Showing 147001 words to 150000 words out of 163788 words

Chapter 50 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt

11 Jul 2024

32431

bata sake ganin shiba, wanda hakan bakaramin dadi yaimata ba domin tasamu damar zuwa gidan Alh Barau suna holewarsu san ran su.




Shikam ado saida ya kwana biyar suna gadin *Deeya* sannan yabar dajin, bayan ya gargadi su mangal akan sukula da *Deeyar* karta gudu, sannan yanufi gidan kakar shi don yaga Junior saida kuma ya'iske shi kwance ba lafiya sosai duk yarame, hankali tashe ya dauke shi yakai shi asibiti inda aka kwantar dashi, dole yaje yadauko kaka dan tazauna dashi.




Amma sai masifa take mashi wai yarabo d'a da uwar shi maimakon yabari har yakara girma sannan yaje yadauko shi, sai beyi hakan ba saboda shidin bakin mugun d'an gaba da fatiha, bai bitakan ba saida yabiya kudin magani, sannan yace mata to kakar d'an gaba da fatiha zanje gida nadawo ki kulamun da yarona dakyau sannan yafita,




cike da masifa tace shege da aisai bakaje kazakulo uwarka daga kabari, tazo satayi maka jinyarshi dakyau.




*Jana* kam hankalin ta yafara tashi na rashin inda ado yakai Junior, bayan tadawo daga gidan Alh barau tana zaune afalo tana tunani, sai gashi yashigo fuska hade yace keee! zubomun abinci yinwa nakeji yafadi yana kokarin zama akojajjen kushin din falon, dasauri ta tareshi tareda fadin mlm aibaka bani kudin girkinba balle nay sannan gidan uban wa kaje yau kwana biyar kenan rabonka da gidan na, sannan Ina ka kai mun yarona eyeee?...,




Cike da masifa yace gidan ubanki naje shikuma Junior saikin shakeni naji kamshi mutuwa sannan zan fadama ki indan nakaishi kinji KO?..., itama cikin masifa tace wlhy baka isaba saika fitomun da Dana du inda kakai shi tunda bakai kadai kedashi ba eheee.




Cikin tsawa yace keeeee! kalleni da kyau ni ba sa'anki bane dazaki nagaya mun maganar daki kaga dama kinji KO?.. "
Junior dai dana ne nakuma Kai shi inda naga dama don haka sai kiyi abinda zakiyi, cike da masifa taci kwalar rigarshi tareda fadin wlhy baka isaba saika fito mun da D'ana.




Aikam cikin bacin rai yafara dukanta kamar jaka yana fadin dan ubanki ni zakiciwa kwala?..tab! zakiko ci ubanki yau agidan nan, kai! kaga mun shegiya, aikam nan yadinga jibgarta saida yai mata dukan tsiya yabarta kwance tana nishi azaba, sannan yafita abishi.


_Nikam nace wayyo *Jana* kinga arkane๐Ÿ˜‚_




*_Bayan kwana biyu_*
******
Wanda yayi saidai da sati daya kenan da ba cewar *Deeya* Da misalin karfe 5:00pm,
tana zaune akan dankwalin ta data mayar dashi tabarman, ta jingina bayanta da bango tun bayan data idar da sallar la'asar take tasbihi da hannu yayinda hawaye keta faman tsiya a idon ta,




Dasauri ado yashiga kangon wanda yasata firgita domin mugun tsoron shi takeji, tsugun nawa yayi agabanta tareda tsura mata jajayan idon shi wanda kana gani zakasan yayi shane, jikinta sai rawa yake cikin kuka hade da tsoro tace dan Allah kakaini wajan hmm na, na tabbatar duk abinda kakeso zaya baka,




hannu yasa yadamki gashin kanta kamar yanda yasaba aduk lokacin da yai sha yakoshi sai yabata wahala ta hanyar damkar mata gashi kai, kara tasaki cikin kuka tace kayi hakuri dan Allah.




murmushin mugunta yasaki sannan yace kikace duk abinda nakeso zaya bani ko?...kai ta gyada alamar "eh yace yauwa haka nakeson, yau satinki daya kenan da muka saceki ko?..tace "eh yace yauwa yanzu kam nasan duk wani tashin hankali na duniya mijinki da iyayenki sun shiga, wanda dama inason hakan ne shi yasa na tun ranan ko flashing ban sake yi mashi ba,




