Showing 30001 words to 33000 words out of 92932 words

Chapter 11 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt

safe manyan mata da yamma. maza kuma da daddare. Da fatan zaki bada gudummawarki a cikin wannan tafiyar. ta yiwu Allah ya shigo dake cikin wannan k'auyanne dan mu had'u mu fitar da jama'ar k'auyannan daga cikin duhun jahilcin da suke ciki. Rayuwa su ke yi tamkar mutanen da." Lumshe idanu yayi tare da bin k'irjina da wani mayen kallon da saida komai na jikina ya saki.Kamar zai cinye ni tsabar kallo. kasa cewa komai na yi. Dagowa nayi muka had'a idanu."
Hak'ik'a ni ba yarinya bace na fahimci a halin da Aliyu ya ke ciki. Sai dai kash bazan iyayi mishi komai akan hakan ba. Har zuwa lokacin xuchiyata ta na faman jinyar soyayyar Ahmad ne. Mik'ewa na yi.
Sai da safe. nace da shi, Da sauri na nufi k'ofar d'akina.
"Sadiya" ya kira sunana k'asa k'asa. Na kasa ko motsi a wajan na tsaya cak. kallon surata da Aliyu ya ke yi. k'ara ruramai wutar san kasancewa dani ya ke yi. Ban sani ba da zan tashi. jikina yayi rawa sosai. hakanne ya sa Aliyu ya kasa rik'e kan shi.
Ahankali ya iso gabana ya in healing k'amshin da ke fita a jikina. wanda ya sake shid'ar da shi. Ya kasa cewa komai sai ajjiyar zuchiya ya ke saukewa ahankali, jikinshi har rawa yake yi, amma ya kasa tab'ani. Da sauri na rab'a ta gefenshi na shige d'aki da sauri. K'ofar d'akin na kulle har da sakata."


Haka dai al'amura su kai ta turawa. na sake da Aliyu, mu na hira babu laifi, shak'uwa ta shiga tsakaninmu sosai. Amma Goggo ko gaisuwata bata amsawa. kuma ta dena amsar abincina. amma ban gaji ba kullum ina kai mata.
Matan gidan tsakaninsu da ni harara da habaice habaice ne kawai, ni kuwa ko a jikina, domun ba zamansu na ke yi b. A wajan Aliyu kad'ai na ke samun farin ciki. Gashi shima yanzu bashi da lokaci sosai. ginin b'arayina da b'arayin khadija su ka sa a gaba. dan an samu an shawo kan mahaifinta da kyar ya amince. yau kuma ya tafi zuwa Birni.
Ina zaune a tsakar gidana shiru bani da abokin hira, shewa da raha nake ta jiyowa a tsakar gida. Su Bilkisune suke hira a tsakaninsu, hirar da bata tab'a bani sha'awa ba kenan, rana d'aid'aikune suke wanyewa lafiya, anfi k'arkewa da fad'a da cacar baki.Ko kuma a kama wasu sunyi gulmar wasu a bayan idansu, da dai sauransu. Aliyu na tuno da yananan da mu na zaune a tsakar gidan tare muna hirarmu. Idanu na lumshe tare da tuno cewar saura sati guda Aliyu ya zama ba mallakina ni kad'ai ba. Sai na ji babu dad'i, bansan dalilin da yasa na ji hakan ba. haka nai ta tunane tunane na. Sannan na mik'e na shiga kitchen."


