Showing 45001 words to 48000 words out of 163788 words
Chapter 16 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt
*Harees* yashiga kun nan shi makale da waa *Deeya* tace Hmm *Harees* sannu da dawowa, yace yauwa karbi nan mijinki ne yake son magana dake jitayi gabanta yafadi, bin wayar tayi da ido ba tareda ta karba ba yace ke karbi mana dasauri takarba jikinta na rawa.
Shikuma yanufi gurin *Feeya* yana cewa me Darajata tashi muma muyi soyayar mu, Cikin jin kunya tace a ah nidai bacci zanyi yace to yi hakuri ki bude mun fuskarki nagani, ahankali tabude fuska ta na dariya yace yauwa ko kefa to me zan samu??. tace bakomai yace kai! haba kodan kiss din bazan samu ba?.
tace kai๐ณtareda bude baki saikuma taja bargo tarufe kanta tana dariya,
Shima dariyar yayi tareda cewa bani mana zan koma office ne, tace nidai ba ruwa na idan "Hajiya taji ka dariya yayi yace to shikenan natafi tunda bazaki bani ba, Queen of beauty idan kin gama ki kawo mun wayar ina falon kasa sannan yafita.
Ita kam *Deeya* tunda ta karbi wayar tasa akunne ba tace komai ba, sai *Habeeb* ne ke tafaman magana shi kadai, zaune yake acikin faffadan office din shi saman lallausan kujera me juyawa yayi release sosai akujeran idon shi rufe,
Sanye yake da wata dakakkiyar shadda dark green dataji aiki kanshi babu hulla suman nan sai kalli take hannun shi daure da agogon gold, kafarshi kuma sanye cikin farin takalmi sauciki kamshin turare sai tashi yake ajikinsa, ahankali yake juya kanshi
akujeran cikin cool voice din da harshan turanci yace *Leemah ta* kice wani abu mana umm?,.
Inason naji sweet voice dinki ne da nayi missing kwana biyu, Cikin sanyi murya tace Ina wuni yace lafiya lau *Leemah ta* nayi kewarki sosai fa, fadamun kema kinyi kewata?.. ba tace komai ba sai faduwa da gabanta yake aikin yi, haka dai yaita janta dafira daga umh sai um-umm! take cewa.
Daga karshe yace mata ranan juma'a yana nan zuwa kar ta manta da jagwalgwalon nan๐,dariya tayi me sauti har saida yaji ta cikin waya, ido yarintse domin saida yaji wani irin yarrrrr! ajikinsa Cikin sanyi murya tace ai bazan manta ba, yace yauwa *Leemah ta* ki gaida mun da "lnna da "Baffa ki kuma kula mun da kanki kinji ko?..
Cike da kunya tace Hmm yace byeeee tareda yo mata kiss yace oya to nima kiyomun naji kinji?. *Leemah ta* dasauri tace um-umh tareda cire wayar daga kunnanta tana dariya, shima dariyar yayi tareda kashe wayar.
Sannan taje takaima *Harees* wayar shi tadawo suka fara fitar *Habeeb* Da *Harees,* sai yamma lis suka koma part din lnna kasan cewar can suke da kwana, murmushi lnna tayi data gansu tace sannu ku *_yan gudun hijira_* (Littafin dr Zain) tace saidai kuma kun gudu amma baku tsira ba, ga sauran maganin nan ku zauna kushanye kubani ko fina. fuska suka yamutsa tareda zama sai kuma suka kalli juna suka kyalkyace da dariya.
*******
Kwanci tashi a saran me rai yau alhamis kuma ayau ne su Adda Mamu suka shirya ma su", *Deeya* Da *Feeya* sister's night only family ne sai kawayan amare kawai, Wanda za'ayi yanzu agarden karfe 8:30pm na dare.
"Amare sunsha gyara sungaji sunyi matukar kyau, sanye suke cikin wani hadadden bakin materi me ratsin ash color, dinki riga da siket ne irin me bajewar nan ne takasa kayan yadan kama jikin sun kadan, ta yadda sharp dinsu yafito
gwanin sha'awa sai aka daura masu goggwaro ash color jaka da takalmi suma ash color, kai gaskiya amare sunyi kyau sosai kamar kasa ce su ka gudu.
