Showing 69001 words to 72000 words out of 92932 words
Chapter 24 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt
nace.
"Haba Ahmad wannan nacin ya isa haka, dan saura kwanaki k'alilan ya rage in auri masoyina, wanda ya san darajata. Da ka san ka na sona, shine ka fasa aure na."
"Assalamu Alaikum Malam" Muryar Safwan ce ta daki dodon kunnena, gabanane ya fad'i ras. Da sauri na juyo, mu ka had'a idanu, idanunnan nashi sun kad'a sun yi jawur. Hannun Ahmad ya mik'a mishi, su kai musabaha. Ya ce.
"Ba dai_dai bane nema a cikin nema, saura kwanaki na mallaketa, sadakina ya na gidansu, matatace, ka kiyaye." Sab'ule hannunshi yayi a cikin na Ahmad, dakalin da mu ka saba zama ya je ya zauna, Ahmad ya shige motarshi rai b'ace, ni kuma cikin sanyin jiki na isa wajan Safwan. Waje na samu na zauna. Amma mun fi minti goma babu wanda ya ce da wani komai, Safwan sai ajjiyar zuchiya kawai ya ke saukewa. Minti talatin na cika ya mik'e, ya kasa cemun komai, tafiya yayi ya barni a zaune a wajan.
Idan raina yai dubu ya b'aci yau, domun jikina har rawa ya ke yi, ko ma meye ai bai dace ya shanyani na tsawon minti talatin ba, kuma ya yi wucewarshi ya barni a zaune ba."
Tafiyata na yi gidan Amina, raina a dagule sosai, da murna ta tarbeni tana zaulayata.
"Amarya mai maganar siga.Sai yanzu kika zo, ni harfa na cire rai da ke."
Tsaki na ja na zauna, bance da ita komai ba. Zama ta yi a kusa da ni.
"Ke lafiyarki kuwa, ko dai ke da Mama ne?"
Hmmm wacce Mama, Amina Safwan ne ya b'ata mun rai wallahi."
Labarin abunda ya shiga tsakaninmu na bata, dariya ta fashe mun dashi, tace."
"Amma Sadiya ke 'yar rainin hankalice, shine kika kasa bashi hak'uri bisa laifin da kika aikata mishi? Baki kyauta ba, shima k'ila shi yasa yai tafiyarshi, kinsan zai ga kamar kin raina shine, shi yasa ki ka kasa ba shi hak'uri? Kuma maganar gaskiya, ko waye zai yi fishi sosai, Sadiya baki kyauta ba."
Jikina ya sake yin sanyi k'alau."
"Hakane Amina, sai da nake tawowa ne na gane sake k'ular da Safwan na yi shi yasa ya tafi ya barni, tunda na kasa ba shi hak'uri, kuma na kasa yi mishi bayanin da zai fahimta. Yanzu yaya zanyi Amina?"
"Hak'uri za ki yi, ki bari zai zo da kan shi, sai ki bashi hak'uri, ba daraja bane ki bishi makaranta ki ba shi hak'uri, da sai in ce ki je. Shawara d'aya ce, ki sai mishi card na ban hak'uri, da fulawa me kyau, sai ki ba Haidar ya ta fi mishi da shi makaranta."
Ido na zare nace
Haba zan azabtu da yawa, yaufa asabar ne, kina nufin har sai monday? Bazan iyaba gaskiya, meye mafita kawai?"
Dariya Amina ta yi, uwar d'akinta ta shige, da goruna manya biyu ta fito a hannunta"
"Ga wannan ki shanye dukka, ko da a hankali a hankaline, in kin tashi tafiya kuma, akwai gumbar 'yar gata da zan baki, k'aramar robar fenti guda, kita ci kawai har ta k'are. Maganar Safwan kuma, ki sai card d'in yau, sai ki je layinsu ki tura yaro ya aika mishi gida."
Amina ai bansan gidan shi ba, shine matsalar."
"Ai kuwa ya zame miki dole ki yi hak'uri zuwa monday dan ba ni da mafita ni kam."
Haka dai mu ka d'an tab'a hirar, na yi dawowata gida.
