Showing 63001 words to 66000 words out of 163788 words

Chapter 22 - KYAUTAR ALLAH COMPLETE by Amina umar faruk.txt

11 Jul 2024

34780

tareda marurru kan dayai mata ba kamar yadda taji zafin karyewar asirin, Bayan ta gama wa Junior wanka sai itama tayi ko data fito ta'ise shi yai barci wanda kana gani zakasan barcin wahala yake.




Dasauri ta dauki wayarta dake kan gado afili tafurta Oh! Allah yasoni dazu na'ajiye wayata anan, da yanzu tana dakin shi kilama idan naje dauka yakara mun wasu marurrukan, layin Shafa tafara nema bayan tagani saita kira cikin sa'a tasa me ta bude karan wayar tayi, don haka anaji daga can Shafa ta dauka tareda cewa ke! ta *BB* bada kanki asare kije gida ki ce yafadi mutanan small London kuna shanawa fa,




*Jana* tace hmm Shafancy kenan ai yau nafada maki duk wani shanawa babu shi, dasauri Shafa tace kamar ya bangane ba?... nan tafada mata duk abunda yafaru wani uban ashar Shafa tayo tareda cewa amma dai ke banza ce wlhy shine kika Bari har "suka hada?..tace wlhy Shafancy banyi tsannanin zaya dawo dawuri ba, tunda bai saba dawowa a wannan lokacin ba, yanzu yaza'ai kenan?..




tace gaskiya ban saniba sai dole mun koma gurin mlm "Dare, kuma kinsan shiba'ai masa sako saidai kaje da kanka tace haka ne yanzu kuma kozamu dawo gida sai anyima yara hutun makaranta, gashi ban sannan lokacin da zasu yi hutun ba, don Allah Shafancy idan akwai wani gurin daki kasani kifara zuwa mun kafin nadawo kinji?..




tace to Zan duba saidai bayani kudi, *Jana* tace ba damuwa kibayar idan nazo saina baki tace to shikenan sannan ta kashe wayar, saiga Lili tashiga dakin da gudu tana cewa Aunty *Jana* buyeni "Daddy jaya kai Aunty *Deeya* allula bana cho yaje dani, _kasan cewar haka *Habeeb* din yace" mata saboda tace zata bisu itakuma ba tason allura._




Dasauri *Jana* tace to zo nan kiboye tafadi tareda nuno mata kuryar gado, dasauri Lilin taje ta boye, yayinda ita kuma ta tashi ta nufi bakin kofar ta tura tareda labewa tana kallon lokacin da *Habeeb* yashiga dakin *Deeya* yadauko akwataiya sannan ya kulle dakin murmushi tayi me daukeda tsantsar farin ciki tace shegiya Allah yasa mata tafi kenan.




*_Bauchi bayan kwana biyu_*
*******
*Deeya* kam ta murmure abinta tayi kyau sosai
tamkar ba'ita ce
tashiga damuwa ba kwankin baya dasuka wuce,




"Aban garen *Habeeb* kam ba'a cewa komai
Cikin kwana ki biyu nan idan kagan shi, sai yabaka tausayi damuwa tayi masa yawa domin gaba daya yakasa shawo kan Abba da Hajiya, har dauwar tafiyar wato *Deeya* gawani irin *SONTA* dake sake ruruwa *ZUCIYAR* shi ga kuma gurin aikin shi sai faman kiran sa ake don hakane ma komai
yasake da gule masa.




Washegari yakama laraba da misalin kar 10:00am *Habeeb* yafito sanye cikin wani brown din yadi Wanda kallo daya zakai masa kagane me tsadan gaske ne, duk dacewa yarame hakan be hana yadin yimai matukar kyau sosai ba, yayinda kamshin turare ke faman tashi ajikinsa saidai fuskar shi babu walwala, fitowa yayi yanufi part din Baffa.




Da sallama yashiga falon Baffa ne ya amsa kasan cewar suna zaune shi da lnna su nafira, Cike da fara Baffa yace a ah *Habeebu* ne?.. Cikin sanyi jiki ya amsa tareda zama kusada Baffan, bayan ya gaida su sai yayi shuru tareda dukar dakai kasa yayinda lnna ta tashi tanufi daki,




Baffa kam ido yatsurwa *Habeeb* din inda ya fahimci akwai abinda yake tafe dashi, saidai ya fahimci yanajin kunya fadine wanda kuma ya tabbatar bazai wuce maganar *"KYAUTA* ba,




Don haka cikin hikima Baffa yake janshi dafira har *Habeeb* din yafadi masa abinda ketafe dashi, inda ya karashe fadi dacewa Baffa gashi inason zan koma gurin aiki tunda anata ki rana a waya saidai inajin tsoron kar bayan natafi "Abba yaraba aurena da *Leemah* ta, kamar yadda yafada.




