Showing 45001 words to 48000 words out of 92932 words

Chapter 16 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt

musu gajiyawata da yi musu hidima ba, har masoyina ya gushe ya na mai shi mun albarkar da su gani su ke yi na dabaibaye shi da asirine, kyakkyawar mu'amala da fahimtar halin juna shine ginshik'in zaman aure, in kina so ki more miji, yai miki biyayyar da bai ma san yana miki ba, ki kasance mai tausayinshi, ki kasance mai amsar ya kwai wa babu, juriya, kawaici, fahimtar me gidanki, girmama danginshi, yi musu hidima, nuna mai zallar soyayya. In kuka kama wannan abun kunci zuchiyar namiji kyauta ba boka babu malam, ni ban tab'a yaji ba, domun ban taso na tab'a ganin mahaifiyarmu cikin samun sab'ani da mahaifinmu ba balle har ta kai su da yin yaji, irin yakana, da alkunya irinta iyayenmu, da ace zamu dawo da ita cikin wannan zamanin namu da ba haka ba. Malam bahaushe yana da al'adu tsabtattu kuma nagartattu, amma yanzu Hausa fulani, ta fi ko wacce k'abila yin watsi da aure, saki da yaji ya zama ba bakin komai ba, wai shin duniyar nawa take ne? 'yan uwana ku duba tun sanda Sadiya ta bar gabana, ta tafi aure dangin mahaifinta, na shiga tunani da zulumin abunda kaje kazo, har hakan sai da ya haifarmun da hawan jini. Samun lafiyata shine ta samu farin ciki a hannun mijinta. Alhamdullilah Sadiya ta yabi Aliyu, na kuma ji dad'in hakan, halamu sun nuna a maganarta sun samu fahimtar juna a tsakaninsu, ku yi hak'uri ku barta ta koma cikin gatanta, Asabe duk haukar da ke damunta bazata iya cutar da Sadiya ba, jininta ne ke yawo a jikinta." gabaki d'aya su Goggo Hansatu jikinsu ya mutu murus, ko wacce cikinsu sai da kunyar abunda suka aikata ya lullub'esu, Goggo.Hansatu tace.
"Gaskiya ne Yaya, kinyi magana mai ma'anar da mai hankali zai d'auka. In sha Allah da zaran Sadiya ta warware, ni da Ya Binta za mu maidata d'akinta, za mu ci gaba da k'arfafa guiwarta in sha Allah, burinmu shine ta zauna lafiya, kuma Sadiya ta yi k'ok'arin rungumar k'addararta, ta yi biyayyar da bazata tab'e ba." Mama tace.
"Akan Sadiya saida idona ya soye, sam bana samun bacci, tsaiwar dare, sadaka, Ina tawassali da wad'annan aiyuka wajan rok'on Allah ya sanya haske da albarka a cikin rayuwar Auranta." Goggo Binta tace.
"Yaya wallahi kin maye mana gurban mahaifanmu da su ka kwanta dama, ke uwace wacce za'a bigi k'irji a nuna ma duniya, madalla da samun Yaya kuma uwa kamarki. Sadiya kuma daga asibitinnan sai gidan mijinta, kuma zamu bada hak'uri, dan mu dawo da martabarta da kimarta, dan gudun kar ai mata kallon wacce ta gaza, yanxu na gane yin yaji gazawar hak'urine a wajan mace, musamman yajin da zaka dako badan zafin abunda miji yai maka ba, sai dan maganganun mutane." Dr ce ta fito daga d'akin da Sadiya take, tace da su mama.
"karku dama, k'aramin ciki gareta, kuma abunda ke cikin nata ya sha wahala ne da ita kanta ma, Allurai nai mata, sai ruwa dana d'aura mata. zuwa anjima zata tashi, sai kuma ku tafi gida." Mama tace.
" 'yannan mun gode, amma ba mu yanki kati ba, bamu biya komai ba." murmushi Dr d'in tayi tace.
"Sadiya ta wuci haka anan asibitin, kuma wannan asibitin yayi rashin jajirtacciyar ma'aikaciya. Irinsu Sadiya ba su da madadi sam." wucewa ta yi ta bar su Goggo na zunduma mata Albarka. mama tace.
"Hansatu, ki zo ki tafi gida, a had'o kan kayan Sadiya. Sannan ki yi mata siyayyar abunda kike ganin ya dace kuma zata buk'ata, sai ki biyo ku kama hanya, ta lallab'a." Goggo Hansatu, ba tai musu ba ta amshi key a hannun mama, da kuma dubu ashirin data mik'a mata ta wuce.
Bayan awa biyu


