Showing 6001 words to 9000 words out of 92932 words

Chapter 3 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt

sunan mahaifin malam Buhari mai Hula ya ci, shine d'an auta. Ya taso a cikin gata sosai daga wajan iyaye, har wajan yayyu.
K'auyan RAQUMA shine sunan k'auyan da aka haifi mahaifina. Kuma shine k'auyan da zan je zaman Aure. A cikin garin Zamfara k'auyan yake.a kar'kashin 'karamar hukumar MAFARA
Kauye ne wanda ya kasance mai cike da duhun jahilci. babu ko asibiti a cikin kauyan. . Sai in gagarumin ciwo ya rabke su. sai a kai mutum mafara local government akwai asibitin gwamnati a wajan, asibiti ne wanda ba su da wadatar kayan aiki, haka ma likitocin ba su da yawa. Ko kuma a shiga k'auyan Lamba a sai magani a kemis, wanda wannan kemis ya kasance shi ka'dai ne a wannan yanki, in kuma ba haka ba dai, sai an dangana da k'auyanTuraita, anan ma akwai wani 'dan asibiti gajiyayye mai su na SHA KA TAFI. Ba su da gadajen ajjiye mara lafiya.Amma abunda jama'ar 'kauyan RAQUMA su ka fi ga ne ma shine. in yara da manya ba su da lafiya. Sai a shiga jeji duk bishiyar da aka soma cin karo da ita a hanya, toh fa ta zama magani, ganyenta za'a debo ayi sirace ma mara lafiyar nan. Kuma cikin amincewar ubangiji sai ya tashi. In kuma gudawa ce ta kama babba ko yaro, kashin giwa za'a debo a jik'a sai a sha ruwan. Kuma gudawan zai tsaya. Daidai da ban 'daki na ba haya , basu cika yi a gida ba. Sai dai su je gonakan su, aciki su ke yi, maza da mata. Ban 'dakin wanka kawai su ke yi a cikin gida. Bangaren makarantar muhammadiyya kuwa, babu sam a wannan zamanin. malami sau d'aya yake zuwa a shekara ya ba da karatu, wanda ya ri'ke ya samu na Sallah, wanda ma bai ri'ke ba a hakan zai yi Sallah. Maganar makarantar boko ma ba'a magana. 'Yan boko tamkar kafurai mutanen kauyan RAQUMA, su ka d'auke su. Babu arabi babu boko haka su ke rayuwa kara zube. Ba su da hasken wutar lantarki sam. Kuma ba su da injinan ni'ka. A turmi su ke daka hatsi, su sarrafa shi ya zama abinci. Mata da kan su, su ke fita su yo karar da za su d'aura sanwa. Ba sa noman masara. Dawa, gero, su ne abunda su ke nomawa. Da yawansu makiyayane. Kuma har yanzu wannan 'kauyan a haka su ke gudanar da rayuwarsu, babu wani canji, ko tallafi da su ka samu, daga b'angaren gwamnati, ko ma daga fararen hular ne.
