Showing 81001 words to 84000 words out of 92932 words

Chapter 28 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt

kawo kunun kanwa da tuwo, kafin fitarmu na sa Jamila ta yi, ina zuwa ni kuma." Fice wa Innah ta yi a d'akin, ni dai a cikin duhu na ke sosai.
B'arayin Zulai Innah ta soma zuwa, ta sanar da ita, ta je ta ta ya Maman Ummi aiki. Daga nan ta wuce b'angaren Anty Jamila.
Badiyya ta na d'akin, Anty Jamila ta na kwatanta mata yanda zata shayar da Jaririn. domun har ruwan nono ya zo mata. Ana cikin haka Innah ta d'aga labule, Kawar da kai ta yi dan gudun ganin abun takaici.
"Jamila, yarinyar nan mun dawo, ki had'a wuta a d'aura kwatanniya, sannan a kai mata kunun tsamiya da tuwon, ki bad'e shi da ya jin daddawa, da man shanu.
In kuma Safwan ya shigo, ki ba shi sak'o cewar ya kawo naman gashi, da kaza da za'ayi mata farfesu, ki lillisa mun farin kwalli."
juyawa ta yi abunta, Anty Jamila ta yi tsaye jiki a mace, dama irin abunda ta gudanma Safwan kenan tun farko, ita kanta tasan hukuncin da ya yanke, yayi tsauri, ba daidai bane abunda ya aikata.
Duban Badiyya ta yi wacce ta ke zubar da hawaye, tace.
"Ki dena Kuka Badiyya da sakel bari Safwan d'in ya shigo, ki dank'a mishi d'an shi, ni dama na fad'a miki ma da baki sha wani gadali ba, domun wannan kyauta bazata kyautu ba. I na dai zuwa bari in aiwatar da abunda Innah ta sa ka ni."
MRS BUKHARI
75/76




Sadiya
Ni dai ina zaune kamar wata gunki, tea na ke kurb'a amma ruhina baya tare da gangar jikina sam. Al'amuran sai d'aure mun kai su ke yi, zarge_zarge iri_ iri ne su ke bijirowa a zuchiyata.
Anty Jamila ce ta kawo mun tuwo da kunun kanwa, Goggo Hadiza ta tusa ni gaba, kan lallai sai na ci a gabanta."
Bayan awa guda, su Maman Ummi su ka kammala gyaran d'akin da Innah ta sa musu hannu aka yi tare da ita. Dukkan su ukun su ka shigo nan in da muke.
"Sadiya ta so kinji, ki ta fi d'aki ki kwanta, kafin ruwan wankan ya tafasa. A d'akin da na sa aka gyara miki za ki zauna zuwa wasu lokacin. Ki yi hak'uri da duk abunda zan zo in sanar miki." Inna ce ke magana da ni, Anty Zulai ta ce.
"Innah ba'ayi haka ba, ni bari Safwan d'in ya zo da kaina zan sa ya karb'o jaririn a hannun Badiyya ya dank'a ma uwarshi kayanta, bai yi tunani ba ne shi yasa ya yanke wannan hukuncin."
" Zulai ba na so a sake ta yar da wannan maganar, iyalanshi ne, shima jaririn ai na shi ne. Ki je d'akin ki kawai maganar ta k'are daga nan."
Ni dai jikina har rawa ya ke yi haka na fita ina gauraye hanya, Maman ummi ce ta rik'e ni har zuwa cikin d'akin da su ka gyara yai tsab. A kan gado ta zaunar da ni. Dubanta na yi ina murmushi na ce.
Badiyya ya ba kyautar Jaririna in dai na fahimci zancan. Lallai kuwa zamana da Safwan ya k'are, tun a daren farko da na yi a gidan na fahimci dan in haihu mishi ya auro ni, tsantsar so kuma matarshi kad'ai ya ke yi ma. Kaico na. Kukan da na ke dannewa ne ya kwace mun, na jima ina kuka mai cike da tuk'uk'in bak'in cikin da duk wanda ke saurarom sautin kukan zai ga ne. Maman Ummi ta san abunda a kai mun mai girma ne irin wanda harshe baya iya bayyana zafi da radad'in shi, shi yasa sam ba ta yi yunk'urin hanani kukan ba. Har sai da na yi ma'ishina tukunna, na yi shiru a karan kan kin kaina. Sannan ta dafa ni.
