Showing 15001 words to 18000 words out of 92932 words

Chapter 6 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt

yi mun shine. Abar yaronnan ya Auri Khadija. kar a tauye musu hakkinsu. Aure kuma, ai ba Aliyu bane ya ga mace ya ce ya na so ba. ni ma kaina fa na fi son Khadija." mai gari ya ce.
"maganar gaskiya Asabe. ba na jin zan iya sauka akan wagga baka. Aure ko? na amince ya Aure ta. amma in ya Saki waccan 'yar barikin daya Auro. in kuwa ba haka ba. wallahi sai dai a hak'ura da Auran. dama yarinya ta na da manema. sabida al'kawarin da ke kanmu ne yasa ban ba ma kowa dama ba"
Goggo Asabe gabaki d'aya kanta ya chaza sosai. kuma ta san Aliyu zai shiga tashin hankali mai yawa in aka ce yau ya wayi gari ya bar Khadija. cikin sauke murya tace.
"Toh ranka shi dad'e, ni zan koma. duk abunda mu ka yanke da 'yan uwa na, da shi kanshi k'usar yak'in in ya dawo, za ka ji a bakin mai dambu. Maganar saki daya dawo, kafinma ya shiga d'akinta ta juya mishi kai, zan sa ya sauwak'e mata. Ka sauraremu." ( hmm maman Yaseer ke fa kinji)
"Toh madallah ina saurarenki Asabe, yaro Allah ya dawo dashi lafiya."
sallama ta yi mishi ta fito.
ta na tafe ta na ta faman tunani akan wannan lamari da komai ya ke son lalace mata.
"duk Bala ne ya ja mun wannan tsiyar. ya k'ak'aba ma yaro Auran dole, yaro da wacce ya ke so shi kuma. ni wannan kafiya ta me gari ta ishe ni wallahi"
duk maganganun nan ta na yin su ne, ita kad'ai a hanya. har ta iso gida. ( Oum Shuraim tace, "kya ji da shi dai )


