Showing 27001 words to 30000 words out of 92932 words
Chapter 10 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt
D
MRS BUKHARI
23~24
WANAN SAFIN NAKI NE MAMAN YASEER KI YI YANDA KIKE SO DASHI.
Jiki a mugun sanyaye kowa ya bi Iya a baya. wad'anda su ka d'aura tukunyar sanwa ba shiri su ka sauke. Dan su kansu sun san mai k'watar su sai dai Allah, dan Iya bata da wasa sam.
Iya na zaune a babban falon Kawu Sulaiman. Da sallama dukka mu ka shiga. a tabarmar da ta malale falon kowa ya nemi waje ya zauna. Iya tace.
"kai Gadanga, ka shiga b'arayin Safiya, da mariya. suma su tawo. munafukan kawai, yau zaku sha mamakina."
Cikin Nutsuwa Aliyu ya tashi ya fice. Iya ta dawo da dubanta gun Hasiya tace.
"ke kam hukuncinki da girma ke da wanda ya ajjiyekin, da ma ubanshi dukka. Kina tunanin har kinyi kafuwar da za ki taka Sadiya a cikin gidannan. in banda lalacewa irin ta Asabe? Toh yau a gidan ubanki zaki kwana, kije ki ci gaba da tallar kalwa.Sallamar su Goggo Safiya ce ta katse Iya. waje su ka samu a d'arare su ka zauna.
"Iya saukar yanzu?. Bata ko kalli Goggo Safiya da take tambayarta ba, magana ta soma yi kawai.
"Na tara wannan taron ne dan k'wato ma Aliyu hakkinshi da uwarshi Asabe ta ke so ta danne mai. kan cewar sai ya saki matarshi. tare da yi mai barazanar tsinuwa in ya kusanci Matarshi. Kafin in ce komai, zanso Asabe ta fad'i hujjojinta dan bazan tauye ta ba. Albarkacin nak'uda da reno. Amma ki sani ba halittar Aliyu ki ka yi ba."
Goggo Asabe cikin sanyin murya tace.
"Iya a gaban idanki Aisha ta dinga mulkar rayuwar Adamu. Matarnan 'yar duniya ce, kuma 'yan shige shigen asiri ce. dad'in dad'awa kuma. Yarinyar nan Sadiya ta girmi Aliyu wayo za tai ta yi mishi a banza. 'Yar boko ce a gwamnati take aiki a b'angaren kiwon lafiya. 'yan bokonnan mafi yawansu basa iya ma zaman aure. idanunsu ya gama bud'ewa, sun saba cud'anya da maza. Iya da ba dan Sadiya ta kasa Auruwa ba. Aisha ba za ta yarda d'iyarta ta auri wani daga cikin dangin Adamu ba. Nifa cutata za'ayi wallahi in dai su ka ci gaba da zama. tsanar da Nai ma Aisha ita ta shafi Sadiya. Ina tsoron kadda ta shafi k'usar yakin shi kanshi. A karon farko kenan da yaronnan yayi abubbuwan mamaki har kashi biyu. na farko. Na bashi umarni ya sab'a. Na biyu, yayi fad'a da Dauda....."
" Ke dakata mai ragaggen tunani. wad'annan labaran marasa tushe da madafa fa? Bari ki ji Asabe karki sake ki zame ma d'iyoyinki bak'ar uwa mai sa a zubda hawaye. ki yi k'ok'arin zama farar uwa farin cikin 'ya'yaye. Ba'ace kasancewarki na uwa ya baki lasisin da za ki yi tsiyarki yanda ki ke so ba. Asabe in baki janye maganar sakinnan ba. Zan iya tsine miki nima dan ubanki." Ke wacce iriyar bijire mana ne baki yi ba lokacin da ki ka kawo mana shi mahaifin na su Aliyun? Dan dai akwai surukai nan da na yi miki figar kaza. Daudan banza kike magana dan anyi sa in sa da shi, inta kama ai sai a doke shi ma. Aliyu yace bazai yarda da marin da Dauda yaima matarshi ba, nima ina bayanshi, dan haka zan d'aukar mishi fana da kaina. Kai kuma
Sulaimanu na god'i. sunan da ya fi dacewa da kai kenan. Kana cikin mata kana haddasa husuma ko? Sabida jahilcin dake damunka. kuka Iya ta fashe da shi tace.