Safwan kuwa yana isa gida, sai zazzab'i mai mugun zafin gaske ya kama shi, sai had'iyar zuchiya kawai ya ke yi. Allah ya halicceshi, namijine mai tsananin mugun kishin da har ya ke jin tsoron duk wani abu da zai motso mai da kishin abunda ya ke so. Kishin da yake da shi, ya zame mai matattakalar daya taka ya gama karatu da sakamako mai kyau da first class ya fito. Badiyya a rud'e ta fita siyo mishi magani a kemis, shi kuwa ya fice a hayyacinshi, hawaye kawai ke bin gefen idanunshi, ya na jin kishi da takaicin ma son Sadiya da ya ke yi. Ya ma zata kula wani da ranar shi a kanta? Kuma dan ya fad'a mishi gaskiya, Sadiya ta yi fishin da ko hak'uri ta kasa bud'e baki ta ba shi, sai k'aratar zaman shi ya yi ya tafi. Ga shi ya ganta a cikin kwalliya da k'amshi."
Mrs Bukhari ce
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
Instagram links👇
https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Facbook group
https://facebook.com/groups/463653111781414/
Telegram links
https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
MRS BUKHARI
61-62
Badiyya ce ta shigo d'akin hannunta rik'e da kofin silver na ruwa, da maganin zazzab'i. Tallafo kan shi ta yi, ta jinginar da shi a jikin pillow. Magani ta b'alla ta bashi, tare da kora mishi ruwa.
Hawayen gefen fuskarshi ta share mishi."
"Me ya saka a cikin wani hali haka ne, ashe son da ka ke yi ma Sadiya ya kai haka? Safwan ka tausaya mun kar ka tunzura kishina ya fito waje, kullum a cikin son faranta maka nake, kar ka bar hawayena zuba tun kafin Sadiyan ta shigo mana." Tausayin kalamanta ya ji, sai kuma kunya duk ta lullub'eshi. Matsowa yayi ya d'aura kan shi a cinyarta.
"ki yi hak'uri uwar gida, kishinki bazai tunzura ba, ki yafe mun bazan sake ba" Hawayen daya taru a idanunta ne suka shiga suntiri a kumatun ta, kishin Sadiya ta ke yi, tamkar ta kashe kanta. Son da take ma Safwan kuma bazai barta ta juya mishi baya ba. Tunda su ka yi aure, ta kasance a cikin son duk wani abu da Safwan ya ke so. Saukar nunfashinshi ta jiyo halamar bacci ne ma ya kwashe shi."
Sadiya
A kwance na ke ina jiran bacci yai awon gaba da ni, amma ji kake shiru malam ya ci shirwa. Sai juyi na ke yi akan gadon, ban yi zaton son da na ke yi ma Safwan ya kai wannan matakin ba. A daren ranar dai, kusan raba dare na yi ina tunanin Safwan.
Weekend d'in baki d'aya banyi a cikin walwala ba sam.
Yau ya sakance Monday ranar aiki. A shirye na fito tsab da ni, cikin doguwar rigar atampar soso, mai kalar bak'i da ruwan goro, card d'in dake hannuna na saka a cikin jakar bayan Haidar.
In ka je makaranta, ka ba ma Abba wannan katin kaji?
"Toh Umma, yaushe Abba zai dawo gidanmu, Jafar abokina ya ce, Abbanshi gidansu d'aya. Kuma tare da Ummanshi su ke kwana. Ni Abbana kullum sai dai mu had'u a makaranta."
Wani mikin rashin Aliyu Haidar ya fama mun a zuchiyata. Take na birkice da kukan da Haidar ya dinga rarrashina.
"Umma ki yi hak'uri ki share hawayenki. Umma 'yan makarantar mu duka na kullum su ke yi, suna ture ni, wai ni k'azami ne, Zabiya."
Bakin shi na toshe mishi da hannuna, cikin tashin hankali nace.
Haka su ke kiran ka Zabiya! Abbanka ya sani kuma?"
"A'a bai sani ba, ni bana fad'a mai, zai musu bulala."
Ka yi hak'uri kai ba k'azami bane, haka Allah ya so ganinka Haidar mai kyau."
Murmushi ya yi mun, kanshi na shafa nace.
Adawo lafiya Haidar."
Hawaye ya dinga share mun. Mama ce ta fito da mayafi a jikinta."
"Toh jikalle mu je kar ayi latti. Sadiya aikin safe ki ke da shi ne?"
Eh mama, aikin safe ne." Mama tace.
"Toh aje lafiya a dawo lafiya. Da
Ameen" Na bita.
Ko da na je Asibiti sam bani da walwala da kuzari a jikina. Tunanin Aliyu ya hanani sukuni sam, sai hawaye na ke yi.
Sister Zarah ce ta iso cikin ofishinmu."
"Sister Sadiya, Dr Rabo na nemanki, akwai mata masu labour a labour room har biyu." Dubanta na yi na ce.
