Showing 18001 words to 21000 words out of 163788 words
Chapter 7 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt
kwana biyu*
**********
Da misalin karfe 11:00Am na rana lahadi Su *Habeeb* ne suka fito cikin shirin su nazuwa kaima abokinsu ziyara dake zaune a new makama estate,
*Harees* yace mushiga muji kiran da Baffa yakeyi mana kafin mutafi ko...?
yakara she fadiyana kallon *Habeeb* yace "eh,
Zaune suke gaban Baffa Kansu duke akasa cike da ladabi suka ce Baffa ga mu, gyaran murya Baffa yayi sannan yace shin kunsan dacewa duk daraja da mutuncin mutun Da mutane" suke gani, dazaran ance baya da iyali
Shikenan daga ranan darajarshi tazube "a idon "mutane kuma bazasu sake mutun tashi ba,
Don haka abunda nakeso daku shine kowa nan ku yafito da matar dayake son ya aura, domin dai lokaci yayi da yaka mata Ku ajiye iyali kun jiko...?, har *Habeeb* zatayi magana sai kuma yayi shuru,
Cikin ladabi *Harees* yace toh" Baffa Insha'allah zamu fito dasu yace yau Allah yaimaku albarka suka Ce ameen sannan suka fita.
Tunda suka fito har suka shiga mota suka nufi inda zasu babu Wanda yace komai, yayinda *Habeeb* yake tuki ahankali can sai *Harees* yace toh" wai da me zakace ma Baffa..?
tsaki *Habeeb* yayi tareda cewa hmm! aini wani irin kwarjini Baffan yaimun shiyasa nakasa Cewa komai, murmushi *Harees* yayi yace ai Baffa kam akwai kwarjini sosai, toh" wai yanzu ta'ina zamu fara..? yace hmm! kodai ta'ina zanfara,
Da saurice bangane ba..? yace toh" kaifa kanada Safeena kuma tana sonka kaine dai baka sonta, murmushi *Harees* yayi yace aiba wai banason taba ne "eh yesss! Ina sonta saidai kagane akwai wadda nake matukar so fiyeda "ita, kamar yadda kaima kake matukar son wata
fiyeda yadda kakeson kanka,
Wani irin wawan burki *Habeeb* yaja tareda kallon gefen da *Harees* yake, cikin matsanancin mamaki yace...?
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
(Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นMeenart๐น
[7/2, 11:28 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
1โฃ4โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
"Kai tunda muke dakai ka taba jin nace maka ga yarinyar danake so...? hararan shi๐ *Harees* yayi tareda cewa haba don Allah mlm wannan wani irin abune haka sonake ka kashemu tun ba mukai ga cimma burinmu ba,
"Dasuri yace kaga mlm dalla ka fadamun "wace yarinya ce" nake matukar so fiye da kaina eye..? *Harees* yace ban saniba, harara *Habeeb* yasake watsa masa tareda cewa ah! tunda abun kulin sharrine ai baza kasani ba, wani irin kallo ya watsa masa sannan yace kaga mlm banason _pretending_ fa,
"asukule *Habeeb* yace anyi _pretending_ din kaji ko..? tsaki *Harees* yayi tareda cewa Oho Kaidai kasani waikai sarkin yan *ZURFIN CIKI KO..?* kag mlm idan zaka fito kafadi abunda ke cikin *RANKA* kafito kafada, idan kuma bazaka fadi ba Kai kasani,
*Habeeb* yace "eh bazan fadi din ba kaji ko..? yace toh" shikenan ka cigaba da ajiye shi acikin *RANKA,* saidai kuma kasani idan Kai wasa watara na zaka iyarasa shi, muddun baka fitar dashi ansani ba kuma na tabbatar alokaci dakai yunkurin fitar dashi yariga yaimaka babbar *ILLA A ZUCIYA*,
Cike da jin haushi yace waikai ina ruwanka dani ne...? yace da ruwana tunda ni dan uwanka ne kuma shakikin amininka ne, amma tunda kace ba ruwa na toh" aje'a hakan saidai kasani nidai Ina nan akan bakana nason wacce" nafada maka lokaci kawai nakejira yayi na baiyya na mata zallar kaunar danake yimata",
tsaki *Habeeb* yayi tareda cewa kadaiji kunya wlhy, da sauri *Harees* yace ah! yanzun kam banji taba saidai ko zuwa gaba idan na'ajiye girmana gefe kila naji, cike da mamaki *Habeeb* yace ita" kunyar...? yace "eh ita din, kaga yallabai kaja mota mutafi kuma anjima zamu gidan lnna "Hafsatu muga "Safeena mudai-daita, don haka saikafara Neman wacce za'a aura tun yau don idan aka tsayar da maganar mu bazan jira kaba,
_"lnna Hafsatu kanwar Mahaifiyar *Harees* ne "Safeena yartace" tana matukar so *Harees*, shine dai bai damu DA ita sosai ba_ .