Saida yau zan sa daki da shegen katon mijin naki me dan banzan karfi kamar doki, amma sai yabani miliyon ashirin tukun na idan kuma ba haka ba saina farke cikin nan naki naga abinda shegen ya kunsa maki, sai kuma ya saki wata mahaukaciyar dariya sannan yace Kai! mangal
mijinta kamar irin mutanan nan nada yanema sunan su?... Dasauri mangal yace Oga samudawa, cikin dariya mugun ta yace hakane to bari mu kira me kirar samudawa yakawo mana dalaaaa! mubashi aljanar matar shi yakareshe fadi yana sake sakin wata dariyar da karanta yacika kangon, Sannan yaciro wayar shi ya kuna yalalibo lambar *Habeeb.*




******
Aban garen *Habeeb* kam ba'a cewa komai duk yanda kuke tsamanin shigan shi tashin hankali yawuce hakan, hakama *Feeya* da Hajiyarmu su kam harda kwanciya agadon asibiti abin gwanin tausayi sosai rashin *Deeyar* ya taba su, saidai basu kai *Habeeb* ba, itama inna kam har da zazzabi tayi saidai kaf family babu wanda yasani daga baffa sai *Hafeez.*




Addu'a kam sosai suke yin ta musamman *Habeeb* da Baffa wani kusan kullum sai yayi istahara, dan gani halin datake ciki shin tana arayene kota mutu saidai kuma duk lokacin da yayi yana ganin ta araye saidai cikin dubu tana tsananin kuka alamar tana cikin matsananci hali,




Amma yau dayayi istaharan ya ganta cikin haske wanda hakan yana nufin Allah yakusa kubutar da'ita daga hannun mugayen mutanan don haka suka tsananta da addu'a.




*Habeeb* suna zaune afalon kasa dake part din su Abba shida *Harees,* tun bayan da akagama mitin din dasukayi duka family wanda anyishi ne akan sace *Deeya,* to bayan kowa yafita har dasu abban sai su biyu suka rage suna sake tattaunawa ne akan yanda zasu bullowa ado, aduk lokacin daya kira dan akawo mashi kudi
domin suna da tabbacin zaya kira tunda yau sati daya kenan,




Aikam suna cikin haka saiga daya daga cikin wayoyin *Habeeb* dake zube akan tebur tana kara, da kamar bazaya dubaba saida *Harees* yace dan'uwa duba kagani ko "shine, tsaki yayi tareda dubawa sai yaga wata lamba tsaki yasake yi ganin ba lambar ado bane har zayayi rejecte kenan, sai *Harees* yace "a ah kar kayi haka ka dauka muji ko wanene.




daukan yayi tareda kannu karan wayar yanda za'aji magana, aikam saiga dariyar ado ta bayyana dasauri yarintse ido domin jiyayi kamar ya watsa mashi garwashin wuta a zuciyar sa, yanajin sa yanata dariya saidai yayi me isarshi Sannan ya tsaya, yace abokina yakake cikin kasaita *Habeeb* yace....












*_Duk me son cigaban KYAUTAR ALLAH CE don yaji yanda za'a kaftaaa wasa tsakanin Habeeb da ado, tofa sai yabiya kudi naira nagugan naira dari uku da hamsin kacal๐Ÿ˜‰ Kai! ๐Ÿ˜ณto yaseeeen wasa nakayi ๐Ÿ˜‚, labarin KYAUTAR ALLAH ai KYAUTA CE babu KO kwandalla ina nufin kosisi aha! ๐Ÿ˜œdon kar wata taza geni eheeeee_*๐Ÿ˜.










Muje zuwa




*_Don jin yanda za'a kafta wasan wanda zatayi matukar kayatar wa, ga Habeeb ga ado kuttt haduwar zata bada kalaaaa._*๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚




A




*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)




Tareda




โœ๐Ÿพ


๐ŸŒนmeenat Lufhat๐ŸŒน
[11/9, 10:13 PM] My Ameena: ๓ฐผ๓ฐผ๓ฐผ๓ฐผ๓ฐŠ ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ


_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_


๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ


8โƒฃ0โƒฃ




WRITTEN
By
๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ


OR


๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ




SADAUKARWA


*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*


___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~






โœ๐Ÿฝ




_*Bismillahirrahamanirraheem*_




_NOT EDITS_




Yanda kake haka nake, dariya ado yayi yace Kai! abokina bazaka taba zama yanda nake baka ba, aranshi yace Insha'allah har abada bazan taba zama irin kaba,




afilin kuma yace saboda me kace haka?...yace saboda nasan kai kam kana cikin matsanancin bakinci datashi hankali na rashin sanin inda nakai maka matar ka naboye, yayinda nikuma nake cikin tsananin farin ciki saidai kasan me?...




