Showing 57001 words to 60000 words out of 92932 words

Chapter 20 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt

Dariyar jin dad'i na gani a bayyane a fuskarshi, yace.
"Sadiya raina ne kawai bazan iya zare miki ba, amma zan iya miki komai a rayuwa, zaki ji dad'i fiye da ko wacce mace." Godiya nayi mishi, dawon da Goggo ta kawo mun yake ta sha yana santi abunshi. Har akai kiran sallar magriba muna hira, da kyar na yakice Aliyu a jikina, ya fita zuwa masallaci, nima na lallab'a jikina nayo wanka, naxo na gabatar da sallar magriba, bani nabar wajan ba, sai da na gabatar da sallar isha.
kamar daga sama nake jiyo kururuwar kuka da ihu a babban tsakar gida, sai na ji gabana ya yanke mun ya fad'i, da sauri na fita, zuwa inda nake jiyo kururuwar. cincirindon mutane naban mamaki na gani a cure a waje d'aya, da halama wani abun tashin hankalin suke kallo, ni dai ina dosar su, gabana yana yawanta fad'uwa"




Mrs Bukhari
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*








1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_


5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_




Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300


*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇


0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.


Domin tura shaidar biya👇


0810 433 5144


Masu tura katin MTN👇


0814 179 9224


Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇


0817 952 3215


Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f


*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨




Instagram links👇


https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=




Facbook group


https://facebook.com/groups/463653111781414/




Telegram links


https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk




*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -


*Enter your name:* (Cikakken sunanki)


*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)


*Enter your password:* ( misali 12341234)


*Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


Masu iPhone


Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
47~48


Tutture jama'a na ke ta yi, ni dai burina in ga shin me suke gani ne.
Tashin hankalin dana gani ayau bazan tab'a mancewa da shi ba iyakar tsawon rayuwata ba. Aliyu na gani a kwance yana aman jini, Anas da kamilu suna rike da shi, Hawaye sun gama wanke mun fuskata, har bana iya ganin Aliyun ma da kyau, zubewa nayi a gabansu, na tallafi kan Aliyu ya dawo cinyata, baki naga yana motsawa amma ya kasa magana.
"Sadiya yaci wani abunne? Goggo ce ta jefo mun wannan tambayar, itama a cikin matsanancin tashin hankali mara misaltuwa take. Cikin rawar murya mai cike da gunjin kuka nace.
"Dawon da kika kawo mun kad'ai yasha, yana gama sha ya fita sallah, tarin da Aliyu ya ke yi ne, ya sa na mai do hankalina dukka a kanshi, hannuna ya rik'e tsam, ni kuma nace.
"Ku taimaka mu kai shi asibiti karya mutu, jinin yayi yawa. K'ank'ame hannuna Aliyu yayi, yana girgiza mun kai, bakinshi sai motsi yake, cikin kad'awar hanta na matso da kunnena saitin bakinshi, maganar ta fito a bakinshi kamar an fisgeta.
"Sadiya d'ana a hannunki har abada, ki.......Nan maganar tashi ta shiga karkatsewa, salati kawai Aliyu naji ya kama, Mala'ikan zare rai ya zare ran Aliyu kanshi na kan cinyata, hannunshi na cikin nawa. D'imuwa da zaucewar da na yi, bazata fad'uba, duk wani mai imani saida ya tausayamun, jikin Aliyu na fad'a sumammiya. Ban sake sanin ina kaina yake ba, sai farkawa na yi na ganni a cikin uwar d'akin Goggo, su Goggo Safiya ne a kaina, ina ganinsu na sake fashewa da kuka, domun fuskokinsu kawai ya sake tabbatarmun da Aliyu ya rasu a zahiri ba mafarki nake yi ba, babu wanda yace dani wani abun, kuka dukkanmu muke yi, duniya ta yi mun zafi sosai, sai salati nake ta jerowa ahankali, sai a sannanne wata nutsuwa da tsoron Allah ya sake shigana, kuka mai sauti na dena, sai hawaye kawai nake sharararwa, sai a lokacin na gane babu duhun dare a gari, da dukkan halama safiya ta yi dan gari ya soma wayewa. Kamilu ne ya shigo.
"Baaba Sadiyan ta farfad'o? Goggo Safiya yake tambaya, cikin sarewa tace.
"Ta farfad'o, amma ta kasa yi ma kowa magana, Asabe ta farfad'o kuwa? girgiza kai yayi halamar a'a.
"Baaba a tawo da Sadiya tai ma Aliyu adda'a, zamu kai shi makwancinshi, ku tawo da ita."
Haka su Goggo Safiya suka rirrik'eni, muka fito, gidannan damk'am da jama'a, niko gabana bana iya gani, duhu kawai nake gani, ga muryar Aliyu dake ta faman yi mun amsa kuuwa, wani matsanancin jiri ke d'ibata, zazzab'i kuwa mai azababben zafi ne ya lullub'eni sosai. cikin maza mu ka kutsa xuwa ciki inda gawar Aliyu take shinfid'e a cikin makara. durk'usawa na yi a gaban gawar Aliyu, daurewa nayi dan bana son in yi kuka a gaban gawar tashi, adda'a na dinga yi mishi, muryata na d'aukewa tsabar tashin hankali. Mutum ba a bakin komai yake ba. Yanzu yanzu Aliyu yake a raye amma gashi a kwance a mace a gabana. Goggo mariya ce ta rik'o hannuna, ta fito dani. Sai lokacin na fashe da kuka mai sauti, kamar na zautu, haka ina ji ina gani aka fita da gawar Aliyu, jiki na sake yankewa na fad'i Hangurarriya ( sumammiya)