Kakana mai Hula ya ci alwashin ya na so d'aya daga cikin yaranshi maza su kawo canji a kauyan RAQUMA. Amma ko da kawu sulaiman ya ta so, sai ya k'i sam ya ta fi almajirci, ya fi mai da hankalinshi akan Noma da kiwo. Ga shi shine babba a gidan ragamar gidan ba'ki daya a hannunshi take, ga iyalai ya tara. Matan shi biyu, Ladi da Tabawa sai dai a wannan lokacin bai samu magajiba tukunna. Toh sai Hankalin mai Hula ya dawo kan Baba na. Ya na da shekara biyar aka tura shi almajirci. Ya shafe tsawon shekaru sama da goma sha biyu, ya na almajirci. A K'auyan makoli da ke jihar kanon dabo.Har Allah ya amshi ran Malam Mai Hula, burinshi shine Adamu ya yi karatu mai zurfi. Ragamar gidan kacokam ta sake hawa kan kawu sulaiman duk wani kadara ta na hannunshi, kama daga kan gonaki, shanu da rak'uma, har zuwa kan dukiya tsabarta. Sai malamai su ka je su ka samu a garin Zamfara, su ka raba musu gadonsu. Ananne su Goggo Asabe su ka samu gidajen da su ka dawo ciki tare da mazajensu, da yaransu. Kuma gidajen sun kasance a Jere suke reras har guda shidda da asalin family house d'in su.
Goggo Asabe yaranta uku. Anas shine Babba, sai fatima, sannan Aliyu. Goggo safiya kuma Allah bai bata haihuwa ba. Goggo Mariya kuma yaranta maza ne guda hu'du, akwai Adamu, Sulaiman, kabiru, sai Dauda. Kawu Sulaiman kuma yaranshi uku, Sajida, Rukayya, Safiya. Babana daya kammala karatun almajircin shi, Kano ya dawo sai ya shiga makarantar boko abu kamar wasa kawai sai ya soma yin yaron shago a kasuwar kurmi. Shagon Alhaji Nuru doron nera mahaifin Mama na. wasa_wasa Baba ya na ta karatun boko, kuma ya mai da hankalinshi sosai. Shine har matakin jama'a. Kakana daya lura Baba mai amana ne sai ya d'auki diyarshi Aisha wato Mama ya aura mishi. Mama na ita ce babba a gidansu. 'Kannenta uku kuma dukka mata. Goggo Hansatu itace mai bi mata, sai Goggo Sadiya wacce Allah yai ma rasuwa, sai Goggo Harira, sai kuma Goggo Binta. Wacce take garin saudiyya da aure. Gidan su Mama 'yan boko ne sosai. Ana yin karatun boko da na muhammadiyya sosai.
Mama tasha tsangwama a wajan dangin Baba sosai ba sa kaunarta sam su a tunaninsu ita ce silar da ya sa Baba ya ki komawa kauye. Kuma gani su ke yi, ta mallakeshi ne, kuma ta na mai wayo sabida 'yar boko ce ita. Baba ya yi aiki ne a kar'kashin gwamnati. Haka ma Mama, ma'aikaciyar gwamnati ce. Ni ka'dai Babana ya haifa. Mahaifiyata ta samu matsala a mahaifarta, wanda hakanne yasa ban da k'ane bare wa. Na taso cikin soyayya da gata na mahaifa. Burin Baba shine in zama ma'aikaciyar asibiti. Alhamdullah na cika ma Baba burinshi. Ko da Allah yai mai rasuwa karatuna bai tsaya ba. Da ku'din pension da garatutin Baba na samu na ha'de karatun likitanci na. Sai dai na fuskanci kalubale da dama a rayuwa. A sakamakon k'alubalantar karatun 'ya mace da Malam bahaushe ya ke yi. Hakanne ya kawo mun jinkirin aure. Sau uku ana kawo sadaki na. Daga baya a dawo a kar'ba. Sabida kawai na kasance 'yar boko kuma ma'aikaciya a 'kar'kashin asibitin gwamnati.Wannan shine ta'kaitaccen labarina.