Murmushi yayi tareda cewa *Habeebu* kenan ai nafada maka babu wanda zaya raba auren Ku don haka katafi gurin aikin ka, saidai inason kasake riko da ibada ka dogara ga Allah kuma rike addu'a sosai ga wasuma zan baka yace to Baffa nagode, nan dai yafada mashi addu'o'i masu yawa sannan yatashi zaya fita yanata godiya inda Baffa yaketa maimaita masa ya rike Addu'a tareda yawan anbato Allah domin yanason harshen dayake yawan anbato nashi.




Part din Hajiya yanufa gaban sana faduwa bakin sa daukeda addu'a yashiga falon saidai be'iske kowa ba, don haka sai yashiga dakin Abba zaune ya'iske shi adan karamin falon sa zama *Habeeb* din yayi kusada Abban tareda sake gaida shi amsawa yayi fuska sake Wanda yasa *Habeeb* yaji wani irin sanyi zuciyar shi domin raban dayaga fara'ar Abban tun ranan dasu kazo, aranshi yake fadin Allah yasa Abba ya hakura yajenye maganar sakin ameen.




Abba yace ya'akayi ne Na ALLAH?.. kalar tausayi *Habeeb* yayi tareda cewa
Abba dama yau nake son koma wa gurin aiki shine nazo nasake baka hakuri, don Allah kayi hakuri wlhy bazan taba iya sakin *Leemah* ta ba, sannan don Allah Abba ko bayan natafi kar karaba auren kamar yadda kace wlhy Abba ina *SONTA* sosai.




Murmushi Abba yayi tareda dora
hannun shi saman lallausan suman kan *Habeeb* din, sannan yace *Habeebullah* da *Haleematus "Sadeeya* hadin Allah ne wanda babu wani mahalukin daya isa ya rabashi ba,




kamar nidin nan ban'isa na rabaka da "itaba domin itadin "takace ALLAH yabaka *KYAUTA* tun fil'azal, shin wakake gani zaya rabaka da abinda Allah yabaka?..babu shi Na ALLAH don haka ka kwantar da hankalin ka kaje kayi aikin ka idanka dawa wani zafi sai katafi da matarka, sai ka kula sosai banaso wani abu makamancin wannan yasake faruwa kaji ko..?




Cikin wani irin farinciki mara musaltuwa yace to Abba nagode sosai, kuma insha'allahu hakanan bazaya sake faruwa ba Abba yace to shikenan Allah yasa haka, yace ameen, to tashi kaje ka sallami hajiyarku tana nan sama yace to tareda tashi yanufi saman, *ZUCIYAR* shi fari tas kamar wanda akaima bishara da aljanna.




Zaune ya'iske Hajiya yayinda *Deeya* ke kwance akan kafafunta, fira suke abun su gwanin sha'awa zama yayi tareda kallon su jiyayi kaunar su tana bin dukkan ilahirin jinkinsa, cikin sanyi murya ya gaida Hajiya domin yaga tahade fuska wanda hakan ne yasa yaji jikinsa yai sanyi, dai-dai lokacin da *Deeya* ta tashi fuska daure ba'alamar fara'a,




Sanye takeda wata jar tamfa me ratsin yalo dinki riga da siket ne wanda yadan kamata kadan, saidai hips dinta yafito sosai wanda yasa gaba daya *Habeeb* ya shagala da kallon ta domin wan irin kyau tayi masa marar musaltuwa, itakam ba tareda takalli inda *Habeeb* din yake ba tace ina kwana,




Dasauri yace lafiya lau *Leemah* ta kin tashi lafiya?.. bata amsa ba saidai tace hajiyarmu zanje na kwanta, tace to hali dubu na atashi lafiya tace Allah yasa tareda shigewa dakin Hajiyar.




Hajiya ta kalli *Habeeb* tareda cewa inason naje umara, cikin girmama wa yace to Hajiya yaushe ki keson tafiyar?..
tace wani sati tunda akwai komai akasa tare kuma zamu tafi da "hali dubuna, dasauri yace Hajiya maganar komawar tafa ?..gashi "Abba yace" idan nazo wani sati na tafi da'ita".




tace "eh zata koma tunda yace" takoma amma sai mun dawo umara ko shima da sharadi cike da tsoro yace...