Sadiya
wunin wannan ranar cikin nasiha Goggo Hansatu ta k'arar mana da yinin.
washe gari ma ta d'aura daga inda ta tsaya. na saki jiki na sosai babu laifi.
kullum da safe ina zuwa gaishe da Goggonnina da kawu da matan shi. haka duk wacce na had'u da ita a tsakar gida, ni dai zan gaishe su. wasu su amsa, wasu su yi kunnen uwar shegu da ni. Ina jiyo su, suna hirar tsakar gida tare da shewa. Amma ban tab'a ko lek'awa ba.
Allah ya kawo mu ranar Dawowar Aliyu. Goggo Hansatu tun safe ta yi ma matan gida sallama ta kama hanyarta. Ni kuwa a ranar na ci kuka har sai da idanuna su ka yi wani mummunan kumburi. ji na ke yi tamkar in sa hannu na a ka, in rintima uban ihu, ko zan ji sanyi a raina. Wani irin suya zuchiyata take yi mun.
bayan na share hawayena ne, sai na mik'e na duba agogo na 'karfe biyu da rabi na rana.
kitchen na shiga, na kunna ritso na d'aura ruwan tea. ina tsaye ya tafasa. a cup na zuba wanda zan sha. sauran kuma na zuba a tea flase na barshi a kitchen d'in.
dai dai zan fito daga kitchen kenan. sai ga Fatima yayar.Aliyu ta shigo da sallamarta. cikin fara'a na tarbeta. amma kuma sai na ga ta turb'une fuskarta. babu yabo babu fallasa ta amsa gaisuwata. na ce da ita.
mu shiga daga ciki mana Fatima, naga kin tsaya daga nesa. Bud'ar bakinta tace.
"Fatima kuma, hala kin manta ni Yar Mijinki ce? Koda ma, mun yi tunanin ganin rashin d'a'a a wajan 'yar boko. dama d'abi'arku ce rashin kunya da fitsara. Goggo na jiranki ki fito za mu je d'auko K'anina mijinki kuma a filin jirgi. cijewa na yi. tare da bin bayan Fatima da kallo wacce ta fice fuu. murmushin ba'kin ciki kawai na yi.
kaya na sake daga atamfa zuwa material mai taushi. d'inkin riga da siket wanda ya kama ni ya zauna.daram a jikina. kirjina ya d'an fito ta saman rigar har ana ganin tsagun daya raba mamana biyu. gyalen kayan babba ne sosai kuma yana da kauri. yane shi na yi a kaina tare da kama shi da pin. turare na fesa mai cool k'amshi. takalmi na mai tudu na d'auko na sa kalar kaya na. ni kaina da na dubi madubi nasan na yi kyau sosai. amma gabana sai fad'uwa ya ke yi. ga maganar da Fatima ta caka mun yana ta dukan zuchiyata, ga ganawa da Aliyu da zanyi. Shima sai fad'ar mun da gaba ya ke yi. Da hanzari na fito tare da sa ma k'ofata kwad'o na rufe ruf.
A babban tsakar gidan na samu su Goggo. ita da kawu, da Anas, da Fatima, Sai wata yarinya fara da ban santaba. Amma kuma naga ta na watsomun wani mugun kallo.
"Ku yi hak'uri in na b'ata muku lokaci."
Kawune kawai ya ce.
"Babu komai Sadiya. Khadija ma yanzu ta zo."
kallon ta na yi muka had'a idanu. harara ta sakar mun. Sai yanxu na gane ta. Itace yarinyar da Aliyu zai Aura.
ta b'angaren khadija kuma gabanta ne ya fad'i da ganin kyau da tsarin sura irinna Sadiya. ta ke ta shiga kokawa da hawayen da ya ke shirin zubowa ya kunyatata. jikinta ne yayi sanyi, tare da karayar zuchiya..Amma kuma data tuno Aliyu na dawowa zai sake ta. kafin ma ya shiga d'akinta. sai ta yi dariyar mugunta kawai.


Sadiya


D'unguma mu ka yi baki d'ayan mu. mu ka hau Babur dan zuwa kan iyakar da za mu samu motar zuwa sokoto.
na sha wuya a wannan hanya. mai tarin kwazazzabai. kafin mu sauka na yi wurjanjan dani.
kai tsaye mu ka shiga motar cikin garin Sokoton Shehu.
ina zaune a mota, gabana sai fad'uwa ya ke yi. kuma ni kaina ina jima kaina kunyar in kalli Aliyu A matsayin mijina. Babba dani. Sannan ina fargabar irin amsar da zai yi mun. da ma irin Rayuwar da za mu shinfid'a, mai dad'i ko akasinta.




mrs Bukhari ce


*GAWURTATTU BIYAR,5🀚TAFIYAR TA MUSAMANCE*






1, *MU GANI A ƘASA..πŸ”₯*
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..πŸ₯š*
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*πŸ’₯
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_


5_ *AUREN WATA TARAπŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨*
_Miss Hajo_




Guda Ι—aya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huΙ—u N700
Guda biyar 1k


*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYARπŸ‘‡*




Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.




Shaidar biya tanan πŸ‘‡
0810 433 5144




Masu tura katin MTNπŸ‘‡
0814 179 9224


...........πŸ₯šπŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ‘¨πŸ’₯🌎....


*Ζ³AN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKUπŸ‘‡


Guda biyar 1000f
Guda huΙ—u 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda Ι—aya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224






*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*


*INA MATAN MASU AMSA SUNANSU NA MA, INA UWAR GIDA, INA AMARYA, INA 'YAN MATA 'YAN KWALISA?* *HAK'IKA DUK MACEN DATA ISA, SAI DA K'AMSHI DA GYARAN JIKI BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI. 'YAR MUTAN KATSINAWA NAZO MIKI DA SIHIRTACCEN K'AMSHIN DA ZAI JIJJIGA MIKI OGA, TA YANDA OGA ZAI LIK'E MIKI.* *SUNAN WANNAN K'AMSHIN MANNE MATA, MAK'ALE MATA* * *WASU KUMA SUKAN KIRASHI DA D'AYE MANNA* 'YAN MATA AKWAI NAKU HAD'IN NA DABAN.