"Sadiya kar ki ce za ki yi wani abu da za ki zo kina cizan yatsanki, ki bi komai sannu kan hankali ke fa ba yarinya bace, kuma kin d'and'ani zafi da gararin zawarci."
Ban d'and'ani komai ba, ilimina ya d'ebe mun kewar da ko lokacin kaina aiki baya ba ni balle har tunane tunane su addabi rayuwata. Ke ba ki ga k'ask'antar da ni da.Safwan ya yi ba? Jaririna ya na tsumman haihuwa ya raba ni da shi, sabida ya fi kyaunar ganin Badiyya ta na dariya. Maman Ummi da wanne idon ma Safwan zai dube ni yai mun bayani?"
"Ni Sadiya abunda na ke nufi shine, ki nunar mishi kuskuren shi ko dan ya gyara gaba. Sannan lallai a baki d'anki ya kasance dake, in kuwa ya ci nasarar raba ki da wannan Jaririn, kuma ya hana ki shayar da shi, toh wallahi ko me yaron zai zama a gaba, bazai dube ki ba, Badiyya zai bud'e idanu ya gani a matsayin uwarshi. Shi goyo yana da mugun tasiri, bawai dan kin yi nak'udar silar zuwan shi duniya bane kad'ai zai sa ya soki har ya dinga jin motsin sonki da shak'uwa a ranshi ba. goyo da cin kashin yaro da fitsarinshi, da shayarwa, da kula da rayuwarshi, shi ke haddasa wannan soyayyar a tsakanin D'a da uwa. Ko gidan marayu ki ka je ki ka d'akko d'a sabowar haihuwa, ki ka rene shi, ki kai wahala da shi, toh fa ko da bayan ya girma za ki nunar mishi ke fa ba ke ki ka haifeshi ba. Shi kuma a wajan shi babu wata uwa bayan ke. Har abada kuma ke ce uwarshi...
Ya isa Maman Ummi kar ki sa zuchiyata ta fashe. Saurin dakatar da'ita na yi tare da saurin mik'ewa. Ficewa na yi daga d'akin ina kukan da hawayena ya ke 'kok'arin makanta ganina.
Da Innah na ci karo, kuka na fashe mata da shi, ba wani kawaici da zan iya ci gaba da yi, domun cutata hakan zai yi. Duk wata kunya dole na shureta gefe, ina kukan fitar hayyaci, muryarta ma sai katsewa ta ke yi.
In nah, D'ana na ke so in karb'o zuchiyata ba za ta samu nutsuwa ba. A bani in shayar da Jaririna, d'uminshi kawai na ke son ji. Wallahi Innah shima ya fi buk'atata..
Kukane yaimun illar da dole na yi shiru, sai kuka da na ke ta rintimawa. Innah da Anty Jamila da za ta mun wankan jego su kai shiru, Anty Jamila ce ta ce.
"Sadiya ki yi hak'uri, dukkanmu iyayene mu san irin zafi da rad'ad'in da ki ke ji. Amma ki yi shiru, bari Safwan d'in ya dawo, ni da kaina zan karb'o miki Jaririn in kawo miki. Na rok'eki kar ki je b'arayin da Badiyya ta ke, dan kin ga Safwan shi ya ba ta Jaririn da hannun shi. zai fi kyau ace shi ya karb'o miki Jaririnki." K'uta Innah kawai ta yi ta ce.
"Shige ai miki wanka Sadiya, ki bar komai a hannuna, bazan zuba ido Safwan ya salwantar miki da hakkinki ba."
Ban d'akin na wuce ina sharar hawaye, ga nonuwana sun yi mugun nauyi, sun ciccika da mama, har zuba su ke yi. Take nonon su ka sakarmun da wani mugun zazzab'i mai zafin gaske."


Safwan
Jiki a sab'ule ya shigo gidan, matan gidan kowa ya yi jigum jigum a cikin tausayin Sadiya, tare da ganin rashin kyautawar Safwan da ita kanta Badiyya. Anty Jamila ta ce.
"Yauwa Safwan kai na ke ta zurga zurgar jira, mu je mu yi magana.
Ledar hannun shi ya mik'a ma Anty Zulai ya ce.
