Showing 36001 words to 39000 words out of 92932 words
Chapter 13 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt
sosai Anas yayi, rik'e Aliyu ya yi a b'arayin damanshi, dan ya zame mai garkuwa. d'akin zaure ya kaishi, ba kowa a ciki, zaunar dashi a k'asa yayi.
"Zan je in kira maka wanzan, kafinnan zan kira maka Kawu, ita kuma khadija zan kira Baba ta dubata." Bai ko tsaya jin abunda Aliyu zai ce ba ya fice a guje. b'arayin Goggo ya nufa. Kwankwasa k'ofar ya shiga yi da k'arfi. abunka da aikin dare. har makwabta sai da su ka ji wannan bugun k'ofa, da sunan Goggo da Anas yake ambata, Ba ma 'yan cikin gida ba. Kawu ne da su Dauda, da Kabiru su ka fito cikin hanzari, har da gora a hannunsu, dan su a tunaninsu ko b'arayine suka shigo musu, ga tsirarin mata da su ka tawo biki, basu koma ba, ciki duk ya d'uri ruwa. Ji yayi Goggo na bud'e sakata, ta na mita. Kawu ya hasko Anas da tocilarshi yace.
" kai Anas lafiya kuwa?
da sauri ya isa gaban kawu, daidai fitowar Goggo.
"Ba lafiya ba kawu, Aliyu ya na cikin d'akin zaure, rai a hannun Allah sai zubar jini ya ke yi, Yaji ciwo faca faca haka matarshi khadija ma a cikin uquba yace mun ya barota." ras Goggo gabanta ya fad'i taji wani abu ya tsirgo daga k'afarta zuwa kwanyarta, da sauri ta matso tace.
"Aliyu fa kace Anas?
"Eh Baba, ki je wajan khadija, kawu ku zauna dashi, zanje wajan malam wanzan yanzu. A wajan ya tafi ya barsu cikin taraddadin abunda ka je ka zo, Goggo duk ta bi ta rud'e. Babu shiri ta fad'a d'akin da khadija ta ke kwance a cikin jini male male ta taddata, sai risgar kukan azaba take yi.
kuka Goggo ta fasa, tallafo khadija ta yi, wacce ta gama galabaita ta fice a haiyacinta.
"Khadija me ya faru aka samu matsala? na shiga uku na, duk abunda ya faru da yaronnan ni na jawo mishi. me dambu ta cuce ni da ta bani gurguwar shawara. A matsayina ta uwa, za'a had'a baki dani a kassara rayuwar yarona mai tsananin yi mun biyayya. Kuka take yi sosai. khadija ba ma ta gane sam me ta ke cewa. Bilkisu ce ta shigo da sallamarta. Amma gani halin da khadija ta ke ciki da yanayin da take ciki ta girgiza sosai, hankalinta yai matuk'ar tashi.
"Baba cewa na yi ko a d'aura ruwan magarya da lalle a wuta ne, shima zai taimaka mata. Abun yazo musu da tsautsayi sosai, ko ta sha maganin daya fi k'arfinta ne k'ila. Goggo ta na hawaye, cikin girgiza kai na nadamar da bata da amfani tace.
"Ki d'aura Bilki. Amma ba abun da kike tunani bane wannan. dubi jini fa faca faca a d'akinnan. ko a wanne hali Aliyu ya ke ciki shi kuma oho. Bilkisu bata ce komai ba, ta fita. kara ta had'a a murhu. ta d'aura tukunyar ruwa. ganyen lalle da ganyen bagaruwa, da ganyen magarya ta zuba a cikin ruwa. Sai da yai ta tafasa, sannan ta juye a kwatanniya. ta surka yanda khadija zata iya shiga. D'akin ta shiga da kwatanniyar.
"Goggo ko za ki koma d'akin ki, zan kira Hasiya ta taimaka mun." Goggo bata ce komai ba ta fice tana sharce hawayen da su ke ta sabunta kansu.
Hasiya Bilkisu ta fita ta kira. A cikin ruwan zafi su ka sa khadija, ihu ta zunduma cikin muryar galabaita. Haka dai su ka tsaya a kanta akai ta canja mata ruwan.
