Showing 48001 words to 51000 words out of 92932 words
Chapter 17 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt
zulumin abunda kaje kazo, har hakan sai da ya haifarmun da hawan jini. Samun lafiyata shine ta samu farin ciki a hannun mijinta. Alhamdullilah Sadiya ta yabi Aliyu, na kuma ji dad'in hakan, halamu sun nuna a maganarta sun samu fahimtar juna a tsakaninsu, ku yi hak'uri ku barta ta koma cikin gatanta, Asabe duk haukar da ke damunta bazata iya cutar da Sadiya ba, jininta ne ke yawo a jikinta." gabaki d'aya su Goggo Hansatu jikinsu ya mutu murus, ko wacce cikinsu sai da kunyar abunda suka aikata ya lullub'esu, Goggo.Hansatu tace.
"Gaskiya ne Yaya, kinyi magana mai ma'anar da mai hankali zai d'auka. In sha Allah da zaran Sadiya ta warware, ni da Ya Binta za mu maidata d'akinta, za mu ci gaba da k'arfafa guiwarta in sha Allah, burinmu shine ta zauna lafiya, kuma Sadiya ta yi k'ok'arin rungumar k'addararta, ta yi biyayyar da bazata tab'e ba." Mama tace.
"Akan Sadiya saida idona ya soye, sam bana samun bacci, tsaiwar dare, sadaka, Ina tawassali da wad'annan aiyuka wajan rok'on Allah ya sanya haske da albarka a cikin rayuwar Auranta." Goggo Binta tace.
"Yaya wallahi kin maye mana gurban mahaifanmu da su ka kwanta dama, ke uwace wacce za'a bigi k'irji a nuna ma duniya, madalla da samun Yaya kuma uwa kamarki. Sadiya kuma daga asibitinnan sai gidan mijinta, kuma zamu bada hak'uri, dan mu dawo da martabarta da kimarta, dan gudun kar ai mata kallon wacce ta gaza, yanxu na gane yin yaji gazawar hak'urine a wajan mace, musamman yajin da zaka dako badan zafin abunda miji yai maka ba, sai dan maganganun mutane." Dr ce ta fito daga d'akin da Sadiya take, tace da su mama.
"karku damu, k'aramin ciki gareta, kuma abunda ke cikin nata ya sha wahala ne da ita kanta ma, Allurai nai mata, sai ruwa dana d'aura mata. zuwa anjima zata tashi, sai kuma ku tafi gida." Mama tace.
" 'yannan mun gode, amma ba mu yanki kati ba, bamu biya komai ba." murmushi Dr d'in tayi tace.
"Sadiya ta wuci haka anan asibitin, kuma wannan asibitin yayi rashin jajirtacciyar ma'aikaciya. Irinsu Sadiya ba su da madadi sam." wucewa ta yi ta bar su Goggo na zunduma mata Albarka. mama tace.
"Hansatu, ki zo ki tafi gida, a had'o kan kayan Sadiya. Sannan ki yi mata siyayyar abunda kike ganin ya dace kuma zata buk'ata, sai ki biyo ku kama hanya, ta lallab'a." Goggo Hansatu, ba tai musu ba ta amshi key a hannun mama, da kuma dubu ashirin data mik'a mata ta wuce.
Bayan awa biyu
Sadiya
Ahankali na bud'e idanuna. Salatin Annabi S A W na soma jerowa a hankali, wata iriyar nadama da jin haushin kaina duk suka lullub'eni. Mama ita kad'aice a zaune a kan gadon da nake, da sauri ta matso.
"Kin farka Sadiya, sannu yaya k'arfin jikin?" Dubanta nayi, ta rame ta lalace nace.
"Mama ciwo kike yi ne, jiya na ji jikinki da zafi? cijewa Mama ta yi tace.
"Zazzab'ine na kwana biyu na yi Sadiya, jikin naki da dama dama ko? Lumshe idanuna nayi, uwa mai dad'i ji yanda mama take nannan dani, in banda uwa wazai ma haka? Aliyu ne ya fad'o mun, shi kam ya rasa wannan kulawar a wajan Goggo sabida ni kawai, na tabbatar kawaici yake yi mun, amma bazai tab'a jin nutsuwa ba. Mama ce ta katseni da cewa.
