Showing 42001 words to 45000 words out of 92932 words

Chapter 15 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt

a kotu, tunda su 'yan boko ne, masu sanin hakkokin kansu.
Ina shiga d'aki na soma harhad'a kayana iyakar wanda zan iya d'auka. Hijabina na zura, fitowa nayi tare da kulle b'arayin nawa. Hawaye kuwa ya gama wanke mun fuskata, ga wani matsanancin ciwo da kaina ya ke yi mun. K'ofar baya na bi nai ficewata.
wajajen Azahar Babur d'ina ya sauke ni a bustop, motar dake kan lodin zuwa zamfara na shiga. Na galabaita ainun, har amai sanda na yi. Ina zaune a motar nan shiru, ina tunano maganganun Goggo da irin k'iyayyar da take yi mun ni da mahaifiyata. Yau ina ma Baban da ake magana ma a kanshi? Babu ya kwanta dama, amma ace har zuwa wannan lokacin su Goggo baza su xubar da makaman ya'kinsu da mahaifiyata ba. A ganina tsantsar son da zan nuna ma Aliyu shine in fita a rayuwarshi ya samu daidaito da mahaifiyarshi, duk da akan daidai yake, amma mahaifiya tafi gaban a dinga jayayya da ita, kullum tana cikin fishi da Allah wadai a kan ka. Girman uwa yafi gaban misalin da za'ayi wasa da furucin da zata dinga fad'ama marasa dad'i, kullum a hassale take da kai. Hakan sai ya tab'a maka rayuwa ta yanda baza ka samu albarka rayuwa ba. Babban farin cikin ka yau shine, iyayenka ka yi duk yinka ka rabu da su lafiya." Idanu na lumshe, motar mu kuma ta hau tafiya. wani nishin kukane ya taso mun, ina ganin nayi nisa da Aliyu. Da kyar na sa harshe na danne kukan, sai wasu wahalallun hawaye ne su ka gangaro mun, da sauri na sa hannu na share su.
Misalin k'arfe hud'un yamma motar mu ta shiga cikin tasha, inda ake lodi gari gari, sa'ar da na yi, motar kano saura mutum guda su ke jira, ina shiga mota ta cika, mu ka d'auki hanya, sai kano."