Babu laifi a cikin kaso d'ari, kaso talatin na zugi da rad'ad'in da yake damun ta sun ragu. jinin ma ya koma zuba kamar yanda mace mai al'ada jini ke zubar mata.
k'unzugu tayi, Bikisu ta taimaka mata ta saka wata doguwar rigar atampa. Amma ji take tamkar gabanta zai jijjigo ya fice ne.
Goggo kuwa ko da ta koma d'aki ta kasa zama sai zurga zurga take ta faman yi. fita ta yi, zuwa d'akin zaure.
kawu ne ya lek'o"
"Ya ake ciki Yaya, sun iso kuwa?" Ajjiyar zuchiya kawu ya sauke, cikin damuwa yace.
"Ba su iso ba tukunna, gashi yaron ya na cikin rad'ad'i mai azaba, rauni a wannan wajan ba'abu bane na wasa. Amma Asabe ko mai ya faru da yarannan?" shigowar su wanzan ce ta katse su.
shigewa su ka yi aka bar goggo a tsaye. Aliyu yana zaune kamar 'dan shayi, yakan cije lebenshi, kai da gani kasan ya na cikin azaba.
wanzan yayi duban da duk zaiyi. ya ciro wani koren magani yace.
"Anas kawo ruwan d'umi a kofi yanzu. fita Anas yayi a d'akin. Wanzan ya goge jinin dake zubowa a jikin Aliyu, ya barbad'a mishi magani a wajan da ya kwaile, ya yi jawur, fatar wajan ta sab'ule. wani zugine ya shiga kwakwalwar Aliyu,na azabar wannan magani na wanzan. take jinin ya tsaya tsak.
dawowa Anas ya yi da kofi cike da ruwan d'umi. magunguna wanzan ya zuba a cikin ruwan, Aliyu ya mik'a ma kofin ya ce.
"kafa kai kasha maganinnan zai taimaka maka wajan rage rad'ad'i, bacci zai d'ebeka, sai ka huta."
Hannu Aliyu ya mik'o ya amshi kofin maganin. kafa kai yayi, bai d'ago ba sai da ya shanye tas.
"Sannu Allah ya yaye. ga wannan maganin kullum da safe a dinga basu a cikin ruwan kokko suna sha.
Amsa Anas yayi, wanzan ya kuma mik'o mishi wani k'ullin maganin
"wannan aba mata, kamar yanda na barbad'a mishi, itama a barbad'a mata, zan had'a mata wanda za'a bata yanzu. In sha Allah, za su samu sassauci. gobe zan dawo in duba su, da wasu magungunan ma, har zuwa su warke.
magungun da ya ha'dama Aliyu, irinshi ya had'ama khadija a kofi yace a zuba ruwan d'umi a bata.
tare da Kawu su ka fito, Anas kuma ya tafi ya kai maganin khadija, Dauda ke zaune da Aliyu da baccin wahala ya kwashe shi a zaune.
"Agaskiya malam Sulaimanu akwai matsala tattare da lalurar yaronnan Aliyu, domun abune mai wuya ace gabanshi zai tashi har ya yi aiki. Ba lalle bane har ya iya samun magaji. raunin yayi yawa, sab'ulewa fa, ga wasu wajan sunji raunin da yawa. Amma kar ka fad'ama mata. Allah ya kare gaba, k'una babu kyau." Kawu ya yi shiru kai a k'asa ya na nazari akan maganganun wanzan, can ya nisa ya ce.
"yanzu wanzan babu wani taimako kenan daya dace a bashi, yaronnan in haka ta faru, rayuwarshi durk'ushewa za ta yi, yana matashi mai k'arancin shekaru ace gabanshi ya dena aiki,ko bazai haihu ba. Ai za'a shiga mummunan tashin hankali da damuwa. wanzan duk wani abunda ya dace na magani da kulawa a mai." Shiru wanzan yayi cikin tausayawa yace.
"zuwa wayewar gari, zan lek'a jeji. zan harhad'o duk wani kauci da ya ke da nasaba da wannan lalura, zan d'aura shi akan magungunan hausa. in Allah yasa da rabon farfad'owar abun, sai ka ga ya farfad'o" Sallama wanzan ya yi ma kawu. shi kuwa kawu yafi sama da awa d'aya a inda wanzan ya barshi, ya shiga rud'u da tashin hankali. ya na mamakin garin yaya su Aliyu su ka k'one daga shi har matar tashi."
