Showing 78001 words to 81000 words out of 92932 words
Chapter 27 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt
ka yi zurfin karatu suna fuskantar tsangwama da kyara. Gani su ke tamkar mace bazata tab'a fitowa da kwalin gama jami'a lafiya ba face sai ta siyar da darajarta na d'iya mace. Da yawa yawan mazan dalilinsu na gudun 'Yan bokon kenan. Iyaye ma wannan dalilin ke sa su hana Yaransu yin zurfin karatun sai ki ga an yi ma yarinya aure da k'arancin shekaru a jikinta. Kuma hakan ba k'aramin cutarwa bane. Sai kin je asibiti b'angaren 'Yan yoyyon fitsari. Nan zaki ga mata k'anana wanda wasu garin haihuwane cutar ta kama su, wasu ta hanyar saduwa ne cutar ta kama su."
Baiwar Allah'n nan tace.
"Sadiya ni kaina, ina da shekaru goma aka aurad dani, na sha bak'ar wahalar rayuwar aure, dan a lokacin ma bansan mai ke mun ciwo ba, dan ko jinin al'ada ban soma ba. Haihuwata ta fari, a lokacin shekaruna sha uku, na haifi ni'ima, sai da na yi wata shida a b'angaren 'Yan yoyyon fitsari. A lokacinma turawane likitocin da suke duba mu. Shekaruna Talatin da yin Aure. Babbar yarinya ta, ta na jami'ar Bayare dake kano. Sauran kuma duk suna gabana. Sunana Safara'u Maman Ummi."
Sunana da na ta mu ka jiyo ana kira, tare mu ka shiga d'akin awo da'ita. Tare mu ka gama komai, mu na tafe mu na hira dan Maman Ummi akwaita da hira.
"Nan shine gidana Sadiya, wata me zuwa in mun had'u na biki in ga na ku gidan.
Toh Maman Ummi nagode sosai, a gaida yara."
Sallama mu ka yi da Maman ummi, na wuce gida.
Wasa wasa cikina na ta girma, kuma yanzu garau na ke ji na sosai. Xumunci ya k'ulle sosai a tsakanina da Maman Ummi, dan da ta haihu ma har suna na je, turmin da ni da omo na kai mata.
Ciiki na ya na da wata bakwai, Mama da Goggo Hansatu su ka kawo mun ziyara. Na ji dad'in ganin Mama yanda ta sauya, ta yi kyau sosai.
Haka su ma sunyi farin cikin yanda su ka ga zaman mu da Badiyya. Yaro na aika zuwa gidan Maman Ummi, kan ta zo su gaisa da su Mama.
Ai kuwa kafin ma ta zo, ta aiko yaranta da lafiyayyen tuwon masara miyar karkashi.
Shi su Mama su ka ci, sun yi farin cikin ganin k'awata Maman ummi.
Kwana d'aya tak su ka yi, shima kamar a kan k'aya su ke su ka ta fi.
Ciki na na wata takwas, Safwan ya sa yi komai da komai, siyayyar har da ta hauka abuka da ba saban ba 😀.
Ranar wani Lahadi kuwa da daddare nak'uda ta kama ni, Safwan da Badiyya ne su ka kaini asibiti.
nak'uda na ke ta faman yi, kafin gari ya waye asibitin ya cika da jama'a. Har zuwa lokacin nak'uda na ke yi. Sai wajajen bakwai saura na haifo kyakkyawan Yaro mai tsananin kama da Safwan."
Mrs Bukhari ce
MRS BUKHARI
71-72
D'akin hutu a ka wuce da ni, tuni bacci ya d'ebe ni.
Safwan
Sai suntiri Safwan ya ke yi a k'ofar labour room. Wata nose ce ta fito hannunta rik'e da jariri wanda ya sha seti mai ruwan madara."
"Ina ta ya ku murna. Sadiya Adam ta sauka lafiya, Allah ya azurtata da haihuwar D'a namiji.