Goggo Asabe
a firgice ta farka, 'yan uwan nata duk suna kanta, tace.
"Ya mutu ko? shikenan na cuci kaina, na mutu na lalace, kai jama'a, na kashe d'ana da kaina, rayuwarshi ta k'are, ya barmun duniyar, ya sani a masifar da bansan k'arshenta ba. Zabura ta yi zata mik'e. Goggo Safiya ta danne ta, nan suka shiga salati. A tunaninsu d'imuwace ta yi dan babu abunda suka kawo a ransu.
"Ina Aliyun yake? Kawu ne ya shigo d'akin da Goggo take, yace.
"Oh jama'a Asaben itama bata farfad'o ba tun jiya? wallahi duk mai imani in ya dubi Sadiya dolenshi ya tausaya mata sosai, sai suma take ta faman yi, ana yayyafa mata ruwa. Shigowa ciki yayi, Goggo ya gani a zaune tana kuka sosai.
"Asabe kin farka ashe? ki dena kukannan Aliyu kam Ya samu mutane, kuma ya samu yabo a cikin k'auyannan, Allah yayi shi ba mai tsawon rai bane, adda'a yake buk'ata. Ita kuma matar tashi, Allah ya sauketa lafiya, ko babu komai zamu dinga kallon jinin Aliyu. Kinga Asabe zafin rabone ya kawo Sadiya aure cikin k'auyannan, rabon mai zafi ne, Allah ya nufa ta jikinta zai samu rabo, Anas ya wuce tuni dan ya sanar ma da Aisha halin da ake ciki, itama ko zata ga 'yan uwanta ta ji sanyi. Goggo tace.
"Aliyun da gasken dai ya mutu ya barmu, ya mutu saidai matarshi ta haifa mana madadinshi, harma an kaishi makwancinshi? wayyo Allah na tuba ka yafe mun. Da kyar suka rarrashi Goggo ta koma falonta da zama, hannunta rik'e da carbi, sai ja take, k'awayenta da 'yan uwa sun cika falon suna taya ta amsar gaisuwa.