"Yaya, lafiya, mekakeyi anan?" Su Goggo Safiye da Goggo mariya, da Goggo Asabe ne suka iso gabanshi.
Juyowa yayi ya kallesu, cikinshi a matuk'ar mace. Bayanin da wanzan yayi mishi yanzu, ya zayyana musu suma.
Goggo Asabe babu abunda ta iya cewa sai kuka, tasan ta zalunci d'anta. Gashi ta jefa shi a cikin mummunar lalura, mai cike da tashin hankali, yaya zata iya wanke laifinta? Ji tayi wutar tsanar Sadiya na sake ruruwa a zuchiyarta, domun duk sabida k'iyayyar da take ma Sadiyanne ya ja wannan abun. yanzu kam lokaci yayi da zata tasanma cin mutumcinta har sai ta yi zuchiya ta bar auran. Allah Allah take yi gari ya waye ta je wajan mai dambu, su san nayi. Goggo mariya tace.
"wannan tashin hankali da mai yayi kama, bama fatan haka ta faru, zan je k'auyan me gidana, zan karb'o mishi magani, a wajan wani shahararren mai bada magani ko za'a dace.
Goggo Safiya tace.
"Amma Yaya kar'a sanar da kowa wannan lamarin. Ni ina zargin Sadiya da sa hannunta a cikin wannan ciwon. Asiri k'ila ta yi, danta lalata musu rayuwa, uwarta ma fa haka take muguwa, in ba asiriba me yasa ita hakan bai faru da ita ba, sai khadija?."
Kawu yace
"Asabe kiyi hak'uri, karki d'aga hankalinki. Ba na fad'a miki wannan abun bane, dan ki tayar da hankalinki ba. na fad'a miki ne, a matsayinki na uwa dan ki san da zaman hakan." kiran sallar asuba su ka soma jiyowa. Barin wajan su ka yi, kowa ba guiwa.
Anas ne ya ta fi b'arayin Sadiya dan sanar mata meke faruwa.
Sadiya
fitowa ta kenan daga ban'daki, sai naji ana doka mun sallama. Cikin fad'uwar gaba na so jin waye.
"Anas ne, Aliyu ba lafiya yana d'akin zauran su Baba. Ki je ki zauna dashi, za mu ta fi masallaci. Rass gabana ya fad'i. Rashin lafiya, mutumun da muka rabu da shi cikin farin ciki. Anas tuni har ya yi gaba. A rud'e na koma ciki, hijab d'ina na d'auka na fita cikin sauri.
Da sallama na shiga d'akin, Aliyu ya farka ya na kici kicin mik'ewa amma ya kasa. Da sauri na k'arasa nasa hannu dan in taimaka mishi ya tashi.
Kai ya girgiza mun halamar a'a. zamewa yayi da dabara ya koma. Dubana yayi idanunshi sun kad'a sun yi jawur yace.
"k'addarace ta same ni Sadiya. Bansan dalilin faruwar hakanba. d'an tsumman da ya rufe jikinshi da shi ya yaye mun. tocilar dake cikin d'akin na jawo, tare da haskawa." zare idanu na na yi waje. take na soma zubar hawaye. cikin gijijicewa nace.
"Aliyu k'onewa kayi garin yaya?"
Labarin duk abunda ya faru da su ya bani turyan turyan.
"Ki yi hak'uri Sadiya mu d'auka wannan k'addararmuce, bana son ganinki a mawuyacin hali plz. Shesshek'ar kuka na ke yi na ce.
Kayi hak'uri, amma bai dace ace irin wannan ciwon ana zaune a gida ba. Aliyu ka tashi mu je Asibiti. plz" Hannuna ya rik'o yana d'an murzawa a hankali yace."
" ki kwantar da hankalinki Sadiya na. dama ina jira ki zo ne, sai mu tafi, ki kaini Asibiti, nasan zako iya kulawa dani, amma nasan ba lallai bane su Baba su yarda da hakan." Matsawa nayi kusa da shi dab, sumbatar leb'enshi na yi. A take ya lumshe idanunshi. murmushi mu ka sakarma juna. Rarrashinshi na shiga yi, tare da bashi baki. Lamo yayi a jikina. Sai can ya ce.