Cike da takaicin shi yace saika fada, dariya yasake yi sannan yace farin ciki danake ciki yau yafi na kullun, saboda zaka bani dalaaaah! ni kuma zan baka matar ka.




Wani miskilin murmushi *Habeeb* yayi, wanda harsai dayaba *Harees* mamaki, sannan yace anzo gurin shiyasa nace maka yanda kake haka nake,




Kai kana farin cikin zan baka dalaaaa! nikuma Ina farin cikin zaka bani matata hakane KO?...yace "eh haka ne yace to yanzu yaza'ayi?...




yace na yanke shawaran yanzu miliyon ashirin zaka bani, idan kuma bazaka bani ba Zan kashe matar ka ta hanyar farke mata wannan katon cikin nata, koba komai naga abinda ka kunsa mata yakareshe fadi tareda sakin dariya sannan yace to yah! me kace?...




ahankali *Habeeb* yasaki wani asirtattacen ajiyar zuciya wanda KO" *Harees* dake kusada shi bejiba to balle Oga ado.




Sannan yace baka da matsala indai dalaaah! kake so kasamu fadamun inda kake sai nakawo maka ko?.




Yace zan fada maka amma karkayi kuskuren zuwa dakowa musamman yan'sanda, muddun kazo dasu to zan kashe matar ka.




Jiyayi kirjinsa yai wani irin mugun bugawa amma saiya basar ta hanya fadin Kai! haba ai wasan daga ni; sai "kai muke bugawa, saboda haka ba abinda zaya kawo yan'sanda ciki.. dariya yayi yace Kai! abokina *BB* smarter ashe dai kanada matuka wayo...


_Oh!๐Ÿค” readers kuji ado da renin hankali๐Ÿ™„_


Dariyar kasan lebe *Habeeb* yayi sannan cikin turonci yace jaki to ai ma'anar smarter din kenan, dasauri adon yace "eh me kace?...cikin turanci yasake cewa Oh! ashefa da jahili nake magana, afili kuma yace nace" ne Kai kayi wayo balle ni yanzu dai fadamun inda kake.




yace kasan hanyar liman katagum KO?...yace "eh nasani, nan dai yai mashi kwatance tareda sake gargadin shi kar yakira yan'sanda sannan yasake sakin dariyar mugun ta tareda kashe wayar.




Zumbur *Habeeb* yamike wanda kusan lokaci daya suka mike da *Harees,* yace kai amman wannan akwai shege, *Habeeb* yace humm aini tunda nake ban taba ganin dankwalin mutun jakin irin shiba, yace gaskiya kam jakine wlhy yace barshi ai yau sai yagane yayi kuskuren shiga gonata
yanzu bari naje na shirya.




*Harees* yace to yanzu yaza'ayi gashi yace kar kazo da kowa to balle police?..




Murmushi yayi tareda dafa kafadar shi yace alhamdulillahi mukam mun godema Allah, da ya azirta mu da ilimi yace kwarai kuwa, yace to da ilimin mu zamuyi aiki zanje zansa wannan yar karamar kwanfutan nan wacce take nuna maka ta'inda mutun yake, so kaima sai kasa taka kabiyo ni sannan kazo da yan'sanda bana bukatar yan jarida kosu yan'asanda saboda sutafi dashi, su'ajiye mun shi bayan naci uban shi sannan nabasu umarni suyi ta dukan shege har saiya fadi uban dayace" yasake shigowa rayuwata akaro na biyu.




Yace to shikenan tareda fita da sauri, yayinda shikuma yahaye sama da gudu-gudu inda ya'iske Hajiya da su adda mamu kasan cewar basu tafi gida ba, nan yafada masu yanda sukai da ado da kuma yanda suka tsara tun karan shi shida *Harees,* murna sukayi tareda yimashi fatan nasara.




Cikin lokacin kan-ya yashirya cikin kananan kaya Riga brown wando black da takalmi boot, har da hulla face cap da'alama bayason agane shine, kasan cewar yabar kasumba buzu-buzu don haka ba kowa zaya gane shidin bane.




Dasauri yafito hannun shi rike da bakar jaka katuwa wacce yazuba kudin, *Hafeez* yace hmm nabiyo ka?..yace "a ah kadaije kutaho tareda dan'uwa yace to shikuma yafita da sauri.




Zaune ya'iske su Abba tsugun nawa yayi yai masu bayanin komai, nan suma sukai farin ciki tareda yimashi Addu'an fatan samun nasara, sannan yace ma saminu su tafi kasan cewar dama yakira shi a waya yace yacire uniform din shi yasa wasu, don haka shima kana nan kayan yasa suka hau mashin Saminu ne yaja mashin din, suka tafi bakin *Habeeb* dauke da Addu'a cin galaba akan makiya.




