Showing 90001 words to 92932 words out of 92932 words
Chapter 31 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt
kawai ya ke yi bai san ko su waye ba."
"Umma Inane nan? Naga kowa ya sanni ni ban san su ba."
Hannunshi na rik'o nace.
"Gidan kakanninka ne nan, a tsakar gidannan mahaifinka yai rarrafe har da ma wasan k'asa. wannan daya wuce wan mahaifinane, kuma wan mahaifiyar Abbanka ne." Hannunsu na ja muka shiga.
wani wari da zarni ne suka doki salansar hancina, cikin daurewa na kutsa kaina cikin k'uryar 'dakin.
Goggo Asabe na gani a kwance, ga k'afarta ta kunbura ta yi him sosai, k'afar sai fitar da wani irin ruwa ta ke yi.
"Sadiya kece a tafe. Aliyu kaine?"
Jikina a mugun mace na isa gabansu ina hawaye.
Dukkansu sun yi mugun tsufan da na yi mamakin ganeni da suka yi. Muryata na rawa nace.
"Goggo Mariya, mai ya samu Goggo Asabe haka, ji k'afarta yanda ta koma?" Goggo Safiyya tace.
"Ke dai bari Sadiya Sankara ce ke damunta, anyi maganin anyi har mun gaji komai namu ya k'are tas, abinci ma da k'yar muke samu muci, duk akan ciwon Yaya, ga k'afa daga k'urji ya fito mata, shine fa wajan ya dinga rurewa. Munje asibiti suka yanko mana kud'i masu yawa har nera dubu ashirin wai zamu biya a yanke k'afar, in ba haka ba zai cinye mata duk jikinta. Toh wallahi a haka dai muka komo gida, watanmu biyu a asibiti mun kashe kud'i masu yawa. Na gargajiya dai yanxu muka mai da hankali kawai muke yi....
maganar Goggo Asabe ce ta katsemu, ta na kiran sunana da wata murya mai amo. Duban Haidar da Adam na yi nace.
"Haidar rik'e hannun k'aninka kuje wajan Abbanku a d'akin zauren da muka shigo gidan."
Kai Goggo ta girgiza halamar kar su fita, hannayenta ta ke ta mik'o mana.
Ni da Haidar mu ka kama.
"Sadiya ki yafe mun na saki takaba da rasa miji. Aliyu ka yafe mun na saka maraici. Sadiya nina kashe Aliyu, wajan boka naje dan ya bani maganin da cikin ki zai zube, ya bani ni kuma na zuba miki a dawo. Aliyu kuma yasha ya mutu. Ciwon mazantaka da Aliyu yayi duk nice sila. Ku yafe mun ko haske zai lullub'e kabarina, a baya na fad'a ma Iya a gabanki, amma ban rok'i gafararki ba Sadiya. Aisha ma ta yafe mun, ni kad'ai nasan mai nake ji. Tunda Aliyu ya mutu na rasa duk wata kwanciyar hankalin duniya, kullum a cikin mafarke mafarken na shiga wuta ko kabarina ya kama da wuta na ke yi, ga rad'ad'in ciwo wanda bazan iya kwatanta muku ba. Gadon Aliyu k'arami na had'a na handame ki rok'amun shi ya yafe mun"
Da sauri na zame hannuna na dinga kuka Haidar na lallashina. A haka Kawu Da Anas suka shigo su ka same mu, gafarata su ka dinga nema. Ni nama kasa magana fir. Sai Haidar ne ya ke ta tambayata su d'in su waye.
Ajjiyar zuchiya na sauke, na gabatar mishi da kowa, na kuma rok'eshi ya yafe musu. Nima na yafe musu dukka, Haidar ya so ya kafe mun kan cewar shi bazai yafe ba,amma da nai mai nasiha take sai ya yafe musu.
Amma kawu ya kamata a kai Goggo Asibiti aci gaba da kulawa da'ita acan."
A kunyace Kawu yace.
"Sadiya na, ki bar Asabe kawai a gida ta mutu a suturce a d'akin mijinta. Iya ma Allah ya yi mata rasuwa da jimawa."
Allah sarki rayuwa. D'akin Bilkisu aka kaini, matan gidan sai nan nan su ke yi damu baki d'aya.
Bilkisu ciwo Hasiya ta yi ne?