tsaki *Habeeb* yayi tareda tada motar yace kaidai kasani kuma kada Allah yasa kajirani din mlm duk ka wani cika ni da surutu.
"Akan hanyar su ta koma wa gida ne *Harees* yaketa cewa *Habeeb* ya tsaya zayayi fitsari, amma Yaki tsayawa saida yace don Allah ka tsaya kasan fa babu kyau mutun yarike fitsa saboda yana yiwa mutun illa, duk da haka *Habeeb* bai tsaya ba saida suka shiga Unguwar wintin dada sannan *Habeeb* din ya tsaya gefe titi,
Da sauri yafito yanufi gefen kwata ya tsugun'na.
Doguwa ce fara tana da kyau balaifi saidai tana da yar kiba kadan
wanda yanayin jikin nata yanuna idan zata samu Hutu zatayi irin kibar nan ne mara fasali, sayen take da uniform din islamiyya riga da wando da hijab shekarunta zasu kai 18 to19, tunda ga nisa *Habeeb* yake kallonta ta madubin mota har tazo kusa da shi zata wuce, ahankali yaleka ta wundon motar ya cigaba da kallon bayanta,
Wato tafiya take ahankali saidai a yadda take takun tareda motsa jikinta, zaka fahimci cewa tana yinsa ne domin daukar hankalin duk wani d'a namiji, gyaran murya *Harees* yayi Wanda yasa *Habeeb* juyawa dasauri suka hada ido daure fuska *Habeeb* yayi, shikam *Harees* murmushi yayi tareda cewa yaaa! kodai..?
Da sauri yace kodai me..? yace ah! kar kadamu Ina zuwa, dasauri yabi bayanta sallama yayi mata ahankali tajuyo ba tareda ta amsa sallamar ba sai yatsina fuska datayi saidai kuma gani kyakkyawa saurayi yasa tasaki fuska,
Yace sannu ko..tace yauwa yace don Allah kiyi hakuri na tsayar dake kan hanya tace lah! ba komai , yace dama inason magana dake ne saidai ban saniba ko" Unguwar nan kike..? tace "eh ga gidanmu ma can tafadi tareda nuna wani kujajjan gida me da kali duk ya faffashe, yace toh" kije gamu nan zuwa kofar gida sai muyi maganar tace toh".
********
Gurin *Habeeb* yakoma yace masa don Allah yazo yara ka shi, ba musu yafito ya kulle motar sannan suka nufi kofar gidansu yarinya, tsaye suka isketa suna hada ido *Habeeb* duk sai ta rikice domin wani irin kyau tagani da kwarjini atare dashi lokaci guda kuma sai taji mugun sha'awar shi ya dira zuciyarta,
Bayan sun gaisa sai *Harees* yace yasunan mlmar..?.tace Murjanatu amma a nakira Na *JANA,* yace masha'allah mlma murjanatu ni sunana *Harees* dan'uwana kuma *Habeeb* KO" kice *BB smart,* yaganki ne yaji kinyi masa ma'ana yana sonki kuma da aure dafanta Zaki karbeshi hannu babbiyu, Dasauri tace badamuwa na amince,
yace Alhamdulillahi toh" Bari nadan Baku gurin KO..? tace toh," ya kalli *Habeeb* dayayi sororo yana kallon shi yace zanjiraka amota, baijira abunda zayace ba yawuce, ahankali *Habeeb* ya kalli *Jana* wadda yarasa meyasa yaji wani abu game da'ita tun lokacin daya hango ta, murmushi yayi Wanda yasake gigita *Jana,*
karo na farko kena arayuwar sa daya taba tsayawa da budurwa, don haka duk sai ya rikice yarasa abunda zayace can saya tsinci kanshi yaname ce mata inafata dai baki yiwa wani alkawarin kanki ba..? Dasauri tace "a ah yace toh" shikenan ai kinji abunda dan'uwana yace KO..? tace "eh, yace toh" kibani dama naringa zuwa gurinki idan mun fahimci juna saina turo magaba tana, domin bana son adauki lokaci tace badamuwa Na amince,
yace toh" nagode sannan yasa hannun aljanu yaciro kudi da baisan konawa bane yamika mata, tareda cewa ga wannan sai mun dawo anjima, jikina rawa takarba tana godiya sannan ya'iske *Harees* suka tafi gida.