"Allah wadaranka Sulaimanu. Bari kaji kar na ji kar na ga wanda ya sake takura ma Aliyu da Sadiya. Ka jama Dauda d'anka kunne akan Sadiya, da matarshi 'yar mai kalwa. Maganar Auren shi da ake yi. ni na baku umarni a dakatar da maganar Auren Sadiya ba za ta zauna da kishiya ba.
surukan gidannan kuma ina mai gargad'inku akan Sadiya, dan ba sa'arku bace. ita mai ilimi ce, wayayya wacce ta fi ku sanan rayuwa da makamar rayuwar. Dan haka ku girmamata. ke kuma Wallahi saina dake ki zan bar wajannan, saina tabbatar a gidanku kika kwana zan bar Raquma. ta mik'e ta nufi Hasiya da duka kakakaf kakakaf. sai da ta yi mai isarta ta dawo ta zauna. Ba wanda ya iya cewa komai, Dauda sai dariya k'asa k'asa yake ma Hasiya. Ita kuma sai kuka take yi danta mugun daku.
" Ke Sadiya ki sake ki kula da mijinki. A yau ba sai gobe ba. Ku zama cikakkun ma'aurata tun kafin in tafi ta sauya zane. Dan Asabe kunnen k'ashi gareta. Na rufe wannan babin. Sai maganar zama da akeyi duk shekara da aka daina yi. Toh an dawo dashi, a aikema kowa da kowa. da bikin sallah kowa ya hallara. Aci gaba da d'abbaka zumunci. Ko a bari in an taru a bikin Dauda, sai a tattauna. Yanzu Ramatu na hannuna da yara goma. miji ya gudu ya barsu. Sabida rashin zumunci an kasa samun mai taimakon mu. duk yawan da mu ke da shi. yarinyarnan sai aikin shara take fita ta yi. Sulaimanu ka na da ranka?"
Kuka sosai Iya ta fashe da shi. falon yayi tsit na wasu dak'ik'u. Daga bisani Kawu ya dinga ba Iya hak'uri shi da su Goggo baki d'aya. Haka ma surukan gidan su kai ta ba ta hak'uri. Da kyar Kawu sulaiman ya shawo kan Iya tayi hak'uri akan maganar sakin surukan gidan. Musamman ma Hasiya. Iya tace.
"Nifa banyi fishi ba. Asabe ina fatan kin janye maganar tsinuwa da saki ko?"
Goggo cikin 'dacin zuchiya da bak'in ciki mai mugun tsananin daya kasa b'oyuwa a fuskarta.tace.
" Na janye Iya amma gaskiya maganar Auranshi da khadija ta na nan babu makawa. Domun Iya, yarinyarnan tsawon shekaru ta kwashe a matsayin mallakin Aliyu. girma zai zube in aka ce daga b'angarenmu aka fasa, ki yi hak'uri Iya."
Iya tace.
"Uban yarinya ya ce bazai aurad da d'iyarshi ga Aliyu ba, har sai ya saki 'yar boko. Ita kuma 'yar boko mutu ka raba takalmin kaza. bansan meyasa ki ke son wannan yarinyar ba."
Kawu yace.
"Iya ayi hak'uri a tuntub'i iyayenta. In sun amince shikenan. in basu amince ba shikenan.
"Kai Aliyu kana son ita Dijangalar har yanzu, ba za ka yi zaman ka da zuk'ek'iyar matarka ba?" Sauke kai Aliyu yayi, sai ya ji ya na jin nauyin ya amsa tambayarnan a gabana, a yanda na lura Aliyu mutum ne da yasan darajar mutane. Kasa cewa komai yayi, sai Kamilu ne ya wakilceshi da cewa.
"Iya yana santa. Duk da akwai bincike daya taso ta b'angarenmu mu na so mu kammala tukunna." Da fad'a Goggo Asabe tace.