*AKWAI KULACCA TA SUDAN*
MAI SIRRIN K'AMSHI DA GYARA FATA, GA UWA UBA SA LAUSHIN JIKI, DA KUMA DAWWAMAR DA K'AMSHI A JIKIN FATA.


*AKWAI SIHIRTACCIYAR HUMRA, 'YAR SUDAN*
WACCE AKAI MA LAK'ABI DA 'YAR BAIWA MAI ABUN MAMAKI.
ITA KUMA TADA SHA'AWAR ME GIDA TAKE YI, TARE DA K'ARA DANK'ON SOYAYYA, DA KUMA DAWO MA DA MATA MARTABARSU. UWA UBA AN HAD'ATA NE DA ITATUWAN GYARAN JIKI, DA KUMA SIRRIN K'AMSHI MAI MOTSO SHA'AWAR DUK WANDA YA SHAK'ETA.
πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ
BAN TSAYA IYA NAN BA.
AKWAI TURAREN KWANCIYA, WANDA AKE SHAFAWA A MATSE MATSI, DA SAMAN CIKI.
πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€πŸ˜€
KE DAGA JI KINSAN AKWAI AIKI, DAN MAI GIDANKI SAI K'ARA SONKI DA KUMA MAK'ALE MIKI.
🀣🀣🀣🀣🀣
INA DA TURARE D'AN GASKE NA TSUGUNNO, MAI FARFAD'O DA MARTABA DA KIMAR GABAN MACE, K'AMSHI YA DAWWAMA A WAJAN, YANA SAUKAR DA NI'IMA, YANA KASHE INFECTION, YANA MACE MACE TA HAD'E TSAM. YANA K'ARA D'AND'ANO.
πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ
INA HAD'A TURAREN FANT 'YAR UWA, WANNAN MA WANI SIRRINE NA MUSAMMAN
πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ
TA B'ANGAREN KAYAN MATA KAMA DAGA NA NI'IMA, NA INFECTION,DAMA NA MATSI IRI IRI. DA DUK WANI MAGUNGUNAN MATA A KWAI SU, 'YAN GASKE, MRS BUKHARI 'YAR MUTAN KATSINAWA TA ZO MUKU A SHIRYE TSAB.


AKWAI SETI NA MAI JEGO, WANDA YA K'UNSHI KOMAI DA KOMAI A CIKI.
πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ
KANA AKWAI SETI NA AMARYA, ITAMA NA MUSAMMAN NE, YANA D'AUKE DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN JIJITA ANKO.
'YAN MATA WANDA SUKE SHIRIN SHIGA DAGA CIKI KUMA AKWAI NAKU SETI NA MUSAMMAN.


AKWAI MAN DILKAR GYARAN JIKI NA AMARYA, DA SABULUN AMARE NA MUSAMMAN
*BANGAREN TURARUKAN WUTA NA INA NAN*
*TURARUKAN D'AKI, DANA KAYA, DA TURAREN GASHI, DA TURAREN WANKA, TURAREN MOPPING, TURAREN WADROPE, TURAREN BAYAN GIDA. KUJERAR TSUGUNNO, KABBASA, DUK INA SIYARWA. DOMUN NEMAN K'ARIN BAYANI TU TUNTUB'I MRS BUKHARI 'YAR MUTAN KATSINAWA.
08179523215
saina ji ku
*GISHIRIN*
*ZAMAN*
*DUNIYA*
_Daga Al'kalamin_
_Badi'at Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)




Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.