Sadiya
Na suma bansan sau nawa ba, da kyar hankali da nitsuwata suka farfad'o adda'a ce kawai a bakina, haka aka shiryani, xuwa falon Goggo, dan jama'a na tambayata, kowa a lokacin yasan akwai k'aramin ciki gare ni. Ina zaune bana ko iya amsar gaisuwar, khadija tana gefe na, ita ke iya amsa gaisuwa, ni kuwa sai hawaye ne ke zubo mun, ga zazzab'i dake mugun damuna. Wannan ranar, wani yanki ne na musamman a rayuwata, ranar da na d'and'ani 'zakin ainihin son Aliyu, ranar da na furta mai kalmar so, ranar da Aliyu yai mun girki, ya goyani a bayanshi. kuma a dai ranar ya mutu akan cinyoyina, hannayena na cikin nashi. Har duniya ta nad'e bazan manta da wannan ranar ba, rana mai d'unbun tarihi a babin rayuwata. Hawayena na share, ina tuno, murna da farin cikin da Aliyu ya shiga a lokacin dana sanar da shi juna biyu gareni. kalmar shi ta k'arshe kuwa sai kad'a mun k'ararrawa take yi.
"Sadiya d'ana a hannunki har abada ki..... daga nan maganar ta yanke, a hankali na soma magana.
Aliyu zan tsaya ma d'an ka ko 'yar ka irin tsaiwar da ka so kayi a rayuwata, zan bashi/bata ilimi, arabi da boko, dan ilimin 'ya mace mahimmanci gareshi.
wunin ranar maza da mata sai shigowa gaisuwa suke yi, ni dai tunda na zauna na kasa cewa komai, Haka ma Goggo wacce sai ana zaune jingum, sai ta soma kururuwa tana sambatu. tukwane naga anata shigo da su manya manya, murhuna aka kafa manya, kamar za'a dafa abincin gidan biki.
tuwon dawa da miyar kuka su ka yi, ina kallon mata, suna ci suna hirarsu tamkar ba gidan mutuwa ba, wanda aka yi ma mutuwa shi kad'ai abun yake shafa. zuwa yamma lis kuwa, har da su dariya ina jiyowa anayi. kusa da magriba su Goggo Hansatu, da mama, ds Goggo Binta, da Amina suka iso. Ganinsu ya kuma jefa ni cikin wani irin mawuyacin hali, mutuwar saita fama kanta. Kuka su ka ta yani mu ka dinga yi, ana bamu hak'uri, Goggo Hansatu ce ta kama hannuna tace.
"Xo mu je ciki, ki samu kisa wani abun a bakin ki, in dai kina so, abunda Aliyu ya bari, ya rayu har ya dinga yi mishi adda'a, toh dole sai kin tursasa kan ki wajan cin abinci."
Tea kakkaura aka had'amun, kai na d'aga na shanye dukka, dake babu zafi sosai, kuma bakina d'aci ya ke yi mun. A tak'aice a deren ranar a babban asibitin cikin sokoto na kwana, likitoci na ta k'ok'arinsu dan ceto rayuwata dana abunda ke cikina. Da kyar suka samo kan munfashina ya dawo, hankalin kowa a tashe yake, Goggo ita babban damuwarta kar cikin dake jikina ya zube dan a halin yanzu babu abunda take so sama da cikin jikina"
Ina kwance ina zubar da hawaye, Goggo Hansatu hannunta ri'ke da kofin tea, amma fur nak'i juyowa balle in karb'i tea d'in. kawu ne ya shigo.
"Hansatu, tunda yarinyar nan aka samo kanta taci wani abun kuwa?. Goggo tace
"Wallahi Yaya Sulaiman bata ci komai ba, tea ma na had'a mata ta samu ta d'umama cikinta, hanjinta ya samu ya warware, Sadiya kiwa Allah karki wahalar da bawan Allahn dake rayuwa a jikinki, cinki da shanki shi ke bashi kariya, wannan damuwar kad'ai ta isa ciki ya zube, ko a haifeshi lokacin haihuwar bai ba." Jin furucin Goggo ne yasa na tashi zaune, a baki ta dinga bani shayin har saida na shanye tas. Allura nose ta sake zuwa ta yi mun, sai bacci."
Goggo Hansatu tace
"Yarinyar nan, in anason gano kanta, dole sai dai in tafiya da ita zamu yi, zamanta a gidan bazai yuwu ba, hakan zai iya fama mata ciwon da muke burin lafawarshi. Mama tace.
"Ita musulmace dole ta d'auki k'addarar data tunkaro mata, amma yin takaba a d'akinta yafi ye mata, Hansatu ke zaki zauna a wajanta kawai dan ki dinga lura da ita, ni da anyi bakwai zan koma. Goggo tace.
"Batun Auranki da Kaka sai dai a d'aga kenan ko kuma za'ayin? Mama tace.
"Shi da kanshi, tun a hanya ya ce mu dakatar da maganar bikin zuwa wani lokaci"
"Gaskiya Kaka yana bala'in sonki, dubi yanda ya shiga dangin Baban Sadiya, dashi ake ta k'arbar makoki. Mama tace
"Na yi mai ta yin tafiya ma, yace sai tare dani zai tafi, ya ba da ajjiyar motar shi, a wajan makiyayan da suke kula da dabbobinsu a wajan bustop d'in.