"O'o sata aka kamata ta na yi, hatsin da ake adanawa a cikin rumbu, shine take sacewa, tana kaiwa gidansu,ana siyar mata a birni. Da dubu ta cika Dauda da kanshi ya kamata, shine fa jama'ar k'auyannan su ka tasar mata da jifa, mata da k'ananun yara, da kyar ta sha. Sanadin da ta soma cutar ajali kenan, tace ga garinku nan." Na tausaya mata sosai.
Toh ina khadija da mai dambu fa? Ajjiyar zuchiya ta sauke tace.
"Bayan tafiyarki daga Raquma khadija ta auri wani hamshak'in mai arziki a Zamfara, tana zaune dashi cikin rufin asiri, ta yi kyau ta canja, sai ya mutu. yara biyu ta haifa dashi, sun samu dukiya mai yawa mai dambu ta dinga watayawa a gari, sai wani saurayi ya fito neman auren khadija, ya kuma ci nasara ta aureshi, ke daga k'arshe dai ciwon sida ce ta kasheta ita da mijinta na uku. kuma ance a wajan mijinta me rasuwa ta kwaso, cutar da tai sanadinshi kenan"
Me dambu tana nan, amma bata da hankali sosai kwakwalwarta ta tab'u, dan wani sa'in a waje sai ta shiga tub'e sutura ga tsufa a jikinta. Ciwon tashi ya ke yi. wasu na cewa asiri taje ayi mata sai abun ya dawo kanta.
Lallai duniya zancan banza, da d'aya da d'aya kowa ya girbe duk abunda ya shuka. Shi yasa a rayuwa ka shiga Alkhairi yafi.
mrs Bukharice
MRS BUKHARI CE
85/86
Washe gari muka wayi gari da mutuwar Goggo Asabe,mutuwar data girgiza ni matuk'a. k'auyan rak'uma duk ya d'auka.
Kafin rana gidan ya cika ya batse, k'ofar gidama haka.
Khadija ma ta xo Ta'aziyya anan muka had'u, yaranta biyar, ta zama babbar mace sosai.
Ranar sadakar uku muka baro garin Raquma. Muka dawo Kano.
Da rasuwar Mama na ci karo. Kwananta biyu da rasuwa ban sani ba.
Iya tashin hankali na shigeshi, amma duk wani mai rai mamacine, haka na dangana, ban tare ba har sai da Mama ta yi arba'in sannan na tare a gidana.
Zaman lafiyan da muka bud'e da soyayyar juna ba'a magana. Mak'ota har sama gidanmu suna su ka yi da GIDAN ZAMAN LAFIYA. Yarana uku yanzu, banda Adam, Na samu Aisha, da mai sunan Innar Safwan wacce bata jima da rasuwa ba itama.
shekaru da dama sun shud'e rayuwa sai tafiya ta ke yi, Haidar ya kammala karantu shi, ya zama malamin Addini, Adam kuma Likitan k'ashi ya zama, Aisha tana gama sakandare tayi aure, tana zaune da mijinta a Abuja, y'ar auta Ummi kuma tana kan yin karatune.
Gidan yau a hargitse yake sosai, domun dumu dumu mun shiga shirye shiryen bikin Haidar ne, wanda ya rage saura sati uku cib.
A zaune nake a falo ina danna salulata. Haidar ne ya shigo falon da Sallama, yana sanye cikin malum_malum wanda su ka kasance sune kayan shi, kasancewarshi na matashin malamin da ake ji dashi.
A gabana ya tsugunnan."
"Hajiya barka da Safiya, an tashi lafiya?" Jigum na bishi da ido, tsantsar kamsnninshi da Aliyu sai yanzu ne ya sake fitowa, ina hango Aliyun a shekarun shi da bai haura na Haidar d'in ba.
Lafiya lau Haidar ya k'ok'ari? Jiya umman naka ta kawo mun akwati da ka yi mana, na ce har da mu? mu muna ta faman kici kicin mu kammala had'a maka laifen a samu akai, ashe kai a shirye kake. Toh madallah Allah yayi albarka."
"Ameen ummi, dama Adam ne ya aike ni wajan Abba da kuma na je na samu Abban sai ya fatattakoni da maganar da na kawo mishi, ni je wajan ummanshi itama saita koroni." Cikin mamaki nace.
Menene wannan sak'on da ake ta fatattakar ka da shi haka?" Kai Haidar ya sosa yace
"Dama cewa yayi in sanar ma Abba ya samu matan da ya ke so ya aura. Toh da na je ma Abba da zancan jin mata biyu a lokaci guda da Adam ke son yi shine ya koroni, itama umman nashi abunda yasa ta koroni kenan. Kuma ummi wallahi Adam ya na son 'yan matan dukka, a daure a duba." Ajjiyar zuchiya na sauke na ce.