Sannu ahankali suka fito daga part din Hajiya suka nufi garden inda yan'uwa kejiran su, yayinda su Salma ke take masu baya har suka isa suka zauna akujerun da aka tanadar masu, bayan sun zauna sai Adda mamu tabude taroda addu'a sanna akafara gudanar da liyafar,
Yayinda *Harees* yakoma gefe ya zauna yana video call da *Habeeb* wanda yakejin kamar yai tsuntsu yazo Bauchi, shima ayi sisers night din dashi saidai kuma ba hali, sai misalin karfe 10:00pm sannan aka gama kowa yatafi gidan.
"Aban garan *Jana* kuwa duk wani abunda ake ba uwargida nafadar kishiya "an bata harda kayan daki saida Abba yasake mata wanda iri daya akai mata dasu *Deeya,* sannan Hajiya da lnna sunata lallashin ta to ba laifi ta dan sa ki jiki ana hidimar bukin da'ita.
******
Washegari
Jumma'a akasa amare kalle kuma ranan za'a daura auren *Feeya* Da *Harees* bayan an sauko sallar juma'a,
*Habeeb* kam yana idar da sallah juma'a yahawo jirgi yataho sai ce ma masu tsoron shi su iske shi gida,
yana'isowa ana kokarin daura auren don haka ya tsaya aka daura dashi, bayan angama Sannan yashiga part din Hajiya, atunani shi su *Deeya* na can domin ita kawai yake so yagani,
koda yashiga mutane cike a falon kasa sun ke waye Hajiya gaida ita yayi Sannan yace lna su *Deeya?* akace suna part din lnna, don haka yafito yanufi part din shi
Domin yana jin kunyar shiga ne manta.
Dasauri *Jana* ta tare shi tayi masa sannu dazuwa, Shafa ma dake kusa da'ita taimasa ya amsa fuska ba'annuri yanufi dakin sa,
Shafa tace da *Jana* tashi muje ki zuba masa maganin daya fito "ya tsallaka, tace lna aina fasa na bari sai munje abuja sannan yadda zanji dadin gasama yar'isa gyada ahannu, dariya Shafa tayi tareda mikama *Jana* hannu suka tafa tace shegiya ashe dai kanki yanaja wani lokaci tace sosai ma kuwa, shikam *Habeeb* yashiga ya cire kaya yashiga toilet.
Da misalin karfe 4:00pm amare da angwaye suka fito cikin shirin fulani wanda za'ayi agidan su *Harees*, sunyi kyau sosai ko wani ango yana like da amaryar sa musamman *Habeeb* jiyake kamar yamai da *Deeya* Cikin sa itakam duk kunya yacika ta, hannun ta yana cikin nashi amma jikinta rawa yake Cikin rad'a yace *Leemah ta* ki saki jiki mana, cikin shagwaba tace to nidai kasa kar mun hannu yace bazan iya ba *Leemah ta,* ahaka dai suka karasa gurin. *Jana* kam duk haushi yacika ta sai tsaki take da hare-hare kasan cewar taje gurin, cikin nutsuwa ake gudanar da fulani day din karfe 6:00pm angama.
Karfe 8:00pm akatafi hadadd'en dinner da aboka nan su suka hada masu, wanda sukai ma suna da _only friends_ wato abokai kawai don haka dinner babu mutane sosai shiyasa tayi matukar kaya tuwa, daga abokai da suka saka kaya iri daya farar shadda da akaima aiki da bakin zare, sai kawaye
Suma kaya iri daya suka sa bakin material, su kuma amare suka sa blue
material, angwaye suka sa farar shadda sai akai mata aiki da blue zare, gaskiya sunyi kyau sosai dinner ta hadu sai karfe 10:00pm akagama, *Jana* kam cewa tayi bazata ne ba saboda ba zata'iya gani kayan takaici ba๐ฅ.
*_Nikam nace dataje da taga kayan takaici kam๐_*
Domin da'akace" *Habeeb* yaba *Deeya* cake abaki sai yasa abakinsa sannan ya rungumeta; yahade bakin su yasa mata cake din,
kunya kamar zata kashe *Deeya,*๐
Koda suka dawo agajiye ana ina amare akai su dakin su ba'agansu ba, "Ashe suna can sun shige dakin
Abba sun kwanta suna baccin gajiya, saida yashiga shi da Hajiya sai su kagan su" dariya sukayi zata tashi su sai Abba yace ta kyale su" sai gobe.