Muje zuwa




A


*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)




Tareda


โœ๐Ÿฝ


๐ŸŒนMeenat๐ŸŒน[7/2, 11:49 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ


_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_


๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ


4โƒฃ0โƒฃ




WRITTEN
By
๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ


OR


๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ




SADAUKARWA


*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*


___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~








โœ๐Ÿฝ






_*Bismillahirrahamanirraheem*_






_NOT EDITS_






Hajiyar mu wani irin sharadi kuma?..tace da farko karka kuskura kasake aikata laifi maka manci haka domin bazan dauki hakan ba, kasani sarar ban hada hali dubu na dakowa ba, cikin farin ciki yace nasani Hajiyar mu kuma insha'allahu hakan bazaya sake faruwa ba,




Tace to sannan idan mun dawo bazata koma abuja ba saidai "ta zauna anan Bauchi, don bai yuwa kasake mayar da ita can "matar ka taci gaba da cuta "mata bazan sake yadda da hakan bako kad'an kuma kagaya mata karta sake samata beraye tunda tasani sarar bataso, sannan kuma kafin mudawo ka samo masu admissions "itada *"Safeeya* tunda Jam dinsu yafito kuma yayi kyau don haka inason su cigaba da karatu, idan ka amince to idan kuma baka amince bato maganar rubuto takarda t....




Dasauri ya katse ta dacewa haba Hajiyar mu indai wannan nan ne sharadi na amince, Allah yadawo daku lafiya tace ameen yace to amma Hajiyar Mu ita *"Sofee* "mijinta ya amince taci gabada karatu ne?...tace munyi maganar "dashi kuma ya amince, dasauri yace ah! to ai shikenan, insha'allahu kafin kudawo angama komai saidai kawai su fara zuwa school din KO?...


ya kareshe fadi fuskar shi dauke da fara'a, tace to shikenan yayi kyau tafadi tareda tashi tana cewa bari na iske "Abban naku akwai maganar da zamuyi dashi yace to, yana ganin tanufi falon kasa yai sauri yatashi yanufi dakin ta.




Yana shiga yarufe kofar fuskar shi dauke da fara'a tsaye yayi yana me karama *Deeya* kallo kwance take akan faffadan gadon Hajiya ahankali yake sand'ar tafiya zuwa gurin ta,


_Nikam nace Kai *BB* meye nayin sand'a kuma?.. ๐Ÿ˜‚kaida matar ka ko dai kana tsoron rigimar *Leemar* taka ne?????_๐Ÿคฃ.




Tsaye yayi agaban gadon yana kare mata kallo kwanceta ke rigingine ma'ana tana kallon sili, tayi filo da dukka hannun wanta biyu hakan ne yaba shafaffen cikinta damar sake shafewa wanda yake kullun ashefe kamar wacce bata cin abinci, yayinda dukiyar fulanin ta sukai kamar xasu fasa rigarta, barci takeyi saidai da alama beyi nisa sosai ba zaka fahimci hakanan ne ta yadda takeyi tana juya kanta ahankali.




*Habeeb* kam ahankali ya hau gadon zama yayi agefen ta tareda sa hannun sa dukka biyu ya tallabe fuskaskar sa yana kallon ta, zuciyar shi cike da zallar kaunar ta wanda besan iyakarsa ba,
"Ahankali yakai hannun sa kan shafaffen cikin ta yana shafawa sannu ahankali har yakai saman dukiyar fulanin ta, aikam take yarikice yayinda natsuwar sa take kokarin kufce masa.




*Deeya* kam cikin barcin ta da beyi nisa bataji kamshin daddan turaren sa, dasauri ta bude ido dai-dai lokacin dayake kokari tura hannu shi Cikin rigar ta,๐Ÿ˜‚ Ido tazaro cike da tsoro ta bige hannun shi tareda mikewa zumbur zata sauka daga kan gado, dasauri yajawota tafado masa ta bayanta yayinda yasa dukkan hannu wansa biyu yaima ta kyakkyawan runguma afaffad'en kirjin sa tareda sauke ajiyar zuciya me karfi.




Cikin rawar murya yace Kai! *Leemah ta* nazo ne famu yi sallama shine zaki gudu ummh?... Bata bashi amsa ba saidai jikin ta dake ta faman rawa yayinda tafara mutsu-mutsu kwatar kanta, amma takasa cike da shagwaba tace nika kyaleni kaji KO?...idon sa lumshe yana murmushi tareda shakar daddad'en kamshin turaren ta yace um-umhhh! *Leemah ta* kibarni mana naji kamshin jikin nan naki me dadi, ummh! yafadi yana tura kanshi ta bayan wuyan ta wanda lallausan suma ke kwance luf-luf.