"Kar ku ji komai, bari su fito zamu tattauna, yanxu ba sai anjima ba, yaro yazo da abu mai kyau sosai. Kila zaman mu da kyatumarshi ne ya bashi sha'awa harya kwad'aitu da mata biyu. Yanxun ina zaka je naga kaci ado. Gidan su mai sunan Mamana zaka je da safennan?"
"A'a ummi. Raquma zani, kuma zan yi sati guda, inaso in zama nine malamin da zai shiga Raquma a wannan shekarar, na tanadar musu abubbuwa da yawa da zai taimaka musu, kafin su samu d'auki daga gwamnati, kuma in sha Allah da kansu wata rana za su buk'aci a bud'e musu makarantar addini, ni kuma a shirye nake ko komawa ne inta kama sai in yi." Hawaye na sharce nace.
"Allah yai ma albarka.Ka fanshi mahaifinka domun ya rasu da tunanin k'auyan raquma."
"Ummi ki dena kuka, komai na da sanadi, in sha Allah sanadiyyar wannan labarin, al'ummar da ke rayuwa a cikin k'auyan Raquma za su zamu tallaifi daga gwamnati, harma da fararen hular. Mutane da dama za su yi mamakin jama'ar da ke rayuwa a cikin raquma. Rayuwa ce suke gudanarwa abun tausayi. Babu makaranta ko d'aya a k'auyen boko da islamiyya, ba wuta, ba Asibiti, ba injinan nik'a. Rayuwa ta wahala rayuwa irin ta mutanen da can."
Hawayen shi ya share dan tsananin tausayin al'ummar cikin Raquma, da yake tunani anya kuwa gwamnatin jihar sokoto ta san da zaman k'auyan raquma kuwa? kai da wuya.
Sallama ya yi mun ya fita. Bayan shi na bi da kallo kawai, na sauke ajjiyar zuchiya.
Ina zaune a wajan Badiyya ta shigo da sallama ta nemi waje ta zauna.
"Yau baki fita bane Hajiya Sadiya,ko ba aikin ne?"
Akwai aikin Hajiya Badi sai zuwa sha d'aya zan shiga Asibiti. Yanxu Haidar ya zo mun da wata magana."
Rai ta had'e tace.
"Wato sai da Haidar ya kuma sanya kan shi a sabgar Adam ko? yaro in banda sakarci babu abunda ya ke yi, ko dan ya ga na damu da shine oho. Wai mata biyu zai aura a lokaci guda fa."
Haba Hajiya Badi, menene abun sakarci anan wajan?" Alhaji Safwan ne ya tsoma bakinshi, fitowarshi kenan daga turakarshi. Ya sha kyau yana sanye cikin malum malum, dattijo d'an kwalisa kenan, ras yake iya jerawa da yaranshi, kuma ba wani tsufa ya yi sosai ba, sai dai yayi furfura sosai.
"Sakarci mana, an fad'a mishi rik'e mata biyu na ragon namiji ne?"
Dariya ni ya bani ma.
Kana nufin kai jarumine kenan?"
"Sosai ma, wuyar da kika bani lokacin da kika tsallake kika tafi ta wasa ce, da ace matasine ya shiga halin da na shiga a lokacin, k'ila haukacewa zai yi." Dariya mu ka sanya mu dukkanmu, waje ya samu ya zauna yace.
"Sadiya akwai wani abu da na aiwatar, ina fatan hakan bazai haifar da matsala ba, tunda dai nasan akwai fahimta a tsakaninmu. Ita Hajiya Badi na bud'ema shago, a kasuwa, shagon siyar da kayan masarufi, duba da yanda ita bata zuwa aikin komai, kuma ba ta yi wani karatuba, kullum sai dai mu fice mu barta a gida. Shine na bud'e mata shago, duk da ba ita zata dinga zama ba, yaro zan nema, amma kuma, zata dinga amfana da ribar da za'a samu, koba komai zata dinga juya taro ya koma sisi."
Murmushi na yi na dubi agogon fatan hannuna, goma da rabi na dawo da dubana ga Safwan."
Alhaji kenan, ai matsayin Hajiya Badi ya wuce yanda kai ka ke tunani, wallahi ko duk dukiyarka zaka mallaka mata bazai mun ciwo ba. Nima fa na tara kadarori, ina da gidaje biyu na zuba haya, ina da d'an shago na, ga Asibiti har yanzu ana lek'awa. Toh bak'in cikin me zan yi mata. Allah ya sanya alkhairi, Allah yasa a bud'e a sa'a." Da Ameen su ka amsa, sannan tace."