Dawowa daga labari
Tafiya su Goggo Hansatu su ke ta faman ci. Tafiya yankin azaba. Hadiza ta ce.
"Goggo wai da ma Sadiya ba a garin Kano za ta zauna bane? Ni na ga wannan kamar hanyar Zamfara ce fa, ina karanta sunayen k'auyukan da ke kafe a allon kan titi. Sai kuma na ga mu na ta kutsawa cikin k'auye." Goggo Hansatu cikin takaici ta ce.
"Gidan Sadiya mu ke zuwa. A wannan k'ungurmin k'auyan k'addarar Aure ta kawo ta." Hawaye ta share tace.
"Ahmad iyayenshi sun 'ki amincewa ya Auri Sadiya. Hakanne ya sa dangin mahaifinta su ka ha'da ta Aure da 'dan uwanta. Da gyatumar shi yaron da gyatumin Sadiya Uwa d'aya uba d'aya. Ku yi mata fatan alkhairi kawai." Mamaki da tausayin Sadiya ya hana Hadiza da Amina samun zarafin cewa komai. Goggo sadiya, da Anas kuwa. In kun tanka ku da ba kwa wajan, toh sun tanka su ma. Sai kauyen kawai su ke bi da kallo su na zubar hawayen tausayin Sadiya. Motar su ce ta tsaya a wata madakata wanda a iya nan mota ta ke tsayawa. Sai dai kuma a shiga a kori kura, ko a hau mashin ya shiga da mutum cikin k'auyan. Daga nan madakatar tafiyar mill 7 za'ayi kafin a isa cikin k'auyan. Ga hanyar sam babu kyau. Sakkowa su ka yi daga cikin motar. Goggo Hansatu ta ce.
"Lafiya Safiya mu ka sauka anan, Kuma banga gida ba kwata kwata? Anas ne ya ce.
" Goggo anan za mu tsaya mu jira motar akori kura, sai mu shiga ta k'arasa da mu. A hakan ma sai dai in yanke za mu bi, wannan hanyar ta mu tayar Babur ce ka'dai ta ke iya bi, da jama'ar da ke tafiyar k'afa. ko kuma ku hau Babur ya isa da ku. Zan shiga motar kayan amarya, mu sai mu bi yanke. Amma k'ananun mota basa iya shiga. Hanyar a lalace ta ke." Salati Goggo Hansatu ta shiga yi ta ce.
"Amma Safiya bakwa jin tsoron Allah, da ku ka dakko yarinya a maraya aka dawo da ita k'auye irin wannan. Wannan wanne irin bala'i ne? Dole a warware wannan auran domun Sadiya sai wahala ta kasheta anan. Hmmm wallahi na ga illar auran 'dan cirani wanda ya fito daga kauye. Da ace Yaya Aisha bata auri Adamu ba, da duk haka ba za ta soma faruwa ba." Cikin fa'da da rashin ilimin arabi da boko Goggo Safiya tace.
"Hansatu kenan. Sai dai in kece ba kya tsoron Allah. Mu sunnar muhammada Rasulullahi ( S A W) mu ka ha'da. Da k'auyan nan ya na kisa, da Adamu bai rayu har Aisha ta aure shi, ta raba mu da shi ba. Ai matar mutum kabarinshi. Bari ki ji, baki isa ki fa'da mun magana in barki ba, yanzu sai mu da ku." Goggo Hansatu tace.
"Toh sai me mu daku mana, mai jaki ma ya ce ai tsere ballantana mai doki? Nanfa rikici mai girma ya 'balle a wajannan. Mata matan wajan da su ka fito cin kasuwar kauye za su koma gida. Su ne su ka raba wannan rikici, da kuma Anas. Hadiza da Amina kasa magana su ka yi, sun tsinke da lamarin. A kori kura ce ta iso, a hakanma a cike take fam babu waje, dole Babur dai su ka hau. Sun sha 'dan banzan wahala a hanya. Domun surquqin jeji su kai ta ratsawa. Ga wasu kwazazzabai a hanyar. Ga tafiya bata wasa ba, mill 7 su ka yi a kan Babur d'innan. Wujiga wujiga su ka isa. A barayin surukan gidan aka musu masauki. Wato matan yara mazan gidan. A d'akin matar Anas a ka sauke su. Dan d'akinta ya fi ko wanne d'aki a gidan kyau. Kasancewar daga kauyan Lamba a ka Auro ta, kuma mahaifinta shine mai gari.
Sai bayan sun huta sun sha ruwa, da tuwon dawa miyar bushasshen karkashi, da ake kira da bak'ar miya. Sai wata dawo ( fura) k'azamar damu babu sikari ba nono, a ka kawo musu. Sannan motar kaya kuma ta iso.
Abunka da 'kauye, kafin kace me gidan ya cika da mata da 'kananun yara. Ana tambayar Anas " Amarya aka kawo ne" sai sanar musu ya ke yi. Cewar Aliyu ne ya yi Aure. Mamaki da almara su kai ta yi. Kafin dare ya rufa kowa a cikin RAQUMA ya ji labarin Auran Aliyu da ya Auro 'yar masu ku'di. Wanda akai mata kaya na mamaki. Mata fam gidan suna mamakin ganin irin kayan 'dakin Sadiya. Matan mazan gidanne su ka ta ya su Goggo Hansatu kintsa d'akin amarya. Har bayan isha su na Abu d'aya. Bacci su ka yi a cikin 'dakin na ta suna jiran wayewar gari su 'daura daga in da su ka tsaya. Sun kuwa sha cizon sauro, har hakan ya tilasta musu hak'ura da baccin ma baki 'daya. Ga babu wutar lantarki sam a k'auyan, sai dai aci balbal da shi su ke amfani.Cikin daren su ka mi'ke, su ka ci gaba da jera komai a in da ya dace.
*WAYEWAR GARI*