*Deeya* kam takasa kwance kanta kamar yadda taso saida kuma takasa hakan, murmushi naga tayi wanda bansan meta tunaba saida naga tadago ta kalli santalelen hannun sa me kwance da lallausan suma luf-luf, bakin ta naga takai.




_Dasauri nace Kai!๐Ÿ˜ณ *Leemah* me zakiyi_?..




Lafiyayyan cizo tayi masa wanda yasashi sakin ta bashiri tareda fadin auchhhhh!, dasauri ta sauka saman gadon tana yimasa gwalo, dariya yayi tareda yarfe hannun yace Kai! *Leemah ta* cizo nafa kikayi, tace "eh din anciza ba nace ka kyaleni ba kakiya shiyasa ni kuma na cije ka eheee! ta kareshe fadi tareda murguda masa baki sannan ta bude kofa tafita da gudu.




Murmushi yayi tareda girgiza Kai! yace *Leemah ta* kenan, sannan yasauko yafito bai ganta ba bai kuma iske kowa afalon kasa ba, don haka sai kawai yanufi part din sa ba tareda bata lokaci ba yadauki abinda yake bukata yafito, direba yabude masa mota yashiga saida suka biya asibiti gurin *Harees* sukai maganar da zasuyi sannan driver yakaisa airport yahau jirgi sai Abuja.




*_Abuja_*
********
Koda *Habeeb* ya'isa *Jana* tanayi masa sannun bai amsa ba asalima ko kallon ta baiyi ba, Lili yadauka yana me sumbatar ta agoshi tace Daddy na where is my Aunty *"Deeya?..* murmushi yayi tareda sa hannun yaja hancinta yace tana gurin me allura ido tazaro sai kuma ta tab'e baki tace Daddy yoche jata dawo?..yace very soon tareda sauke ta yana cewa lilin Daddy bari naje nayi wanka kinji?.. tace to yanufi daki ba tareda yabi ta kan *Jana* ba.


****
Sannu ahankali rayuwa tamike yanzu kam duk sati sai *Habeeb* yaje Bauchi kasan cewar tuni sun *Deeya* sun dad'e da tsufa asaudiya, yayinda *Habeeb* yafita har kar *Jana* kwata-kwata baya shiga sha'aninta harda Junior gaisu warsu kawai yake amsawa, yayinda yamai da hankalin ga aikin sa tareda ruko Da ibadar sa dakuma kama addu'o'i sosai, wanda yake ganin sakaci da'ita neyasa komai yafaru abaya,




Wanda yanzun kam baya fatan hakan yasake *FARUWA* nan gaba yayida kullum safiya jiyake kamar ana Kara masa so da kaunar *Leemah* acikin zuciyar shi tareda wani irin azababben sha'awarta wanda yakeji kamar zai masa illa don haka nema yake yawan yi azumi, domin yana rage kaifin sha'awar Dan adam saidai kuma da yasha ruwa sai yaji yana bukatar mace a tareda shi, saidai kuma yayi alkawari bazaije ga *Jana* ba har saita horu abisa laifin datai masa.




"Aikam tana horuwa domin ita awannan fagen batada hakuri don haka batada aiki sai kallon fina-finan banza awayarta, wanda aganin ta suneke rage mata sha'awar ta, *Habeeb* kam baima san ta nayi ba tunda idan yaje aiki yadawo baya kulata abokirar firar sa lili maman shi,




"Wanda
hakan yana matukar damun *Jana* don hakane ma duk abubuwa suka jagule mata gara shinjin wani gamsasshen bayani daga gurin Shafa, agame da aikin datasa ayimata shiyasa damuwa yai mata yawa duk tarame ga rashin cin isasshen abinci me kyau tunda yanzu bame aiki, ita kuma bata iyaba shiyasa ko tayi bata iyaci, ranan nanma datayi Lili taci saita furzar tareda sakin kuka tace ke! Aunty *Jana* tullun bati iya abunci ba kuma bajan kalacin abuncin kiba tunda babu dadi aikam ranan lili taci duka gurinta.




Da *Habeeb* yadawo Lili tafada masa ranshi bace ya'iske *Jana* yaimata fada kaca-kaca, ya kuma ce karta sake dukan lilin tunda aiba karya tayi mata ba aibata iya abincin ba,




Shikenan tunda ga ranan Lili tadai cin abinci saidai *Habeeb* yayo masu take away suci idan sun rage sannan su *Jana* suci wanda itasam ba'isar ta yake ba, lol alhakin my sweet *Deeya* ne.






