Showing 3001 words to 6000 words out of 92932 words
Chapter 2 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt
sai in ina kawai na ke yi. Nan ta ke duniyata ta yi duhu, tare da yin ta maule da gangar jikina." Zaunar da ni mahaifiyata ta yi.
"Sadiya na sani abun za ki ji shi tamkar albamara, toh a zahiri yanzu ke matar aure ce wacce igiyoyi uku su ka rataye rayuwarki, dai dai da k'ofar gida in za ki lek'a a yanzu haka sai da izinin mijinki. Sadiya girma da darajar miji ya wuce zato ko tsammani, biyayyarki a gare ni shi zai ba ni damar tsallake jarabawar da dangin mahaifinki su ka za na mun. Ki amshi k'addarar da su ka 'kadarto miki.
Sadiya ina so ki cire wannan abun a zukatan al ummar da su ke kalubalantar ilimin Mace, ki nuna musu 'yar boko diyace mai tarbiya kamar ko wacce 'd'iya. Ki nuna musu cewar 'yar boko na iya zaman aure, 'yar boko ba mara tarbiya bace, kuma ba karuwa bace, ki nuna musu 'yar boko ita mace ce tamkar ko wacce mace, kuma 'yar boko ta na daraja mijinta, kuma tana yi mai tsantsar biyayya, ki cire musu k'ya matar macen da ta yi boko, ki fito da darajar gidan mahaifinki, domun ko wanne tsuntsu kukan gidansu ya ke yi, ki nuna musu kin haifu cikin 'yar boko, kuma ta dauraki bisa tartibiyar tarbiya. Sadiya ki yi ma dangin mijinki biyayya, dangin mahaifinki ne. Aliyu k'usar yak'i wanda ya ke karatu a jami'atul madina kar'kashin scholarship, 'kaninki. shine mijinki. Sadiya kar ki ce komai ki yi musu biyayya, sannan ki ajjiye aikin ki babu komai. Amma zuwanki wannan kauyan inaso ki yi amfani da iliminki ki shiga gaba wajan wayar da kan 'yan uwanki mata kan muhimmancin ilimin Mace, da irin gudummawar da ilimin mace ke bayarwa a duniya ba ki d'aya, ita mace uwar duniya ce. Ki yi k'ok'ari ki zama malamar ilimi a kauyannan, amma komai za ki aiwatar ki tabbatar da yardar mijinki. Ki yi ko'karin fahimtar da shi, tunda shi ba jahili ba ne."
Kuka na rushe da shi, wanda ya dauke ni da'ki'ku masu dama. Mama zuba mun idanu ta yi ba ta yi yun'kurin rarrashina ko katsemun kuka na ba. A lokacin zuchiyata da kwakwalwata ba sa amsar ko wanne irin sa'ko, ji na ke yi tamkar na zama wata halitta ce ta daban. Tausayin kai na da kai na ma ka'dai ya isheni. K'ok'ari na yi in tuno da fuskar Aliyun da aka kira shi da mijina. Amma na kasa, domun bai fi sau biyar mu ka ta'ba ha'duwa ba. Abunda kawai na sa ni game da shi, shine. Shine d'an auta a wajan Goggo Asabe, kuma na girme mishi da kusan shekaru biyar. Taya za'a aura mun 'kanina, ina babbar mace mai shekaru talatin da biyar? Wanne irin zaman Aure su ka zab'ar mana mu yi, dama har yanzu a na yin auran dole ne, ko kuwa a kaina abun ya juyo?" Dukkan Wa'dannan maganganun ni da zuchiyata na ke yi. Na shiga rudin da ya fi k'arfin gaban a misalta balle har ya rubutu. Cikin karyayyar muryar da ta ke sa ke jefa ni a damuwa mama ta ce.
"Sadiya! Ko ba za ki yi mun biyayya ba ne?"