*Mrs Bukhari ce*


*GISHIRIN*
*ZAMAN*
*DUNIYA*
_Daga Al'kalamin_
_Badi'at Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
GAWURTATTU BIYAR 🤚🏻




Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.


True life story


Kashi na 1
Babi na 7~8




Shiga 'd'akin da su Jamila su ke na yi. Nan fa su ka soma yi mun gu'da tamkar za su tsinke hancinsu. Sister Murja ta ce.
"Sadiya gaskiya za mu yi matu'kar kewar ki a Asibiti. Kafin ki gama cin amarci ki dawo." Dariya na k'wak'wulo cike da far'a na ce.
"Ni kuwa ba kewar da zan yi. Bazan so ma hutun nawa ya k'are in dawo ba, na fi so in ta zama wajan angona. Sister Jamila ta sa ka shewa ta ce.
" lallai Ahmad ya sa mu babban rabo da ya same ki a matsayin umman 'ya'yanshi. Zai yi alfahari da kasancewarki matar shi. Uwa uba ga ki da tsoron Allah, kin kuma kasance mai alkhairi, da son taimako. Sadiya ba ki ci ka duba kan ki ba, hankalinki ya fi ta'allak'a ne akan ganin ko wacce mace ina ma ace ta samu ilimi , da duniya za ta yi alfahari da ita. Ina ji a jikina wata rana za ki zama wata." Kokawa na ke ta yi da hawaye na kar ya zubo, dan gudun kar ya fallasani. Amma sai da ya ci amana ta ya zubo da gudu. Kukan kawai na shiga rerawa a hankali, ina tuno yaya rayuwa za ta kasance mun a kauye, kuma a k'ark'ashin namijin da na ba shi shekara biyar, wai me ya sa ba'a cika bai ma mace dama bane? Bayan addinin musulunci ya fa'di girma da daraja, da ma baiwar da Allah yai ma mace. Rarrashina su ka shiga yi, a na su tunanin kukan rabuwa da gida ne. Dan har Jamila ta na yi mun tsiya da cewa. "Sai kace wata karamar yarinya, har da kukan zuwa gidan miji?" Ni dai ban da kuzarin da zan ci gaba da biye ma cece ku ce d'in su.
Sha d'aya na yi, Goggo Mariya ta shigo har d'akin da na ke ta ja hannuna, zuwa d'akin Mama na. Mun yi kuka ni da Mama tamkar rabuwar da baza mu sa ke ha'duwa ba. Jaka ta Mama ta zuge ta sa ka mun wani abu. Da kyar ala zare ni a jikin Mama a ka yi waje da ni. Kowa ya shiga mota. Ina zaune a bayan mota kusa da maman su Amina, wacce ta kasance aminiya ga mahaifiyata. A kusa da ita Goggo Mariya ta zauna, sannan Goggo Asabe. A gaban mota kuma Kawu Sulaiman ne zaune bangaren me zaman banza. D'ayar motar kuma su kawu Bala ne da sauran matan da aka tawo da su. Mama na hango a k'ofar gida, ta na d'aga mun hannu. Nutsa kai na, na yi a tsakankanin cinya ta. Na fi awa hu'du ina kuka mai ta'ba zuchiya, abubbuwa da yawa ne a kar'kashin wannan kukan nawa. Zazzab'i da wani irin jahilin ciwon kai ne, su ka rabke ni. Awa takwas mu ka yi a titi mu na zirara gudu. Kauyan mafara mu ka tsaya a ka yi sallar azahar da la'asar. Daga nan kuma mu ka sa ke mi'kar hanya. Su Goggo Asabe sai hira da dariya su ke yi abinsu. Ni kuwa ina zaune na yi tsuru tsuru, ko k'wakk'waran motsi ba na iya yi. Maman Amina takan sa musu baki a cikin firar ta su jefi jefi. A. Haka har mu ka iso bus top. Babura aka tarar mana. Hawaye sai sabunta kansu su ke ta yi a kumatu na. Kowa ya hau Babur dinshi, ga kaya ni'ki ni'ki a hannun ko wacce daga cikin mu, kaya har a gaba aka saka masu Baburan su ka ta ya mu rik'ewa. Gudu akeyi cikin ciyayi da kaucina, Hankalina baya tare da ni sam. Gani na ke yi wani nannauyan bacci ne na ke yi, mai cike da muggan mafarkai kawai, tunda uwata ta haife ni ban ta'ba ganin k'ungurmin k'auye irin wannan ba. Domun ban ta'ba zuwa da wayo na ba. Sai lokacin ina k'arama Mama ta na zuwa da ni, a lokacin bansan komai ba."