"Anty Zulai ga naman k'auri na me jego, itama Badiyya a d'ebar mata, tunda shayarwa za ta shiga." Hannu Anty Zulai ta mik'a ya saka mata ledar. Ya bi Anty Jamila har falonta.
"Safwan ya yanke hukunci mai tsaurin gaske ita kanta Sadiya ta shiga wani mawuyacin hali na jin zafi da rad'ad'i, barin fad'ama gaskiya. Babu wata uwa da za ta yadda a kwace mata Jariri bisa wani dalili mara tushe da kan gado, ko da kuwa wannan uwar a cikin hauka tuburan take. Yanxu haka Sadiya ta na can kwance a cikin mashassara mai zafi, mamanta sun yi tauri, a ban d'aki sai da na d'an matse mata su ta d'an samu sassauci, ga kuka da ta ke ta faman yi. Innah ta yi mugun fishin da za ta iya yin mummunan furuci a kan ka. Ita kanta Badiyya ba za ta iya rik'e Jaririn a wajanta a na cikin wannan turku_ turkar ba. Abune ko da ya yuwu kamar yanda ka ke fata. Toh zukata da yawa za su kasance a jagule kuma a cikin rik'o tare da ajjiye miki a zuchiya mara warkewa sai dai ruruwa. Safwan ka mayar ma da Sadiya Jaririnta." Murmushi abun ma ya ba shi. Sororo Anty Jamila ta bishi da idanu, da ma fa kowa ya san Safwan da kafiya akan duk abunda ya sa a gaba, musamman in ya san cewar ba addininshi ya tab'a ba"
"Anty Jamila kenan ni fa mamakin wannan lsmarin na ke yi. Jaririnnan fa D'a na ne, kuma ina da damar da zan iya kyautar da shi ga duk wanda nai niyya. Kuma Sadiya ta ba ni mamaki da ta kasa yi mun biyayya bisa abinda na yanke duk girmanshi, balle ma Jaririnnan nawa ne. Badiyya kuma matatace, tsawon shekaru goma sha uku mu na tare Allah bai ba ta Haihuwa ba, dan na bata D'a jinina ban yi zaton zai zama damuwa ba.
Anty barin fayyace miki wani sirri. Likitoci sun tabbatar mun Badiyya ba za ta tab'a haihuwa ba, ita kanta ba ta san da hakan ba, shi tasa nai mata wannan kyautar, kuma ni ba na son Jaririn ma yasan ba Badiyya bace ta haifeshi ba, duniya da lahira na ba Badiyya Jaririnnan ita na ke so ta zamo uwarshi. Sadiya hak'uri za ta yi Allah zai ba ta wani, ga Haidar ma.
Ajjiyar zuchiya Anty Jamila ta sauke ta lura Safwan ba zai sauka a kan bakan shi ba, mik'ewa ma ya yi ficewar shi a d'akin. D'akin Badiyya ya shiga.
Tana zaune a takure a bakin gado, Jaririnta na shan nono. Dubanta ya yi cikin tausayawa, Jaririn ya fi dacewa da'ita sosai. Idanu Badiyya ta zuba mishi ta na shirin yin kuka. Da sauri ya k'araso gareta. Waje ya samu kusanta ya zauna."
"Badiyya ki toshe kunnuwanki da duk abunda za ki ji, idanuwanki ma ki runtse su, na tabbatar babu mai iya kwace jaririnnan a hannunki. Ni kuma kyauta na ba ki shi, na rad'a mishi suna Adam sunan mahaifin Sadiya, domun in nuna mata godiyata a bisa jariri da ta ba ni." Kuka Badiyya ta fashe da shi.
"Wallahi Safwan so da k'aunar Adam ta shige ni, wallahi bazan iya rayuwa ba tare da Adam ba, ko ni na haifeshi ban yi zaton zan so shi kamar haka ba. Ka ba Sadiya hak'uri kar ta yi mun mummunar fassara. Adam zai samu kulawa da soyayyar da ko a wajan ta ba zai sa mu ba. Zan gina shi bisa tartibiyar tarbiyyar da za ta yi alfahari da hakan bazan iya ba ta yaron ba." Hawayenta Safwan ya ke ta sharewa.