Kashi na 1
Babi na 13~14


Sultan Abbakar the 3rd international airport Sokoto State


A tsaye ya ke. ya na ciniki da masu taxi d'in da ke sana'a a bakin get d'in Airport d'in.
dogone sosai, ba irin tsayinnan mara tsari ba. domun faffad'an kakkauran k'irjinshi ya k'awata tsayin na shi. Kasancewar su Goggo Asabe irin dogayen sakkwatawanne sosai. domun mahaifin Sadiya har wani doron tsayi ya ajjiye. Haka mahaifinsu mai Hula ya ke. shi tsabar tsayinshi ya wuce misali.
Aliyu Fari ne sosai, irin fararen fatarmu na nan gida Najeria. shi ba siriri bane. kuma ba mai k'iba bane. sai dai ya na da zubin gwarazan maza. kan shi babu tarin suma. saisayan aski ne a kanshi. siririyar fuskarshi na d'auke da k'asumba da gemu me yawa, wanda kuma ya ke shan gyara, da taza a kai a kai. yana da hanci daidai misali amma ba kamar biro ba. bakinshi kuma, madaidaicine. idanunshi su na da tudu ta saman idanun na shi. sai dai a cikin asalin idanun. ba su da girma sosai. gira da gashin idanunshi, irinna mazan mu na gida Najeria. wato dai dai da misali.
Sanye ya ke cikin Farar jallabiyya mai kyau sosai. kanshi sanye da hular ustazan larabawa wacce ake kifata a kai. a gida najeria ma ana samun irenta da mata ke yi mata sak'ar lilo. sannan ana samun 'yan kantinsu a kasuwa.
k'afarshi na sanye da wasu slipas mai yatsa, bak'i. wanda ya fito da zara zaran siraran yatsunshi masu kyau.
yana rataye da k'atuwar jakar baya. da akwatinshi trolla, sai kuma jakar tsaraba.
bayan sun gama daidaitawa da mai taxi zai shiga kenan, motar su su Goggo Asabe ta iso.