Sadiya
Ahankali na bud'e idanuna. Salatin Annabi S A W na soma jerowa a hankali, wata iriyar nadama da jin haushin kaina duk suka lullub'eni. Mama ita kad'aice a zaune a kan gadon da nake, da sauri ta matso.
"Kin farka Sadiya, sannu yaya k'arfin jikin?" Dubanta nayi, ta rame ta lalace nace.
"Mama ciwo kike yi ne, jiya na ji jikinki da zafi? cijewa Mama ta yi tace.
"Zazzab'ine na kwana biyu na yi Sadiya, jikin naki da dama dama ko? Lumshe idanuna nayi, uwa mai dad'i ji yanda mama take nannan dani, in banda uwa wazai ma haka? Aliyu ne ya fad'o mun, shi kam ya rasa wannan kulawar a wajan Goggo sabida ni kawai, na tabbatar kawaici yake yi mun, amma bazai tab'a jin nutsuwa ba. Mama ce ta katseni da cewa.
" Zaki iya tafiya ko, dan yanzu su Binta na dawowa za ku koma Inda kika fito, wannan kuma ya zame miki na k'arshe karki bari ko da wasa ki zubar da kimar ki a idon miji, kar ki sake ya ga gazawarki, Yaya Asabe ai uwace a wajanki, bawai Aliyu bane ya had'aku ba. Duk fad'an da zata miki a 'ya take kallonki ba suruka ba. Ki kyautata mata iya kyautatawa ki yi mata biyayya. Mijinki kuna zaman lafiya ko, in ce dai bakya raina shi? zaine na tashi a hankali na jingina, sannan nace.
"mu na zaune lafiya, wallahi yana kyautata mun sosai, kuma akwai girmamawa sosai a mu'amalar tamu, shi kam bana samun ko wacce matsala da shi"
"Ita abokiyar zaman taki fa, ba dai kwa samun matsala dai ko?"
A'a babu matsala tsakanina da ita."
"Toh masha Allah, kibi mijinki shine tsaninki, sai inda ya ajjiyeki, karki sake Sadiya."
Ahankali ya iso inda muke, sanye yake a cikin malum malum, da hula dara a kanshi, sai k'amshi yake busawa idanunshi sanye da glasses fari, amma da gani na k'arin ganine. dattijo ne,gemunshi da gashin bakinshi duk furfura, hakama 'yar sumar da ya tara a kanshi, akwai furfura amma d'aid'aiku. Mamakine ya cika ni ganinshi tsaye a bakin gadon da nake zaune, hannunshi cike da leda d'auke da lemo da ayaba." mama ta yi murmushi, irin wanda rabon da inga murmushi irin wannan a fuskar mama, tun Baba yana da rai."
"Barka da zuwa yallab'ai, ya kasan muna asibiti?" wani dattijon murmushi ya saki mata.
"Hansatu ce tai mun ido, na isa k'ofar gidan ina jiran yaron aike, sai gata ta fito, shine take sanar mun d'iyarmu babu lafiya, toh ai zama bai ganni ba, sai kawai na biyo ta." Mama tace.
"D'aliban fa, wa kabar ma su?"
"Wa yake ta wasu d'alibai 'diyata babu lafiya?" ni dai sai rarraba idanu nake yi a tsakani, cikin halin girma na gaishe da wannan dattijon da na ji ko iya had'a idanu na kasa yi da shi. Da far'arshi ya amsa mun gaisuwata, tare da tambayata kufan jiki,
Da sauk'i" Shine amsar da na mayar mishi.
"Sadiya wannan sunanshi, malam mustapha kaka, malam mustapha wannan itace d'iyata Sadiya, wacce kullum sai na tsokata maka labarinta." Murmushi yayi, yace.
"Allah yai ma rayuwa albarka, ita ta zo duba ki da jiki, sai kuma ta kwanta jinya kuma, Toh Allah ya baku lafiya, ga kayan marmari ki bata, zan jira ku a waje, in Hansatu ta dawo daga kasuwa sai in kaisu ai, ina fatan za ki rakata ko? murmushi mama tayi kawai irinna manya, ta amshi laidar hannunshi, shi kuma ya ajjiyemun, dubu uku a gefen gadona, yai maza ya fita."
sha'awa soyayyar tsofaffin ta bani, cikin zolaya nace.
"Mama wannan shine Abban nawa? dukan wasa ta kawo mun, na kauce ina dariya. wani farin ciki ne ya lullub'eni da mama ta samu masoyi, dan na jima da lura, ganina a gabanta ne ya hanata ba ko wanne namiji wata dama, dan mama ba tsohuwa bace, kuma ta na da kyan jiki, 'yar boko ce mai son kwalliya da kyaran jikinta. Farin cikina na nuna mata a fili, sannan nace.
"Mama Amma taren za mu tafi ko, tunda a mota zai kaimu? mama tace.
"Sam ni bazani ba, ban tab'a shiga motarshi ba gudun fassarar da mutane za su yi mun, k'ofar gida yake zuwa, shima a bakin zaure muke hirar a tsaye, da rana ko da safe, dan gujema sharrin shaid'an." kai na girgiza tare da jinjina ma mama. Su Goggo Binta na dawowa mu ka wuce, dama ita gida can family house ta je ta d'ebo mun tsarabata. rankaya muka yi wajan motar tashi, bayan na kewaya mun gaggaisa da 'yan tsirarin k'awayena. Sai da malam ya neman ma mama abun hawa, yaga tafiyarta. Sai muma muka kama hanya."