"Badiyya ba na son kukannan na ki sam ki dena. Kin ga yanda yaron da ke kan ki ku ka yi mun kyau kuwa, kamar in mayar da ku ciki." Shafa fuskar yaron su kai ta yi, shi kuwa ya sha nono ya k'oshi baccin shi ya ke yi bawan Allah."
Mik'ewa Safwan ya yi.
"Toh bari in lek'a mai jego da jiki, ba ta jin dad'i zazzabi da ciwon nono ya kamata, ki goya Adam sai ki je ki gaisheta." Murya a sark'e Badiyya ta ce.
"Nauyi da kunyar Sadiya ba zai barni in iya had'a idanu da'ita ba. Sannan na dai ga su Anty Zulai sun fita da gado da katifar ta, da kuma kayanta na sawa da sib d'in tata."
Ji ya yi kanshi ya mugun sara mishi, da hanzari ya fice a d'akin, kai tsaye zuwa d'akin Innah."
Ta na zaune a k'asa ta mimmik'e k'afafunta ta na shan fura. Ba ta ko kalle shi ba. Ko sallamarshi ba dan ta san muhimmancin sallama ba, da bazata iya amsawa ba.
Waje ya samu a nutse ya zauna."








Mrs Bukhari ce
MRS BUKHARI
77/78


"Innah ki yi hak'uri dan Allah a bisa fishi da ni da ki ke yi, ba ku gane manufata na yin wannan abun bane, wallahi na yi tunanin za ki yi farin ciki a bisa wannan abun sai na ci karo da sab'anin hakan...
"Dakata Safwan, ka ga maganar nan? Toh ba na son sa ke jinta a kunnuwana, zab'i d'aya zan baka a cikin umarnin da zan baka biyu, wallahi ka ji na rantse dole ka d'auki d'aya.
Ko ka dawo ma da Sadiya Jaririnta, ko ka sake ta domun ba sonta ka ke yi ba, bazan zura ido ka salwantar mata da hakkinta ba, amfani da ita kawai ka ke so ka yi na lura."
Tashin hankali da firgicin da ya ke ciki yafi gaban k'awatance, kai ya sake sunnewa, ya na jiyo k'wak'walwarshi na kad'a mishi k'ararrawar da ta ke shirin salwantar da nutsuwarshi, da kuzarinshi, ya na son Sadiya so irin wanda ba ya yi ma Badiyya sam, shi manufar alkhairice ta sa ya ba Badiyya jariri, bai jin zai iya kyautar zobe, kamar yanda ya ke jin in duniya zata taru a kan shi bazai iya sakin Sadiya ba. Cikin dashasshiyar murya ya ce ma Innah."
"Ki yi hak'uri dai Innah, babu kyau kyautar zobe, ba dai_dai bane in yi ma Badiyya ta lek'o ta koma ba. Kuma wallahi ina son Sadiya, ni bazan iya rabuwa da'ita ba." Ya na kaiwa nan ya fice a d'akin, kan shi sai sarawa ya ke yi, idanuwanshi sun zama jawur da su, Anty Zulai ce ta zo wucewa da kwanon gashasshen nama, wanda aka bad'eshi da farin kwalli. Duban Safwan ta yi, tare da girgiza kai, har ta gota shi sai kuma ta juyo.
"Safwan ka kuwa shiga wajan Sadiya ka ga yanayin jikin nata kuwa? Jikin sai tsanani ya ke yi fa. Mamanta ya kumbura yayi him, ruwan da ya ke fitowa ma ya sauya kala, daga fari zuwa ja_ja. " cikin rud'ewa ya juyo da mugun zafin naman da bai san ya na da shi ba.
"Ina ta ke Anty Zulai, bansan inda ta ke ba ai."
"Ka biyoni wajanta zani." Bin bayanta ya yi, har zuwa cikin d'akin."


Sadiya
Ina kwance sai cije baki na ke yi, ji na ke tamkar mutuwata ce ta riske ni, a cikin azaba na ke sosai, kirjina kamar zai tsinke dan nauyi, mamana sun yi sutu sutu, sai digar wani ruwa mai kala su ke yi. Ba ko riga a jikina, sai tsumma da na d'aura a tudun cikina da bai gama sauka ba.
Amma ganin Safwan tsaye a tsakiyar d'akin ya sa a take na had'iye duk wani rad'ad'i da na ke ji.