Mrs Bukhari ce


*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*








1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_


5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_




Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300


*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇


0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.


Domin tura shaidar biya👇


0810 433 5144


Masu tura katin MTN👇


0814 179 9224


Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇


0817 952 3215


Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f


*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨




Instagram links👇


https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=




Facbook group


https://facebook.com/groups/463653111781414/




Telegram links


https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk




*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -


*Enter your name:* (Cikakken sunanki)


*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)


*Enter your password:* ( misali 12341234)


*Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


Masu iPhone


Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
49~50


kwanana shidda ina shan jinya a babban asibiti, jama'ar k'auyan Raquma kuwa sai tururuwar zuwa gaisheni suke yi, Malan Kaka kuwa Bazawarin mama ya taka rawar gani, danshi yaita hidima dani, har muka koma gida. Dawowa ta cikin gidan ya fama mun duk wani mikin cikin zuchiyata, gadon da mu kai rayuwar aure tak'aitacce da Aliyu na ke kallo, kwanciyar da mu ka yi ta k'arshe na shiga bege, 'kamshin fatar Aliyu, da yanda yake girmamani, nake ta kallo. Gashi yau ya zama sai tarihi, Aliyu ya shud'e a doron k'asa. wasu siraran hawaye ke kwaranya a kumatuna. Goggo Asabe da k'afafunta ta tako har zuwa b'arayina dan duba lafiyata da na abunda ke cikina, ta rame sosai ta fice a hayyacinta, ni dai nasan Goggo na da sa hannu wajan mutuwar Aliyu na, ko san ganinta bana yi, ta cuceni ta kassaramun rayuwata, ta yi mun yankan k'auna da masoyina. Ranar bakwai kawayena da dama sun zo dan ayi adda'ar bakwai, ciki har da Hadixa 'yar katsina kawata, da Zainab. Sun zagaye ni suna bani magana, a haka na soma samun sassauci, an yi adda'ar bakwai, tare da tattare duk wani kadara na Aliyu dan jiran me zan haifa sai ayi rabon gado. Washe gari kowa ya watse a gidan rasuwar, daga ni sai Goggo Hansatu ne kawai. Ta b'angaren Goggo a lokacinne abun duniya ya kuma isarta, da gida ya watse sai tunanin Aliyu ya soma hanata bacci, sai mafarkai akan Aliyu, kafin a rufa wata da rasuwar Aliyu Goggo Asabe ta kwanta jinya sosai, jinyar da bata ko iya gane wanda ya ke kanta, sai wasu abubbuwa take yi kamar mai shafar aljanu, sanbatu iri iri. Iya bata san da rasuwar Aliyu ba, domun bata nan sai da ta dawo labarin ya isketa, ba shiri ta tawo, tana zuwa kuma ta tarad da Goggo tana cikin halin jinya.