mrs Bukhari


*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*








1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_


5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_




Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300


*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇


0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.


Domin tura shaidar biya👇


0810 433 5144


Masu tura katin MTN👇


0814 179 9224


Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇


0817 952 3215


Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f


*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨




Instagram links👇


https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=




Facbook group


https://facebook.com/groups/463653111781414/




Telegram links


https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk




*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -


*Enter your name:* (Cikakken sunanki)


*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)


*Enter your password:* ( misali 12341234)


*Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


Masu iPhone


Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
37~38


Kano State


Sadiya
motar mu ce ta shiga cikin tashar Anguwa uku. Da misalin k'arfe Goma sha biyun dare, garin yayi shiru babu kowa, babu abun hawa na haya a titi, sai motocin gida.
Ahankali na ke fitowa daga cikin tashar, ashe haka mata masu k'aramin ciki su ke mugun galabaita a sakamakon doguwar tafiya? Kai cikin ma kan shi rainon shi akwai wahala, jiki baya sake samun cikakkiyar lafiya kuma, har sai Allah ya raba lafiya."
Ina tsaye a titi nama rasa tudun dafawa, ga wani zazzab'i da ya addabeni tun a hanya, wunya ta dameni sossi."
motar da bazan tab'a mance mamallakinta a rayuwa ba, itace ta tsaya a gabana.
Kawar da kaina nayi gefe tamkar ban ma san da tsaiwar motar ba." fitowa yayi, zuwa in da na ke tsaye.
"Sadiya, saukar yanzu kenan? Bari in kai ki gida, yanxu ba zaki samu abun hawa ba." wani irin miki Ahmad ke famo mun a cikin zuchiyata, amma jiri da zazzab'in da ke damuna, yasa ban nemi zab'i wajan shiga motar Ahmad ba." Ba wanda ya ce da wani uffan, sai sharara gudu kawai ya ke yi dani a titi, Har zuwa k'ofar gidanmu.
k'wakwalwata sai hasko mun abubbuwa da dama take yi, domun Ahmad ya sha suntirin zuwa k'ofar gidannan. Fitowa na yi a cikin motar, shima ya fito, jakata ya ciro mun tare da cewa.
"A huta gajiya Sadiya, gobe in Allah ya kaimu zan lek'o kafin in je office." Bani da lokacin sauraron Ahmad, jakata na d'auka zuwa k'ofar gida. Ahmad bai gushe a wajan ba, har sai da ya ga shigana cikin gida. k'anwar mahaifiyata ce Goggo Binta da ta ke aure a Saudiyya ita ta bud'e mun k'ofar gidan. Jikinta na fad'a tare da sakin wani irin kuka. k'ofar gidan ta kulle, ta rik'e hannuna, da jakata zuwa ciki. mama na hango a kwance a kan gado, Goggo Hansatu kuma tana gefenta, magani ta ke bata.
