dai lokacin da take kokarin ciro nonon, tana fadin sorry *Haleem* din mom *"Feeya* karbi kasha kafin mom dinka tazo tayi mun masifa nabar mata yaron ta yana kuka, bata gama rufe baki ba saiga *Feeyar* tashigo,




da'alama maganar tafada akunnan ta domin kuwa cewa tayi aikin kyauta dakika barmun yaro yanata kuka, kallon ta *Deeya* tayi cike da mamaki tace wai dama kina labe ne?..hararan ta *Feeya* tayi tace "eh ina laben ne, tace to dai labe ba kyau "eheee don haka gara mutun yadaina ato yakareshe fadi tana dariya kasa-kasa,




tsaki tayi tace ke ni rabani dawani labe labe kina nufin tunda muka dawo sai yanzu kika shigo zakiyi feeding din su?..hajiya ta mike tareda mikawa *Feeya* *Haneef* tace aikam sai yanzu tashigo, karban shi *Feeya* tayi yayinda Hajiyar tashiga daki tabarsu.




kallon *Deeya* tayi tace wai da gaske sai yanzu kika shigo?..koda yake da gaske ne tunda gashi nan har wanka kikayi kika chanja kaya, tace yes! na tsaya hadama sweet hmm abinci ne shiyasa so bayan nagama nayi wanka to yaki kaga wanka?..ta fadi tareda dage mata Kira daya,




tsaki tayi tace to bakiyi kyau ba dariya tayi tace dadin abin badan mutun nayi ba nayine sbd sweetie na, Wanda na tabbatar idan yazo yagani zaya yaba eheee, tace to ina ruwan wani eye?.




tace ah! da duwanshi mana tunda gashi nan yakushe tafadi tareda yin gwalo, tace ke! na kula dake gaba daya kinfi damuwa da "Hmm *Habeeb* akan twice dina KO?.. tace Kai tawan ashe dai kinga ne,




tace ke! *Deeya* watakullaha! takarashe mata da fadin hayyismakuntum my dear muji tsoron Allah adik inda muke, ke! kwarai da gaske nafi damuwa dashi sbd "shi nafara gani kafin su" ke! ni kyaleni da zancan yaran nan naki haka,




ki fadamun inda kika barmun my "Affan boy?..
tace ban saniba idan kuma za'a shakeni ne sai na fadi inda yake to bismillah, tace ah! name ai zancen shaka be ta shiba kawai saita fisge nonon ta daga bakin *Haleem* aikam yasaki kuka dakarfi kasan cewar har yafara bacci,




Dasauri tace wai meye kikeyi haka ne?..tace Oho! mlm amsa mun ina boy dina yake?..tace to dalla "yana gurin lnna ta sai ki bashi ya sha ko?., tace Oh! yanzu naji batu sannan ta cigaba da bashi nonon tanayi mata dariya, itama dariyar tayi tana fadin kai my sweet *Deeya* baki da dama sannan suka fara fira.




Bayan tagama bashi yai bacci saita kwantar dashi sannan takarbi *Haneef* shima tana cikin bashi yai bacci, don haka ta tashi ta kwantar dashi dai-dai lokacin wayarta tayi kara tana dubawa taga *Habeeb* Ne, murmushi tayi tareda dauka video calla ne,




kafin duk tayi magana yace my honey *Leemah* mun shigo fa, tace to alhamdulillahi Allah nagode maka daka dawo mun da my sweet Hmm lafiya, u are highly wlcm my real one lallausan murmushi yayi yace thanks dear,




itama murmushi tayi tace sai kun karaso yace Ok tareda kashe wayar.