Sadiya


jiki a mace na sakko daga cikin motar nan. zuba ma wanda Goggo Asabe ta kira da K'usar yak'i, idanu na yi. ina karantar shi da kyau. daga sama zuwa k'asa na kalleshi. gaskiya in na kushe Aliyu ban kyauta ba. domun yanda na karanceshi, matashine mai hankali da nutsuwa. kuma bashi da k'azanta a ido dana ganshi.
murmushi ya yi yace.
"Ahhh Baba ashe kunsan zan dawo ne?
da sauri ya iso wajan Kawu ya rungumshi. suna murnar ganin junansu. Goggo Asabe tace.
"wato kawunka ya debe ma hankali, wajanshi ma ka soma zuwa ko?
murmushi mai burgewa Aliyu ya yi ma Goggo Asabe. bai ce komai ba ya rungumeta yana lumshe idanunshi. Fatima da Khadija kuwa sai dariya su ke yi.
ni kuwa ina cikinsu tsamo tamkar wata bare. Gabana sai dokawa yake ta faman yi.
"Barka da zuwa Aliyu."
cewar khadija. harda wani sassauta murya dan ta yi taushi.
cikin dariya ya ce.
"Dijengala ke ce ki ka girma haka? Ai ko a hanya na ganki sai dai in wuce."
dariya su ka yi duka. Fatima tace.
"Ai kaine ka girma Aliyu. ji wata k'asumba daka tara. sai kace babban mutum. kuma ka sake yin fari.
"Yaya Fatima kenan. ina yaran?"
"Suna gidan su Kawu na barosu acan.
Goggo Asabe ta ce.
"Ni kaina sai na ga ya mun wani bawai. ji uban gemu kamar soson waya k'usar yak'i. Ai wani sai ya d'aura irin manyannan ne. Yaro da kai da d'anyan jininka ka zama wani babba."
kawu ya ce.
"Ai kuwa yayi kyau sosai. Sai dai dole zai canja mana. Shekaru hud'u fa. malam Iliya ne ya sanar damu ranar da za ka dawo. ya ce kun had'u a Umara da ya je."
kai ya girgiza ya ce.
"Gaskiya ne. har gidan da muke ya je.
carab mu ka had'a idanu dashi. na ji matuk'ar kunya daya kamani dumu dumu ina kallonshi. Da sauri na kawar da kaina.
yamutse fuska yayi, tare da d'aura d'an yatsanshi a gefen kanshi. Alamar tunani.
" Kawu wannan ba Anty Sadiya bace. Ta gidan Baffana?"
mai taxi ne yai musu magana da ya ga hirar tasu tak'i ci tak'i cinyewa.
"Malam ka fa barni a tsaye.
da sauri Aliyu ya juya, wajan mai taxi d'innan. yana mai bashi hak'uri. Sun tattauna ba mai yawa ba. Sannan ya juyo ya ce.
" Kawu muje ko?"
Dawowa yayi zai 'dauki akwatin ya sa a bayan mota.
Goggo Asabe tayi tarab tace.
"Ke Sadiya. Aike ya dace ki d'aukar mishi. Ko a gabana ma zaki nuna mun ke 'yar duniya ce?"
wani abune ya tokare mun mak'oshina. Murya a sanyaye na ce.
"Kiyi Hak'uri Goggo.
take idanuwana su ka kawo ruwa. Ajjiyar zuchiya na ke ta saukewa a hankali. Aliyu da bai fahimci Abinda Goggo Asabe ta ke nufi ba. Na hango rashin jin dad'i a fuskarshi.
Akwatin na d'auka. Har zuwa gaban motar. juyawa na yi, na d'auko jakar na ajjiye a kusa da akwatin.
Mai taxi ya zuba komai a bayan mota.
Aliyu da kawu. suka zauna a gaban mota.
mu kuma mu na bayan mota dukkan mu.
Hira su ke ta yi, cikin raha da burgewa. Ni ko kaina a sauke ya ke, ina share hawayen da na kasa dakatar da shi.
Ashe Aliyu ya na kallona ta glass d'in hannun da yake ta waje. Kasancewar ni ina zaune ne a bak'in kofar shiga. Sabida sai da kowa ya shiga. Sannan na shiga gudun kar in yi wani laifin da za'a sake tsinka ni.
kai ya girgiza tare da cije lebe.
Yace Baaba. Yaushe Anty Sadiya ta zo ne? ni fa ba dan jini ba. Wallahi bazan gane ta ba. Sau biyu na tab'a ganinta."
Goggo.Asabe, ta tab'e baki tace.
"Ni banma san ka tab'a ganinta ba ai.
Aisha ai bazata barta ta shiga dangin Adamu ba.
Su 'yan boko ne. Masu raina mutanen k'auye. kuma ai kasan Aisha bata tare da dangin mijinta sam. Shi kuma Adamun, Inka tab'a jemammiyar matarshi. Sai ya ji gwara ka zare ranshi. Ba a hakan bane ta ci nasarar mallakarshi da asiriba. yai ta ma iyayenta da danginta bauta."
