Showing 21001 words to 24000 words out of 92932 words

Chapter 8 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt

Kamilu ya zarce aboki a wajanshi. Amma wannan wani sirrine da yake a b'oye. hakan cikin taraddadin abunda zai faru yai k'undunbalar shiga b'arayin su Goggo. tura k'ofar d'akin Goggo ya yi a hankali tamkar b'arawo. A falo ya samu Goggo idar da sallarta kenan. da sauri ya tsugunna dan karta kama danshin dake jikin wandonshi, wanda ya fito ta cikin jallabiyar jikinshi, ga Jallabiyyar ta kunbura. kai ya sauke kunya ta lullub'eshi ya ce.
"Barka da Asuba Baba Ina kwana?" Harara ta zabga mishi tana bin yanayin da ya zo mata da kallo. cikin zargi tace."
"Ka aikata abunda na haneka da aikatawa ko k'usar yak'i?" Kuka ta fashe mai da shi tace.
"wallahi tsinema zan yi insan na sallamama duniya kai. Da kuma Sadiya. Sai ka koma.Aisha ta zama uwarka." bakinshi na rawa ya ce.
" Babu abunda na aikata. wallahi a falo ma na kwana." Ajjiyar zuchiya ta sauke. dan tasan Aliyu ba ya k'arya. Balle kuma ya rantse ma. Tace.
"Akwatin kayan na ka ya na can an kaima ita Sadiyar."
"Toh" kawai ya ce.
"Aliyu" ta kira sunanshi da manyan bak'i. Harya kai bakin k'ofa ya tsaya.
"Kar ka manta gobe da safe ka tawo mun da takaddar sakin Sadiya. karka shigo sai da takaddar."
Bai ce komai ba ya fita. Da sauri ya wuce b'arayinsu. Hasiya ce ta bishi da harara.