Da sallama mu ka shiga cikin d'akin, mama ta dube ni cike da kallon tuhuma, kallo d'aya nai mata tsoro duk ya bi ya kamani, dan kallon da take watso mun na riga nasan me ta ke nufi, na ga Mama ta rame sosai, da dukkan halamu bata da lafiya ne. Amon muryar mama ne ya katseni.
"Kin kaso auren naki kenan ko Sadiya? lallai kin ba da mata 'yan boko, kuma ma'aikata, irinku ke sa ake mana kud'in goro a cikin al'umma. D'auka su ke yi cewar ba ma iya zaman aure. kin kyauta, da ki ka nuna ma dangin mahaifinki ban gina ki bisa tartibiyar tarbiya ba, na kuma gode da kika kunyata ni." Kan ta ta kawar a kaina, jikina na rawa na isa bakin gadon da take, hannunta na kamo, ajjiyar zuchiyace ta kubce mata ba shiri.
Mama ba aurena na kaso ba, asalima babu wata b'araka data tab'a shiga tsakanina da Aliyu. Mama amma kowa a gidan ya tsaneni, barin ma Goggo Asabe wacce har abada baza ta tab'a so na ba. Juna biyu dana samu bai sa ta sassauta mun ba, kullum a cikin umartar Aliyu ya sake ni ta ke, kullum a cikin fad'a da shi take. Ni ina tsoron kar Allah yai fishi da shi, a sakamakon fishin da Goggo take yi dashi ne, shiyasa na dawo gida." Rungumeni mama ta yi kawai a jikinta, ina jin dumin jikinta irinna marasa lafiya. Goggo Binta tace.
"Tun farko Yaya ke kika jama yarinyar nan, wanne irin k'iyayya ne Asabe bata nuna miki ba, matar da har gobe ba k'aunarki take ba, sai Sadiya za ta k'aunata, ni fa ina ganin dole aurannan yazo k'arshe bazai yuwu mu xuba idanu muna kallon Sadiya a cikin irin wannan halin ba, gashi har rabo ya shiga tsakaninsu." Goggo Hansatu tace
"Gaskiya kam, bafa k'aramin cutarwa su kai ma Sadiya ba. Yarinya da iliminta da aikinta, a kai ta aure k'auye. wallahi ko musulunci ma bai yarda da wannan ba, domun akwai cutarwa da durk'usarma da mutum rayuwa, ni ya bata takaddarta kawai, Yaya Binta in zata koma Saudiyya su tafi tare da ita kawai." dam gabana ya yanke ya fad'i, tsuru tsuru na yi a cikinsu. mama tace.
"Binta da Hansatu hoo, ai in muka yi haka ba mu nuna dattaku ba, kuma ba haka iyayemu su ka koyar da mu ba, mun zama bamu da banbanci da su kenan. ba zan tab'a sa hannu wajan mutuwar auran Sadiya ba, sai dai ma in bata ha'kuri, domun duk wani aure in za ki kalla hak'uri ke rik'e da shi, bawai soyayya kad'ai ba. Ga rabo a jikinta, bazan so ace Sadiya ta haihu kuma bata tare da uban d'an ko 'yar da zata haifa ba. wuya fa bata kisa, ni d'innan babu da irin abunda Asabe bata jefe ni da shi ba, na kunshi takaici da bak'in cikin Asabe kashi kashi. Yanzu nan damar da bata samu ba a baya, sabida Adam bai bama kowa k'ofar da zai wulak'antani a gabanshi ba, shine take so tai mun horo akan Sadiya. ita bata girma, duhun jahilci na cin rayuwarta." Ajjiyar zuchiya na sauke. Mama ta sauka daga kan gadon da take, ta rik'o hannuna ta zaunar dani akan gadon, sannan ta fita.
Goggo Hansatu ta dube ni tace.