Sannan ta kalli *Feeya* wacce itama kallon ta take gira daya ta dake mata tareda fadin, yadai mom din twice matar dr to nifa zanje natari habiby na don haka ga yaranki nan, Kai ta girgiza tace to sarki me habiby sai kin dawo amma fa akulamun da hmm na da kyau,




murmushi tayi tace karki damu hakan aifarilla ne tace Oh! my sweet *Deeya* Allah ya shirya ki dariya tayi tace amin tareda nufa hanyar fita dai-dai lokacin da Hajiya tafito tace ah! ita kuma Ina zata?..tace hum Hajiyar mu kyale ta Hmm *"Habeeb* ne ya'iso shine zataje tarban shi,




cike da farin ciki tace oh! hali dubu na kenan shidai wannan hmm din ba'a hada shi da kowa ba, tace shima aibe hadata da kowa ba domin idan kanason ganin bacin ran shi to kataba *Leemarsa,*
yanzu zaku kwashi yan' kallo,




murmushi tayi cike da jin dadi tace to aigara haka, tunda kulawar da be samu da ba yanzu yana samu aidole yaki hadata dakowa tace gaskiya kam hum ai wlhy sai yanzu hmm yasan yayi aure, tace aikam to Allah yabada zaman lafiya da zuri'a dayya ba,




tace amin, kudai ta kula da mazajen ku dariya tayi tace to hajiyar mu, tace yauwa sannan ta zauna suka fara tattaunawa tsakani y'a da Uwa.




*_Bayan kwana biyu_*
******
Ranan lahadi da misalin karfe 7: 30am na hango *Jana* tana tazabga uban sauri kamar mahaukaciya sanye take da zani daban riga daban, hijab din datasa yayi cumun-cumun kamar an
kwato shi abakin akuya, kallo daya zakai mata kaga ne bata cikin hayyacin ta tana tafiya ta waiwaye kamar mara gaskiya,




Sosai take sauri kamar zata tashi sama saida tayi tafiyar kusan awa daya da rabi sannan ta'isa anguwar su akafa, kamar koda taushe tashiga gidan ba tareda sallama ba direct babban falon tanufa Baba yana zaune yana kallon Labarin safe, kai yad'aga ya kalle ta sannan ya girgiza kai,




yace ai sai ke wai sallama Murjanatu sai ta gagareki sai kace ba yar musulmain ba?..Allah ya shirya ki, zama tayi tana fidda numfashi kamar tayi tseren gudu fuska had'e yace lafiya ki kazo mana gida haka tunda uwar safiya ke! ashe bama nace Karna sake ganin ki gidan nan idan ba tareda yaron mutane ba?..




shine kikazo ba kuma tareda shiba sbd ban isa nafada maki magana kiji ba ko?..to tashi maza kifitar mun agida kinji ko?..Cikin tashin hankali tace baba kaimun rai wlhy bazan iya sake kwana gidan can ba sbd kullm sai nayi mafarkin wani katon mutun baki yana bina da wuka zaya kashe ni, yace Murjanatu kenan ke atunanin ki Allah bazaya hukun taki akan abinda kike aika tawa ba?..




hum to kinyi kuskure dole ne ki fuskanci mummunan hukunci agurin ubangiji wanda na tabbatar shine kika fara fuskata tun yanzu, hum ZINA fa kuma da aure akanki Murjanatu harda yaranki Kai ko bakada aure ai ZINA ba'a banyi bane, tunda Allah yahane mu da yinta amma ke kikeyi KO?.to kisani ni bazan zauna da mazinaciya agida na ba don haka tashi ki tafi gidan ki kuma ki, tabbatar kin kawo mun yaron mutane kinji.




Cikin kuka tace Baba dan allah kayi hakuri har ado yadawo kuma wlhy na daina ZINA, yace dayafi maki alkhar dube kifa dan Allah dukkin lalace ke kodaga haka ma ai ya'isaki gane ZINA ba'abiyi bane, sai kuma yafara yimata nasiha me shiga jiki, cikin sanyi murya tace to baba inasan nafada maku wata magana amma sai agidan su *"BB* agaban shi da "iyayanshi harda yan'uwan shi dan Allah baba kaji?..




Shuru yayi yana kallon ta inda yahango nadama akwayar idon ta, cike da tausayin ta sannan yadaga kai ya kalli dija wacce tafito tunda zatayi tsaye tana jinsu yace tashiga ciki, kibata abinci ta karya sannan tayi wanka ta sake wasu tufafin dan banza muje da'ita gidan mutane haka ba, bari nakira yayan su yazo yakai mu tace to tareda tashi tashiga daki Dija kam tuni tashige daki.