Aliyu
jagob ya zauna, kan shi har wani juyawa ya ke yi, kalmar da goggo ta fad'i game da cikin Sadiya yafi gomai d'imauta shi, dolen shi ya cire kunya ya fayyace ma Goggo a yaya ya samu Sadiya.
"Baba kar ki sheganta mun jini, wallahi Allah Baba, Sadiya na sameta a matsayin cikakkiyar budurwar data tsare kanta, tai ma mijinta kyakkyawan tanadi, khadija ce ban sameta a hakan ba ma. Amma na rufa mata asiri ko ita bata san da hakan ba, cikin nawa ne." kukan shi ya ke son had'iyewa dan gudun kar Goggo tace, Sadiya ya ke yi ma.
"Na ji ka sameta Budurwa. ka sani, indai jika daga tsottson Aisha zai samu, harko duniya ta nad'e bazan k'aunace shi ba, nama gwammaci ace baka da d'a Aliyu. Son da kake ma Sadiya ya wuce kimar da za'aimai kallon hankali, dubi fa yanda ka gigice dan kawai ta ce ma zata tafi, tunda khadija ta koma gida sau nawa ka tambayeni ita, ko ita ba matarka bace? Ahir d'inka dani." yaya Fatima ce ta banko cikin d'akin tana kururuwa, Goggo tace.
"Ina fatan ba dukan ki yayi ba? dan in dukan ki yayi, mai rabani da uwarshi Habi sai Allah." cikin shesshek'a Fatima tace.
"Saki na yayi Baba, shikenan dama shekarun baya ya mun saki d'aya, yanzu kuma ya mun saki biyu, ya rabani da yarana Baba."
Duk kurin Goggo sai da wannan mutuwar Aure ya jijjigata. D'akin ya d'auki shiru na fin minti goma. Ko wanne a cikinsu da abunda ya ke sak'awa."
Tabawa ce ta doko sallama tare da shigowa a tare. Goggo ce ta amsa mata, Tabawa ta bi kowa da ido"
"Lafiya ciwonne ya tashi ko yaya?" Goggo ta nisa tace."
"Ko d'aya, ita wannan sakinta mijinta yayi, shi kuma shanyayye kan mace ne ya shiga wannan yanayin. Kawata kamar kinsan ina nemanki ruwa a jallo. Tabawa tace
"Badai ruwa a jallo ba, Dan ban ganki a cikin gidana ba. Aliyu ya jikin? "da sauk'i" ya ce mata, sannan ya gaisheta. Fatima ma gaisheta tayi. Goggo tace.
"Fatima ki je d'akin Safiya ki jira mu, kai kuma zaka iya komawa, b'arayinka, tunda ga Fatima ta dawo gida, dole zan bar kwana a wajan Safiya mu dawo nan"
Suna shiga ya mik'e da sauri, har yana fama ciwonshi, ya nufi gidanshi. kwad'on da ya gani a k'ofar shi ya tabbatar mishi da Sadiya ta tafi. zama yayi a kofar gidan nashi, yana sauke ajjiyar zuchiya. Lallai tafiya kano ta kama shi dole. Jiki a sab'ule ya nufi wajan kamilu.
"Kamilu ka ji duk abunda ya faru, Baba so take in mutu kowa ya huta, su suka sa ni a cikin wannan halin, Baba ta kasa kwantar da hankalinta ta d'auki Sadiya, 'ya kuma suruka, Cikina ne fa a jikin Sadiya, ya zanji in sanadin wannan doguwar tafiyar da take gabanta wani abun ya cutar da ita ko abunda ke cikinta fa? Kamilu likitoci cewa su ka yi, ba lallai gabana ya sake tashi har yayi aikin da zan iya saduwar Aure ba, balle samun rabo, toh ga rabo Allah ya bani, da daren mu na farko, daren da mummunar k'addara ta gifta mun. Sadiya ita ke kula dani, tunda na soma ciwonnan, khadija ta na gidansu, tana jinya ita ma, amma ai an fad'amun ana ganinta tana lek'a waje, daidai da sau d'aya bata tab'a zuwa dubani ba, haka mahaifiyarta da mahaifinta. Ashe Sadiya ba ta yi k'ok'arin da yaci a yaba mata ba? Baba ta ki yadda da k'addarar auran daya kawo Sadiya wannan k'auyan ta na 'yar boko, ma'aikaciya, mai ci daga asusun gwamnati kai tsaye.
Kamilu ya dafa kafad'ar Aliyu yace.
"Ni ina ga zuwa gobe ka yi shirin zuwa bikon matarka kawai, domun ba baza su dawo maka da ita ba, sai anje biko, a al'adance. Baba kuma bazata wakilta kowa dan zuwa bikonnan ba. Aliyu baka da d'an wani wajan zuwa ne, a birni haka? Da mamaki ya ke kallon Kamilu, domun bai san me ya kawo zancannan ba.
"Meye had'in tambayarnan da maganar Sadiya?"
"In da ace kasan wani a birni, da sai in ce, kud'anyi wata 'yar tafiya da Sadiya mana dan samun keb'ewa, ace itama ta samu kulawa daga gareka, duk da dai kana cikin lalura ne." Aliyu yai shiru kamar mai nazari, can sai ya ce.
"Ai kuwa akwai Abokina Haidar tare mu kai karatu da shi a madina, kuma wallahi ya ban adireshin shi, suna garin Abuja. Dan ko da jirginmu ya sauka a garin, ya gabatar da ni a wajan iyayenshi, kuma mutanen kirki ne. Mahaifinshi na da wata babbar makarantar boko da arabiyya a cikin garin na Abuja, Haidar d'inma makarantar zai je ya kular ma da mahaifin nashi, sakamakon 'yan bani na iya da su ke son durk'usar da makarantar, dama karatun makarantar. Ya had'ani Allah Annabi kar mu watsar da zumunci, zai zo har inda nake." Kamilu yace.
"Lokaci yayi da za ka kai ma Haidar ziyara a Abuja. Kuma ina son sanar maka kafin ka dawo zan kwashe iyalaina za mu bar Raquma. Aliyu babu ci gaban komai a Raquma. Ko dako zan fita in nema. sokoton shehu zan koma. Aliyu yai shiru"
"Amma kamilu zan yi kewa sosai."
"Kai ma ina mai baka shawara kar ka ce za ka 'kare rayuwarka a cikin Raquma, domun ba lallai burinka ya cika ba, nason bud'e makarantar addini a Raquma ba. kar kaso kaji yanda matasa da mata ke zaginka kan wannan ci gaba da kake son bayarwa a wannan k'auye namu. Yau in dai bakwa Raquma ziyara ku ke shigowa yi, ai za ku zauna lafiya da Baba." Dariya kawai Aliyu yayi, dan ya san babu wani abu da zai fad'a wanda Baba zata amince dashi har yabar k'auyannan. domun in banda almajirci, babu wanda yake rayuwa a wani wajan a gidan su, kowa ya na gida, da dama sun yi yunk'urin hakan Amma manyan gidan sun k'i su amince da hakan, dan Goggo ita baki ma tai ma yaranta akan duk mai son barin Asalinshi, bata yafe ba."