****
Washegari akai masu jere, da misalin karfe 8:00pm na dare,
Abba yace akai ko wacce dakinta;
saidai me cewa sukai basu san wannan zancen ba, domin kuwa rungume juna sukai suna kuka
gwanin tausayi
ganin haka yasa Abba yace abarsu har gobe, idan su *Deeya* suka tafi Abuja dole *Feeya* ta yadda akai ta dakinta.
Haka ko akai da gariya waye lokacin da zasu tafi dakyar aka rabasu, *Harees* ya rungume *Feeya* zuwa part din shi.
*Habeeb* kuma yashiga da *Deeya* mota dazaya shiga kasan cewar *Jana* sun shiga guda itada yara dayar kuma masu tsoron sane, haka suka dauki hanyar zuwa Abuja *Deeya* na rungume jikin *Habeeb* tana sauke ajiyar zuciya.
*_to readers kubiyo ni kuji wata wainar za'atoya a'Abuja_*
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นMeenart๐น
[7/2, 11:48 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
3โฃ0โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
"Basu dad'e dafita garin Bauchi ba bacce yasace *Deeya* yayinda Direbobi keta sharara gudu akan titi, itakam tana kwance ajikin *Habeeb* abunta sai sharan baccin ta take hankali kwance, yayinda duk wani mutsin Da zatayi sai *Habeeb* ya gyara mata kwanciyar ta, tareda sake rungumeta ajikinsa sosai yana me shakar daddad'a kamshin turaran ta,yayinda yake jin zuciyar sa tana wani irin tsinkewa sai yana ji ajikin sa kamar akwai wani abun dazaya rabashi da ita.
******
Saida misalin karfe 5:00pm suka isa Abuja kasan cewar dama bawai sun tashi dawuri bane, kai tsaya _housing senetors_ suka nufa dake _Maitama_ gidan *Habeeb* upstairs ne dai-dai kofar gidan direbobi suka tsaya, _Alhamdulillahi!_ shine abunda *Habeeb* yafurta akasalce,
Domin wani wani irin kasala ne yasauka ajikinsa tun lokacin da *Deeya* ta kasan ce kwance ajikinsa sosai yakeji wani irin matsanancin kasala, ido ya kurama kyakkyawar fuskarta me cike da haiba da kwarji gawani irin annuri datake fitarwa na musamman wanda wannan sirrine na amare.
Shikam bai taba ganin wacce bacci yayima kyau irin *Leemar* shiba, idonsa yarintse yanajin wani irin *SONTA* yana ratsa shi, saidai kuma yanaji ajikinsa kamar wani mummunan al'amari zaya faru dasu, ahankali yafurta yah ilahee wannan baiwa taka tun ranan da tazo duniya nayi tozali da ita nakeji wani al'amari me girma game da ita,
Wanda bansan ko menene shiba sai sannu ahankali na fahimci cewa "Ashe kaunar Ce kadasa mun a *ZUCIYATA,* nashiga wani ahali lokacin narasa yadda zanyi ta zamo mallakina; ashe ma bansani ba tuni ka mallaka mani ita;
"Aranan dana fahimci haka nayi *FARIN CIKI* mara musaltuwa wanda har yanzu ina cikin shi, duk da cewa inajin tsinkewar zuciya amma hakan bazaya hana ni godia agare kaba Da wannan *KYAUTAR* dakayi mun, ta mallaka mun abunda *RUHINA* yake kauna gangar jikina ke *MURADI.*
yah! Allah nagode! nagode!! nagode!!! saidai kuma inaji kamar akwai wani al'amari dazaya faru tsakani na da "ita; wanda kai kasani amma ni bansani ba domin bansan gaibi ba, saidai KO" menene zaya faru tabbas nasan *KADDARAN MUCE* nida ita don haka yah Ubangiji inarokon ka, kasa yazo mana da sauki ameen yah Allah.
"A hankali yasa zara-zaran yatsunshi yana shafar cute fice dinta tareda fadin wake up sleepy beauty mun iso, ahankali tabude fararan idonta wanda KO" kuka tayi ba suyin ja to balle bacci, salati naji tayi tareda kura masa lumsassun idanun ta masu kashe masa jiki, lallausan murmushi yasakar mata tareda cewa, *Leemah ta* mun iso kinata bacci.