*_Bauchi_*
*******
"Ayau alhamis kuma yau ne su *Deeya* zasu dawo daga ummara da sukaje, Da misali karfe 11:30pm jirgi su yasauka *Harees* ne da *Hafeez* da kuma *Feeya* sukaje dauko su,
da d'an gudu *Feeya* taje suka rungume juna itada *Deeya* suna murnan ganin junan su, Cikin dan tsawa *Harees* yace stop it my precious.




Baki ta turo tareda cewa to ai my sweet *Deeya* nace tadawo ba dole nayi murnan ganin ta ba, yace to ai nasani amma aisai kiyi ahankali tunda kinsan bake kadai bace, *Hafeez* kam harara ya watsama su tareda cewa waiku bakusan kullum girma kuke ba amma sai kuyi tayi abu irin na kananan yara mtww yai tsaki tareda cewa ai sai ku wuce mutafi ko, baki suka turo batare da sun ce komai ba, Hajiya kam tana gefe tsaye sai Murmushi take.




Kasan cewar babbar mota sukaje da'ita dan haka gaba dayansu ta dauke su Hajiyata can sit din baya, su *Deeya* kuma suna sit din tsakiya yayida *Hafeez* ke tuki *Harees* kuma yana gefen shi,




"Ahankali *Deeya* da *Feeya* suke fira inda *Feeya* keta yaba kyanda *Deeya* takara, tace ai kema kinyi kyau unborn yakara maki kyau sosai murmushi *Feeya* tayi tareda cewa albishirin ki?.. *Deeya* tace goro fari kalkal, tace angama komai ranan Monday zamu fara zuwa school inda zaki karanta Law dinki nikuma zan karanta medicine Dina, cike da farin ciki *Deeya* tace da gaske?..




tace Allah Da mana bari sai kun dawo nafada maki, tace kai! amma naji dadi shikenan burinmu zaya cika tace insha'allahu, kuma Hmm *Habeeb* ya siya mana mota ke daya ni daya taki fara tawa baka yace muringa zuwa school, baki *Deeya* ta tab'e tareda cewa mungode, sannan *Feeya* ta cigaba da cewa shi kuma Hmm *Harees* yabude mana account tareda sama na kudi dubu dari biyu da hamci hamci, yace" muyi hidimar school dariya tayi tareda cewa Kai! amma mungode sosai.




Cikin kwantar da murya *Feeya* tace my sweet *Deeya* yanzu dai komai yawuce zaki koma dakin kiko?.. Dasauri *Deeya* tace wa?.. ni tab! tafadi tareda pointing din kanta, tareda cewa aini babu inda zan koma cike da mamaki *Feeya* tace...








Muje zuwa




A




*_KYAUTAR ALLAH CE_* (Labarin Sadeeya)




Tareda


โœ๐Ÿฝ


๐ŸŒนMeenat๐ŸŒน
[7/4, 12:23 PM] My Ameena: ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ


_*KYAUTAR ALLAH CE*_
_(Labarin Sadeeya)_


๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ


4โƒฃ1โƒฃ




WRITTEN
By
๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ


OR


๐ŸŽ *MEENAT* ๐ŸŽ




SADAUKARWA


*GA SADEEYA SADEEQ UMMU (Haidar)*


___________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
___________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~








โœ๐Ÿฝ






_*Bismillahirrahamanirraheem*_






_NOT EDITS_






Saboda me bazaki koma ba?..tace saboda ban manta da'abun da akai mun ba, tace haba sweet *Deeya* ki manta mana.




Dasauri tace bafa zan manta sweet *Feeya,* ke bakisan irin wahalar dana shaba ne shiyasa, tace to kiyi hakuri kiyafe masa" kinga fa ba'a cikin hayyacin "sa yayi maki haka ba, tace hmm to nayafe masa" saida bazan koma ba don idan nakoma bansan irin bakar wahalan da matar sa zata sake bani ba.




*Feeya* tace ai insha'allahu hakan ma bazaya sake faruwa ba, tace hmm my sweet *Feeya* kenan kedai kawai muyi hakuri da juna yabani takarda na shiyafi alkhairi, tace aganin ki hakan shine mafi alkhar agare ki?.. tace "eh, *Feeya* kam jitayi ranta yadan sosu har tana fadi aranta wato hakan yana nufi *Deeya* batason Hmm *Habeeb* kenan KO?..




Cikin d'an bacin rai tace OK" shikenan dama can bakison shi don haka kike so yasake ki, amma inda kina son shi ai da duk abinda yaimai kin zaki hakura, itama Cike da bacin rai tace "eh aishima baya sona Da sauri tace karya ne kinsani sarar "yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login