Sadiya
ina zaune ina karatun Qur'ani cikin suratul maryam. ya shigo da Sallamar shi. A hankali na Amsa. Kaina na k'asa na ce.
"Barka da asuba an tashi lafiya?. Jin dad'in shi har ya kasa b'oyuwa a fuskarshi. cikin kulawa ya ce.
"Lafiya lau Anty. Amma bari na yi sallah sai in zo mu gaisa a tsanake." Wajan Akwatinshi da ya gani a gefen sip ya wuce.
Jallabiya ya zaro da wandonta. Sannan ya koma falo ya wuce band'aki yayo wanka. Sallah ya yi. Mik'ewa yayi. ya soma nad'e kayan na shi. Daidai fitowata. Ahankali na ce.
Dama ka barshi." Da murmushi ya ce.
"Babu damuwa Anty. Zo ki zauna mu gaisa." dukkan mu a kunyace muke magana. Amma kasancewar shi namiji ne harya soma sakewa.
Zama na yi a saman kujera. Na yi shiru ina sauraronshi. Shima shirun ya yi. Sallamar da aka doko a bakin k'ofar d'akin ce ta katse shirun.
Anas ne. Da dauri Aliyu ya fita.
"Yaya Anas? Rungume juna su ka yi cikin tsananin murna. Anas ya d'agoshi daga jikinshi ya ce.
"Aliyu kaine ka zama babban mutum haka? kai kawai ya sosa yana dariya.
"Yaya naga kowa amma banda kai da yaya Dauda."
"Kaidai ka bari. masu sayan hatsine daga Zamfara su ka shigo. Shine mu ka tsaya a kansu sai da aka gama komai. Ni da Dauda mu ka lissafi. Kusan buhu talatinne ba mu samu ba. Ana yawan yi mana satar da ba mu da masaniyar ko waye a cikin gidannan. Ni da Dauda ne ke rike da makullin rumbun."
"Aliyu ya ce idanu za'asa sosai Yaya. Tunda dai a cikin gidane. Kai amma ko waye ke yin wannan b'arna bai kyauta ma kanshi ba. mu shiga daga ciki mana Yaya."
"Wanne ciki kuma? tsarabata kawai za ka bani malam." Dariya Aliyu yayi. Tare da zura takalma yace.
"muje tsaraba na d'akin Baba ai. Su murtala suna almajirci har yanzu basu gama ba ko? Ficewa su ka yi a gidan nawa. sai da na dena jin muryarsu sannan na mike.
Kitchen na nufa. Na yi tsaye ina tunanin shin mai zan girka a matsayin abincin safe?" shiru na yi can sai na tuno bari kawai in dafa kuskus tunda bani da d'anyen kayan miya a hannuna. cikin k'ank'anin lokaci na dafa kuskus dina. Ta yi warawara sosai abun sha'awa. kula na sake farkewa na zuba ma.Aliyu. ruwan wanka na d'aura minti goma yayi akan wuta na juye. Rishon na rage tare da d'aura dumamen miya.
Cikin minti Talatin na gama kintsawa. ina sanye cikin wata jar atamfa hightaget. Dinkin diga da siket. Atampar ta amsheni sosai ta kuma dace da kalar skin dina. Dan jan abu na haska bak'i sosai. Kitchin na koma na kashe miyar. zubawa na yi a cikin kular Aliyu ta miya. Sannan na zubama Goggo Asabe nata. a basket na jera komai. takalmi flat shoe ne ja a k'afata. bak'in mayafi na yafa. Sabida atamfar da bak'in kala akai mata ado.
fitowa na yi babban tsakar gidan. Da Hasiya na ci karo ta na k'arema takuna kallo. Shewa na ji ta yi tace.
"Allah ya wadaran naka ya lalace. An salwantar da budurci dole a fito babu d'ingishin komai. Mu kuwa a ranar da komai ya faru munfi sati muna jinya." Da sauri na dubi Hasiya. Tana rik'e da k'ugunta da ganin fuskarta a cike take da ni. Karasawa nayi har inna take nace.
Wannan jahilcin naki ya soma isata. Ya kamata kisan ni ba sa'arki bane, sannan ni ba kishiyarki bace balle in zama abar tsokanarki. Ya isheki na Fad'a miki kenan.
Tafi Hasiya tayi tace.
"ke ce dai jahila wacce ba ta san me ke yi mata ciwo ba. wacce ta kasa auruwa a maraya kawai. Kuma ki sani duk wani wanda ya ci ciwo da ni miya yasha."
"miyar ma bazai gane ya sha ba. "Wato ke Sadiya rashin kunyar taki har takai ki zagarmun mata a matsayinta na matar.wanki? Dauda ke magana daga bakin k'ofarshi.
"Toh ki sani mu a gidannan baza mu d'auki raini da iskancinnan naki ba. Maras kunyar kawai. Ai dama barewa baza ta yi gudu d'anta yai rarrafe..... Kafin ya idasa na daka mishi tsawa.