" Zaki iya tafiya ko, dan yanzu su Binta na dawowa za ku koma Inda kika fito, wannan kuma ya zame miki na k'arshe karki bari ko da wasa ki zubar da kimar ki a idon miji, kar ki sake ya ga gazawarki, Yaya Asabe ai uwace a wajanki, bawai Aliyu bane ya had'aku ba. Duk fad'an da zata miki a 'ya take kallonki ba suruka ba. Ki kyautata mata iya kyautatawa ki yi mata biyayya. Mijinki kuna zaman lafiya ko, in ce dai bakya raina shi? zaune na tashi a hankali na jingina, sannan nace.
"mu na zaune lafiya, wallahi yana kyautata mun sosai, kuma akwai girmamawa sosai a mu'amalar tamu, shi kam bana samun ko wacce matsala da shi"
"Ita abokiyar zaman taki fa, ba dai kwa samun matsala dai ko?"
A'a babu matsala tsakanina da ita."
"Toh masha Allah, kibi mijinki shine tsaninki, sai inda ya ajjiyeki, karki sake Sadiya."
Ahankali ya iso inda muke, sanye yake a cikin malum malum, da hula dara a kanshi, sai k'amshi yake busawa idanunshi sanye da glasses fari, amma da gani na k'arin ganine. dattijo ne,gemunshi da gashin bakinshi duk furfura, hakama 'yar sumar da ya tara a kanshi, akwai furfura amma d'aid'aiku. Mamakine ya cika ni ganinshi tsaye a bakin gadon da nake zaune, hannunshi cike da leda d'auke da lemo da ayaba." mama ta yi murmushi, irin wanda rabon da inga murmushi irin wannan a fuskar mama, tun Baba yana da rai."
"Barka da zuwa yallab'ai, ya kasan muna asibiti?" wani dattijon murmushi ya saki mata.
"Hansatu ce tai mun ido, na isa k'ofar gidan ina jiran yaron aike, sai gata ta fito, shine take sanar mun d'iyarmu babu lafiya, toh ai zama bai ganni ba, sai kawai na biyo ta." Mama tace.
"D'aliban fa, wa kabar ma su?"
"Wa yake ta wasu d'alibai 'diyata babu lafiya?" ni dai sai rarraba idanu nake yi a tsakani, cikin halin girma na gaishe da wannan dattijon da na ji ko iya had'a idanu na kasa yi da shi. Da far'arshi ya amsa mun gaisuwata, tare da tambayata kufan jiki,
Da sauk'i" Shine amsar da na mayar mishi.
"Sadiya wannan sunanshi, malam mustapha kaka, malam mustapha wannan itace d'iyata Sadiya, wacce kullum sai na tsokata maka labarinta." Murmushi yayi, yace.
"Allah yai ma rayuwa albarka, ita ta zo duba ki da jiki, sai kuma ta kwanta jinya kuma, Toh Allah ya baku lafiya, ga kayan marmari ki bata, zan jira ku a waje, in Hansatu ta dawo daga kasuwa sai in kaisu ai, ina fatan za ki rakata ko? murmushi mama tayi kawai irinna manya, ta amshi laidar hannunshi, shi kuma ya ajjiyemun, dubu uku a gefen gadona, yai maza ya fita."
sha'awa soyayyar tsofaffin ta bani, cikin zolaya nace.
"Mama wannan shine Abban nawa? dukan wasa ta kawo mun, na kauce ina dariya. wani farin ciki ne ya lullub'eni da mama ta samu masoyi, dan na jima da lura, ganina a gabanta ne ya hanata ba ko wanne namiji wata dama, dan mama ba tsohuwa bace, kuma ta na da kyan jiki, 'yar boko ce mai son kwalliya da gyaran jikinta. Farin cikina na nuna mata a fili, sannan nace.
"Mama Amma taren za mu tafi ko, tunda a mota zai kaimu? mama tace.