Aliyu
Da sallama ya shigo gidan shi da Kamilu. da akwatuna kici kici. Kai tsaye d'akin Goggo su ka wuce da akwatunan. Tana zaune ta gansu da akwatuna. Gintse fuska ta yi. Dan ganin akwatin kala biyu daban daban.
" Ya naga akwatin daban daban Kamilu?" Goggo ta watso wannan tambayar ga Kamilu. cikin sosa kai Kamilu yace.
"Dama Baba wai da na Sadiya ne. Tunda itama ba'ai mata ba. Al'adace ta tanadar da hakan....." shiru Goggo tayi ta na k'arema Aliyu kallo. Cikin b'acin rai tace.
"Da kyau Aliyu. sai ka had'a mata dukka tunda ita sarauniya ce. Sabida baka d'auken da mahimmanciba, Ai ba'a fad'amun ba. Ashe wannan kitumurmurar kuka k'ulla kai da Kamilu. Wallahi baka isa ba. dukka za'a kaima khadija."
Aliyu cikin tashin hankali da damuwa yace.
"Baba kiyi hak'uri aba Sadiya nata. ki duba ki gani komai na siyo ne akan farashi d'aya ban fifita kowa ba. Baba Sadiya bazata ji dad'i ace ban mata akwati ba. Amma na yi ma khadija."
" Lallai 'kusar yak'i. Sadiya ta mallakeka tsoronta ma kake ji.
Hawayene su ka gangaro a idanun Aliyu d'aya." Salatu Goggo ta zabga. mik'ewa tayi ta fice a d'akin"
Kamilu yace.
"Aliyu gudun matsala ka barma ita khadijan dukka. In yaso zan koma wajan Salisu mai kaya zuwa bayan biki, ita Sadiya sai a had'o mata wasu kayan ko a leda ne, domun in ka sa a akwati Baba baza ta yadda ba, sai a siyo a b'oye ko maman Aliyu uwargidana sai ta kawo mata a b'oye." cikin damuwa Aliyu yace.
"Kamilu tunda na dawo Baba ta hana mun kwanciyar hankali kawai sabida Sadiya. ita kanta a cikin tsangwamar kowa take a cikin gidannan. nine kad'ai abokin hirarta. kuma Khadija tana 'kara rura wutar tsanar Sadiya a zuchiyar Baba.
"Ka yi hak'uri Aliyu. k'ila in anyi auran da Baba ta ke so. za ku samu nutsuwa da ga kai har Sadiyan. ka rage damuwa a ranka. Duk ka rame ka yi duhu sabida Sadiya." Aliyu ya ce.
"Bakasan matsayin da Sadiya take da shi a rayuwata bane. Jinta nake tamkar jigo." Goggo ce ta shigo da masifa kamar zata ari baki tace.
"Ai sai ka mayar da ita da dawo uwarka. Aliyu ni na hak'ura da kai. na barma Sadiya kai. ka je ta maye maka gurbina. kar ka kuma zuwa dubani. nayafe bazan yi ma baki ba. Amma kuma ka dena ganin walwala da farin cikina. Tunda ka ki sakin Wannan 'yar bokon data lashe ma xuchiya." dam dam Aliyu gabanshi ya fad'i. kalaman Goggo sun d'umama kwakwalwarshi sosai. a take jikinshi ya soma rawa. Kuka kawai ya saka yace.
"Baba ki yi mun rai. Wallahi ina son Sadiya da yawa. Rabuwa da Sadiya zai iya zamemun matsala mai mugun girma."
Sallamar Iya ce ta katse musu maganar su. Ajjiyar zuchiya Aliyu ya sauke, yai saurin share hawayenshi.
"Lafiya kuwa naga angon duk ya rame haka?" d'agowa yayi ya kalli Iya.
" Lafiya k'alau Iya har kin tawo bikinne?
Zama iya ta yi a k'asa. Kawu ne ya shigo. Goggo kuma duk sai ta dibibice.
anan Aliyu ya samu ya kub'uta daga hannun Goggo. Bayan an gama gaisawa. Sulalewa su ka yi shi da Kamilu su ka fice."


Sadiya
Ina kwance akan kujera sai kuka nake yi. dan yanzu Goggo ta bar gidana. Zagina ta yi ta uwa ta uba har tana cewa bazata yafe mun ba. A wannan yanayin Aliyu ya shigo ya sameni. Yanayin da ya firgita shi. Nan ya shiga tambayata amma fur naki sanar dashi komai. Haka dole yai hak'uri ya shiga aikin lallashin. Aliyu namijine mai nuna kulawarshi ga mace. ina jin dad'in kasancewarshi a b'angarena.