"Hajiya Sadiya, a gaskiya ke macece mai tausayi da k'arfin zuchiya, tunda har kika mallakamun d'anki meye ma ba zaki mallakamun ba, naso ace na yi ilimi mai zurfi domun shi ilimi gishirin zaman duniya ne, ko ba komai da na yi ma k'asata hidima. Amma tunda mai gida da abokiyar zama, dama yara sun yi sai dai in ce Alhamdullahi.
Safwan ma yace.
"Sadiya nagode, Allah ya yi muku albarka. Da ace haka magidanta suke samun walwala da farin ciki a tsakanin matan su, wallahi da ba gidan da zaka shiga kaga mace d'ayace ke rayuwa a ciki, da mata hurhud'u za'a dinga yi, domun a rage ma yawan matan da suke gararanba a gari, ga zawarawa da suka cika gari. Mu fa maza wallahi muna son mata a kusa da mu, fitintinu da rabe raben kawunan yara ke sanya da yawan maza su hak'ura da mace guda. Amma wallahi mata biyu, uku, hud'u sun fi dad'i. Da wannan nake ganin zan k'aro aure, sannan Adam na bashi dama yayi aurenshi, duk a had'e auran namu a d'aura rana guda."
Mrs Bukhari ce.
MRS BUKHARI CE
87/88
"A haba wasa dai ko, tsofai tsofai da mu, za ai mana kishiya?" Cewar Hajiya Badi, ni kuma nace.
Ke ma dai kya fad'a Hajiya Badi, ina dai fatan ba yarinya zaka auro mana ba? Yanda nake da k'ibarnan zaune ta zanyi."
Mik'ewa yayi yace.
"Taso mu je in sauke ki a wajan aiki, in wuce nima. Tashi na yi, mu kaima Hajiya Badi sallama muka fice."
Wai director da gaske kake yi zaka sake aure, duk mu d'in bamu isheka ba?"
"Wasa na ke yi Sadiya, ke kad'aima ai bakya isata, kina gani kullum sai na yi mik'i sambatu, kullum yarinya kike dawowa."
Haba dai, wane yarinya, nono da tuwon mazaunai duk sun yamushe, ciki duk nankarwa."
Juyowa yayi ya dubeni yace.
"Ba yarana bane su ka mayar mun dake haka ba? Ai ba'a haka na auroki ba, ras kike, ni da yarana ne muka sukurkutaki, gashi yanzu kin zama 'yar lukuta, jibi tumbinki fa yanata girma. Amma wallahi a hakan kike d'iban hankalina, sabida kece daidai dani Sadiya."
Shiru nayi ina nazari gaskiya Safwan adaline, kuma masoyine masanin darajar mace. Duk yanda tsufa da lalacewar fata da gashi ta ruskemu, amma shi ganinmu yake yi tamkar 'yan mata 'yan bana, baya nuna gyama ko jin wani iri idan zai yi mu'amar aure damu, kullum a cikin yi mana santi yake a wajan kwanciya.
Har ya kawo Asibiti bance komai ba,
"Dr mun iso asibiti, na saki cikin tunani ko? Kinga"
"Soyayyar gaskiya ita bata tsufa, sai dai ma'abotanta su tsofe, ni a zuchiyata gadagau nake jinku Sadiya. Kome zaku zama ni kune taurarina, kije aikin ceton rai, ga wata mai ciki can an kawo ta.
Haka rayuwar taci gaba da garawa damu, kwanakin mu na ta k'ara tafiya, Haidar yayi aure har da yara biyu, Badiyya Da Sadiya, Adam kuma yaran shi uku, Safwan, Aliyu, da Adam, mai sunan shi. Tsufa ya saukar mana sosai, musamman ma ni, ga ciwon baya da na k'afa, kasancewar ni mai k'ibace, kullum Hajiya Badiyya a cikin taimaka mana take yi, da Safwan ma yana kwance ciwon suger, da ciwon tsufa ya kama shi, Su Haidar su ke jinyarshi. Dangina duk sun k'are, su Goggo Hansatu, dasu kawu, Sulaiman, da su Goggo Kulu, da mijinta Kawu Shafi'i. Duk sun shud'e.
Haka yau muka wayi gari da mutuwar Safwan, mutuwar data gigita iyalan gidan.