Goggo
Tabawa, nifa tunda Aliyu yai Aurannan bana cikin hayyacina. Har mafarki na ke yi da matar tashi tana bina da wuk'a zata kasheni. Aliyu har kuka ya ke yi tsabar son yarinyar, ta gama lashe mai zuchiya da asiri. Toh ga ciki kuma yanxu ya b'ullo, kinga data haihu zata mik'e k'afa sai kuma abunda ta ce shi za mu yi ni da Aliyu, Ga fatima aure ya k'are. ga masifar da mai dambu ta jefa ni a ciki, ta kaini wajan boka aka kashema yaro al'aurarshi, boka fa cewa yayi bazai sake mik'ewa ba, shi da mace sai dai kallo."
Tabawa ta yi dariya irinta 'yan duniya tace.
"Ta xo ma da sauk'i ai Asabe, rashin lafiyar da ya ke d'auke da shi, bazai barta ta dauwama da shiba, dole za'a je matsayar da za ta buk'aci saki dole. maganar zubar da cikin ne a gabanmu, sai kuma mu had'a da sa boka ya cusa k'iyayyar juna, da jin haushin juna a tsakaninsu. da na zuba miki idanune ke da Aminiyar taki mai dambu, ba gashi ba. Mai dambu k'ananan bokaye take bi, kixo in kai ki gidan 'yan bori da 'yan tsubbu."
Goggo tace.
"Hmmm ai mai dambu ta ban mamaki. Kuma a hakan so su ke Aliyu ya saki d'iyar ta su, wai har da mai gari ma sakin dai su ke buk'ata. Tabawa ta ce.
"Ke dai sako mayafi mu wuce, dama ni ma da kyar guntuwar matsalata. ma karashe hirar a hanya" cikin sauri Goggo ta saka mayafi su ka fice a gidan, Babur su ka hau zuwa can cikin k'auyan nasu."


mrs Bukari ce
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*








1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_


5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_




Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300


*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇


0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.


Domin tura shaidar biya👇


0810 433 5144


Masu tura katin MTN👇


0814 179 9224


Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇


0817 952 3215


Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f


*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨




Instagram links👇


https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=




Facbook group


https://facebook.com/groups/463653111781414/




Telegram links


https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk




*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -


*Enter your name:* (Cikakken sunanki)


*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)


*Enter your password:* ( misali 12341234)


*Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


Masu iPhone


Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
[8/14, 8:36 PM] Badiat Ibrahim: G Z D
MRS BUKHARI
37~38