"Ba mu da lokacin jiran komai. Bikinnan tare da Dauda ne, Ba za a d'aga ba. Duk wannan wata sabuwar hanya ce kuke shirin kawo wa, dan a fasa bikin kawai."
"A ta ki cewar kenan ko? in ji Iya. ta d'aura da cewa.
"bincike halas ne a neman Aure. Je ku yi binciken ku. ku kuma ku bani waje, zan gana da 'ya'yana.
Sum sum sum Su Bilkisu su ka fita. Hasiya na cizon yatsanta."
dafata Bikisu ta yi tace.
"Amma wannan tsohuwar matar Aliyunnan ta ci mutumcinki. kinga a ruwan sanyi tasa an rama mata marin da mai gidanki yai mata. duka ma ki ka samu. Dubi yanda ta tara k'aton taro ta juyar ma da Aliyu k'wak'walwa har ya na so ya fasa auren khadija." Hasiya ta yi wata dariyar mugunta tace.
" Bilkisu sai Sadiya tai nadamar shiga harkata da ta yi. ni cikakkiyar basakkwaciya ce, kuma fulanin daji. mugunta zama damu ake yi a koya. taurin kai da taurin rai, daga kan fulani ake shafa fatiha. sai na saka mu a cikin ukun da ni da ita ba za mu iya fita ba. Amma raina zai farantu, tunda tana cikin ukun. ki xuba idanu duk daren dad'ewa.
Bilkisu ta girgiza da maganar Hasiya. domun tasan karo da Hasiya ba wasa bane, amma da ya ke ta na cikin k'iyayyar Sadiya, a wajan ta mara ma Hasiya baya, kan cikar k'udirinta.
Iya ta dubi Aliyu da ni kaina tace.
"Ku yi tafiyarku kuma. Kamilu kafin in tafi zam shigo in ga amarya."
Fita mu ka yi. Nidai ban tsaya ba, b'arayina na wuce. Aliyu kuma na barshi a tsaye tare da Kamilu. Basket d'in abincin da na dafa da safe na tsinta a k'ofar d'akina. ko da na bud'e kular kuskus d'in ya na turiri. goge kulolin na yi da tsumma mai kyau a kitchen d'ina, miyar na bud'e na k'ara loda nama a ciki. Iya na kaima har falon Kawu. Adda'a ta dinga zunguma mun.
dana dawo kitchen na koma tare da kunna risho. tuwon alkama da tuk'a na d'aure a leda. a k'atuwar kula na saka. sannan na fito. D'aki na shiga na zaro kud'i a jakata daga cikin kud'in da mama ta ba ni. Barayin Bilkisu na wuce da sallama. Tana tsakar gidan ta na haramar tuk'a tuwo, na shigo da sallama. Babu fara'a a fuskarta dama ban tsammaci hakan ba.
Bilkisu na ce ina zan samu kayan miya d'anye?. da baki ta nuna mun.
"Da kin fita daura da gidannan. gidan kayan miyar kenan. Da mamaki na dubeta, tare da duban yaronta da na ji ana maganar ya dawo daga almarci. yana zaune baya aikin cas bare na as. Amma ba ta ce ya siyo mun ba. yaron ma babu ko tarbiyyar gaida mutane a babin rayuwarshi. Godiya na yi mata na fice. Gidan kayan miyan na shiga da sallama. wata tsohuwa na gani tana gaban murhu ta na kad'a miya ta tarbeni.
"maraba. me za'a baki?"
cikin Harshen ladabin yin magana da manya nace.
"mama d'anyen kayan miya na ke so a had'amun komai da komai na d'ari uku.
Sakin bulugarin data gama burga miyar ta ta yi. kayan miyan ta xuba mun cikin babbar laida mai zane zane. kud'in na bata na fita.