" Toh taimaka mun in tashi, In nayi sallah sai mu tafi kafin su sani ko?. mik'ewa na yi, na kamashi. da taimakon Allah har zuwa b'arayinmu. Nina taimaka mishi ya d'auro alwala. a zaune akan kujera yayi Salla. Ni kuma kaya na sake na d'auki jakata na fito.
"Akwai kud'i a k'aramar jakata Sadiya. Ki debo mu rik'e. Komawa ciki na yi na bi umarnin abunda ya ce mun.
"Ki je ki kirawo khadija mu tafi, dan itama tana cikin mawuyacin Hali, sai Kamilu ya taimaka miki.
Toh. kawai na ce mishi na fice.
Kamilu na je na soma kirawowa. wuce ni ma yayi da sauri, ni kuma ta k'ofar gaba na biyo. da sallama na shiga d'akin khadija. Bilkisu ta na zaune tare da ita.
"Ya mai jikin Bilkisu?" Babu yabo babu fallasa tace.
"Ga jikinnan tana jin jiki, wannan lamari duk mai hannu ya ciki Allah ya toni airinshi." kallon khadijar na yi, tana kwance ido biyu, Bilkisu kuwa banza na ba ajiyarta. nace
"Sannu Allah ya baki lafiya. Zaki iya tashi muje Aliyu nasan ganinki?" Cikin yamutse fuska ta soma yunk'urin mik'ewa. Amma sai ta kasa. Taimaka mata na yi, na mik'ar da'ita tsaye. mayafinta dake kan gadon na yafa mata. Tana rik'e a hannuna har zuwa b'arayina. Ba tare da b'ata lokaciba mu ka fice ta k'ofar baya.
Babur biyu mu ka samu, Kamilu yasa Aliyu a tsakiya, ni ma nasa khadija a tsakiya.
Sun sha wahala sosai, kafin mu isa bostop. kasancewar yau talata, ranar kasuwar mafara ke ci. Mota ba wuya, kuma nan da nan take cika. Muna isa mu ka samu mota mu ka shiga. Kan Aliyu ya na kafad'ata. Hannunshi kuma yana ta bayana ya rik'emun kuguna yana d'an matsamun a hankali. Amma da ganin yanayin shi, jiki ya ke ji. Dauriyace irinta jaruman maza. Amma khadija kuka take yi ita sosai."
Goggo Asabe, tana yin sallah ta fice a gidan, sai wajan mai dambu.
"Lafiya Asabe irin wannan fitowar duku dukun?
"Ga yaranmu can rai a hannun Allah mai dambu, boka ya cuceni, ya mayar mun da yaro ba namiji ba. Gabaki d'aya yaran, gabansu ya lalace."
K'irji mai dambu ta dafe, tace.
"Nashiga uku har da khadijar abun ya shafa. ya boka zai mun haka?" Sororo Goggo tabi mai dambu da kallo, ita kuwa mai dambu bata san ma ta furta wannan furucin ba.
"Ohh mai dambu, kinso komai ya k'are akan shi Aliyun ne? baki da laifi ni ce na zama lusarar uwa mai yima d'an cikinta asiri. In da iyaye za su ji kuskuren dana aikata, nasan za su tambayeni, ina wannan son na uwa da d'a na jefar dashi. kaicona, mai dambu.
mai dambu ta zulle tace.
"Ba abunda ki ke nufi bane Asabe. wato yaronnan dan rashin Adalci sai da yayi tarayya da Sadiya, bacin a d'akin khadija yake? Asabe aiki ne ja a gabanki, ina yaronnan ba haka aka bar miki shi ba.
"me dambu, abunda yake gabana yanxu shine, mu tafi wajan boka ya warware wannan asirin da yai ma yarannan.
mayafi kawai mai dambu ta yafa su ka fice a gidan, sai gidan boka."