"Sam ni bazani ba, ban tab'a shiga motarshi ba gudun fassarar da mutane za su yi mun, k'ofar gida yake zuwa, shima a bakin zaure muke hirar a tsaye, da rana ko da safe, dan gujema sharrin shaid'an." kai na girgiza tare da jinjina ma mama. Su Goggo Binta na dawowa mu ka wuce, dama ita gida can family house ta je ta d'ebo mun tsarabata. rankaya muka yi wajan motar tashi, bayan na kewaya mun gaggaisa da 'yan tsirarin k'awayena. Sai da malam ya neman ma mama abun hawa, yaga tafiyarta. Sai muma muka kama hanya."
mrs Bukhari
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
Instagram links👇
https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Facbook group
https://facebook.com/groups/463653111781414/
Telegram links
https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
39~40
RAQUMA
JIYA
Goggo
Sun sha tafiya a kan Babur na tsawon awa biyu, ko da suka sauka ma, saida su ka kuma yin tafiyar awa guda akan dugadugansu.
Goggo ta tsorata da shiga cikin Bukkar bokan, domun irin abubbuwan da ta gani na ban tsoro a cikin wajan abun ba'a cewa komai. Nanfa Goggo ta tsure tare da raxana, take jikinta ya shiga kakkarwa takota ina. wata tsawa bokan ya saki.
"Ku dakata a wajan yau ba ma marabtar bak'in zuwa." wani garin magani ya jefo musu ya fad'i a gaban Goggo fat."
"ki zuba mata a abinci ko a abun sha, in tasha angama, angama, angama. sai ta zama mujiya a idanun mijinta, cikin zai zube, bazata sake samun haihuwa ba har duniya ta nad'e, duk duniya babu mai makarin wannan asirin sai ni nan boka jemau, mai rauhanai, ku tafi." Tabawa tace.
"Jemau duk wani al'amura nawa yana ga Allah yana gareka, na yarda da kai. Baka tab'a fad'a bai yuwu ba, daga kai ba wani aradun Allah, a lafiya sarkin bokaye."
"Tabawa na baki d'an mutum da uwarsa, Tabawa taki ta yi kyau, bak'uwa ma ta ci albarkacin ki, magani taci kyauta na bata. Ke kuma fad'i ko me kike so kin samu. Tabawa tace.
"Kasuwancin ya ja Baya, amma da in na yi wainar goronnan da k'uli da safennan ciniki har sai na ture." Dariya ya fashe mata dashi.
"Ki sabunta Tabawa, Jeki ya sabuntu."
Haka suka fito, ko wacce zuchiyarta fal da farin cikin cikar buri. sun yi dare sosai sabida nisan wajan, Amma duk da wannan daren Aliyu yana zaune a falon Goggo yana jiranta ta dawo.
da sallama ta shiga d'akin, turus ta yi a tsaye tare da cewa.
"Kai me kake yi a cikin d'akinnan, ba na sallameka ba?" Ajjiyar zuchiya ya sauke, da ganinshi kasan yana cikin damuwa.
"Baba zan tafi, dama inaso mu yi magana ne, dan girma Allah Baba ki saurare ni." Harara Goggo ta bishi da shi, kan tabarma ta zauna.
"Ina jinka, ai bazai wuci akan mayyar matarka ba ko?"