*Wacece Jana*
Kamar yadda tace asalin sunan ta kenan Murjanatu Sani kawayenta ne suke kiranta *Jana,*
Mahaifinta mlm Sani _shoe maker_ ne wato me gyaran takalma talakane shi talak saidai yanada wadar zuci sana'arsa kenan gyaran takalmi kuma dashi yake ciyarda iyalinsa,
matarsa daya Dije ya'ya'nshi uku Jafaru shine babba kuma shi ma sana'ar yake don baiyi karatu ba ,sai Binta ita tayi primary school Bayan tagama aka kukuta akai mata aure, sannan *Jana,* mahaifisu sani shushaina yana'iya bakin kokarin sa nagani yabata tarbiyya, saidai sam *Jana* bata dauka, domin ita banajin magana tana da mugun son abun duniya gata da high test domin tasha cewa, kamata yayi ace ita yar gidan masu kudi ce ba yar gidan talakawa ba,
tagama primary da kyar tashiga secondary tanayin junior wec tadaina zuwa, takama bin gidajan kawaye da dakin samari musamman idan ta shirya zuwa islamiya, *Jana* kenan indai zaka bata kudi to" zata baka jikinta kayi yadda kakeso dashi so biyu tana zubar da ciki, ganin hakan ne yasa mahaifina yace tafitoda miji aimata aure takiya don haka sai ya kyale ta, tanada wani saurayi guda da take bashi kanta yayi yadda yakeso ba tareda yabata kocici ba,
"Wani lokacin ma ita kebashi kudin domin tana mugun son Ado saidai tanajin aranta bazata'iya auren shiba, domin shindi talaka ne ita kuma tace gaskiya bazai yiyu'a haifeta agidan talauci ba, sannan kuma tayi aure agidan talauci ba shi kuma Ado baya sana'ar fari bare Na baki, sai zaman kashe wando da shaye-shaye wannan kenan.
Muje zuwa
A
*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)
Tareda
โ๐ฝ
๐นMeenart๐น
[7/2, 11:28 PM] My Ameena: ๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
1โฃ5โฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT* ๐
SADAUKARWA
*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*
___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
โ๐ฝ
_*Bismillahirrahamanirraheem*_
Da gudu *Jana* tashiga gida tana ihun fadin yau tasamu irin mijin datake son ta aura, zama tayi tsakar gida saman kujera yar tsugun ne, jikinta narawa tafara kirga kudin da bata taba rike irinsu ba tunda take,
dubu hamsin da biyar takirga, wani ihun tasa tareda cewa tayi miji wlhy gobe kasuwa zata tayo siyayya dama kayantaa duk sun tsufa, sannan ta kalli mahaifiyarta dake tsugunne abakin murhu tana faman kokarin hura wuta da toton masara,
tace Dije _haka suke kiranta_ kingani ko"...? dama nace maku nidin yar gidan arzikice, cikin sanyi murya tace murjanatu waya baki kudi masu yawa haka...? dariya tayi tace mijina, dasauri Dije tace ayya murjanatu bazaki daina bin samarin banza ba wato ma acikin su harda da miji kika ajiye ko...?
wani irin kallo tayiwa uwar tareda cewa kefa Dije haka kike toh" mijin da zan aura nake nufi fa, nan dai tafada mata abunda yafaru tsakanin ta dasu *"Habeeb*,
Ajiyar zuciya Dije tayi tace da dai yafi maki da wannan shashancin dakike tafaman yi, agari Allah ya tabbatar da alkhairi tace ameen toh" Saiki fara fadawa Baba tun yanzu nasamu miji don haka zanyi aure nabar wannan gidan da babu komai cikinsa sai zallar talauci, takarashe fadi tareda tashi tana yatsina fuska tashiga dakinta Kai Dije ta girgiza tareda cewa Allah ya shirya ki.