"Ahankali tamike daga ajikinsa tajingina kanta ajikin kujerar dake gaban ta, wani irin nauyi taji kanta yanayi; hannun yasa yadago kan nata tareda cewa *Leemah ta* ya'akayi ne??..; batace komai ba saidai tayi rau-rau da ido zatayi kuka,
Dasauri ya rungumeta tareda cewa "a ah *Leemah ta* karki yi kuka kinji fadamun menene??..Cikin rawar murya tace yanzu shikenan bazan sake ganin my sweet *"Feeya* ba, da "Hajiyarmu Da "lnna ta da "Baffa na ba?.. yace haba *Leemah ta* zakigan su mana, cike da shagwaba tace to sai yaushe?.. yace sai "an kwana biyu zamuje kigansu" kuma kafin muje baga waya ba sai kuringa gaisawa, dasauri tadago fuskarta dauke da annuri tace Lah! yauwa Hmm *Habeeb* inama Waya ta dakace nakawo zaka samun charge da games?..
(Kasan cewar jiya yasiya masu tsadaddun wayoyi masu kyau ita da *Feeya*) murmushi yayi cike da zolaya yace ayya aiko mun barota gida jikin charge, ido tazaro cike da shagwaba tace Kai! Hmm *Habeeb* jikinta charge kuma? yace "eh tace to yanzu idan zankira sweet *Feeya* dasu Inna fa?..yace sai na aramaki tawa, to idan zanyi games kuma fa?.. ta karashe fadi tareda turo baki.
Dariya yayi tareda Kai hannun ya kama pink mouth dinta yace to sarkin buga games ga wayar kinan Cikin bag dinki, inajina ma anata kira kilama Sofee Ce" dariya tayi tareda karban jakar dasauri tana kokarin budewa sukaji "Ana kwankwasa glass din motar.
*Jana* kenan wacce tacika tabatse tayi fam kishi kamar zaya kashe ta, gani tun dazu suka iso duk sun fito daga mota har da direban daya tuko su *Habeeb* tuni yadade da fitowa, amma su suna cikin mota basu fito ba, to KO" uban me sukeyi acikin motar Oho!.
inji cewar *Jana* kenan๐คฃ.
Jin shurun yai yawane gasu kuma tsaye suna jiran su", shiyasa
ta kwankwasa glass din saboda irin me dubu, nan ne Wanda na waje baya ganin na ciki saidai kai dake ciki kaga shi nawajen,
"Ahankali *Habeeb* yabude mota tareda zuro santala-santalan kafafunsa masu saye da bakin takalmi, hannun shi rikeda jamar *Deeya* hannun yamika mata bamusu tasa hannun ta takama, tafito ido suka hada *Jana* ta banka mata wani irin mugun kallon Wanda yasa gaban *Deeya* faduwa,
Dasauri tadukar dakai kasa ahankin yadda balallai bane wani yaji tace, la'elaha'ella'antassubahanaka'inniku tun'meenazzalimeen, da gudu lili mama tazo tarike hannun *Deeya* tana dariya tace Aunty *Deeya* tale jamu kwana KO?.. dariya *Deeya* tayi tareda gyada Kai alamar "eh tace ada Kai KO" Dad? tafadi tana kallon *Habeeb* murmushi yayi tareda cewa yesss my lili,
Sannan yakalli dan matashin direban dake tsaye yace Saminu a shiga da kayan ciki mana, Cikin girmama wa yace ranka yada'e ankai- tun dazu yace OK " mujen ku ciki KO?.. *Leemah ta* Cikin sanyi murya tace to hannun ta guda na cikin nashi, gudan kuma yana rikeda lili mama suka nufi cikin gidan.
Cikeda takaici *Jana* taja tsaki mtww tareda Jan hannun Junior suka bin bayan su aranta kuwa tana fadi zakuga ne baku da wato.
Tadaga kafa za shiga kenan sai kuma tafasa, Dasauri *Habeeb* yajuyo yakalleta yayinda yaji kirjin sa yafara bugawa, Cikin fargaba yace menene?.. bata bashi amsa ba saidai tasaki hannun sa, yayinda tadaga hannun ta duka biyu tafara jero Addu'a kuri yai mata da ido wani irin son ne yake ratsashi har yanajin tsigar jikinsa yana tashi, tadauki lokaci tana addu'ar sannan ta Shafa wanda tare suka Shafa da *Habeeb* harda lili mama data shafa tareda fadin ameen Aunty *Deeya*๐.