Gidan ya cika mak'il da 'yan uwa da abokan arziki, Alhaji Safwan mutum ne na jama'a, yana d'aya daga cikin dattijan anguwa, wanda suka kafa kwamitin matasa,dan tallafama rayuwar matasa da aikin yi.
Rabuwa da masoyi babu Dadi, hak'ik'a mutuwar miji tana rad'ad'i da zafin da sai wanda akaima ne kad'ai zai fahimta.
Haka mu ka shiga takaba ni da Badiyya.
Ranar da Safwan yai arba'in aka raba gadonshi. Adam yaso ya d'auke mu, mu koma gidanshi, fur muka k'i amincewa, domun baya baya da zama da surukai yafi alkhairi. Ragamar rayuwarmu ta yi tsalle, daga kan Safwan, zuwa kan yaranmu, da sannu sannu har yayi tsalle ya koma kan jikokinmu. A lokacin bana iya gani sosai, tafiya kuwa sai da sanda bibbiyu. Rayuwa kenan, duniya budurwar wawa.
Yanzu ina diri da kyau da nake tak'amar ina dashi, duk babu ya tsud'e, fatata duk ta yamutse, gashin kaina ya kakkab'e tamkar wacce akaima aski, hatta gashin idanuna sai da tsofa ya k'one mun su tas. Rayuwa kenan.
Ina tsakar gida a zaune, ina d'an shan iska. Dattijon d'ana ya shigo da Sallama ya zube a gabana.
Duk tsufana da yank'wanewar da nayi, bai hana Haidar ya sa hannayenshi duka biyu ya tallafoni jikinshi ya mik'ar dani tsaye ba."
"Ummina daure ki tattaka, kinji fa abunda likita yace miki."
Badiyya ta fito, harta fini yamutsewa kasancewar ita fara ce sosai. tulin gashinta da take yanga dashi lokacin 'yanmatanci, ya dawo fari fat babu kyan gani.
"Yauwa Alhaji Haidar, ka tattaka da ita, saita zagaye duka gidannan, Bata ji Sadiya sam."
Turjewa nake ta yi, irinna rikitattun tsofaffi, da rarrashi Haidar ya dinga zagawa dani. Oh rayuwa, yaron dana haifa a cikina, wai yau shike ri'ke da hannuna ya na koyar dani tafiya, rayuwa rud'un banza, duniya zancan banza. Mutum ba a bakin komai yake ba.
Haka rayuwar taci gaba da tafiya, muna tsakankanin jikokin da k'adanne ma ba su yi aure sun haihu ba.
Haidar ya zama hamshak'in malami wanda ake ji dashi sosai, yanxu haka, d'anshi na jami'atul madina shima yana karatun addini."
End
Alhamdullahi
Anan na kawo k'arshen wannan littafi mai suna GISHIRIN ZAMAN DUNIYA labarin daya faru a gaske. Darasin dake cikin wannan labarin Allah ya bamu damar d'auka muyi aiki dashi. kura kuran dake ciki kuma Allah ya yafe mana baki d'aya.
Sai Allah ya sake sadamu a cikin sababbin littattafan Gawurtattu biyar 🤚🏻
Masoyana sai mun had'u a cikin littafina mai suna......
wanne irin darasi kika koya a cikin wannan littafin?
menene yafi burgeki?
Menene ya baki haushi?
A dunk'ule wanne sak'o littafinnan ya isar, a naki ganin?
duba da ya tab'o manya manyan jigo.
Amma wanne jigo ne yafi jan hankalinki, kuma ya k'ayatar dake?
Shin wanne irin maki zaki ba Badiyya da Sadiya a cikin zamantakewarsu?
Ita data mallaka mata d'a, ko ita data mallaka mata miji?
Nagode sai na ji sharhinku akan wannan littafin.
sannan duk mai son wannan littafin a buge, zan buga shi, saidai bazai shiga kasuwa ba, a hannuna kawai za'a samu, duk mai so sai ta yi magana a sa sunanta.
NASAN BA KOWA BA KOWA ZAN FARANTAMA RAI BA, AMMA INA BAMA KOWA HAK'URI, INA MAI KARA JADDADA MUKU TRUE LIFE STORY NE MASOYAN LITTAFINNAN INA GODIYA.
GISHIRIN ZAMAN DUNIYA PAID GROUP INA ALFAHARI DA KU BANASO MU RABU HAR GA ALLAH 😭😭😭😭😭