Waya yadaga yakira Abba Bayan sun gaisa yace mashi ga sunan zuwa shida iyalinshi don allah shima yakira iyalanshi sbd *Jana* zata fadi wata magana amma sai agaban Alh *Habeebu* da kuma su, yace to ba damuwa dama akwai meeting da sukeyi duk ranan yau da karfe 10 zuwa 11 don haka kowa zayazo Insha'allah yace to shikenan sai sun zo, yace to Allah yakawo su lafiya yace amin tareda kashe wayar sannan yakira jafaru yadama shi.




******
Misalin karfe 10:15am su *Jana* suka isa gidan su *Habeeb* direct part dasu Abba suka shiga sun'iske mutane cike duk kowa yazo amma banda *Deeya* da *Habeeb,* nan dai suka gaggaisa sannan suka zauna, *Jana* kam sai rarraba ido take alama *Habeeb* take duba.




Abba yace wai yau lafiya har yanzu su na Allah basu shigo ba?. Kai *Hafeez* tashi ka dubosu,har da zaya tashi sai su kaji daddad'an kamshin turaren su wanda yariga su shiga falon,




cikin nutsuwa suka shiga bakin su daukeda sallama *Habeeb* yana gaba rungume da *Haleem,* *Deeya* tana biye dashi rugume da *Haneef* sanye suke da wata ubansun shadda me ruwan gwal kallo daya zakai mata kane me tsada ce,




irin dinki da wayayyu samari yanzu ke yayi, ita kuma dinki dogon riga tayi me stones work irin Wanda manyan mata yanzu ke yayi, yaran kuma sanye da wasu kyawawan riga da wando me ruwan ja da yalo gaskiya sunyi kyau sosai, yayinda suka dauke hankalin mutane falon suka kuma birge su sosai.




Bayan sun gaggaisa da mutane sannan suka zauna yayinda kowa keson daukar twice kunsan suda farinjini saida kam tuni iyayensu sun karbe su, wato *Feeya* takarbi *Haneef* yayinda *Harees* yakarbi *Haleem,*




gyaran murya Abba yayi haka ne yasa kowa yanutsu, sannan Baffa yayi addu'a bayan ya gama sai Abba yafadi abinda yatara su duk da sun saba, amma nayau akwai dalili sannan aka umarci *Jana* tafadi abinda takeson fad'a,




Wacce gaba daya hankalin tayana kan *Habeeb* jitayi kamar taje ta rungume shi saboda so, sosai take kallon shi Mrs senato *Habeeb* kam be masan tanayi ba asalima hankalin shi nagurin Affan daya karba hannun *Hafeez* wasa yake mashi ahankali sai yanata wangale baki,




tsawa Jafaru yadaka mata da fadi mlm kefa ake saurare aikam tayi firgigit tadawo hayyacin ta, domin tuni ta lula duniyar tunani sabuwar rayuwa itada *Habeeb* still idon ta yanakan *Habeeb* din tace...








*_Kuyi hakuri nazo wannan page din yazama na kashe amma allah be nifa ba_*




Muje zuwa




A




*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)




Tareda




โœ๐Ÿพ




๐ŸŒนmeenat Lufhat๐ŸŒน
[11/9, 10:19 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ


_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ


8โƒฃ7โƒฃ


*_END_*


WRITTEN
By
๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ


OR


๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ


*_DAGA MARUBUCIYAR_*
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_(Labarin na)_*
*_KYAUTAR ALLAH_*
*_(Labarin Sadeeya)_*


SADAUKARWA


*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~




โœ๐Ÿฝ




_*Bismillahirrahamanirraheem*_




_NOT EDITS_




umh! ummh dama zan fad'a maku gaskiya cewa Junior ba d'an *BB* bane gaba daya falon aka dauki salati, *Habeeb* kam ajiyar zuciya yasauke tareda lumshe ido aranshi yana godiya da Allah yanuna mashi wannan Rana,




yayinda dija ta mike zumbur cike da tsoro da tashin hankali tace me kika ce?...tace "eh wlhy dija da gaskiya nafada "Junior badan *BB* bane dan ado ne, aikam tuni tazube kasa sume,gaba daya falon yarikice da hayaniya, Binta kuka tasaki tareda dago dija tana Allah ya'isa tsakanin su da *Jana,*