Cikin gaggauwa na tsaida sanwar miyata ta kub'ewa bushasshiya wacce na wadata tata da kifi bushasshe, tare da sunadarin k'amshi dangin su citta, kanunfari, d'iyar miya, tafannuwa, tumeric, corry, thiyme, da dai sauransu. kan kice me gidan ya cika da k'amshin miyata. haka kawai na ji ina samun wata nutsuwa ta na saukarmun. Zuwa bayan isha, na kammala komai, na fesa wanka, cikin shigar doguwar riga 'yar kanti wanda ta amshe ni sosai. Sai da na kunna turare d'an tsinke, da kuma turaren wuta na hulut. na d'auki basket d'in abinci na fice. Kawu na soma kai ma na shi. sannan na wuce b'arayin Goggo Asabe. Gabana ya na bugawa. a haka na shiga d'akin da sallama a bakina. Iya ce ta amsa mini Sallamata, Goggo Asabe kuwa kawar da kanta ta yi gefe ta ba banza ajiyata.
Iya ga tuwo na kawo miki ki ci. Iya ta washe baki ta ce.
"kai Sadiya Allah yai miki albarka. A gaskiya Aliyu ya fi yaran gidannan more mace mai kirki. Sadiya ki sake hak'uri, ki yi k'o'karin ba mara d'a kunya. Da sannu za ki samu farin cikin a gidan auranki. murmushi kawai na yi kaina a k'asa, har ta kammala mun nasiharta. Sallama nai musu na nufi b'arayina.
A k'ofar d'akina na ga takalman Aliyu a gefe halamar ya na cikin d'akin. cikin sallama na shiga. Ya na zaune a k'asa, daura da shi na zauna.
Sannu da shigowa. Murmushi ya sakar mun yace.
"Yunwa na ke ji sosai, ban ko karya ba yau, sai k'wad'on da mu ka ci a zamfara, toh ina kwanciyar hankalinma na samu?" ta ke sai na ji na tausaya mishi. ni kaina sai lokacin na tuno in banda zogalen da na ci a gidan Iya, babu abunda na ci. ko ba komai na ga halamar zan samu sauk'i a wajan Aliyu, dan a wunin yau da mu ka kasance a tare, na fahimci ya na da sanyin hali. kular tuwo da miya na kawo gabanshi,sannan na koma na kawo ruwan wanke hannu tare da ruwan sha. Zama nayi na zuba mishi tuwon.
Bismillah ka ci abinci. Kallona ya yi, cikin tausasawa ya ce.
"Amma ke kinci wani abu ne?" Yanda ya k'ure ni da idanunshi, sai na ji yai mun kwarjini sosai a idona. Ahankali na bud'e baki na ce
Aa ban ci ba."
Turo abincin ya yi gabana ya ce.
"Bismillah mu ci tare Anty. Ai hakkinane in tabbatar kin ci abinci. mu ci, ko in baki a baki, sabida karki fama ciwonki?
Da sauri na zaro ido. na ce.
Aa zan ci zuwa anjima."
Da wata iriyar murya ya kira sunana ya ce.
"Sadiya. bana son gaddama ki sa hannu mu ci, kar ki bari wannan hatsaniyar da ke faruwa ta shiga tsakanin mu. Sadiya nasan ba'a kyauta miki ba da aka had'aki aure da ni. Abun bazai zo miki da sauk'i ba. Amma idan kin bani dama, zan kula da ke kamar yanda ko wanne miji zai kula da matarshi. Ni nasan yaro ne, Amma zan iya baki abunda ki ke so, zan sama miki nutsuwa. kin amince da maganganuna?
Jikina ya mutu murus da jin kalaman Aliyu. Bayanan shi ne, ya sa na auna mizanin iliminshi. Domun komai Aliyu cikin nutsuwa da kamala irinta manyan maza ya ke yi. in yana magana nakan manta cewar ni ce gaba dashi. cikin juyayi na ce.
"Amma ta ya kake tunanin zan samu kwanciyar hankali, bacin Goggo ta na cikin fishi da mu. Aliyu ni ina jin tsoron mai fishin Goggo zai haifar mana a zamantakewarmu. Aliyu uwa ta fi gaban hankali ya kwanta in tana cikin fishi da kai. domun fishinta zai iya tab'a duniyarka. Ni abunda na ke so shine, ka je ka rok'i Goggo ta yafe maka, ko zamu ga Haske a rayuwar auranmu.