Gidan Amarya
Goggo Hansatu na hango a tsaye a dan k'aramin tsakar gidan da ke b'arayin Sadiya hannunta ri'ke da k'ugunta ta tusa kayan kitchen d'in Sadiya a gaba, ta na ta tunani. Amina ta ce.
"Goggo me zai hana mu yi ma yayan shi Angon magana, ko da kafinta ne a nemo mana wanda zai buga mata kitchen ko da na langa langa ne, kamar yanda aka yi mata bayan gida da langa langa. In ba hakan mu ka yi ba, sai dai in da kayan za mu koma. Goggo Hansatu ta zare idanu ta ce.
" mu koma da me? 'Yannan ni kai na da taimakon Allah na iso lafiya a Babur. Ni ka'dai ma kenan balle kuma ace da kaya. Shawarar da ki ka bayar ta yi kyau sosai. Bari in je wajan matar Anas d'in, ko Allah zai sa mu dace a samu kafintan." Goggo Hansatu da kanta tayi tattaki har zuwa b'arayin Matar Anas. Bilkisu na tsugunne ta na ta kici kicin hura kara ta na son d'aura d'umame. Shi kuma Anas d'in fitowarshi daga d'aki kenan zai fita waje, Goggo Hansatu ta shigo.
"Ahh Goggo Hansatu, ai da kin aiko ni nazo, da ba ki wahal da kan ki ba." Cewar Anas. Bayan Goggo Hansatu sun gama gaisawa da Bilkisu. Sai ta ce da Anas.
"Babu komai 'dannan. Ka ga kafinta na ke so ka ne mo mana. Zai buga mana madafi ne da langa langa, kamar yanda aka buga ban d'akin na Sadiya. Na ga wajan ba madafi. Shiru Anas ya yi, sannan ya ce.
" toh bari zan fita yanzu, in je gidan mai gari, yaron wajan shi shine kafinta, sai mu zo da shi ya ga wajan." Godiya Goggo Hansatu ta yi mishi ta fita, ta koma b'arayin Sadiya. Amina ta ce.
"Andace kuwa Goggo?" Zama Goggo Hansatu ta yi tukunna, sannan ta ce.
"Za dai a dace. Ya ta fi kiran kafintan sai ya zo ma ji ta bakinshi. Ba ma wannan ba Hadiza, ina ganin dole ku zan aika zuwa cikin garin Zamfara. Yarinyar nan a siyo mata tocila irin wanda su ke yin chaji da hasken rana. Wannan duhu ya yi yawa, damuwar za tai mata yawa, a siyo mata kalanzir shima, ta 'danyi amfani da shi, kafin ta ko yi kunna kara kuma, abun tuwo na buhu ma, a k'aro mata kamar buhu hud'u. Da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login