Kano State


Sadiya
motar mu ce ta shiga cikin tashar Anguwa uku. Da misalin k'arfe Goma sha biyun dare, garin yayi shiru babu kowa, babu abun haka na haya a titi, sai motocin gida.
Ahankali na ke fitowa daga cikin tashar, ashe haka mata masu k'aramin ciki su ke mugun galabaita a sakamakon doguwar tafiya? Kai cikin ma kan shi rainon shi akwai wahala, jiki baya sake samun cikakkiyar lafiya kuma, har sai Allah ya raba lafiya."
Ina tsaye a titi nama rasa tudun dafawa, ga wani zazzab'i da ya addabeni tun a hanya, wunya ta dameni sossi."
motar da bazan tab'a mance mamallakinta a rayuwa ba, itace ta tsaya a gabana.
Kawar da kaina nayi gefe tamkar ban ma san da tsaiwar motar ba." fitowa yayi, zuwa in da na ke tsaye.
"Sadiya, saukar yanzu kenan? Bari in kai ki gida, yanxu ba zaki samu abun hawa ba." wani irin miki Ahmad ke famo mun a cikin zuchiyata, amma jiri da zazzab'in da ke damuna, yasa ban nemi zab'i wajan shiga motar Ahmad ba." Ba wanda ya ce da wani uffan, sai sharara gudu kawai ya ke yi dani a titi, Har zuwa k'ofar gidanmu.
kwakwalwata sai hasko mun abubbuwa da dama take yi, domun Ahmad ya sha suntirin zuwa k'ofar gidannan. Fitowa na yi a cikin motar, shima ya fito, jakata ya ciro mun tare da cewa.
"A huta gajiya Sadiya, gobe in Allah ya kaimu zan lek'o kafin in je office." Bani da lokacin sauraron Ahmad, jakata na d'auka zuwa k'ofar gida. Ahmad bai gushe a wajan ba, har sai da ya ga shigana cikin gida. k'anwar mahaifiyata ce Goggo Binta da ta ke aure a Saudiyya ita ta bud'e mun k'ofar gidan. Jikinta na fad'a tare da sakin wani irin kuka. k'ofar gidan ta kulle, ta rik'e hannuna, da jakata zuwa ciki. mama na hango a kwance a kan gado, Goggo Hansatu kuma tana gefenta, magani ta ke bata.
Da sallama mu ka shiga cikin d'akin, mama ta dube ni cike da kallon tuhuma, kallo d'aya nai mata tsoro duk ya bi ya kamani, dan kallon da take watso mun na riga nasan me ta ke nufi, na ga Mama ta rame sosai, da dukkan halamu bata da lafiya ne. Amon muryar mama ne ya katseni.
"Kin kaso auren naki kenan ko Sadiya? lallai kin ba da mata 'yan boko, kuma ma'aikata, irinku ke sa ake mana kud'in goro a cikin al'umma. D'auka su ke yi cewar ba ma iya zaman aure. kin kyauta, da ki ka nuna ma dangin mahaifinki ban gina ki bisa tartibiyar tarbiya ba, na kuma gode da kika kunyata ni." Kan ta ta kawar a kaina, jikina na rawa na isa bakin gadon da take, hannunta na kamo, ajjiyar zuchiyace ta kubce mata ba shiri.
Mama ba aurena na kaso ba, asalima babu wata b'araka data tab'a shiga tsakanina da Aliyu. Mama amma kowa a gidan ya tsaneni, barin ma Goggo Asabe wacce har abada baza ta tab'a so na ba. Juna biyu dana samu bai sa ta sassauta mun ba, kullum a cikin umartar Aliyu ya sake ni ta ke, kullum a cikin fad'a da shi take. Ni ina tsoron kar Allah yai fishi da shi, a sakamakon fishin da Goggo take yi dashi ne, shiyasa na dawo gida." Rungumeni mama ta yi kawai a jikinta, ina jin dumin jikinta irinna marasa lafiya. Goggo Binta tace.
"Tun farko Yaya ke kika jama yarinyar nan, wanne irin k'iyayya ne Asabe bata nuna miki ba, matar da har gobe ba k'aunarki take ba, sai Sadiya za ta k'aunata, ni fa ina ganin dole aurannan yazo k'arshe bazai yuwu mu xuba idanu muna kallon Sadiya a cikin irin wannan halin ba, gashi har rabo ya shiga tsakaninsu." Goggo Hansatu tace