"An yi auran shi Aliyun da ita khadijar da Asabe ta fi so? kai na d'aga mata kawai, dan wani zazzab'ine ke hawa kaina, na kasa ko da magana.
mama ce ta shigo da ruwa a boket, ta shigar mun da shi toilet.
"ki watsa ruwa, sai ki zo ki sha tea, kamar cikin na baki wahala ko? naga kin rame sosai. A hankali nace.
"Zazzab'ine ya rufe ni mama, tun a mota nake jin shi, na sha wuya a mota sosai." Nan su ka shiga yi mun sannu tare da lallab'ani. Ai wankan da na yi kamar zazzab'in na tsokano, na fa jikina ya shiga kerma, amai na tunkud'omun, gashi babu komai a cikina. A kaina su Goggo Hansatu su ka kwana, dan har zabura na ke yi, washe gari da sassafe sai asibiti, cikin gaggawa aka bani gado."
"Yaya Aisha, yarinyar nan bai fa kamata ace mun tursasa mata komawa dangin mahaifinta ba, ga k'aramin ciki a jikinta amma su ka barta ta fito, ai shima Aliyun ya kamata ya biyo sawunta. Goggo Binta tace.
"In baki da k'arfin fad'a da su, mu muna da shi, Sadiya kuma da ita zan koma Saudiyya kowa ma sai ya huta, ji yanda ta fad'a ta yi duhu." mama ta dubesu ta girgiza kai.
"Baku da lissafi sosai, taya zamu zama silar mutuwar auranta, saidai in shi Aliyunne ya bata takadda, toh anan fa ba wanda ya isa ya tank'warani Sadiya ta sake koma mai, amma dan komawa d'akinta zata koma. Ana Sallamarta ni da kaina zan mayar da ita. ba dole sai ta rayu a birni bane zata samu farin ciki, haka ba dole sai ta samu dukkan wani abu da take so ba. Mu bi komai a sannu, indai Asabe ce, zata tursasa sai Aliyu ya saki Sadiya, saidai in rabon da ke tsakaninsu mai yawa ne, Asabe muguwar jahilar macece, tsabaragen masifarta, kab 'yan uwan nata tsoronta su ke ji, har shi Yaya sulaiman, sai fa abinda tace mishi. Ziyara kawai Asabe zata kawo mana, amma sai ta ne mi ta fini iko da komai. Wallahi ban tab'a nuna musu fishi ko da akan fuskata bane, ban tab'a nuna musu gajiyawata da yi musu hidima ba, har masoyina ya gushe ya na mai shi mun albarkar da su gani su ke yi na dabaibaye shi da asirine, kyakkyawar mu'amala da fahimtar halin juna shine ginshik'in zaman aure, in kina so ki more miji, yai miki biyayyar da bai ma san yana miki ba, ki kasance mai tausayinshi, ki kasance mai amsar ya kwai wa babu, juriya, kawaici, fahimtar me gidanki, girmama danginshi, yi musu hidima, nuna mai zallar soyayya. In kuka kama wannan abun kunci zuchiyar namiji kyauta ba boka babu malam, ni ban tab'a yaji ba, domun ban taso na tab'a ganin mahaifiyarmu cikin samun sab'ani da mahaifinmu ba balle har ta kai su da yin yaji, irin yakana, da alkunya irinta iyayenmu, da ace zamu dawo da ita cikin wannan zamanin namu da ba haka ba. Malam bahaushe yana da al'adu tsabtatattu kuma nagartattu, amma yanzu Hausa fulani, ta fi ko wacce k'abila yin watsi da aure, saki da yaji ya zama ba bakin komai ba, wai shin duniyar nawa take ne? 'yan uwana ku duba tun sanda Sadiya ta bar gabana, ta tafi aure dangin mahaifinta, na shiga tunani da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login