Can saiga *Jana* tafito sanye dariga da zani nawata kodaddiyar n atanfa tareda yafa wani tsohon gyale hannun ta rike da jaka, Dije ta kalleta tareda cewa ina kuma zakije yanzu da yamma..? ba tareda ta kalli inda Dijan take ba tace gidan su Shafa zani _shafa kawar tace_ sannan tafita abunta, Kai Dije ta girgiza tareda cewa Allah ya kyauta.
Da *Jana* tafita bata tsaya ko'ina ba sai dakin Ado saurayin ta, yana zaune bakin kofar dakinsa sai faman busa taba yake yana ganin ta yamike tareda Kama hannun ta suka shiga daki,
Ba tareda bata lokaci ba suka shiga aikata bad'alarsu saida sukayi mai isarsu
Sannan suka sararawa kansu, sai *Jana* taciro kudi dubu goma taba Ado jikinsa narawa yakar ba yana cewa *Jana* Waya baki kudi..? tace mijin dazan aura fuska ya daure tareda cewa yanzu da gaske bazaki aure niba saboda banida kudi..?
Cikin sanyi murya tace kayi hakuri Ado gaskiya niba zan'iya rayuwa acikin talauci ba, yace toh" yanzu kina nufi idan kinyi aure mun rabu kenan..? tace "a ah zansan yadda zanyi muna haduwa yace toh" shikenan kinsan nariga nalasa zumarki tace nima haka, sannan tafito ta tafi gidansu Shafa tafada mata tareda cewa gobe zata rakata kasuwa tayi siyayya daga nan suje gidan Aunty Binta tace toh"
sannan takoma gida.
*******
Kamar yadda *Harees* yace zasuje gidan lnna Hafsatu gurin Safeena sunje,
Safeena takasan ce doguwa kyakkyawa yar siriri, yace saidai tanada _sharp_ me kyau itadin ba fara bace saidai kuma ba za'a kiranta baka ba irin _chocolate, color_ din nace alokacin shekarunta goma sha bakwa alokacin satin ta biyu dagama secondary.
Ba tareda bata lokaci ba *Harees* yafada mata abunda ketafe dasu ta, amince tareda nuna farin cikinta.
*Bayan kwana biyu*
**********
Acikin kwana biyu *Habeeb* da *Jana* sun dan shaku ba laifi sun kuma fahimci juna, domin *Jana* ta'iya jan hankalin namiji da kalamai tareda kwarkwasa, don haka tuni tasamu dan wani matsayi agurin *Habeeb* kodon kasan cewar su talakawa, duk da bawani mugun jinta yake aransa ba, saidai kawai yana jin tausayin ta, kuma yaji aranshi yana son ya aure ta kodon yanayin dayake ciki,don haka yanemi tabashi dama yaturo magaba tanshi.
ba tareda bata lokaci ta amince mashi yaturo gidansu don a tsayar da magana, mahaifin *Jana* yakarbrsu Baffa hannu bibbiyu cikin mutunci musamman ma dasuka fadi cewa *Habeeb* dan Alh Hashim soro ne tsohon gwamnan su me adalci, su Baffa sunji dadi yadda yai masu, kuma batareda bata lokaci ba yace yaba *Habeeb Jana* *KYAUTA* bayan sadaki baya bukatar komai,
Don haka sadaki kawai su Baffa suka bayar akasa biki tareda na *Harees,* Wata daya wanda zayayi dai-dai da lokacin angama gini sabon gidajen da Abba yasa aginina masu a New G R A,
*******
Akwana atashi bawuya agurin Allah saura sati daya buki alokaci tuni angama ginin gidajen harsun koma inda aka gina part uku biyu _upstairs_ Na Abba da *Habeeb,* daya kuma na Baffa shi yace bayason gidan sama, sai nasu Baffa Al-mustafa wanda yake ta can bayan nasu *Habeeb* suma tsari gini iri daya ne Dana su Abba,
wato Baffa Al-mustafa da *Harees* sunan _upstairs_ ne su kuma Kakanni *Harees* irin ginin su Baffa akai masu domin suma basu son gidan sama.