Mrs Bukhari
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
Instagram links👇
https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Facbook group
https://facebook.com/groups/463653111781414/
Telegram links
https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
33~34
"Boka ta fa b'aci, yaronnan sai da ya sadu da d'ayar matar tashi, sannan ya je ga d'ayar. Yanzu haka dukkansu suna kwance, jinya su ke yi, sosai ga zubar jini, muna cikin tashin hanali mara misaltuwa."
Dariya boka ya saki, yace.
"Dama ni nasan da wuya su tsallake, laulayine da asirin sosai. gashi da wuyar karyuwa. Aikine a gabanku ja. Domun har sai furen da shine mahad'in makarin, asirin ya fito. Kuma sai shekara ta zago, da damina yake fitowa."
Goggo Asabe wacce ta kasa magana tun zuwansu tace.
"shi yaron fa, wanne taimako za'a bashi?"
"Ai tashi ta k'are, shi da kwanciyar Aure kuma, sai a mafarki. maganin kashe namiji mus yake yi, sai dai ha'kuri." wasu hawayene suka shiga sunturi a kumatun Goggo, tana mai nadamar kuskuren data tabka. Mai dambu duk da dai ba ta so, abun yai tsanani haka ba. amma taji fari a ranta sosai, kuma kad'anma Asabe ta gani indai itace. A nata wautar tana ganin kamar Sadiya bazata amince ta zauna ba.
magani ya mik'o musu.
"Ga wannan, a samu bado a dafa musu da shi, sai su cinye badon, su kuma shanye romon. Za su samu sassaucin d'aukewar zafi."
Jiki a mace su ka fito
"Mai dambu ki kaini wajan wani bokan ko za a dace ya warware wannan asirin yaronnan ya samu zuriya. Na cuci kaina dana biye miki, mu ka zo wajan boka. na gwammaci da dole na yi mishi ya saki Sadiya, ko na fatattaketa da kaina, ai ina da wannan k'arfin.
"Haba Asabe, taya zan cutar da mijin 'diyata da gangan? Ni kaina bansan hakan bane zai faru. Kina ji fa, itama kanta a cikin hatsarin take, tunda shekara guda za ta yi a cikin ciwo."
"Shifa da rayuwar duniyarshi na lalata mishi fa? mai dambu na yi nadamar saninki ma a rayuwata, Allah ya tsine miki, ke da halinki, da masu irin muguwar nifak'a irin taki, tsinanna matsiyaciya"
A wajan Goggo Asabe ta tafi ta bar mai dambu. Mai dambu kuwa sai kiran sunanta take yi.
"Haba Asabe, fishi ba naki bane a cikin wannan halin. ki biyo ni mu je wajan fa'da da cikawa."
Goggo Asabe, ba ta da mafita. Haka su kai ta zagaye bokaye da 'yan tsibbu, har wajan 'yan bori sai da su ka je. Nasarar samo makarin Asirin khadija kawai aka samo. Amma Aliyu magana d'aya ake yi, cewar gabanshi har abada bazai sake aiki ba. Iya tashin hankali Goggo tana cikinshi.
cirko cirko su ka samu mata da mazan gidan. Gabanta ne yai mummunan fad'uwa.
"Sun mutu ko? Allah sarki Aliyu ka yafe mun. mai dambu cikin kuka tace.
"Shikenan khadija ashe hanyar Ajalinki kenan.
"Ba fa mutuwa su ka yi ba" Kawu ne ya katse musu, sambatun da su ka shiga yi. tsit su ka yi.
"Ba mu gansu bane, daga Aliyun har khadija, Sadiya ma ba ta nan.
Abokin su Aliyu ne Bilya ya shigo, cirko cirko ya samu jama'ar gidan. Bayan ya gaishesu ne yace.
"Kamilu ne ya bani sak'o in sanar da ku, sun wuce babban Asibitin cikin gari, domun ciwon bana gida bane." Godiya kawu yai ma Bilya.
"Ni nasan wannan matar tashi uwar kilbibi ita ce zata kawo wannan gurguwar shawarar, wannan ciwon ai ba na asibiti bane." Kawu ya ce.
"Ba komai, kai Anas sai ka zo mu tafi, zamu dawo da su gida, ga wanzan ya kawo magunguna. Sadiya kuma sai na ci mutumcinta baza ta zo mana da iyayin zuwa