Kwanciya na yi tare da juya mishi baya. Har ga Allah ba na son ganin Safwan sam_sam, sanin shi ma ina nadama.
Anty Zulai ta ajjiye kwanon gashsshen naman a gefen gadona."
"Sadiya, sannu, na ga jikin sai tsananta ya ke yi, bari kirawa Yaya Jamila ta zo ta ga ni." Ficewa ta yi a d'akin, hakan ya ba ma Safwan damar zama a bakin gadon da na ke, ya d'aura hannunshi a gefen wuyana, kau ya ji zafin jikina. Wuff na mik'e zaune, ina huci kamar wacce ta ci gudu. Wani rad'ad'ine ya shige ni sosai, sakamakon na fama Mamana."
Kar ka sake k'azamin hannunka ya sa ke tab'a jikina. Ka fita a d'akinnan wallahi bana son ganinka, zan iya zaginka na rantse da Allah." Cike da mamaki ya zuba mun idanuwanshi kawai, mamakina k'arara a shinfid'e a fuskarshi."
"Sadiya ni ki ke fad'ama maganganu son ranki, akan wani dalili na ki can na sakarci?" Idanu na ware cike da tsiwar da bansan na iya ba.
Kaine sakarai amma ba dai ni ba. Kuskure na tabka ashe na zab'an tumin dare, ka bani mamaki da ka iya aure na dan kawai in haifama yara ka kwace ka dinga ba bagidajiyar matarka, ka sani sai Allah ya saka mun.
Kuka na raushe da shi, na d'aura da cewa.
Allah Sarki Aliyu, kaine ka nuna mun son da babu wanda zai iya min irinshi, kai ka soni da zuchiya guda, ka sadaukar da farin cikinka domun ka kasance da ni...
"Sadiya baki da hankali ko, a gabana ki ke kiran sunan mataccen tsohon mijinki ko?
Jikin Safwan har rawa ya ke yi, cikin tsawa ya mun wannan maganar idanunshi na kawo ruwa."
Eh na fad'a, Aliyu sabo ne fil a zuchiyata, shi ya soma sanina mace, shiyasa ya fi ko wanne namiji sanin mutuna da darajata, na yi imani da shine bazai mun haka ba....
Tas na ji saukar mari a kuncina, wanda ya makanta mun ganina na wucin gadi, na ji mugun zafin marin. Kuka na saka tare da zama a kan gado jagwab, na fama mamana, nan su ka shiga sabon zugi, amma na ji dad'i na motso ma da Safwan kishi, na tabbatar ya na cikin cunkushewar zuchiya.
Da wata murya mai rawa ya ce mun.
"Bansan baki da kunya ba sai yau ai, Jariri kuma na kyautar da shi ki yi duk abunda za ki yi. D'anane ni ke da iko akan kan shi. Ki kula da irin furucin da zai dinga fitowa a bakin ki dan bazan d'auki rashin kunya ba." Innah ce ta shigo d'akin, ina ganinta na ce."
Ni ka mara Safwan, ga mari ga tsinka jaka?" Innah tai saurin matsowa in da na ke, fuskata ta d'ago, shatin hannun Safwan ta ga ni kwance a kuncina. A zafafe ta d'ago ta zabga mishi mari, hawayene ya gangaro a idanun da ya ke kuncin da Innah ta mare shi. Wani abu ya had'iye k'ut, ya na jin zuchiyar shi na tafasa. Cikin rawar murya da jiki ya ce."
"Ta taso mu je Asibiti."
"Ba zata taso ba, ka je abunka. Ko mutuwa Sadiya za ta yi ina ruwanka? Dubi jikinta yanda yai zafi, ga mamanta na ciwo, ga gyanbon da zuchiyarta ta samu sanadin zaluncinka, amma a hakan ka d'aga hannu ka doketa, sabida zalunci da son kai na maza." Dubana ya yi idanunshi tamkar garwashi, ya kad'a kai. Wani zazzab'ine na kishi ke saukar mishi.
"Sadiya saka hijabi mu je asibiti kinji?"
Ban yi mata musu ba, dan jikina har rawa ya ke yi tsabar azabar da mamana su ke yi mun.
Hijabi na saka kawai, ta rik'e hannuna mu ka fita.
Yana biye da mu har Asibiti.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login