An shiga hidimar biki zanga zanga babu tsayawa. Dangi sun cika gidan dam daga gari gari. Ni kuwa aiki Goggo take ta sani bako tausayina.
ranar sakun lalle na koma sabon b'arayina. wanda matan Kamilu su ka ta ya ni kwashe kaya da jerawa.
masha.Allah Aliyu yayi mana gini mai kyau da yalwa. ban d'akina mai kyau. kuma bana langa langa ba. haka ma kitchen d'ina. da b'arayina da na amarya duk an shafesu da farar k'asa."
washe gari tun safe aketa toya wainar gero ga fura anata dakawa. ga mata masu kid'an kwarya suna ta bugawa.Anata rawa irinta gad'a, kuma msnyan mata ne da 'ya'ya, harda masu jikoki. suna wata waka mai taken shaudi. ga baitin wakar kamar haka.


shaudi shaudi
shaudi shaudi
shaudi ta cikin wando, bata bar yaro ba bare babba, balle jikanta abun tausai.
shaudi shaudi
shaudi shaudi.
Da abani ruwan tulu gara abani ruwan shaudi. ruwan tulu na k'arewa ruwan shaudi bai k'arewa.
shaudi shaudi
shaudi shaudi
mai gwalagwalan zan ba
shaudi shaudi
mai d'an kulu jajaye
shaudi shaudi.
Har zuwa dai k'arshen wak'ar, mata sai ihu suke yi a tsakar gida.
Tun safe rabon da in sa.Aliyu a idanuna. Sai na ji na kasance a cikin begen san ganinshi. da wannan muryar tashi, mai cike da kulawa da girmamawa.
Misalin k'arfe biyun rana. Aka d'aura Auran Aliyu, da matarshi khadija. tare da Dauda shima da Amaryarshi.
a wannan lokaci na ji na tsinci kaina a cikin wani irin yanayin da ya, tilastamun guduwa d'aki dan in ba kuka hakkinshi. Na yi kuka mai yawan da sai da na ba kaina da kaina mamaki. wani abune yake tsokanar.xuchiyata. Kuna had'iye kukan inason fita. Sai inji na sake b'allewa da kukan. hakanne ya tilastamun samun waje in zauna.
Saida na shafe sama da awa d'aya a zaune zama mara tushe da makama. gabana sai fa'duwa ya ke ta faman yi. Addu'o'i na shiga cabko duk wacce ta zo bakina. harda ta su shiga band'aki.
sowa na ke jiyowa daga tsakar gida. ana fad'in angwaye kun sha k'amshi."


Aliyu
Tunda ya shigo ya ke baza ido ko Allah zai sa ya ga Sadiya. Amma wayam bata wajan, taraddadin had'a idanu da Sadiyar ya ke yi. Dangi sai sanya Albarka su ke yi. Ana cikin haka masu danki su ka iso (jere)
Aliyu da sauri yayi b'arayin Goggo, dan ya na da tabbacin tana jiyo gud'ar matan da su ka taryeshi sanda ya shigo. A k'ofar d'akin ya tsugunna kai a k'asa,ya gaishe da Aminan mahaifiyarshi wanda su ne a cike da falon. Goggo ta zuba mai idanu, tabbas sai yau ta ga ramar da Aliyu ya yi a cikin kwana biyunnan. Bata jin kuma za ta sarara mai, har sai ya saki Sadiya. ko tsirara za ta yi yawo, ta d'aura d'amarar kwato d'anta daga hannun muguwar 'yar bokon matarshi." Daga nan ya wuce b'arayin kawu, Kamilu da sauran abokan nashi suna biye da shi. Anan ya tarar da dangin mahaifinshi, da dangin Goggon ma duk suna wajan matan kawu. nan ya shige cikin kakannin aka soma barkwanci. Iya tace"
" Ba za ku yi kid'an garayar bane abokan ango?" Kamilu yace.
" Ke dai bari Iya. ya mayar mana da biki lami, ba'a tab'ayin bikin matashi a k'auyan Raquma ba'ai kid'an garaya ba, sai na shi." Iya ta yi gud'a tace.
"kai ilimi yayi rana Wallahi, masha Allah ko kufa. rawa ai mata aka sani da shi, wak'a kuma sai 'yan daudu."
Nan su kai ta wasan barkwancinsu. Aliyu bai samu ganawa da Sadiya ba. dan abokai sun jashi zamfara yin cefanan shiga siyan baki.