Sannan suka shiga wani abun mamaki shine tsarin gidan kamar nacan Bauchi saidai akwai ban-banci kadan, babba falon kasa yana dauke da set din kushi manya-manya da kuma t.v bango da fridge sai d'a kuna biyu, _sukam bansa yasuke ba don banshiga ba,_ sai guda shikam wannan kicin ne domin gashi nan arubuce.
Kallon su *Habeeb* yayi yace nan ne falo na ga dakina nan wancan kuma na Junior wannan kuma kitchen ne kungani ai so mujen ku sama na nunawa KO" waccen ku dakinta.
Still hannun shi yana rikeda na *Deeya* suka nufi sama, falon saman baikai nakasa girma ba shima yana dauke da daku a uku sai set din kushi tareda table a tsakiyar falon, sai babban t.v bango da kuma fridge, dakin farko yace ke *Jana* gadakin ki ke kuma *Leemah ta* ganaki nan wannan kuma na my lili, Dasauri lili tace Dad ni wajan Aunty *Deeya* Jan kwana yace OK" Dasauri *Jana* tace gaskiys BB ni wancen dakin nakeso,
wani irin kallo ya watsama ta tareda cewa tsarina kenan kuma babu wanda ya'isa ya chanja mun, kuma da wannan dakin da wancan duk dayane abunda ke cikin wannan shi ke cikin wanca, sannan yaja hannun *Deeya* suka shiga dakin ko shima saida ta tsaya tayi addu'a
Sannan tashiga, da gudu lili taje tahaye saman katafaran gadon dake shimfide da lallausan bedsheet tareda wasu manyan pink din teddy guda biyu masu kyau, tsalle murna lili tayi tareda daukar teddy din tana dariya.
Yace *Leemah ta* bari na dauko maku kayan ku ko?... tace to Sannan yafita ita kuma tafara kallon dakin,
wanda yai matun ahankali tanufi gurin mirror mamaki ne yakama ta ganin kayan dake saman mirror duk irin wanda take amfani dasu ne murmushi tayi tareda karasawa gaban mirror.
Saida *Habeeb* yakai ma *Jana* kayanta daki wanda yake komai iri daya ne dana dakin *Deeya*, Sannan yadauko nata yashiga hannun sa dauke da akwatina guda biyu, tsaye ya'iske ta gaban mirror, dasauri tajuyo tace Hmm *Habeeb* kaine ka siya mun duk wannan kayan make up din?..
murmushi yayi tareda cewa yesss! *Leemah ta* I hope you like it?..dariya tayi tace sosai ma, yace to kinga ga kayan kinan bari na dauko sauran saimu jera acikin wedrof ko?..tace to, bayan yadauko sai suka jera harda na lili mama bayan sun gama jerawa sai yace to kishiga kiyi wanka nima zanje nayi idan nagama zan zo saimuje muci abinci da lnna da Hajiyar mu suka bamu ko?..,kai ta gyada alamar "eh, har zaya fita saita tsinci kanta da rike masa hannu dasauri yajuyo tareda ma tsawa kusa da'ita yace ya'akayi ne?.. *Leemah ta,*
Cikin sanyi murya tace thanks, yace for what?.. baki ta turo cike da shagwaba tace for komai ma, dariya yayi tareda kallon gefe da lili take; wacce wasan ta kawai take da baby doll ba tareda tasan suna gurin ba,
Gani hakan ne yasashi sake ma tsawa sosai kusa da ita yaimata rumfa har sunajin bugun zuciyoyi juna, wanda hakan ne yahaifar masu da faduwar gaba, dukka su gaba fuskarsa dauke da annuri yace wato for komai mako?..
Cikin dariya kanta naduke akasa tace
"eh, shima dariyar yayi cike da kaunar ta yasa hannu yadago fuskarta tareda tsura mata ido, itakam tuni ta lumshe idon ta domin bazata jure kallon kwayar idon shiba, Murmushi yayi yace to shikenan Zantafi, amma kafin nan pls *Leemah ta* let me kiss u; dasauri tabude ido tareda zaro su cike da tsoro tace...
*_Pls ku yin hakuri da wannan yau Cikin a ciwo yake dakyar ma nayi typing din, pls I need yours prayers๐_*
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_*(Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นMeenart๐น
[7/2, 11:48 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin