Showing 54001 words to 57000 words out of 92932 words

Chapter 19 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt

ko wanne tsuntsu kukan gidansu yake yi, Ba za ki sai ma Aisha k'uri'ar mutumci a idanunana ba." Tsaki ta yi, tare da kawar da kai, Goggo Hansatu zata yi magana, Goggo Binta ta d'aga mata hannu cikin dauriya tace.
"Bari mu shiga daga ciki, mu samu daga nan mu wuce, Asabe da alkhairi" Ba su tsaya jiran amsar Goggo ba, mu ka fita zuwa b'arayina.
Aliyu yana zaune a falo shi da Malam mustapha Kaka, suna ta hira cikin sakewa tamkar sun san juna. Da sallama muka shiga d'akin, Goggo Hansatu tace.
"Malam Kaka kuna tab'a hira da surukin naka ne?, toh bari mu zo sai mu koma." D'aki muka shige, Aliyu ya bini da kallon zan kama ki ne, murmushi kawai na yi mishi.
"Sadiya ki yi hak'uri da duk abunda Asabe zata yi miki, ki mayar da hankali wajan kula da kan ki da mijinki, kinga bake kad'ai bace, kar ki sama kan ki damuwa, na ga sonki a idanun Aliyu, kuma yaron yana da hankali kamar ba Asabe bace uwarki, nan da wata bakwai zan dawo in zauna dake har sai kin haihu kuma, sai in koma." Goggo Hansatu ke magana, Goggo Binta tace.
"Kar ki sake yin yaji koma meye zai faru in dai ba shi Aliyun bane ya ce ki tafi, ai sai matan gidan sui miki dariya, mu za mu koma, Sadiya ki dinga cin abinci ko dan lafiyar Bab'yn na ki, kuma ki tabbatar kinje awo koda sau uku ne. mu kam zamu tafi."
Goggo ba ku ci komai ba toh."
"A'a babu komai za mu sai abinci a hanya, ki kwanta ki huta kinga kina jiri."
Na so in musu rakiya amma fur basu amince ba, sai Aliyu ne ya raka su zuwa waje, Goggo Hansatu tace.
"Aliyu sai ka kula da ita, ka dinga taimaka mata wajan kama mata aiki, dan bata da cikakkiyar lafiya, daga asibiti kai tsaye mu ka dawo da'ita, tasha wuya ita da Babyn."
Aliyu yace.
"Babu damuwa in sha Allah zan taimaka mata, bazan ma dinga barinta ta na yin aiki ba, nagode sosai, ace ma mama nagode, sai mun zo."
Sallama su ka yi,ya na Allah Allah ya koma wajan 'yar matar shi.


Sadiya
a tsaye ya same ni ina gyara gyara gado, kuguna ya rik'e da dukka hannunshi, ya manna bayana a jikinshi. idanu na lumshe kawai, dan naji kewarshi sosai, wani abu ne naji yana yi mini zullo a jikina. a kunnena ya soma mun rad'a.
"Ashe zaki iya tafiya ki barni a lokacin da nake tsananin buk'atar kulawarki a gareni, Sadiya baki san cewar zan iya sadaukar da dukkan abunda na mallaka domunki ba? Soyayyar da nake miki tafi gaban misalin da harshe zai iya furtawa. Gangar jiki ce kawai zata iya amfani wajan fallasa miki asirin zuchiyata."
Ahankali ya juyo da ni, ya manna ni a jikinshi.
"kin ji Sadiya na samu lafiya, kin ji ko?" kai na kawai na gyad'a mishi, dan bana jin harshena zai iya sarrafuwa wajan had'a kalma mai ma'anar da zai fahimta. Amma naji takaicin tafiyar da nayi na barshi. Kuma ni kaina na jigata
"A shirye nake na kai ki duniyar ma'aurata. kuma daga yau har zuwa ranar da zaki haihu na haramta miki yin ko wanne irin aiki ne, zan miki komai da kaina, ke sarauniyace ki zauna, ni bawanki ne Sadiya."
Bakinshi ya saka a cikin nawa, harshenshi nai ma rik'on alawar yara, munfi minti goma muna turama juna sak'on kewar junanmu. kwana d'aya babu Aliyu ji nake tamkar shekara ne. Ina mamakin yanda Aliyu ya cika zuchiyata, har yake shirin zuba, dan zuchiya ta cika da son nashi."
kwantar dani yayi a hankali, jikina ya bi yana ta yi mun tausa mai dad'i, wani feelings yana fisgata, idanuna a lumshe suke sosai. Hakan ya sa Aliyu shiga wani halin, gashi bai warke ba, balle in bada kai bori ya hau."
Bansan sanda bacci yai awon gaba da ni ba.


Aliyu
zuba ma Sadiya idanu yayi, yana ji tamkar yafi kowa more mata a duniyar nan, yana mata wani irin so da bazai musaltuba. yanxu ganinta har ya warware mai duk wata damuwa da ya tsinci kanshi a ciki."
Fita yayi kai tsaye zuwa kitchen, kananzir, ya duba ko akwai, ai kuwa ya 'kare.
karar da take gefe a tsakar gidan ya nufa, murhun dutse ya had'a, ya jera karar nan, ya kunna mata wuta, duk ya had'a zufa. Bayan wutar ta kama mishi da kyar, sai ya d'aura ruwan tea. Komawa yayi cikin d'aki ya fito da wankin shi da na Sadiya, ya soma yi. Ya gama shanya mata rigar baccinta kenan. Goggo na shigowa gidan.
turus ta tsaya ta zuba ma Aliyu idanu wanda ya ke ta gurzar siket d'in atampa, bai ma san Goggo ta shigo ba. Hawaye ta soma zubarwa.
"Aliyu kenan, kai ne da girki da wanki, ka ce bawa Sadiya ta mayar mun da kai? Ni ko har ina damo mata fura, ashe ni ta mayar mun da yaro bawanta." Ahankali Aliyu ya d'ago ya dubi mahaifiyarshi yace.
"ko d'aya Baaba Sadiya bata san ina yin wannan aikin ba, ni na saka kaina, Manzon Allah S A W ma yakan ta ya matanshi aikace aikacen gida Baaba." Kuka Goggo ta ci gaba dayi tace.
"Kace kai kafin tace ne, Gaskiya Aisha ta cuceni" Kofin silbar dake hannunta ta dangwarar a k'asa tace.
"In ta fito tauraruwar taka sai ka bata tasha, yana taimakama masu juna biyu." Ficewa ta yi a b'arayin, cikin b'acin ran da ya makanta ganinta, zama ta yi shiru akan gadonta mai rumfa, tunanin yanda zata cire Sadiya daga cikin rayuwar Aliyu kenan. Fatima ce ta shigo, itama duk a dame take, tunanin tsohon mijinta duk ya addabeta, tun kamun aje ko ina ta soma jin nadamar baro d'akin auranta ta dawo gida. akan Goggo ta tsaya.
"Baaba amma lafiya na ganki a cikin wannan yanayin?" Goggo ta dubi Fatima rai a jagule tace.
"Aliyu naje na tarar yana yi ma Sadiya wanki, harda girki fa, abun mamaki ita kuma tana d'aki, in nayi sake wallahi wata ran sai Aliyu ya ne mi izini a wajan Sadiya zai gaishe ni, ni burina shine ya sake ta uban kowa ya huta, abunda ke cikinta ma ni bana buk'atar sake had'a iri da su. Ni da Aisha ta fi tsana, yau d'iyarta ce ke aure a cikin gidan d'ana? Kai ina wallahi sai yarinyar nan ta bar gidannan nasan yanda zan b'ullowa lamarin" zama Fatima ta yi.
"Baaba raba auran Sadiya da Aliyu shi ya fi, domun wayau za ta yi ta mai, balle yanzu data samu ciki, zata fake da ciki tai ta gasa shi, shi kuma dake sabon shigane, haka zaita rawar kai." Tattaunawa suka jima sunayi, tare da shawarwarin ina zasu b'ullo dan ganin wannan auran ya rabu.


Sadiya
Na jima banyi bacci mai dad'i irin wannan ba, mai cike da mafarkan alkhairi. sakkowa nayi, na fito falo dan zuwa bayan gida, a tunanina Aliyu ya fita ne, ina d'aga labule, sai kawai na ganshi a gaban murhun dutse yana juya abinci, d'aga kan da zanyi, naga ya yi wanki nawa da na shi. Tausayinshi ne naji ya kama ni, lumshe idanu nayi, tare da gode ma Allah a bisa ni'imar da yayi mun, na auran miji irin Aliyu.
Bai san na fito ba har na iso bayanshi, tsugunnawa nayi, na sak'a hannuna na zagaye cikinshi, na d'aura kaina a bayan shi.
"Ina sonka Aliyu, zan rayu da kai rayuwa irin ta har abada." Aliyu baisan sanda ya saki ludayin da ya ke juya miya da shi ba, idanu ya lumshe, hannuna dake zagaye a cikinshi ya rik'o taushi da d'umin hannunshi sune suka shige ni sosai.
"wannan ta zama rana mai mahimmanci sosai wacce bazan manta da ita ba a cikin kundin rayuwata, a karon farko da kika soma furta mun kalmar so kenan, zan kasance mai rik'e miki amanar kaina, na karb'i amanar sonki, bazan tab'a kasancewa silar zuban hawayenki ba, sai dai in kasance silar saki dariya." mik'ewa yayi dani a bayan shi, nan ya shiga zagayawa dani a bayan shi.
"Da naso ki raka ni Abuja wajan abokina, wanda muka gama jami'atul madina da shi, toh sai na ji Goggo tace mun har a asibiti kika kwanta, kuma a hanyar dawowa ma kinsha wuya, gashi jikin ki da zafi sosai. Yau zan ciyar dake girki na, na soyayya, in kika ci sai in miki wanka, ko? sannan sai ki yi sallah ki koma kiyi kwanciyarki, ai kece da ni baki d'aya, sai yadda giyar k'aunarki ta jani ta kaini." Ni dai nayi lakwas, ji nake tamkar mu kwana a cikin wannan shauk'in son."
Aliyu harya juya zai kaini d'aki, sai kuma na ga ya juyo. Fatima da Goggo muka gani a tsaye a bakin k'ofar shigowa, da dukkan alamu kuma sun jima da tsaiwa. Turus Aliyu yayi a tsaye, ni ma tsabar fad'uwar gaba, da yanda jikina ya ke rawa, ga kunyar data baibayeni kasa sakkowa sam nayi a bayan Aliyu, shima ya kasa sauke ni,k'asa mu ka yi da kanmu.
Goggo kuma ta zuba mana ido tana k'are mana kallo, ita kad'ai tasan me take ji a zuchiyarta a wannan lokacin, domun yanayinta ya nuna cewar ta shiga cikin tashin hankali sosai.




mrs Bukhari ce


*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*








1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_


5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_




Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300


*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇


0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.


Domin tura shaidar biya👇


0810 433 5144


Masu tura katin MTN👇


0814 179 9224


Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇


0817 952 3215


Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f


*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨




Instagram links👇


https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=




Facbook group


https://facebook.com/groups/463653111781414/




Telegram links


https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk




*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -


*Enter your name:* (Cikakken sunanki)


*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)


*Enter your password:* ( misali 12341234)


*Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


Masu iPhone


Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
45~46








----" Kasame ni a shashe na, in ta baka umarnin amsa kiran mahaifiyarka, in kuma uwarka ka mayar da ita ma dai na gani"
Tafiya ta yi ta barmu a wajan jiki a mace, ahankali Aliyu ya sauke ni, idanunshi sun kad'a sun zama jawur ya juyo ya kalleni, karayar da ya gani a fuskata ne yasa shi ya rungumeni tsam a jikinshi, yana shafa mun baya na, cikin rad'a yace.
"Karki damu kan ki, zanje in dawo, ban amince ki yi kuka ba, ai ke matata ce kowa ya shaida, ke dai shiga d'aki. Idanu na xuba ma Aliyu wanda ya ke takawa ahankali, ban bar tsakar gidan ba har sai da na daina hangoshi. Ko da na shiga d'akin na kasa tsaye na kasa zaune, in kai mari in kai gauro, haka nai ta suntiri, kirjina na aikin dokawa, dan bansan meye zai biyo baya ba."
Goggo sai zagaye falonta take yi, tana yi tana dukan tafin hannunta da d'ayan hannun nata wanda ta dunk'ule, idanuwanta sunyi wata iriyar kad'awa. Da sallamarshi ya shiga falon, Goggo ta yi saurin matsowa kusa da shi daf. Mari ta zabga mai, ta sake zabga mai, bata tsaya nan ba, kawai ta rufeshi da duka kamar wani k'aramin yaro, shi kuwa yana durk'ushe a gabanta, kanshi a k'asa. sai da ta dake shi ya isheta sannan tace."
"Ashe mulkin mallakar dake faruwa a cikin gidan naku kenan, kai ne wanke wanke, kaine wanki, girki, wanka, bada abinci a baki, ni da nake uwarka wanne ka tab'a yi mini a cikin dukka wannan abun dana lissafo, duk d'awainiya da wahalar da na sha akan ka? Alokacin da na samu cikin ka, ban sake samun lafiya ba, saida kaxo duniya, Bantab'a yin ciki mai wahala irin naka ba, 'yan uwana sun yi tunanin mutuwa zanyi, tsabar wahala, kuma nazo na haifeka bakwaini, babu iriyar wahalar da ban sha ba Aliyu. Yau gashi kayi girman sanin mace, wai kai ke mata hidima irin wannan, ko Adamu Aisha bata bautar da shi irin haka ba. Ka saki Sadiya yanzu na fad'a maka kenan." Aliyu bai ce komai ba, amma jikinshi har rawa ya ke yi mishi.
"Ka saketa nace, wallahi yau Sadiya ba zata sake kwana da igiyar auranka a kanta ba.
Runtse idanu yayi, dan wata iriyar girgiza da k'irjinshi yayi, duniyarshi sai faman hajijiya take yi da rayuwarshi, bakin shi, har wani d'aci ya ke yi mishi, tsabar tashin hankali." Tabawa ce ta fad'o d'akin kamar an jefo ta.
"Haba Asabe ya zaki ce yaro ya sau matar shi, ga juna biyu a jikinta? ki dai ja mishi kunne akan abunda kika ga bazaki iya d'auka ba. Kai kuma Aliyu ka kula, duk abunda ta nuna bata so. Toh ka kiyaye aikata hakan dan gudun fad'awa fishin iyaye." Shi dai baice komai ba, dan zuchiyarshi ta riga da ta kad'a.
"Kiyi hak'uri Baaba hakan ba zata sake faruwa ba." Harara ta bishi da shi kawai har ya fice, dawo da dubanta tayi wajan Tabawa.
"Me yasa kika kashe maganar nan Tabawa, kinsan shaid'aniyar yarinyar nan ta samu yaro sai azabtar da shi take yi da aikace aikace? Wannan jaraba da mai ta yi kama, ni naga yaro sai rama ya ke yi. Tabawa ta dafa kafad'ar Asabe tace.
"Asabe irin makiran matannan wuyar sha'ani gare su, abunda nake so dake shine ki rabu dasu har sai ta ji buk'atuwarta ta kai matakin da ba zata iya rik'e kanta ba, dole zata ne mi saki, a lokacin zai ji ya tsaneta sosai, itama ta gane baida wani amfani. amma yanda aikin bokansu ke ci, ko kinsa an sake ta, to tsugunne bata k'areba. Yaya kin zuba mata maganin taci?" Ajjiyar zuchiya ta sauke tace.
"Na zuba mata a cikin dawo, ni da kaina ma na kai mata, ai shine naga masifa zuwan nawa."
"Ke dai kiyi fatan tasha cikin ya xube, kuma ita da sake samun rabo har duniya ta nad'e. kinga dole ya sake wani auran, tunda mai dambu ta miki tsiya, amma ai akwai 'yan mata a gidana har guda shida, kika kasa bashi guda. da nice yaushe haka zata faru.
Zama su ka yi, Goggo tace.
"Yanxu ma bata b'aci ba ai in dai zaki yadda, amma matsalar guda d'aya ce, kinga ba lafiya gare shi ba, kar aje a cuci 'yar mutane." Tabawa tace. kwantar da hankalin ki Asabe, zan ma Talatu 'yar gayu magana, in ta amince sai ayi ai, kuma zata yaga miki yarinyar yanda bakya zato, domun ko ni wallahi ta isheni, so nake ta yi aure in huta.
Goggo tace
"Zan so hakan ta faru Tabawa, ki tuntub'eta in fa ta amince, aure kuwa kamar an yishi an gama, in kuma bata amince ba, shikenan ba rabon shi bace"


Sadiya
Tunda Aliyu ya fita, nake tsaye gashi ya jima da yawa, ya sani a cikin zulumi sosai.
Shigowa yayi, da sauri na isa gareshi, da niyyar tambayarshi yanda suka yi da Goggo na bud'e baki, Amma Aliyu sai ya zura bakinshi cikin nawa, ya jani na fad'o jikinshi, lumshe idanuna nayi, sak'onnin Aliyu suna ratsa jikina, tsaiwarce ta gagare mu, da baya da baya Aliyu ke tafiya, ni kuma idanuna a rufe suke dan na kasa bud'esu. kan gado ya jefa ni, yai mun rumfa, a wannan ranar naji zafi da dad'in da bai tab'a ratso tarihin rayuwata ba, in dai haka ma'aurata suke hawa jirgin yawo duniyar soyayya, toh lallai zan kasance a cikin layin matan da suke kasancewa harijai. k'ank'ame Aliyu na yi a jikina, dukkan mu ajjiyar zuchiya muke saukewa, amma ni fa bai isheni ba, amma kunya ba zata barni in iya sanarwa ba, kallon k'urullah Aliyu ya ke yi mun, da dashasshiyar murya yace.
"Baki k'oshi ba kema?"
kasa cewa komai na yi, jawoni ya kuma yi jikinshi, nan muka kuma shiga jirgin yawo." Ni dai bansan sanda bacci yai awon gaba da ni ba. zuchiyata fal farin ciki, tuni mun manta da zancen damuwar da muke ciki, shi kanshi Aliyun yayi hakanne dan ya kawar mana da damuwa, duk da gwaji yayi, kuma masha Allah sauk'i ya samu, sai dai ya fama ciwon nashi har jini yake yi, nan bacci shima ya kwasheshi.
Ba mu muka farka ba sai yamma sakaliya,a tare muka farka, Aliyu ya sake jawoni jikinshi, a cikin shagwab'a yace.
"Ciwona ciwo yake yi, na fame shi. idanunshi nake kallo, ina yima Aliyu wani irin so nagartacce, mara misaltuwa, amma son da ya ke yi mun yafi gaban misali.
Kaga ni ko, kana son mayar mun da jinyata baya ko?" kunne ya kama cikin muryar yara yace.
"Bazan sake ba toh" Dariya muka yi dukka.
Aliyu Amma ya kamata ka soma sana'a inaga zaifi, ko kana son ka tsaya a iya noma da kiwo ne?. k'ur na zuba mishi idanuna. Fuskata yake zagayewa da d'an yatsanshi yace."
"Na yi tunanin bud'e makaranta Ne kamar yanda kika sani, amma kuma bazai yuwu yanzu ba, domun ban samu had'in kai ba. Zan soma koyarwa a Zamfara nan da shekara guda mu gani." Na sake dubanshi da kyau, yau inajin motsin son shi sosai a raina.
"Toh Allah yasa mudace, saidai bazan so ka yi nisa da ni ba." Bakina ya kamo, idanuna na lumshe, bayan ya saki bakina yace.
"Bari in yo wanka, sai in zubo miki abinci ko? Baaba ma ta kawo miki dawo, yana waje a sulba, kina sha'awa?. Kai na girgiza dan bana ko san ganin dawon ma. Ina kwance Aliyu yayi wanka, ya shigo mun da abinci, abun mamaki tuwo na gani miyar d'anyar kub'ewa. Da zumud'ina na soma cin tuwonnan, a gaskiya Aliyu ya iya girki sosai.
"Ina ka koyi girki haka mai dad'i, anya zan sake yin girki a gidannan kuwa?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login