"Dakata cin kashin ya tsaya iyakar kaina. Kar ka kuskura iyayena su shigo. Dan zamu yi uwar watsi. iyayena sunfi mun kowa da komai a daniya." Da sauri Dauda ya nufoni Banyi Aune ba na ji saukar hannunshi akan fuskata ya zabgamun marin da saida idona ya makance na wucin gadi. ya sake d'aga hannu zai sake sauke mun . Da sauri na tare fuskata Ina jiran inji a inda hannun nashi zai sauka. sai na ji shiru. Ahankali na bud'e idona. Aliyu ne a tsaye ya had'e ranshi hannun da Dauda ya d'aga zai mare ni Aliyu na rik'e da shi. Rannan nashi a murtuke.
"Ba daidai bane dukan mata. Balle macen da take matar Aure. Danme za dukar mun mata? Bakasan darajarta bane ko me? Ina daraja matata bazan ba da wata k'ofa da za'aci kashi a kanta ba, domun a k'ark'ashin kulawata take, kuma hakkinane kula da mutumcinta. Kai wane girmanka ya dace ka rik'e. Dauda ya fisge hannunshi ya na nuna Aliyu da yatsa jikinshi har rawa ya ke cikin d'aga murya ya ce.
"Akan wannan karuwar 'yar bokon ka rik'emun hannu a matsayina na Yayanka. Kuma ba tare da ka yi tambaya akan wanne irin rashin kunya ta yi ba?" Bilkisu ce ta fito dan taji ana hayaniya har da ihu. Ganin abunda ke faruwa ne ta zame jikinta.zuwa b'arayin Goggo Asabe ta sanar mata. Ta wuce wajan kawu ta sanar mishi.
Aliyu ya rintse ido, dan kalmar karuwa ta gigita tunaninshi ya ce.
" Babu buk'atar sai na ji me ta yi maka. Amma ai kasan ba matarka bace. Matata ce kuma inasonta duk karuwancinta. Domun y'ar uwata ce ita, Anty bakiji ciwo ba ko?."
"Ai kuwa wallahi baka isa ka ci gaba da zama da ita ba yau ba sai goben ba Auranka da Sadiya ya k'are." cewar Goggo Asabe wacce ta iso ita da kawu da matanshi. Gabana ya yanke ya fad'i take na soma zubda hawaye. Isowa ta yi gabana tace.
"Makirar 'yar duniyar mace. Harkin juya mishi kai kenan yau k'usar yaki ne ke yin fad'a. Fad'anma da wanshi. yaron da ya samu shaidar jama'a a gari bai tab'a fad'aba. Shine da zuwanki kin soma haddasa husuma ko. Kinaso ki raba shi da danginshi kamar yanda uwarki ta raba mu da d'an uwanmu. wallahi Allah ba ki isa ba." Nidai ina tsaye jikina har rawa ya ke yi. Aliyu yace.
"Baba zuwa na yi na tadda ya mareta fa. me yasa zai d'aura hannu a jikinta matar Aure ce fa."
"Auran wa? kama daina kallonta a matsayin matar Aure dan indai nonona kasha toh sai ka saki Sadiya yau d'innan ta koma wajan muguwar uwarta." Kawu yace.
"Ke Sadiya ba su fad'a miki doka da tsarin gidannan bane akan girmama kowa ba? kuka na ke yi sosai kukan da ba na ma iya ganin kowa. cikin shesshek'a kuka na ce.
An fad'amun. Amm"
"Dakata Sadiya iyakar abunda na tambaya kenan. Dauda ya ce.
"kuma fa fitowa na yi sai na ji ta na zage Hasiya. Har da ma Goggo Asabe. Shine daga magana ta hau zagina. kuma ita ta soma marina." cikin kururuwa Goggo da Fatima su ka rufu a kaina da duka kakaf kakaf. ina tsugunne ina kuka. ko yunk'urin guduwa na kasa yi. Aliyu duk ya bi ya rud'e Goggo ya ke ta ba hak'uri. Amma ta k'i fur. Sai da tai mun lis bakina da hancina duk sai yayyon jini ya ke yi sannan ta na huci tace.
"Shegiya maras kunya fitsararriya. kai kuma ka kawo takaddarta yanzu ina jiranka ko kaga mai zai biyo baya. Shashasha mai fad'a akan macen da bata cancanta ba." Fuuu ta fice a gidan. Kawu kuma ya ce.
"Kai Dauda kar ka sake dukanta. Kome ya faru ka kawo gaban manya. Kai kuma Aliyu ka bi umarnin mahaifiyarka kar tai ma baki."
watsewa kowa ya yi ya barmu. Zuchiyar Hasiya da Bilkisu fes dan murna. Aliyu ya zuba mun idanunshi da suka kad'a su ka zama jawur, tausayina tsantsa na gani a idanun Aliyu, kuma ko ba komai ya daraja auranmu, ya kuma kira ni matarshi. Wani sanyi naji a zuchiyata.