Na riga da na amshi k'addarata hannu bibbiyu, tun lokacin da lamarin ya iso mun. Babu komai, ina tare da kai, kuma zan yi maka biyayya, tare da mayar da kai jariri a cikin mazaje.."
Aliyu ya sauke ajjiyar zuchiya ya ce.
" Sadiya ke macace mai kaifin hankali da tunani. Naji dad'in yanda kika fi maida hankali kan fishin da Baba ta ke yi a kaina. Baba na bata lokacine ta d'an huce sai in je in bata hak'uri, In sha Allah. Yanzu dai mu ci abincin sai ki bani labarin wanne fannin kika karanta a matsayinki na malamar kiwon lafiya."
Murmushi kawai na yi mishi. mu ka soma cin abincin. Nanfa Aliyu ya shiga yi mun santin dad'i. Ni kuwa murmushi kawai na ke yi mishi. Bayan mun kammala. Sai na kwashe kayan da mu ka ci abincin, tare da gyara wajan. dawowa na yi na zauna."
"Toh ina jinki, me kika karanta?"
widwive na karanta wato anguwar zoma. ina b'angaren karb'ar haihuwa ne. na yi aiki a asibitin Aminu kano. Ina samun albashi babu laifi." kai ya shiga jijjigawa sannan ya ce.
"uhmm. Amma me ya ja ra'ayinki wajan karantar fannin anguwar zoma?" kallonshi na yi. sannan nai murmushi na ce.
"Sabida kishin mata 'yan uwana. Ina da sha'awar ganin mata sun samu sakewa a ko wanne fanni. nakanji takaicin ganin mace ta tafi asibiti da matsalarta. kuma ace Namiji ne zai ganta. musamman ta fannin haihuwa. Hakanne yasa na zab'i wannan fannin, kuma ina jin dad'in aikina sosai" shiru yayi ya na tunani. tare da auna kalamaina. sannan yace."
"Babu abunda zance da Kawu Bala da Kawu Sulaiman da su ka zab'a mun mace mai ilimi wacce ta zamo uwar gidana. kuma in sha Allahu uwar 'ya'yana, zan baki farin cikin da sai kin manta duk wata rayuwar da kika yi a baya. Kin tabbatar ma da duniya ke 'yace mai biyayya ga iyayenta. Na tabbatar zaki zama mai biyayya ga Aliyu ko?"
mrs Bukhari ce
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
Instagram links👇
https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Facbook group
https://facebook.com/groups/463653111781414/
Telegram links
https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
25~26
wannan shafin naki ne Anty Hadiza Bara'u ( Gidan Iko) Alkhairin Allah ya kai miki
Sadiya zan baki cikakkiyar dama, tare da cikakken lokacin da zamu fahimci juna. Ina fatan zaki saki jiki da k'anin na ki?" Hararar wasa na yi mishi. Ashe hararar ta shigi Aliyu sosai. Take naga ya canja, idanunshi sun sake launi. Ahankali ya ce.
"Ni kuma karatun boko na iya secondry ya tsaya. wannan da na samu ma, A lokacin ina hijar gomber ne a cikin wani k'auye mai suna Bara, Gari mai arzikin kankana. Almajirci ne ya kaini. Sai na ji sha'awar karatun boko. Ina shiga kasuwa dakon kankana da abokaina, da d'an kud'in da na ke samu nasa kaina a makarantar gwamnati dake cikin k'auyan bara. tare da karatun bokon na kammala karatun almajircina. ko da na dawo gida. sai ban zauna ba, sai na shiga makarantar Arabiyya ta manya. na soma daga S S 1. Na kammala da sakamako mai kyau, ina d'aya daga cikin hazik'an d'alibai a makarantar, duk inda za'ayi musabak'a, ni suke turawa, kuma ban tab'a fad'uwa ba. gwamnati ce ta d'auki nauyin tura mu madina. dan yin digiri a Arabiyya, mu goma cib. Alhamdulllahi. Burina shine kawo canji da haske cikin wannan k'auyan, kamar yadda ki ka ji d'azu muna hirar da Iya. makarantar Arabiyya na ke so in bud'e tare da ta bokon baki d'aya. yara da