"Ohh duniya ni haihuwar sokotawa, Asabe kece kika zama haka a wata d'aya da rasuwar Aliyu? me yayi zafi haka kamar ba musulmaba, Ina daga gefe ina sauraronsu, cikin murya irinta halin jinya, mai cike da d'imuwa tace.
"Iya ki rok'amun Allah ya yafe mun a bisa zaluntar Aliyu dama kaina da na yi, a sanadiyya ta Aliyu ya ma bar duniyar" Kaina na sauke wani tuk'uk'in bak'in ciki na turnik'eni,tuni hawaye ya gama wanke mun fuskata, ni daman nasan akwai wani abu a cikin dawon da.Aliyu ya sha, da nasan da wani abun a ciki da ni na sha na mutu Goggo ta huta ai. Muryar Iya ce ta dawo dani daga nisan da xuchiyata ta yi.
"Asabe akwai wani abunda kika aikata kenan akan mutuwar Aliyu ko? cikin nishi Goggo tace.
"Iya na cuci kaina, Tabawa ta kashe ni, mai dambu ta cuceni. ita ta kaini wajan bokan da zai zubar mun da cikin Sadiya, na zuba a cikin dawo, ashe Aliyu ne zai sha. mai dambu kuma ta kaini wajan 'yan bori aka bani maganin da zai kassara rayuwar Sadiya. Iya Aliyu ne ya fad'a halin jinyar da bai ma warke ba ya rasu." Kuka ne ya ci 'karfinta, nima fashewa da kuka nayi, da gudu na bar d'akin ina haki.
"Lallai Asabe kin cika jahilar uwa, mara tsoron Allah, kin kasa d'aukar wannan auren a matsayin k'addara, kina wasa da auran da akwai rabo a cikin shi, Asabe har rashin imanin naki yakai ki iya aikata wad'annan abubbuwan da kika aikata? Toh Aliyu ya bar doron duniyar, sai ki zuba ruwa a k'asa kisha ya rabu da Sadiya, rabuwa irinta har abada. kuka ta fashe dashi, tace.
"Amma Allah wadaranki Asabe, Allah ya tsine masu hali irin naki, ni kinga tafiyata" Iya ta suri jakar ledar ta ta fice, batai ma kowa sallama ba a gidan." Fatima da take zaune a wajan, a gabanta aka tattauna komai tace.
"Baaba amma baki kyauta ma Aliyu ba, yaron da yake yi miki biyayya sosai, gashi kin kasheshi, nima kin zugani inai ma mijina rashin kunya, kin kashe mun aure na, kin raba ni da yarana, Aliyu kuma kin rabashi da duniya da, d'iyarshi ko 'danshi da za'a haifo a matsayin maraya." kuka ta fashe da shi, me ciwo. Goggo kuwa hawaye ya gama jik'e pillown da take kwance a kai.


Sadiya
jikin Goggo Hansatu na fad'a tare da rikice mata da kuka, ina fad'in nidai tazo mu bar gidannan. Da kyar Goggo Hansatu ta rarrasheni na dawo Hayyacina, fayyace mata duk abunda Goggo tace na yi, ta tsorata sosai, kuma ta sake ganin amfanin ilimin mace, dan wannan aikin jahilci ne.


kwanci tashi asarar kwana
yau cikina yana da wata takwas, yayin da Aliyu ke da wata bakwai a kwance, ga laulayin ciki, ga rashin miji duk sai na had'e na lalace sosai, nayi wata muguwar rama, ga b'aki da na kuma yi, babu a duniya abunda ke mun dad'i. duk kwanan duniya mutuwar Aliyu sabunta kanta take yi. Dan dare da rana a cikin rok'a mishi rahamar ubangiji nake. Goggo kuma tasha jinya mai tsayi har da kwanciya gadon asibiti, amma yanzu ta warke sumul, saidai ta dawo shiru shiru abun tausayi, tayi rama sosai sai dai ta bi jama'a da ido kawai. khadija kuma ta na gidansu har ta mance da Aliyu a rayuwarta, ta sake ta na harkokinta na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login