mrs Bukhari ce
*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*






1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_


5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨*
_Miss Hajo_




Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k


*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*




Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.




Shaidar biya tanan 👇
0810 433 5144




Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224


...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎....


*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇


Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224






*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
*GISHIRIN*
*ZAMAN*
*DUNIYA*
_Daga Al'kalamin_
_Badi'at Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
GAWURTATTU BIYAR 🤚🏻








Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.




*INA MIK'A SAK'ON GAISUWA GA DUKKAN MASOYAN LITTAFIN GISHIRIN ZAMAN DUNIYA, HAK'IK'A NAJI DAD'IN ADDU'ARKU GARENI. GISHIRIN ZAMAN DUNIYA YA D'AUKAKA FIYE DA TUNANINA, YA TSALLAKA INDA MA BANYI TUNANIBA. TUN JIYA NAKE TA SAMUN SAK'ONNI DA KIRAYE KIRAYEN MASOYANA. INA GODIYA SOSAI, ALLAH YA BAR K'AUNA.*




Kashi na 1
Babi na 19~20


Kallona ya sake yi cikin tausayi da tausayawa. Hannunshi ya saka ya d'agoni tsaye. Tare da jinginani da jikinshi. wani irin shocking mu ka ji a jikin juna. wata wawuyar ajjiyar zuchiya na sauke, tare da haki, ga bakina a fashe sai jini yake zubarwa Hannu yasa rik'e mun k'uguna, ahankali ya soma tafiya. Har d'ingishi nake yi tsabar azaba." Hasiya ta na lab'e ta na cizar yatsa. Domun ko a mafarki Dauda bai tab'a mata hakanba. ko a Zamanin amarcinta Sanda gishiri ya ke kan kaza kenan. Ko yau ta ji mamaki da ya shigar mata fad'a. Dauda ne dake bayanta, inda take a lab'e ya ce.
"malama matsa zan wuce in kin gama gulmar. Da sauri ta saki labulen nata. Tare da sauke kanta.
"Dama nasan ko me ake ciki kece mara gaskiya. munafuka mai ta da husuma. Amma Abokiyar husumarki ta nanan zuwa, 'yar sarkin magulmata." Wucewa ya yi ya barta a wajan tare da ficewa a gidan. Ita kuma ya barta da cizon yatsa.


Sadiya
Ahankali muke ta fe. Aliyu ya jera mun sannu ya fi sau a k'irga. akan doguwar kujerar falona ya sauke ni. Hawaye kuwa bai bar.zuba a idanuna ba. tsugunnawa yayi a gurwarsa ya ce.
"Anty ki yi hak'uri dan Allah da dukkan abubbuwan da suka Faru. Goggo ba ta tsaya ta yi bincike bane, kuma zan d'auki tsattsaran mataki akan Yaya Dauda, bazan bari ya bige ki a banza ba.Amma me ya had'aki da Yaya Dauda?.
A cikin kuka na bashi labarin kab habaice habaicen da Hasiya ta sani a gaba da shi. Har zuwa wanda tai mun yau. Shiru yayi ya na kallona k'ur, kallon da duk shekaruna na kasa fassarashi. na ce.
"Yanxu sakin nawa zaka yi ko?"
Bansan sanda bakina ya furta hakanba. Domun duk abunnan da ake ciki maganar sakin ya girgizani. Ban sani ba ko dan ban jima da yin auran bane. Bana son duniya ta kafa hujja a kaina wajan zagin 'yan boko. Na dai tsinci kaina cikin tsoron SAKI. tunda nai wannan maganar ya ke bina da kallo kawai. Ni kuma kunya duk ta kama ni.
"Bari in hura kara in d'aura miki ruwan zafi ki gaza jikinki. zanje Lamba in siyo miki magani a kemis. Da sauri na ce. Akwai kalanzir a risho. Magani kuma i na da shi a box d'ina."
bai ce komai ba ya fita. hawayen fuskata na share. zuchiyata a cikin zugi da tashin hankali ta ke. Haka


Aliyu
Aliyu ma. Tunda ya d'aura ruwan wankan a kan risho. ya ke tsaye a kitchin din. sai tunanin mafita kawai yake yi. shi bai ji cewar zai iya sakin Sadiya ba. baisan alkhairin dake cikin auran shi da ita ba. Kuma a zahiri Sadiya ta kai macen da ko wanne namiji ya sota, ya kuma ji yana son kasancewa da ita. bugu da k'ari gata 'yar uwa ta jini, wacce bai kamata a yasar da'ita ba.Amm ya na auna kalaman da Goggo ta jefe shi da shi. cewar indai nononta ya sha ya rayu toh dole ya saki Sadiya. Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya rasa tudun dafawa, balle makamar da zai kama. Ruwan ya juye mata ya sirka. har ban d'akin ya kai ruwan.


Sadiya
ya shigowa yayi ya sameni da box d'ina da mirro ina dressing bakina da Goggo ta fasa mini. Zama ya yi yana kallona k'uri yace."
"Ashe da likita na ke tare ban sani ba. Kai masha Allah. Murmushinshi ya fad'ad'a.
Bance dashi komai ba. sai da na gama tas nace.
" 'yar koyo dai waneni da likita. murmushi yai mun.
"Ki je ki yi wankan. zan je in dawo yanzu, ina mai baki hak'uri a karo na barkatai, kuma ki sani ina tare da ke." fita ya yi. ni kuma na shiga toilet na dinga gasa jikina dan ko ina ciwo ya ke yi mun, juyayin maganganun Goggo kawai nake yi, cike nake da mamaki. Wai dama ashe haka lalurar jahilci take? Wallahi gara mahaukaci sau dubu akan jahili.