Safwan jikinshi har rawa ya ke yi ya sa hannu ya amshi jaririnan. Rungumeshi ya yi a kirjinshi, ya na jin so da k'aunar d'an na ratsa duk tsokokin jikinshi. Kunnen yaron ya kai bakin shi ya shiga jero mai adduo'i tare da yi mishi hud'uba. Badiyya ya mik'a ma jaririn. Ta yi maza ta amshe shi ta rungumeshi tsam.
Su Anty Jamila duk su ka d'auki jaririn ana ta yi mishi adda'a. Zukatan su cike da ta ya Safwan farin ciki, Kallon Anty Jamila ya yi ya ce.
"Anty wannan jaririn na mallaka ma Badiyya shi duniya da lahira, d'anta ne, kuma ko mutuwana na yi ban amince a k'wace yaronnan da ga hannunta ba."
Kuka Badiyya ta fashe da shi tare da sake k'ank'ame jaririn a jikinta."
"Hak'i'ka bani da kalmar da zan iya maka godiya bisa ga wannan kyauta da ka yi mun, ina godiya Allah ya ba ni lafiyar shayar da shi, kuma in sha Allah ba za a samu matsala ta b'angare na ba." Anty Jamila ta ce.
"Amma fa wannan d'anyen hukunci ka yanke Safwan, Sadiyan ba za ta shayar da jaririn ba ma?"
"Eh Anty kuma na wakilta ki yi ma Innah baya ni, ko da wasa wannan yaron ba na son yasan cewar ba Badiyya ba ce ta Haifeshi ba. Ita za ta shayar da shi, Anty ku ta fi gida ke da Badiyya, da jaririn, a samu gadali a bata ta sha, dan ta samu ruwan nonon da zai sha, Anty Zulai mu je ciki mu ga jikin Sadiyan."
Mamakine ya ishi kowa a wajan, Anty Jamila ta ja hannun Badiyya wacce ta k'ank'ame jariri kamar za'a kwace mata, su ka bar cikin asibitin zuwa gida.
Su Anty Zulai kuma su ka bi bayan Safwan zungui zungui. a bakin gadon da Sadiya ta ke kwance su ka tsaya. Anty Zulai cikin rashin hak'uri ta ce.
"Hukuncin da ka yanke babu abunda zai haifar sai d'a mara ido, ni na tab'a jin irin wannan lamari Safwan, Anya ka na son Sadiya kuwa, ko dai yaran da za ta haifa maka kawai ka ke dubawa, tai ta haifa ma yara ka na ba Badiyya su, ita ta na shayar da su, kai kasan me ye zafin nak'uda kuwa? Tun wuri kafin Sadiya ta farka daga wannan baccin hawalar haihuwar gara ka yi tunani akan wannan lamari, kar zaman lafiyan da ya ke gidanka ya lalace a sanadin abunda ka aikata." Safwan ya dube ta, ya ce da ita."
"Anty Zulai ni a nawa ganin, yaronnan dai nawa ne, kuma ba wani gida na kai shi ba, Sadiya na da damar ganin shi a ko da yaushe. Banyi tunanin wannan zai kawo rashin fahimta a tsakani ba. Dukkansu matana ne, yaro kuma nawa ne." Cikin juyayi Anty Zulai ta ce."
"Tsakanin d'a da uwa sai Allah, bana ko shakkar zuchiyar Sadiya ba zata iya jure wannan horon ba. Ta ya ma zaka raba ta da yaronta tun a tsunman haihuwarshi, ka dank'a shi ga kishiyarta, kyauta ta halak malak, me yasa ba za ka bar mata wannan d'in ba in yaso in ta kuma haihuwa sai ka ba ma ita Badiyyan, gaba na ke jiye maka me hakan zai haifar."
Sadiya
Ahankali na bud'e idanuna wanda su kai mun mugun nauyi, gefena na soma kallo dan sake kallon jaririna amma sai na ga wayam. Muryar Safwan na ji yo.
"Sannu Sadiya kin farka?" Murmushi na yi mishi na ce
Na farka." Ina son in tambaye shi yarona amma kunyar su Anty Zulai da su ke ta yi mun sannu ya hana ni tambaya. Maman ummi ce ta k'araso hannunta rik'e da katon flacks na ruwan zafi, da kuma k'aramar kular abinci."