"Gaskiya kam, bafa k'aramin cutarwa su kai ma Sadiya ba. Yarinya da iliminta da aikinta, a kai ta aure k'auye. wallahi ko musulunci ma bai yarda da wannan ba, domun akwai cutarwa da gurk'usarma da mutum rayuwa, ni ya bata takaddarta kawai, Yaya Binta in zata koma Saudiyya su tafi tare da ita kawai." dam gabana ya yanke ya fad'i, tsuru tsuru na yi a cikinsu. mama tace.
"Binta da Hansatu hoo, ai in muka yi haka ba mu nuna dattaku ba, kuma ba haka iyayemu su ka koyar da mu ba, ba zan tab'a sa hannu wajan mutuwar auran Sadiya ba, sai dai ma in bata ha'kuri, domun duk wani aure in za ki kalla hak'uri ke rik'e da shi, bawai soyayya kad'ai ba. Ga rabo a jikinta, bazan so ace Sadiya ta haihu kuma bata tare da uban d'an ko 'yar da zata haifa ba. wuya fa bata kisa, ni d'innan babu da irin abunda Asabe bata jefe ni da shi ba, na kunshi takaici da bak'in cikin Asabe kashi kashi. Yanzu nan damar da bata samu ba a baya, sabida Adam bai bama kowa k'ofar da zai wulak'antani a gabanshi ba, shine take so tai mun horo akan Sadiya. ita bata girma, duhun jahilci na cin rayuwarta." Ajjiyar zuchiya na sauke. Mama ta sauka daga kan gadon da take, ta rik'o hannuna ta zaunar dani akan gadon, sannan ta fita.
Goggo Hansatu ta dube ni tace.
"An yi auran shi Aliyun da ita khadijar da Asabe ta fi so? kai na d'aga mata kawai, dan wani zazzab'ine ke hawa kaina, na kasa ko da magana.
mama ce ta shigo da ruwa a boket, ta shigar mun da shi toilet.
"ki watsa ruwa, sai ki zo ki sha tea, kamar cikin na baki wahala ko? naga kin rame sosai. A hankali nace.
"Zazzab'ine ya rufe ni mama, tun a mota nake jin shi, na sha wuya a mota sosai." Nan su ka shiga yi mun sannu tare da lallab'ani. Ai wankan da na yi kamar zazzab'in na tsokano, na fa jikina ya shiga kerma, amai na tunkud'omun, gashi babu komai a cikina. A kaina su Goggo Hansatu su ka kwana, dan har zabura na ke yi, washe gari da sassafe sai asibiti, cikin gaggawa aka bani gado."
"Yaya Aisha, yarinyar nan bai fa kamata ace mun tursasa mata komawa dangin mahaifinta ba, ga k'aramin ciki a jikinta amma su ka barta ta fito, ai shima Aliyun ya kamata ya biyo sawunta. Goggo Binta tace.
"In baki da k'arfin fad'a da su, mu muna da shi, Sadiya kuma da ita zan koma Saudiyya kowa ma sai ya huta, ji yanda ta fad'a ta yi duhu." mama ta dubesu ta girgiza kai.
"Baku da lissafi sosai, taya zamu zama silar mutuwar auranta, saidai in shi Aliyunne ya bata takadda, toh anan fa ba wanda ya isa ya tank'warani Sadiya ta sake koma mai, amma dan komawa d'akinta zata koma. Ana Sallamarta ni da kaina zan mayar da ita. ba dole sai ta rayu a birni bane zata samu farin ciki, haka ba dole sai ta samu dukkan wani abu da take so ba. Mu bi komai a sannu, indai Asabe ce, zata tursasa sai Aliyu ya saki Sadiya, saidai in rabon da ke tsakaninsu mai yawa ne, Asabe muguwar jahilar macece, tsabaragen masifarta, kab 'yan uwan nata tsoronta su ke ji, har shi Yaya sulaiman, sai fa abinda tace mishi. Ziyara kawai Asabe zata kawo mana, amma sai ta ne mi ta fini iko da komai. Wallahi ban tab'a nuna musu fishi ko da akan fuskata bane, ban tab'a nuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login