Aliyu
Fitarshi ke da wuya ya zarce gidansu kamilu.
Kamilu ya fito k'ofar gida, Sai kawai ya ga abokinshi a cikin yanayin tashin hankali mara musaltuwa. Dafa kafad'arshi yayi dan bai ma san Kamilu ya fito ba.
"Aliyu lafiya kake kuwa na ganka a cikin irin wannan yanayin, Meke faruwa? Aliyu ya juyo ya kalli kamilu, idanunshi sunyi jawur, ga wani ciwon kai dake addabarshi, hatta d'and'anon yawunshi ya gurb'ace tsabar tashin hankali.
"Kamilu Baba ce ke son birkita mun fissafi na. Waifa magana take yi akan sai na saki Sadiya, kuma ni bazan iyaba wallahi." Hannunshi Kamilu ya rik'o zuwa cikin gidan na shi. Kai tsaye su ka shiga d'akin da anan ya ke. Kasancewar matanshi biyu ne. Sai da su ka zauna Kamilu yace.
"Saki kuma daga dawowarka. wani abun Sadiyar ta yi ko me?" Labarin komai da komai Aliyu ya ba Kamilu ciki harda abunda ya faru yau."
"Tabb aiki ja kenan. Amma tunda Sadiya ta amince ta zauna da kai a wannan k'auyan namu da mu kanmu muke gudunshi. Ai kuwa ta cancanci a yabeta. Ni nasan duk akan khadija Baba ta ke yin wannan abun. Ita bata san khadija ta canja ba shiyasa." Aliyu ya gyara zama ya ce.
"kamar ya Kamilu wanne irin canjawa ta yi?"
" Aliyu nasan k'ila abun bazai xo maka da sauk'i ba ko. Amma sau uku ina had'uwa da khadija da mahaifiyarta a wajan rabe. Amma su ba su ganni ba. Duk fad'in k'auyannan waye bai san Rabe ba?. Bazan bari ka cutu ba, dama naso sai ka huta sannan zan sanar maka, yanayin da ake cikine yass dole na sanar maka yanzu. Aliyu ya girgiza da jin wannan labari. take har idanunshi ya sake kad'awa yayi jawur, har wata jijiyace ta faso a goshinshi. yace.
"Indai har na yi bincike na gano abunda ke kai khadija da mahaifiyarta wajan Rabe. Toh Aure ni da khadija babu shi. Yanxu mu kawar da wannan matsalar Kamilu Baba na can tana jiran in kawo mata takaddar sakinne fa. Kamilu yace.
" Ni ina ganin muje mafara wajan Iya mai Tubani. A ganina ita ce kawai za ta iya dakatar da Baba akan abunda tai k'udiri."
"Kamilu Baba mahaifiyata ce na santa fiye da tunanin mai tunani. Iya mai Tubani kuma k'anwa ce ga gyatumarsu Baba. Baba babu wanda ya isa ya sa ta yi hakuri akan wannan sakin, kasan muguwar tsanar mahaifiyar Sadiya dake zuchiyar Baba kuwa? ina tunanin ubangiji ya bani Sadiya ne dan mu zama silar kawar da duk wani gaba. Ni tunani nake yi ko in mai da Sadiya gidane zuwa komai in ya lafa sai ta dawo, wallahi Kamilu ina son Sadiya. Amma me ka ce? Kamilu yace.
"zuwa gidanne bazai mata kyau ba Aliyu. Sati guda da.Aure a ganta a gida, Hakan zai iya b'ata mata suna. Sannan mahaifiyarta abun zai mata ciwo. Kaga da haka sai zumunci yai ta lalacewa. Mu jarraba zuwa wajan Iya. In yaso mu tafi da Sadiya. Ko a can ne sai ta zauna xuwa wani lokacin." A hakan su ka samu matsaya. Mik'ewa Aliyu yayi yace.
"Ka shirya bari in sanar da ita ta shirya sai mu tafi kawai." Kamilu ya dafa kafad'ar shi yace.
"Kar kayi sake lu'u lu'un da rabbi ya baka ya subce a hannunka. Ka yi iya yinka, Saki dai a hannunka yake. Kuma ka k'arfafi guiwarka karka basu damar karaya. Sadiya alkhairice.
Ficewa yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login