"Me jego sannu, Angon k'arni ina ta ya ku farin cikin samun k'aruwa Allah ya raya shi da imani, ai ta gida na biya na ga yaron a hannun Badiyya wallahi tubarkallah masha Allah." Da mamaki a fuskata na juyo na dubi Safwan, yayin da maganar maman ummi ta shiga yi mun amsa kuuwa. Safwan kuwa dakewa na ga ya yi, ya wani kawar da kan shi daga kallona. Anty Zulai na kalla, amma ban fahimci komai a fuskarta ba, na dai ga ta girgiza kai irinna wanda takaici ya isheshi, sai na ji ta ce."
"Maman Ummi tunda ga ki kin zo, mu za mu je gida, mu rarrage aikace aikace, Sadiya sai kun dawo, Allah ya ba da lafiya."
Ameen" kawai na iya ce wa da su, kamar wawuya na bisu da ido, Safwan ne ya mara musu baya, k'asa_k'asa ya ce.
"Bari in raka su waje" Ya ma kasa had'a idanu da ni sam, sai wani sun sun da kai ya ke yi.
Kamar mahaukaciya haka na d'amk'i hannun Maman Ummi nace."
Ki ka ce kin ga jaririna a gida, a hannun Badiyya?" Da mamaki Maman Ummi ta kalle ni, d'an nazarina ta yi na wasu dak'ik'u, sannan ta ja nunfashi tace."
"Safwan bai sanar da ke komai ba ne Sadiya?" Haushi tambayar da ta je fo mun ma ta bani, ba abunda na shirya ji kenan a matsayin amsa ba. Wato nose ce ta iso hannunta rik'e da takadda, Maman ummi ta mik'ama."
"Gashi in ya shigo a bashi, an yi sallama, Tana cikin k'oshin lafiya haka ma abunda ta haifa. Malama sai ki kula da jikin ki, da ma jaririnki, Allah ya ba da lafiyar shayarwa." Ko kallo ba ta isheni ba, Maman ummi ce ta had'a mun ruwan tea.
"Ungo Sadiya ki sha, ki samu hanjinki ya warware, ki kwantar da hankalinki, ni shawarar da zan baki shine ki bi komai a sannu, kuma da za ki iya zuba ma Safwan idanu kiga iyakar in da zai k'are gudun na shi ruwan da zai fi. In kin lura kunyarki ce cike a guraben idanunshi. Kar kuma ki tambayeni komai, domun babu abunda za ki iya ji daga gare ni, kar kuma ki tambayi Safwan jaririnki. Ungo sha." Hannuna na rawa na karb'a, dan dama wata iriyar muguwar yunwar haihuwace na ji tana kad'a hanjina. Da zafi zafi na kukkurb'i tean har na shanye. Farfesun d'anyen kifi ta zuba mun, shima na cinye, amma banji na k'oshi ba sam, nan ta ke cikina ya soma murd'amun, marata na wani irin karta, ji nake tamkar mutuwa zan yi, dan abunda na ke ji a k'asan marata ya fi k'arfin abunda na ji a cikin labour room. A guje Maman Ummi ta fita, tare da noses ta dawo. Nan su ka rufu a kaina, sai zufa ke keto mun, idanuna na neman kakkafewa. Daga nan ban sake sanin in da kaina ya ke ba, Allura na ga anyi mun, nan na soma ganin kowa dishi dishi, harda Safwan da shigowarshi kenan."
mrs Bukhari ce
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
Instagram links👇
https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Facbook group
https://facebook.com/groups/463653111781414/
Telegram links
https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
MRS BUKHARI
73/74
SAFWAN
"Maman Ummi lafiya me ke damunta kuma, da ta farka sumul?"
Nose ce ta ce.
"Ba wata matsala bane babba, ku kwantar da hankalinku, wannan yana faruwa da mata a bayan haihuwarsu, amma ba wani damuwa, da zaran ta farka ma za ku iya tafiya." Ajjiyar zuchiya ya sauke.