Zan yi miki biyayya mama, amma mama me yasa za'a tauye mun hakkina, a hana ni ci gaba da aiki na? Aikin ceton rayuka fa na ke yi, mama na d'auki ilimi a matsayin GISHIRIN ZAMAN DUNIYA. asara ne boye ilmi, domun yin hakan bai baka damar ka sha romon ilmi ba. Na sha wuya wajan karatu, babu irin fa'di tashin da ba ki yi ba akan ganin kin cika wasiccin da Baba ya yi miki, sai kin yi kamar za ki fa'di, sai ubangiji ya taro ki. Dangin ki kuma su ka nuna mun soyayyar da su ka tsaya mun kan lammuran karatuna, har na ta ka matsayin da na ke a yau na anguwar zoma. Mama a iya sanina tun mahaifina da ran shi, kawo yanzu, babu wani tallafi ko gudummawar da ta ta'ba fitowa daga bangaren dangin Baba. Asali ma sai tauye hakkinmu da su ka so yi. Sai yanzu da na zama mutum......" Sadiya" mahaifiyata ta kira sunana da murya mai amo.
"Za ki yi mun biyayya ki amshi auranki a matsayin k'addarar rayuwarki ko yaya?" Cikin rauni da kuka na ce.
Na amince Mama na amshi auran, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi. Amma an dur'kusar mun da rayuwata, ko a addinance ba daidai bane a mai da mutumin daya rayu a maraya kauye, sai dai a fito da na kauye zuwa maraya." Jawo ni ta yi jikinta ta mayar da ni tamkar karamar yarinya shekshekar kukan ta na soma jiyowa, rabon da na ji kuka ko rauni a muryar mama, tun rasuwar Baba. Domun Mama ta kasance mace mai kamar maza jarumar Uwa. Da sauri na dago kaina, na dubeta. Hannu na sa ina share hawayenta, kukan nawa na ha'diye na ce.
"Haba Mama kar wannan auran ya d'aga miki Hankalin ki, ki kwantar da Hankalin ki, zan yi muku biyayya, da sannu dangin mahaifina za su yi alfahari da ilimin da ki ka tsaya mun nayi." A maimakon Mama ce za ta lallashe ni, sai ni ce na ke lallashinta. Akwatin sarka da 'dan kunnen azurfata, da kuma da d'an kunnen zinari na ta mi'ka mun. Hannu nasa na amsa ta ce.
"Ki rike su da kyau wata rana za su yi miki amfani, bansan ko yau za su ta fi da ke ba, ko sai gobe. Amma zan yi ko'karin zuwa in duba ki Sadiya. Sannan wannan dubu ashirin da biyu ne gudummawar biki da na soma samu daga kawayena. Shi ma ki ri'ke ki ta fi da shi, ki adana shi. Ahmad kuma da zaran an watse taro zan sa Hansatu ta ne mo shi, a ba su kayan lefen su da akwatin su. Sadiya ki na da suttura kar ki matsa sai Aliyu ya yi miki lefe, amma bazan hana ki amsa ba in dai sun yi miki adalci sun ba ki." Cikin murya mai taushi na ce
"Amma Mama za'a rake kayan d'aki na ko? Domun za su iya ma in da za'a ajjiye ni yawa." Sunkui da kaina na yi dan wasu sabbin ruwan hawaye ne su ka sulalo mun. Cike da tausayi da kulawa Mama ta ce.
"Babu abunda aka rage Sadiya kayan ki ne, kuma abunda bazai sa mu waje ba, bazai wuci kayan kitchen ba domun kitchen a tsakar gida ne na matan gida ba ki d'aya. Hansatu za ta ji da komai." Murmushi na yi ma Mama tare da sauke ajjiyar zuchiya mai k'una, na ce.
Toh shikenan Mama. " umarnin sa ke sutura Mama ta ba ni. A ban d'akinta na sa ke yo wanka. Riga da zani na sa ka, na lace d'inkin buba. Lace d'in ya amshe ni sosai. Popul colour ne jikin lace d'in, sai manyan fulawowi da aka zana a jikin lace d'in da bak'in zare. Bak'in mayafi da takalmi mai tsini mama ta ba ni. Bada son rai na na ke yin komai ba. Turare mai k'amshi ta fesa mun a jikina tace.