Sadiya
ni kuwa ina tsakar gida. an tara mun tulin wanke wanken bikinnan. har masu kawo Amarya anan su ka taddani. ina kallon Amarya ta rufu da mayafi kanta kirib a rufe. Wanke wanken na saki, na bisu da kallo har su ka shige d'akin Goggo. wasu hawaye da bansan dalilin zubowarsu ba su ka zubo mun. sun jima sosai a d'akin Goggo, sannan su ka sake fitowa, su ka wuce ni.Babu ma wanda ya dubi inda nike. Jikina a mace na kammala komai na share wajan, sannan na shige gidana. wanka nayo. riga da wandon bacci ne a jikina. Farare masu matuk'ar kyau. wandon rigar ko guiwata bai kai ba. rigar kuma mitsitsiyace mai hannun bra. Turare na cakud'a a jikina, kana na fesa na kaya. maganin gajiya na had'iya, dan iya gajiya yau na gaji matuk'a. Ina kwance na yi rub da ciki. damuwar da bansan dalilin wanzuwarta ba, gami da fad'uwar gaban da bansan ma'anarshi ba. su su ka addabeni. Aliyu yau d'aya da na wuni ban ganshi ba, hakan ya matuk'ar jigata ni. dan Aliyu ya sabar dani, zamu zauna mu yi hira, mu yi dariya, ya taya ni girki, ga kulawa, da wani irin girma da yake bani. tabbas ina hango b'oyayyen sona da sha'awata kullum a idanun Aliyu, dama muryarshi. Amma tun ranar da na gudu na barshi a falo, bai sake yin wani abu makamancin ya nuna mun yana buk'atata ba. Bamu tab'a kwana gado d'aya ba. Na saba da shi da yawa, hancina ya saba da k'amshin shi. Ina dai kwance sai inna kamo wannan tunanin sai in sake. Ni macece mai tsananin sha'awa shi yasa na ke yawanta yin azumi. Amma na yi Auran kuma, na kasa sallamama mijina kaina. Na fiso zuchiyata ta warke fes akan batun Ahmad ne.


mrs Bukhari ce


*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*








1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_


5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_




Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300


*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇


0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.


Domin tura shaidar biya👇


0810 433 5144


Masu tura katin MTN👇


0814 179 9224


Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇


0817 952 3215


Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f


*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨




Instagram links👇


https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=




Facbook group


https://facebook.com/groups/463653111781414/




Telegram links


https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk




*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -


*Enter your name:* (Cikakken sunanki)


*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)


*Enter your password:* ( misali 12341234)


*Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


Masu iPhone


Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
27~28


wannan shafin naki ne Anty Yabi Yunusa Jibril. kin ba da gudunmawa.


Aliyu
Da misalin k'arfe goman dare, aka rako ango Aliyu. Kamilu yana biye da manyan leda har biyu. Cikin sallama su ka shiga dakin Amarya.
sun gudanar da siyan baki kamar yadda yazo bisa Al'adun gargajiya. kowa ya watse, ango ya fito dan taka ma abokan nashi. Kamilu ne ya ja Aliyu gefe
"Aliyu ka rarrashi Sadiya sosai. lallai ba'aima Sadiya adalciba, babu wani lokaci da ta samu na Amarci,Baba ta hana ayi mata lefe. Ga Amarya ta danno kai, na fahimci a halin yanzu Sadiya tafi soyuwa a ranka fiye da Khadija. Amma ka kwatanta Adalci a tsakaninsu. Kaje kar ka jima." Aliyu ya kasa cewa komai. Jiki a mace ya koma cikin gida. d'akin Amarya ya koma, a zaune ya same ta in da ya fita ya barta, amma ta cire rufar. Da murmushi ta tarbeshi. zama yayi a kusa da'ita, bayyi aune ba ya ji ta kawo mishi runguma. sai gata a saman kirjinshi ta na zuba mishi sambatun k'auna.
" kullum sai na yi mafarkin ganina a jikinka. yau nice zan kwana a kirjinka, ina shak'ar k'amshinka."
Sokoko Aliyu ya ke dubanta cike da d'umbun mamakita fal cikinshi. har ta gama ki'danta da rawarta, ya kasa kamata ma. Yanzu ne ya ke sake ganin yarinta da 'karancin shekarunta. Tuno Sadiya yayi, da cikar halittarta da kirjinta cikakku yayi. wawuyar Ajjiyar zuchiya ya saki, wanda khadija ta yi tunanin da ita ya ke yi. murmushi yai mata kawai.
"Amarya ba kya laifi. Ina zuwa, zan je in ma Yayarki sallama. Mirsisi Khadija ta yi da ita tace.
" Bari in taso, sai mu je tare in mata ya gajiyar aiki, da ta biki, ledar kajin ta d'aukar ma Sadiya nata." dad'in hakan ya ji sosai, sai lokacin ta ga murmushinshi na asali. Ita kuma khadija da dalilinta na fad'ar zata bishin. bata k'aunar abunda zai sa su keb'e a cikin darennan da Sadiya. Dan Goggo Asabe ta yi mata jan kunne akan hakan sosai, hakama mahaifiyarta tai ta mata hud'ubar tsiya.
Su na tafe yana d'an janta da hira. Tana amsawa jifa jifa, dan hankalinta baya tare da ita sam."