"Mun gode sosai."
Maman Ummi ta mik'a mishi takaddar sallama.
"Ga takaddar sallama sun rubuto, amma kafin ka je biya ina so in yi wata muhimmiyar magana da kai."
Sallamar shigowar su Innah da Matar Baffa Goggo Hadiza ne ya katse Maman ummi."
Wani mugun kallo Innah ta ke watsa ma Safwan, gabaki d'aya jikinshi yai wani irin mugun sanyi. Flacks d'in da ke hannun su yai maza zai amsa, Innah tai saurin kaucewa, sai na hannun Goggo Hadiza ya amsa ya ajjiye a saman durowar gefen gadon.
Waje Maman ummi ta ba Innah, Safwan ya fita da hanzari ya kawo ma Goggo Hadiza wata kujerar.
"Barka da Goggo, Barka da zuwa Innah." Da fara'a Goggo Hadiza ta amsa mishi, ta na zaulayarshi.
"Ahh kaga Angon k'arni kana asibiti ashe har yanzu? Toh Allah ya raya wannan yaro da imani, Allah ya yi albarka. Na yi murna na yi murna." Innah ta ce ma Maman Ummi wacce su ka gama gaisawa.
"Bata farka ba har yanzu baiwar Allah?"
"Toh farka har ma ta sha tea da farfesu, sai kuma ciwon ciki ya murd'eta, shine su kai mata allura. amma har an ba da sallama ma." Innah tace.
"Sannu Maman Ummi da k'ok'ari mun gode Allah ya bar 'kauna." Innah sam ta k'i yarda su had'a idanu da Safwan, shi kuma sai sosa kai ya ke yi. Goggo Hadiza tace.
"Safwan sak'on ka ya isa, kamar yanda ka wakilta Jamila. Toh ta isar maka da sak'onka. Amma ka sani ka d'auko hanyar rushe duk wani gini na zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidanka, in ban da wauta irin ta ku ta yaran zamani, ina kai ina yin kyautar d'an mutum guda ba b'ari ba. Wannan ai ganganci ne, kuma ba son yarinyar nan Sadiya ka ke yi ba. Yarinya mai hankali da yakana irin haka iyi."
Tsugunnawa Safwan ya yi a gaban Goggo Hadiza ya ce."
"Kui mun afuwa a bisa hukuncin da na zartar a kan iyalina. Ni na yi hakanne dan a sake samun had'in kai a tsakani, Badiyya ba ta tab'a haihuwa ba, ni na yi zaton kowa zaiyi farin ciki ne da abunda na aikata, amma sai na ga sab'anin haka. Ku yi hak'uri, Allah zai ba ita Sadiyan wani." Innah da ba ta so yin magana amma jin abunda Safwan ya ce, ya hasala zuchiyarta, cikin b'acin rai ta ce."
"Ubangiji ne bai ba Badiyya haihuwa ba, shi kuma ya ba Sadiya. Kai baka isa kai ma Badiyya d'a da d'an da ta rayu wata tara a cikin mahaifiyarshi ba, kuma tana rayuwa a doron k'asa, ba nakasa ba ciwo. Amma da ya ke ku maza haka kuke baku da burin da ya wuce ku d'and'ana ma mace mad'aci a cikin rayuwarta, ga ku da son kan tsiya. Safwan za ka yi nadamar abunda ka aikata gaba. Za ka sha ruwan mamaki, ka ci nadama akan irin hukuncin da zan yanke ma. Ka sanar ma duniya ba son Sadiya ka ke yi ba." Maman ummi tace."
"Innah ni ina ganin maganar nan ko a barta ba yanzu ba, in an je gida a tattauna komai, Ni fargabata ma shine ya Sadiya zata d'auki wannan lamarin?"
" 'Yannan ai kinga daga nan ? Toh maganar nan ta k'are, bana so a sake tayo mun da ita, zai ga kafiya nima a waje na, kuma jariri ko ya maido ma Sadiya ba za ta k'arb'a ba, ya je ya kaima mowa."