Su *Jana* anata shirye-shiryan buki itada Shafa, *Habeeb* ya cikasu da kudi sosai ranan Wata Jumma'a, *Habeeb* yaje gurinta dama tace sai yazo yakai ta ta gaida Hajiya, saidai ita badon tagaida Hajiyar zataba saidon taga gidan da'akace duk New g r a babu kamar shi agurin kyau da tsaruwa,
Koda suka isa direct part Hajiya suka shiga, *Safeeya* da *Sadeeya* suna zaune afalo sunsa Hajiya tsakiya sai faman shagwaba sukeyi mata, suna sanye da riga da wando na fakistan yai masu kyau sosai, sallamar *Habeeb* ne yasa sukayi shuru, Hajiya ta amsa tareda cewa yauwa aiga Hamman kunan,
Don Allah Kara bani da rigimammun yaran nan, waisu sai dole nasa Musa direba yakai su gidan "Addansu Mamu nace subari sai gobe tunda yau Murjanatu zatazo sannan yanzu karfe 5:00 yamma tayi waisu a ah saidai sunje, fuska daure yace toh" ance baza kuje yau din ba kuma duk yarinyar data sake damunta sai na 'bata mata rai tunda ku baku da hankali,
bayan yagama fadin haka sai yakalli *Jana* yace zaya shiga gidansu *Harees* idan sun gaisa da Hajiya da "Inna su *Sadeeya* su kawota tagaida Hajiyar su *Harees* tace toh" , sannan yafita bayan sun fito part su Inna sannan suka nufi gidansu *Harees.*
Suna gaba tana biye dasu abaya saifaman kuskus suke suna kallon *Jana* suna dariya kasa-kasa, KO" meke basu dariya oho!, ita kuma *Jana* data kalli *Sadeeya* sai taji gabanta yafadi domin kyan *Sadeeya* ya firgita ta sosai, sannan tarasa meyasa idan suka hada ido saitaji wani irin tsoro tareda faduwar gaba,
Tsayawa sukayi suka sata tsakiya sai kuma suka kalleta sannan suka hada baki sukace, tab amma dai gaskiya Aunty *Jana* ke banza Ce, kirasa wanda zaki aura sai Hamman *"Habeeb* , ido tazaro ๐ณcikeda tsoro tace meyake dashi.?
Sukace tab! ke baki San cewa shi" mugu bane rankwashimu fa yake harda da duka kema idan kiga aureshi haka zaya dingayi maki, KO" *Feeya* tace "eh mana inji cewar *Sadeeya,* ajiyar zuciya tayi murmushi duk da cewa tasan acikin maganar su akwa zallar kuruciya hakan bai hana tajin zafin banza da suka ce mata ba,
Sai tace aini bazai duke ni ba tunda ni matarsa ce Ku kuma kannan shine zaya iya dukan ku idan kunyi masa laifi, ido suka hada tareda tabe baki, *Sadeeya* tace toh" aishiko ba'ai masa laifi ba sai yadinga yima mutane mugunta yana zare masu idanun nan nashi masu ba mutun tsoro ko...?
*Feeya* tace "eh mana bayan ya duke ka koya rankwashe ka sai kuma yace" wai kayi ma shi shuru๐คซ tafadi tareda nunawa dai-dai lokacin da suka isa kofar gidan suka kwankwasa kofar megadi yabude masu suka shiga, basu Dade ba su kafito suka koma gida.
*Habeeb* ne ya Kallin *Jana* yace naga tunda muka baro gida baki ce komai ba sannan naga ranki kamar yabaci lafiya..?
Yatsina fuska tayi sannan tace gaskiya "kannan ka sunbata mun rai sosai musamman ma wadda tafi kyau din nan, dasauri yace me "sukayi maki, nan tafada ma shi abunda su *"Sadeeya* suka cema ta,
Rai bace yace tayi hakuri zatayi maganin su tace toh" sannan yasauke ta tashiga gida azaure ta tsaya tana lekensa, yana rebas tace yan'iskan yara Allah yasa idan yakoma yaimasu dukan tsiya harma dai wannan meshegen kyau kamar aljana sanna taja tsaki tashiga gida shima ya nufi gida.
Part din Hajiya yashiga bai same su nan ba, don haka dasauri yafito yanufi part