******
Ado kam yana gama waya da *Habeeb* yace mangal yau zamuyi kudi sosai, yace haka ne oga, yanzu kaje gurin wannan mutumin yaka baka kudin motar dama aiyace" sai yauko?... _motar *Deeya* suka cire mata lambar suka kai siyarwa, shine zasuje karban kudin._ mangal yace "eh haka, to kayi sauri kafin ba samuden can yazo yace to tareda fita da sauri.




Saida su *Habeeb* sukayi tafiya sosai sannan suka kai isa inda ado yai mashi kwatance, sannan suka tsaya yace ma saminu ya tsaya shizaya karasa ciki yace OK sir.




Yayinda shikuma ya nausa cikin dajin rataye dajakar kudin, yanayin yana kiran lambar adon saidai bai shiga ba saboda matsalar sabis, saida yayi tafiya me nisa sannan yasa meshi yana dauka yace ya'iso yace to yakara yin tafiya zayaga wani kango to nan zaya shiga yace to, haka KO" akayi yana shiga ya'iske su tsaye sunsa *Deeya* tsakiya yayinda ado yadora mata bindiga akai.




Dasauri *Habeeb* yanufe su saidai ado yahana shi karasowa ta hanyar cewa yana karasowa gurin zaya har beta, don haka ya tsaya cak! idon shi yana kan *Deeya* wacce itama idon ta yana kanshi yayinda hawaye ke ta gangarowa ahankali yake girgiza mata Kai! alamar tayi shuru tunda gashi yazo.




Dariyar da ado yasaki ne yasa *Habeeb* daga kai ya kalle shi aikam tuni idon shi suyin jajir tsabar bacin rai, yayinda yaji kamar yaje yashake shege harsai ya mutu,




Saida ado yayi dariya sosai sannan yace barka da zuwa abokina ina fatan ka'iso lafiya?...kai ya gyada mashi cike da bakin ciki aran shikuma yana tunanin irin hukunci da zayayi mashi, yahuce takaicin abinda yai mashi.




sannan yace yayi kyau to bude jakar mugani, haka yabude ado nagani kudi yan naira dubu dubu yasaki dariya yace aikin ka yayi kyau ka tabbatar suncika miliyon ashir din?..kai ya gyada, sai yace to daga hannun ka sama ahankali yadaga hannu yayinda ado ya kalli wanda yake kusa dashi.




yace jaga, yace yah Oga?..yace jeka chage shi idan yazo da makami ka karbo mun, yace Ok" Ogo zuwa yayi ya chaje *Habeeb* amma baiga komai ba don haka yajuya yace Oga banga komai ba fa, yace to dauko kudin dauka yayi tareda kallon *Habeeb* wanda shidima kallon shiyake cike da tsana, yayinda jaga ya juya yakai wa ado kudin.




Saida ya karba sannan yasaki dariya tareda kallon *Deeya* cikin tsawa yace keee! tashi kibi mijinki, ahankali tamike dakyar tasa takalmin tareda daukar dan kwalinta dake shinfide akasa, tayi tafiya daya biyu ana uku jiri ya kwasheta ta tafi luuuuu! zata zube kasa,


aikam tuni *Habeeb* yayi Wani irin mahaukacin tsalle yatare ta tafada kirjinshi, lokaci daya suka sauke ajiyar zuciya sai kuma ka tasaki kuka yayinda, shi kuma yace yah! ilahee my honey *Leemah* ta kece kika zama haka?.




Dai-dai lokacin da yan'sanda su kaima kangon diran mikiya har dasu *Harees* kasan cewar tuni sun karaso, dasauri wani dan sanda ya bige hannun ado bindigar tafadi kasa kasan cewar ya shagala da kallon kudi, yayinda wani dan sandan yai saurin dauke bindigar.




Sannan cikin tsawa yace masu you're under arrested, hakan neyasa suka saki jakar tareda daga hannuwa sama,
da sauri wasu yan sandan biyu sukaje suka ka masu,




Dasauri su *Harees* suka isa gurin su *Habeeb* yana rugume da'ita yana fadi it's Ok" my honey *Leemah* ina tareda ke kinji?..cikin kuka tace pls sweet hmm na mutafi gida banason sake ganin wannan mutuni shi mugu ne yanata bani wahala, cikin bacin rai yace kiyi hakuri Laifi na ne da ban kilallace kiba har hakan tafaru,




amma daga yau hakan bazaya sa kefa ruwa ba insha'allahu kinji?..kaita gyada tana sake tura kanta a kirjinshi.