Sadiya
ina kwance na jiyo Sallamar Aliyu, ban yi aune ba, na sake jiyo sallamar mace. Gabana yayi wata iriyar mummunan fad'uwar da sai da na runtse idanuna, dan ji nake zuchiyata ta na mun tsalle. Take idona ya cika tab da hawaye.
Hannu Aliyu yasa ya amshi ledar hannun Khadija.
"zauna bari in fito."
Muryar Aliyu ce ta ratsa kwanyata. Khadija kuma tunda ta shigo falona ta tsure. dama ta jima da jin labarin had'uwar d'akina a bakunan wad'anda su ka san d'akin nawa.
'kofar d'akin ya turo da siririyar sallama abakin shi, sallamar da banji sanda ya k'arasheta ba.
mutuwar tsaye yayi da ganin kyawun surata. Tim ya yar da laidar dake hannunshi. ni na mance shaf a cikin yanayin ma da nake, sabida shan iska nake yi. sai da na jiyo takun tafiyarshi, wuf na rufe idanuna tamkar mai bacci. a bakin gadon ya zauna. shuru na tsawon lokaci. Aliyu sai karema fuskata kallo yake yi. Ban yi aune ba naji hannun Aliyu a jikina, ya mirgino dani ina kallon sama. but still idanuna a rufe. rumfa yayi mun. jinayi kirjina na gugan nashi kirjin. D'an nishin da ya subce mai abakinshi, ya jefa ni a wata duniyar taurari da gajimare. tsam naji Aliyu ya matseni a kirjinshi, tare da cusa kanshi tsakankanin kirjina. shidewa nayi. ba shiri naja wani numfashi, a hankali na fesar dashi. D'ago fuskata yayi. Amma ni na kasa bud'e idanuna in kalleshi. jin d'umin numfashinshi da d'umun lips d'inshi nayi.Rik'on alewar yara yai ma lips d'ina. A mugun tsorace na bud'e idanuna, tare da k'o'karin kwatar kaina. Ina Aliyu ya yi mun rik'on da bazan iya kwacewa a hannunshi ba. luguiguitar bakina yai ta faman yi. ban dawo hayyacina ba. Sai da naji halamar yana shirin wuce gona da iri.
Kuka kawai na sakar mishi. zare bakinshi yayi a nawa, baya ko iya bud'e idanunshi. kyara mun zama yayi a 'kirjinshi, cikin wata dashasshiyar murya mai zurfi yace.
"Ki Amince in soma gudanar da Amarci a kan ki Sadiya. i want to fill you. kallona ya ke yi kamar zai had'iye ni da narkakkun idanunshi, wad'anda su ke sake zautani a cikin darennan. Wata iriyar sha'awace take fisgata izuwa ga Aliyu, ni kuma sai kokawar tsare kima ta nake, gudun mummunar fassara. Amma inaji tamkar in mayar da lips d'inshi cikin nawa. hakanne ya tilassatamun kasa d'auke idanuna akan lips d'in masu taushin gaske." bakin nashi yake k'ok'arin sake shigarwa cikin nawa, dan ya gane sakon da na ke isar mishi. kwankwasa k'ofa mu ka jiyo a na yi. kai ya dafe kamar mai ciwon kai. runtse ido na yi, har ga Allah an cuce ni. dan an katse mun hanzari.
Sake kwankwasa kofar a ka yi tamkar tamkar za'a b'allata. Ala tilas Aliyu ya mik'e tsaye. Ni kuma kunya duk ta isheni, na kasa had'a ido da shi. Ledar da ya yar a k'ofar d'akin ya koma d'akkowa. Ajjiyemun yayi a gefen gadona.
"sai da safe. zan tattala miki samartaka na, har zuwa lokacin da zaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login