"Ki je ki samu kawayenki Sadiya. Na ji dad'in yanda ki ka shanye duk damuwar da ki ka shiga, tare da rungumar k'addarar rayuwar da dama ba kasan in da za ta gara ka ba. Ki je kar na ri'ke ki." Jikina a mace na fito. Kowa na ta kallona ana fadin "amarya" kunsan amarya ko ta buzuzuce farin jini gare ta. Cikin su Jamila kawayena na koma. Amma tunanina sam baya ma tare da su, su kan ji ina sauke ajjiyar zuchiya minti minti. Ni ba auran dolen da akai mun ba ne ya jefa ni cikin damuwa da tashin hankali ba. Bazan ce ban shiga ru'du ba, amma rashin aikina da karatuna da na ke ganin zai ta shi a tutar babu, ya fi komai caza mun kai na. Lumshe idanu na yi kawai, cikin kan'kanin lokacin jikina ya rincabe da zazzab'in da bibbiyu na ke ganin mutane, kuma na kasa magana sam, ga ciwon son Ahmad na nukurkusar zuchiyata, ga auran Dole da akaimun da k'anina, kuma ake shirin raba ni da maraya, aiki na na fi bashi mahimmanci fiye da komai, dan burina shine in yi suna, na zama fitacciyar unguwar zoma wacce tasan makamar aikinta. Ni dai ban sa ke sanin in da kaina ya ke ba, sai bayan isha, na farka na ganni akan gado na. Ga Mama da 'yan tsirarin dangin mahaifina ciki har da sirikata yar mahaifina Goggo Asabe. Baki ta tab'e tare da cewa.
"Tabbb ke da aka taimakama, kin kasa auruwa ke ce wai har da sumewa. Ashe shi k'usar yak'i, in labarin auranku ya ruske shi, mutuwa kenan ya kamata ya yi. Ai ni sulaimanu ya cuce ni da ya ha'da wannan auran. Yaro karami an ha'da shi aure da Babbar macen da ta fishi shekaru da wayo. Ba lallai bane ya samu tantanin budurci ma a jikinta ba, an gama cudanya da maza, har jiki ya 'd'auki warin maza. Ko wannan ya na karya jazbiyyar jikin d'iya mace, ku kuma gani ku ke yi waye wa ce. Abunda namiji in ba mijin auranki bane, ko a kujera ya zauna ya tashi, bai kamata mace ta zauna ba, dan kare jazbiyyarta, sai ta bari kujerar ta huce dan gudun lalacewar jiki. Amma 'yar boko ai ba ta san wannan ba. Maza su ne abokanta, tunda har ha'da hannaye suke yi da maza da sunan waye wa, tur da irin wayewar da ba ta addininmu da al'adunmu kyawawa na hausa Fulani ba."
Jina yi gabaki d'aya na muzanta a wajan, jina na ke yi tamkar tsirara. Wai surukata ce ta ke ya'ba mun muggan kalamai irin Wa'dannan tun kafin ma in tare a gidan 'danta. Ashe har zargina su ke yi da salwantar da budurcina? Ni tunda na karaci karatuna bana yawan mu'amula da maza, sau d'aya tak namiji ya ta'ba ri'ke mun hannuna. Ahmad ne, shine ya kafa wannan tarihin a rayuwata. Ni babbar mace ce, na kasance mai k'arfin sha'awa da son jin dumin namiji a kusa da ni. Lura da na yi da yanayi na ne, yasa ba na sake ma maza fuska dan gudun samun wata matsalar. Ko da yaushe a cikin azumi nake dan ganin na kare martaba da k'imata ta d'iya mace. Ashe na shiga ban d'auka ba bata fidda barawo. Mama na kalla wacce ta ha'de girar sama da ta k'asa tace.