Dai-dai lokacin da wani dan sanda yakara so gurin su, hannun shi dauke dajakar kudin yace Sir gashi *Hafeez* yakarba sannan yace zamu tafi dasu, dasauri *Habeeb* yace ina zuwa kallon *Deeya* yayi yace pls honey *Leemah* ta bani minti biyu kinji?.




Cike da shagwaba tace nidai sweet Hmm na mutafi gida banason sake zama anan gurin inajin tsoro sosai, yace yanzu zamu tafi insha'allahu amma kiyi hakuri kibani minti biyun da nace kinji zanyi wani abune kadan, tace to tareda zare jikinta daga nashi, dasauri yamike yanufi inda su ado suke tsaye.




Kallon police din dake rikeda adon yayi yace sake shi ka matsa baya sakin shi yayi tareda matsawa,
Wani mugun kallo *Habeeb* yawa tsawa ado me cike da tsana, sannan ya kalli sandar shi ai kam cikin bacin rai yai bal da sandar hakan ne yasa ado yai taga-taga zaya fadi,




Dasauri *Habeeb* yata tareshi tareda zuba mashi lafiyayyan naushi a fuska aikam take jini da majina suka fara ambaliya, sannan yaci kwalar rigarshi dasauri yan'sanda suka nufesu tareda fadin Sir" kabarshi zamu hukunta shi a station..tsawan yadaka masu suka tsaya cak! domin wani mugun kwarjini yai masu,




cikin bacin rai yace sai nafara hukunci tashi akan abinda yaimun, wanda dama nace ranan damuka hadu sai yagane bashi dawayo dukan shiya shigayi tako'ina, yana fadi yausai kasan kashiga gonata akaro na biyu jaki kawai har ni zakakira abokinka?... for how dazanyi abota da jahili fasikin mutuni rinka...tirrrrr,




Allah yaimu tsari da aboki mazinaci shege shine harda sace mun matata ka boyeta awannan mugun dajin kanata bata wahala ko?..,to yau sainayi maka illla akaro na biyu jaki kawai.. Duk yanda yansadan suka so kwatar ado ahannun *Habeeb* sunkasa don haka suka kyale shi saida yaimasa lilis,
sannan yabarshi kwance yace sutafi dashi.




Dasauri yaje yadaga *Deeya* tareda fadin sorry *Leemah* ta tashi mu tafi asibiti dan'uwa yadubaki kinji?..ahankali tace to dakyar ta'iya mikewa tsaye saboda Wani irin mugun rikewa da maranta yayi, dasauri tarike maran da hannun daya, yayinda damki hannun *Habeeb* Da daya hannun cikin tsanani azaba,




tace wayyo Hmm na ka taimake ni marata zata fashe, cike da tsoro yace "a ah *Leemah* ta bazata fasheba Insha'allah yakareshe fadi tareda kokarin daukar ta, sai yaga jini yana gangarowa ta kafarta.




Cike da tsoro yace yah! ilahee *Leemah* ta bleeding kike?..dasauri *Harees* yace Dan'uwa dauke ta mutafi asibiti cak! ya dauke ta suka fita, dasauri *Hafeez* yabude mashi kofar bayan mota yasata tareda shiga ya rungumeta sai zuba mata miliyonin sannu yake, *Harees* yaja suka nufi asibitin.




Suna isa asibintin direct dakin haihuwa *Harees* yace akai ta domin tuni yaga ne haihu wa zatayi, wanda tsabar wahala da tashin hankali zaisa ta haihuwa ta wata bakwai,




Adakin haihu wa kuwa sai gumurzu wahala *Deeya* take, sosai take shan wahala, wanda haka ba karamin tayarda hankalin *Habeeb* yayi ba gaba daya yafita hayyacin sa, kamar yanda itama tafita hayyacin ta, rike yakeda hannun ta gam sai zuba mata sannun yake tareda goge mata gumi kamar zayayi kuka, sai addu'a yake zuba mata,




yayinda *Harees*
da wasu nurse biyu suke ta faman kokarin ganin ta haihu.




Bayan bakar wahalan data kwashe tsawon lokaci tanasha sannan,
cikin ikon allah tahaifo yaranta maza biyu kyawawa masu kama da *Habeeb* sak!, saidai kallo daya zakai masu kagane su din bakwaini ne.




Saidai da'alamar suna cikin ko shi lafiya, domin suna kuka saida uwar su kam tana gama sambalo su
tafara wani irin jijjiga can kuma sai numfashi ta ya tsaya cak! jikinta yasaki hannun ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login