Sadiya
Farkawa na yi, na samu a na wasu irin maganganu da na kasa fahimtarsu, Innah ce ta iso bakin gadon da na ke."
"Sadiya kin farka, sannu, akwai in da ya ke yi miki ciwo ne?" A jere tai mun tambayar. na ce mata
A'a ba na jin ciwon komai Innah."
"Toh tawo mu tafi gida kinji, Sadiya na."
Hannuna ta kama na sakko a kan gadon, Safwan ya na gefe ya jingina da bango, da gani kasan a cikin rud'u yake.
Innah Jaririn fa?" Kasa hak'uri na yi, shi yasa na tambayi Innah, in ji daga bakinta cewar Jaririna na hannun Badiyya."
"Mu je Sadiya, Jaririnki na gida." Safwan na kafe da idanuwana wanda su ka sauya launi, wasu zafafan hawayene su ka surnano daga guraben idanuna zuwa kan kumatukana, ni kaina bansan ko kukan me na ke yi ba, ko dan an ce Jaririna na hannun Badiyya ne oho, amma kuma bakina cike ya ke fal da tarin tambayoyin da kowa ya kasa bani dama balle in amayar da su, abunda na ke ta juyawa a xuchiyata shine, meye dalilin da za'a tafi mun da Jaririna gida, alhalin ni ina asibiti? Gashi kallo d'aya na yi mishi, idanuwana a cike suke fal da son sake yin tozali da kyakkyawan jaririna, wanda k'aunarshi na baibaye jini da tsokar jikina, a matsayina na uwa.
Safwan binmu ya yi da idanu har mu ka bar cikin d'akin.
mamaki ya ke yi da aka kasa fahimtar manufarshi na alkhairi da ya sa ya mallakawa Badiyya Jaririnnan, A d'aya b'anrayin na xuchiyarshi kuma, sai juyayin maganganun Innah ya ke yi, a k'ok'arinshi na son ganin lallai ya fahimci in da furucinta ya dosa, amma ina tunanin na shi ma k'arewa ya yi kab. Idanu ya lumshe ya ce.
"Ya Allah"
Ya rada ina tudu balle ya dafa, jiki a mace ya fice a ofishin kwakwalwarshi na hasko mai videon kallon tuhumar da Sadiya ta bi shi da shi, tare da tausayin hawayen da ya ga suna zuba a fuskarta.
Wajan biyan kud'i ya nufa, duk abunda ya dace yayi sai da ya yi, kafin ya baro asibitin."
Sadiya
Abun hawan da mu ke ciki gudu ya ke yi, amma ni ga ni nake yi tamkar ma baya wata tafiyar arziki, zuchiyata sai tunzura ta ke yi ita kad'ai, har wani amai ke taso mun.
Har k'ofar gida motar ta kaimu, mak'ota ne su ka soma fitowa, ganinmu da basket da flacks, ya tabbatar musu jikina da sauk'i. Tun daga waje aka so ma yi mun barka barka, da saukar Jaririn da kallo d'aya kawai na yi mishi.
Shiga mu ka yi cikin gidan Innah na rik'e da ni. Yayin da ni kuma sai ware ido na ke yi ko zan ga Jaririna. Amma ina babu kowa ma a tsakar gidan.
Kwanar b'arayin Innah na ga mun sha, ni dai ina biye da ita na zuba ma sarautar Allah idanu. A falonta mu ka ya da zango"
"Ungo Maman Ummi da kin sha 'yar kwana bayan d'akina, za ki ga wani d'aki ta damanki. Ki bud'e ki share, a b'allo gadon Sadiya da sib d'in kayanta a mayar mata cikin d'akin maza. Bari in Kira Zulai ta taimaka miki." Key d'in d'akin Innah ta ke mik'ama Maman Ummi, jiki a sab'ule ta amsa ta fice. Innah ta dawo da dubanta ga Goggo Hadiza.
"Hadiza had'a mata tea d'in ta sha, kafin a