"Yaya Asabe, bai dace kina jifan 'yar d'an uwanki da irin Wa'dannan alkaba'en ba. Ai ni a tunanina ya ci ace an jinjina ma tawakkalin da ta yi. Maganar kauye fa ake yi, da mutuwar aikinta. Uwa uba yaronnan k'aninta ne, ku.......... Dakata Aisha yayar za ki yi ma rashin kunya, ashe za ki iya zagin Adamu ma?" Goggo Mariya ce ta ke wannan Maganar. Hannuna Mama ta ri'ke tace.
"Mu je ki kwanta a d'aki na, ki sha magani sai ki yi sallah." Sum sum sum na bita Goggo Asabe kuwa kamar za ta ari baki tsabar fa'da. Sai hak'uri 'yan Uwa da su ka zo biki daga sauran garuruwa su ke ta bata. Wanka na yi dan in samu k'arfin jikina. Sannan na rama sallolina, na jima ina rokon Allah yasa mun albarka a Aure na, ya kare ni daga dukkan wani sharri, yasa in samu rayuwa da sauk'i. Mama ta saka ni a gaba ta ba ni ruwan tea mai kauri na sha, amma daci kawai baki na ya ke yi. Magani na sha, nasa rigar baccina. Mama tace.
"Ki yi kwanciyarki anan Sadiya. Bance da Mama komai ba, domun in nace zan yi magana kuka ne zai balle mun. Kwanciya kawai na yi. Mama ta dinga shafar kaina kamar karamar yarinya. A daren ranar tare da Mama mu ka kwana gado d'aya, ba ta bar ni na yi tunanin komai ba.
Allah ya yi dare gari ya waye, yau ne budar kai, kuma yau za'a wuce da ni gidan mijina.
*Mrs Bukhari Ibrahim*
*GISHIRIN*
*ZAMAN*
*DUNIYA*
True life story
_Daga Al'kalamin_
_Badi'at Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
GAWURTATTU BIYAR 🤚🏻
Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.
Kashi na 1
Babi na 5~6
A zaune na ke a bakin gadon Mama, a cikin ado da kwalliya na ke irinna amare. Material ne a jikina, d'inkin riga da siket, ja ne jikin material d'in, sai fulawowi da a ka yi ma material din milk colour. Dan kunne da sarka na sanya na azurfa harda awarwaro. K'afata sanye da takalmi me tsinin gaske milk colour. Light make up na yi ma kaina. Bak'a ce ni, amma ba can sosai ba, kuma baza a kira ni da wankan tarwad'a ba. Ba doguwa bace ni, gajerace 'yar duma duma, domun ina da k'iba amma ba can ba, amma ba za'a kirani da siririya ba. k'irjina a cike ya ke dam da dukiyar Fulani tamkar za su tsago rigata su fito. Ina da tudun mazaune sosai, sannan ina da fa'di, wato hip's. Idanuna manya ne kuma farare, sai dan hancina wanda bai yawanta tsawo ba, baki na kuwa leben saman bak'i ne, sai leben kasan kuma mai haske ne, amma ba ja bane. Ba ni da gashi sosai, amma ina kama shi da ribbon sai dai babu wata jela mai yawa, amma ina da cikar gashi sosai, gashin kaina ba ba'ki bane sosai ya d'an sirka da ja ta sama saman gashin, kuma ba mai laushi bane sosai, kuma bana amfani da man k'one gashi. Girata ta na ga gashi sosai, gashin idanuna basu da tsayi sosai amma a cike suke. Mata da yawa suna sha'awar irin k'ira da surar da Allah yai mun, musamman inna juya ina muskuta mazaunaina. Ba ni da tsantsar kyau ta fuska amma diri kam sai dai in ce Masha Allah. Ajjiyar zuchiya na sauke nan ta ke na shiga tunani mai zurfi. Hirar da ta wanzu a tsakanina da Ahmad, a shekaran jiya da daddare, bayan masu sanya ni a lalle sun sanya ni, na shiga tunanowa.