"Ba wai a kanta kad'ai maganar tawa zata tsaya ba. Baba ki yi hak'uri a bisa dukkannin wasu abubbuwa da suka faru a baya, Baba ina rik'onki da girman Allah ki sake dani kamar k'usar yak'i naki na da, wannan wanda kike jira sai ya dawo gona za ki ci abinci, wannan wanda kike tarama k'anzo mai tarin yawan da ya fi na kab almajirai 'yan uwan tafiyata, wanda kike yi mai sutura mai kyau, wanda tsabar so kika kashe duk wani dukiyar ki domun shi, Baba kin jani a jiki, nayi sabo dake, bai kamata ace akan mace, muna samun irin haka ba da ke.Baba Sadiya macece da da'ace kin zauna da ita zaki fahimceta, kiga k'ok'arin da ta dinga yi akan lalurata, kuma tanayi mun biyayya, Baba nasan kinfi kowa son farin cikina, kuma bazaki so duk wani abu da zai cutar da ni ba a rayuwa, kuma kinba rayuwata duk gudunmawar daya dace. Ki yafe ma Sadiya in ta yi miki laifi, nima ki yafe mun a bisa sab'a miki da nayi. Ki mun izini gobe in je in dawo da Sadiya, juna biyu gareta Baba Allah ya k'addari rabo a tsakaninmu shi yasa ma akai auran, ubangiji shike tsara komai." Goggo ta ji wani kuka yana tunkud'o kanshi daga huhunta, da kyar ta cije ta mayar da shi, jin yanda Aliyu ke lissafo mata abubbuwa yasa ta karaya sosai, tabbacin da d'a yake da ita cewar mahaifiyarshi bazata tab'a cutar da shi ba, kuma baza'a had'a kai a cutar da shi da ita ba. wannan yana zuchiyar ko wanne yaro, gashi ita a wannan fannin ta gaza, ita ta jefa rayuwar d'anta na cikinta a cikin garari, ta kashe mai gabanshi mus, gashi ta na son a karo na biyu ta kashe mai d'a.
mik'ewa ta yi da niyyar shigewa cikin d'aki, Aliyu ya kirata da raguwar murya yace.
"Baba" wani yar ta ji, Aliyu fa ita ta haifeshi, duk wannan abun tana yi ne, dan ceto d'anta soyayya ce ita a nata wautar yasa take yin duk wannan abubbuwan, dan ganin ba'a shanye mata d'anta ba. Sabida bata da ilimin addini, hakan yasa bata tausaya ma d'an data haifa ba, k'udirinta na b'arar da cikin jikin Sadiya ya na nan bata canja ra'ayiba. Ganin Aliyu a cikin wannan damuwar ya tabbatar mata Sadiya ba k'aramin mallake Aliyu ta yi ba, ita ta tsallake ta barshi, shi kuma yana nan ya hana kanshi sukuni.
"Ka tafi zuwa da safe ka ji wanne irin hukunci na yanke kan zuwa bikon ita mayyar data lashema zuchiya." Shigewa ciki ta yi, a sanyaye ya fita a d'akin.
kai tsaye gidanshi ya nufa, ko ina tsab. jallabiyyar jikinshi ya cire, tare da rataye ta a hannun sip, ya rage daga shi sai gajeren wando, da siglet. kwanciya yayi a daidai in da Sadiya ta saba kwanciya, wani irin kewarta ce ke muk'urk'usar zuchiyarshi, tambayar kan shi ya soma yi, Ashe dama haka so yake da dad'i, kuma ya ke da wahala, ashe haka so yake da nauyin daya zarce a d'aurashi a sikeli dan tantance ingancinshi?" Had'uwa da Sadiya ne ya gane ainihin soyayyar gaskiya ba lalube a cikin duhun da yai ma khadija ba. Bawai son khadija bane ba yayi, a'a mizanin son da yake ma khadija da Sadiya ne da banbanci, baya jin nauyin son da yake ma khadija, in aka auna zai wuci nauyin buhun omo. So yai ma khadija mai cike da yarinta, Sadiya kuma Sonta ya ke yi da girmanshi da hankalinshi, da kuma tunanin abunda zai fi dacewa da rayuwarshi. A cikin wannan dare Aliyu ya kasa bacci sam, sai tunanin Sadiya, tare da son kasancewa da ita yake yi, first night d'insu kuwa sai tariyo kanshi da kanshi ya ke yi, kai tsaye daga kwakwalwarshi.
Hakama Goggo Asabe tunani sukaita yawo a kanta, ta na mai cike da jin ciwon mutuwar auren Fatima, kuma a lokaci d'aya ta na mai takaicin samun cikin Sadiya, ga maganar takaddar saki da su mai dambu su ke so a basu, damuwowi goma da ashirin ne suka dameta, a haka har alfijir ya keto assalatu." Aliyu ne ya mik'e akan daddumar da ya gama sallar nafila, tare da addu'ar in dai alkhairine auranshi da Sadiya Allah ya dauwamar da zamansu a matsayin ma'aurata anan gidan duniyar har da k'iyamar, in kuma babu alkhairi, Allah ya kawo musu mafita. raka'atanilfajir ya gabatar, sannan ya wuce masallaci, dan shine limamin masallacin gidan mai gari wato sirikinshi mahaifin khadija. Bayan an idar da sallar ne Aliyu ya matsa kusa da sirikinshi bayan sun gaisa yace.