baba kam tunda tafadi wannan muguwar maganan kanshi ke kasa tsabar bakin ciki da kunya, jiyayi kamar kasa tabude yashige nan da nan su Hajiya suka rufe Dija ana yimata fiffita,




dasauri aka dauko ruwa aka yayyafa mata saidai numfashin be dawo ba, cikin tashin hankali Abba yace da *Harees* yaduba ta kasan cewar dama yana zuwa da kayan aikin shi gurin meeting din, koda wani abin zaya faru, don haka yafara bata taimako cikin gaggawa.




Ahankali baba yadaga Kai ya kalli jafaru wanda shima kallon Baban yake, aranshi yana rokon Allah yasa kar yashiga wani haki makamancin wanda Dija take ciki yanzu, yayinda zuciyar shi take cike da bakin cikin abin kunyar da *Jana* tayi azuri'arsu,




lumshe ido baba yayi wanda banga ne nufin shi ba ga mamaki na jafaru naga yatashi da zafin nama yanufi *Jana,* kafin kace me yasakar mata barin makauniya wato yahauta da duka tako'ina aikam tafara ihun neman taimako wanda hakan yadawo da hankalin mutane gurin,




Dai-dai lokacin kuma Dija ta farfad'o, cikin tashin hankali Baffa yace subhalallahi! jafaru meye haka kuma idan kaji mata ciwo fa?. rai bace Baba yace mlm yusufa bari ya duki yar banzan yarinya marar mutunci, baffa al-mustafa yace haba Alh idan yayi mata illafa?.




cikin gigita dija tace aigara yayi mata kadake ta sosai shegiyar yarinya da haibuwar irin ku aigara farin ku, aikam jafaru yakara karfin dukan ta dakai mata shuri ta ko'ina, cikin tsawa Abba yace Kai! Jafaru kayi hauka ne kashe ta zakayi?..hakan ne yasashi barin dukan nata, yakoma gefe yana maida numfashi.




Abba yace kowa yakoma gurin zaman shi ya nutsu
Bayan kowa yakoma ya zauna, sai shuru yaratse falon sai sauti kukan Dija dana *Jana* ke tashi, gyaran murya Abba yayi sannan ya kalli *Habeeb* wanda hankalin shi kwance yake yima Affan wasa,




tsawan lokaci Abba yana kallon shi yayinda yake nazarin abubuwa dayawa aranshi ahankali, yace Na Allah kaji abinda Murjanatu tace" KO?..cike da ladabi yace "eh Abba tuni naji hakan na shiyasa ma ai tazo ta dauke "shi takaishi gurin Baban shi,




Cike "matsanancin mamaki kowa yake kallon shi musamman Abban da Hajiya dasu baba, wanda aranshi yake jijjina halin kirki irin na *Habeeb*.




Abba yace na Allah tun yaushe kaji wannan maganar amma kayi shuru baka fada ba?..shuru yayi bece komai ba, yace shin na Allah koshine dalilin dayasa ka saketa?..cikin sanyi murya yace "a ah Abba bashi bane?..yace to menene? nikam zurfin cikin ka yafara bani tsoro irin wannan aisai ka cutar da kan ka, kasani irin wannan maganar ba'abin bari aciki bane,




yace abba ai dan'uwa yasani yace ikon Allah amma mu ba musani ba?..yace kuyi hakuri Abba dama inajiran irin ranan yaune don haka yanzu zanfada maku abinda naboye maku, abba yace muna sauraren ka cikin nutsuwa yafadi komai tundaga ranan da ado yakira shi har da awon jinin da *Harees* yayi masu yakuma muna cewa Lili yarshi ce,




amma Junior ba dan'shi bane inda yakareshe da fadin mutumin dayasa ce *Deeya* shine Baban Junior.




Sosai mutane ke salati kowa yana fadin albarkacin bakin shi, Abba kam be ce komai ba domin lamarin yadaure mashi kai sosai dija kam da Binta sai kuka suke me cike da bakin cikin abinda *Jana* tayi cikin tsananin kunya baba yace don Allah Alh kuyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login