Zaune muke a cikin motar Ahmad k'irar Hala. Shagwab'a ya ke ta zuba mun cewar lailai sai na raka shi dubiyar mara lafiya abokinshi, a gidansu. Ni kuma na ce da shi.
Ahmad ba daidai bane mu fita tare, domun sai zuwa gobe ne za'a d'aura auranmu, ka d'an k'ara hak'uri ka'dan, zuwa jibi ina gidanka sai mu je mu duba shi. Idanu ya zuba mun ya na ma kirjina wani irin mayun kallo, kasancewar doguwar rigar wani yadi mai laushi na saka, kuma yadin yana la'bewa a jiki. K'irjina sun fito sosai ta cikin rigar, har shatin bra d'ina ana gani. Gabaki d'aya sai na lura hakan ya firgitashi sosai, da sigar lallashi ya ce.
"Haba Sadiya ashe ma baki yarda da ni ba har kika amince in zama mijinki gobe?" Da muryar soyayya na ce.
Haba Ahmad wallahi na yarda da kai. Ina kare martaba da darajar kaina ne, da ma gidanmu. Kamata ya yi ka ta ya ni. Ha'da idanun da na yi da Ahmad yasa gabana ya fa'di sosai. Sha'awata k'arara na ke karantowa a idanun Ahmad, sai dai na kasa fassara ma'anar launin fuskarshi gabaki d'aya da ta canja. A cikin mak'oshi ya ambaci sunana.
"Sadiya" shid'ewa na yi, domun duk illahirin tsigogin da su ke jikina sai da su ka tashi. Ban yi aune ba, na ji hannun Ahmad a cikin nawa. Sai da numfashina ya d'auke na wucin gadi. Da kyar na yi kokawar dawo dashi. Cikin sauri na fisge hannuna, na kuma ha'de rai na.
Meye hakan kuma Ahmad, sai da aski ya zo gaban goshi za ka shigo da irin wannan lalatar?" Da sauri na b'alle murfin motar. Wuf Ahmad ya sake rike mun hannuna. A fusace na juyo, kallon dana watsa mai ne, ya sanya ba shiri ya saki hannuna. Ban ko yi waiwaye ba na shige gida, ina ji ya na biyo ni ya na ta aikin ba ni hak'uri, ni kuwa nai kunnen uwar shegu da shi. Da sallama mama ta shigo ta katse mun tunanina. Ta ce.
"Sadiya zo ga karin kumallo ki yi. K'awayenki na wajan aiki sun iso, su na jiranki a d'akin ki. Kuma yaya sulaiman ya ce da wuri za ku wuce, zuwa sha d'ayan rana. Waje ba kusa ba." Ban ce Mata komai ba, na amshi karin kumallon na ci da yawa, dan mama ta ji sanyi. Magani ta ba ni na ha'diya. Sannan na fice zuwa wajan su Jamila.
*******
Asalin tarihin Sadiya da ahalinta.
Malam Buhari mai hula shine sunan kakana, wato mahaifin Babana. Sananne ne sosai a k'auyan su. Domun Allah ya hore mai arziki sosai, ya na da tarin shanu da rak'uma a wannan zamanin sama da guda d'ari. Gonakan shi kuwa sun fi na kowa yawa a kauyan. Gidan malam mai Hula babban gida ne mai k'ofa hudu. Ko yaro ka tara a hanya zai kawo ka gidan. Ya na daga cikin manyan dakatan k'auyan. Matar shi d'aya mai suna Safiya. Yaranshi kuma biyar maza biyu mata uku Kawu sulaiman shine babban 'dan shi, sai Goggo Asabe ita ce mai bi mishi, sai Goggo mariya, sannan Goggo Safiya ita ce ta ci sunan mahaifiyarsu, sai Adamu wato Babana, shi kuma