"inaso in yi magana da talakawanka ne ranka shi dad'e." mai gari yace.
"Babu damuwa an baka izini, in ka gama nima sai muyi tamu maganar. mik'ewa Aliyu yayi, bayan yai sallama tare da bud'e maganar da zai gabatar da adda'a sai ya d'aura da cewa.
"Dama akwai tunani da nake da shi ne akan Al'ummar wannan k'auye namu, duba da bamu da wata makaranta wacce ake d'aukar darasi, kuma gwamnati har zuwa yanzu babu wani tallafi da muka tab'a samu daga gareta, shine nake neman had'in kan ku a karan kanku, inaso in bud'e makaranta wacce zan dinga koyar da ku ku kanku iyaye da yayyu na, sannan da safe kuma sai yaranmu da k'annenmu kuma in koyar da su, zuwa yamma kuma
mata iyayenmu da k'annenmu suma sai su zo gida in koyar da su. wannan wata hanyace da ilimin sanin addini zai yawaita a wannan k'auyan domun muna da k'arancin ilimin addini, bama karatu sai zuwa gona, kiwon shanu, sai zaman hira, da yawa ba su san ma yaya za su yi wankan janaba ba, alwala wannan wani bai iyata ba, baka da wata hujja da zaka gabatar a gaban ubangijinka, wa summu da yawa sun fita yawon almajirci, kun sani na sani, ba wani shiga karatun yake yi ba, wani yaron sai ya shafe shekaru yana koyon bak'ine ma, tukunna azo kan karatun da yunwa, da rashin wanka, da rashin nutsuwa baya bamu damar gane shi. ya ku 'yan uwana muna neman had'in kan ku, domun ceto wannan k'auyan daga cikin duhun jahilcin da yai mana yawa. sunan wannan makaranta. GISHIRIN ZAMAN DUNIYA. nagode" komawa yayi ya zauna. masallaci ya d'auki shiru an rasa wanda zaice wani abun, Yaya kabiru yaron Goggo mariya ne ya mik'e tare da jan tsaki.
"ko su waye sa'anninka da kake tunanin koyarwa oho, mai gari yaro yai kuskure ayi hak'uri. ficewa yayi a masallacin, nan kowa sai yahau fita masu magangun zagi nayi masu harararshi nayi, akwai d'abi'ar mugun girman kai a wajan jama'ar k'auyan Raquma, kowa gani yake yi yafi kowa, gasu da d'an karen taurin kai, domun kusan rabin Raquma fulanine, gashi abun ya had'u da duhun jahilci. Haka dai masallacin ya rage daga Aliyu sai kamilu, sai kuma mai gari wanda ranshi yai mummunan b'aci, dan gani yake yi Aliyu yazo mishi da raini, kuma ya taka wani tsani da talakawanshi za su iya rainashi, tare da ganin gazawarshi, cewar shi bai bud'e musu makaranta ya kuma koyar da su ba, sai Aliyu, bacin shi mai garin yasan bashi da ilimin koyarwa, na sallama fisga akeyi da k'arfi.
"Sannu wanda ya iya ya je ya koyo, ina da rai ni kuma ke mulkin Raquma ka sake zuwa da wagga batu, zan yanke ma hukunci mai tsauri, kaga yaro da tsaurin ido, ko Sulaimanu bazai shiga gonata haka ba, ka fini tunanine? in ma makarantar ce sai dai ta fito a k'ark'ashin mulkina kuma in zama mai makarantar kuma malamin. in ba gwamnati ba banga wanda zai bud'e makaranta a Raquma ba saini." Aliyu yai sororo yana duban shi, yanda yake magana cike da duhun jahilci, an