Aliyu ji yayi tamkar k'asa ta tsage ya fad'a ciki dan kunya. Shiru yayi tamkar ruwa ya cinyeshi.
Ni kuwa dama kaina na k'asa. Hawayene su ka ci gaba da gudu a fuskata. Fatima tace.
"Goggo ki ce kun k'unshi bak'in ciki? ku da kuka sha d'awainiya da k'aninku. Amma tashi d'aya rana d'aya. Sai wata ta malleke muku shi. Ku kun tashi a tutar babu.
Gashi na ji ance har zuwa yanzu, ana biyanshi mak'udan k'ud'ad'e a wajan aikin shi ko?"
Ai fatima dama kamar da biyu tai ma Goggo wannan tambayar. Sai cewa ta yi.
" Sosai ma. Amma ta yi rub da ciki akan dukiyar. Harfa gida ta zo, bayan rasuwar Adamu. Ta samu Kawunku ga shinan. Wai an barta da marainiya, mu ba ma tallafa mata. Dan haka tazo ne a bata gadon mijinta. Za ta ci gaba da kula da karatun yarinyarta. Mu na ji muna gani, Akaima wajan kud'i, sai aka biyata iya nata. Kasancewar mace gare ta. Mu ma aka bamu namu fa."
Fatima tana k'ok'arin bud'e baki ta yi magana. Aliyu ya daure ya ce.
"Yaya Fatima. Su Yaya Anas da Yaya Dauda, basa gida ne? Banga sun zo taryata ba."
" Gona mu ka barosu zasu je. za'a fita da dawa cikin Zamfara."
da k'arfi Aliyu ya canja zancan dole.
na sha muggan maganganu kafin mu iso gida.
dandazon matasan garin, suna k'ofar gida an cika. da ganin Aliyu, su ka shiga sowa suna kiran sunanshi.
A wajan mu ka shiga gida mu ka barshi."
Ina tafe kici kici da akwati da jaka. Duk ni kad'ai. Fatima da Khadija har sun wuce nima. Hasiya matar Dauda. ta dube ni, ta tintsire da dariya tare da tafa hannunata tace.
"Ahhh andai yi fad'uwar bak'ar tasa. wai Yaya da auren k'aninta."
harna tsaya dan inaso in yi ma Hasiya gargad'i. Amma dana tuna ciwon jahilci ke damunta. Sai kawai na yi wucewata.
cikin k'uryar d'akin Goggo na shigar da kayan. Alokacin har gidan ya gama cika da jama'ar k'auyan, sun zo yi ma Aliyu barka da zuwa. zama nake so in yi a falon Goggo, amma carab tace.
"Ai abunda ya fi dacewa shine ki yi maza ki girka ma Aliyu abinci. Tunda baki da wannan tunanin sai an fad'a miki. k'ila haka malaman boko d'in su ka koya miki ko?"
Bazan iya cewa da Goggo komai ba. Fita na yi jikina a mace. ina jiyo dariyar Fatima da Khadija.
Jama'a sai kallona su ke yi, suna xund'ena . baba wanda na nuna na gani, wucewa ta kawai na yi.
bilkisu ce ta yi mun magana ina daf da shiga b'arayina.
"Aliyu ya dawo lafiya?"
Dubanta na yi da kyau na ce mata.
"Bilkisu ni banga aibun Auran yaro ba. Danna girmeshi sai me.? inaga baku da tarihin magabata shiyasa. k'aramin sani k'uk'umi.
tsaki na ja na wuce na barta rik'e da k'ugu a wajan.
Hasiya ce ta iso wajanta da gudu tace.
"Barta za mu yi maganinta a cikin gidannan. ke ni wallahi baki ji yanda na tsaneta ba. kishi na ke yi da ita, fiye da kishiyar da za'a kawo mun.
Bilkisu tace.
"Ni kaina mugun kishi nake yi da ita. Bana ko san ganinta. Ga shegen iyayi wai ita uwar mata. Sai dai uwar mijinta ma kad'ai ta isheta.


Sadiya
shinkafa fara na dafa. Ina da miyar stew wacce ta ji naman kaza da jan nama. Wanda Goggo Hansatu ta yi mun da yawa, akan in tafi da'ita gidan Ahmad dan in samu sauk'i kafin in soma girki.
Ban tab'ata ba tunda mu ka zo. Sai d'umamata da na ke yi sau biyu a rana.
food flaks na bud'e sabo mai guda hud'u.
A ciki na zuba na Aliyu. Goggo da Kawu kuma na bud'e musu wata kular mai biyu.
Sai da na kai na Aliyu da Goggo, Sannan na wuce na kai b'arayin Kawu.
ina dawowa na yo wanka. minti talatin na kwashe a komai da komai.
Ina sanye da doguwar rigar bak'in yadi 'yan kanti. Rigar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login