Sister Fatima da sister Zakiya ke da duty yanzu, ni sai 10 zan karb'i duty."
"Ahh ai an canja tsari, meeting d'in da aka tsaya ranar juma'a da baki halarta ba. An canja tsarin karb'a_karb'a. Daga takwas na safe, 'yan kwana za su hutu, zuwa takwas da rabi 'yan safe su amshi nasu, zuwa k'arfe hudun yamma.
Kai masha Allah, abun yayi kyau."
Mik'ewa na yi, labour room na wuce kai tsaye, dan amsar haihuwa. Yau kam labour room d'in cike yake da mata masu haihuwa, hakanne yasa aiki yai mana face face a wannan ranar, bani na samu kaina ba sai kusan biyun rana. Kai tsaye masallacin mata na wuce dan gabatar da Sallah. Daga nan na wuce ofishinmu dan in ci abinci, amma ga abincin a gabana na tusa shi na kasa ci.
Sister Nadiya ce ta shigo da sallama tace."
"Sister Sadiya, kina da bak'o yana zaune a reseption yana jiranki, kusan awa guda kenan, a lokacin kina labour room, amma an sanar da shi."
Da mamaki na dubeta tare da maimaita.
Bak'o?"
Cike da mamaki na mik'e na fita, bance da kowa komai ba, reseption na nufa kai tsaye, ahankali nake takawo dan babu kuzari a jikina sam, Safwan na hango duk da ta baya na hangoshi, amma shi d'in ne dai.
Assalamu Alaikum yallab'ai barka da zuwa." Idanu ya zuba mun yana kallona cikin kayan aikin asibiti, murmushi yai mun mai sanyi.
Waje na samu na zauna, kaina na sauke ina wasa da zoben zinaren dake hannuna, fuskata babu walwala sosai."
"Ameen wa'alaikis salam, barka da aiki Sadiya."
Murmushi kawai na yi mishi, amma ban d'ago kaina ba.
"Ki yi hak'uri kamar zuwana bai miki dad'i ba ko, ko akwai wani abunda yake damunki wanda ni mijinki ba za ki iya sanar da ni ba, uhm Sadiya?"
Hawayen daya taru a idanunane suka gangaro kamar wata k'aramar yarinya.
Safwan ya sake dubana cikin sigar lallashi yace.
"Haba Sadiya, shin ba gani a kusa da ke ba, ai na d'auka wanzuwata zai goge dukkan wani bak'in cikin da ya ke damunki. Ko dai mai motar nan ya fi baki farin ciki sama da ni ne, ko tunaninki son da nake miki bai kai mizanin da za'a kalla ba? Ina sonki da yawa Sadiya, sonki da kishinki har kwantar da ni su ka yi, yanzu haka ban gama warwarewa ba. Come on ki share hawayenki kinji amarya ta?"
Bansan sanda na yi murmushi ba, ji na yi kalmar so da Safwan ya furta mun a karon farko ya kori duk wata damuwa da take son damuna, fes na ke jin zuchiyata a yanxu, cikin shagwab'a irin ta mu ta mata, mai yanje hankalin wanda a ka yi domun sa na ce."
"ka yi hak'uri akan dukkan abunda ya faru, a bisa akasi duk suka faru. Ahmad ba saurayina bane, mun yi soyayya a da, ranar da za'a d'aura aure na da shi, magabatan shi su ka sanarma nawa magabatan cewar, d'ansu bazai auri 'yar boko ma aikaciyar gwamnati ba. Shikenan aka d'aura aure na da mahaifin Haidar wanda ya kasance d'an yar Babana ne. Shi kuma Ahmad ya auri k'awata Fatima." Safwan ya ce."
"Amma da ma ya na son k'awar ta ki ne, ko yaya?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace."
"Al'amarin da ya ba kowa mamaki kenan, domun a ranar d'aurin auran mu, aka d'aura auran shi da Fatima. abunda zai baka mamaki shine har da kalanda su ka buga"
Murmushi Safwan ya yi mun kawai, agogon fatan hannunshi ya kalla yace."
"Zan gudu Sadiya, kar in tsaida miki da aikin ki." Murmushi na yi na ce.
"Amma ya jikin na ka, da sauk'i ko?" Hararar soyayya ya jefa mun, sai da tsigar jikina ta tashi.
"Ashe kin damu da ciwon nawa? Bacin ke ki ka sa na kwanta"
Ni ma fa na azabtu da rashinka sosai, da ma san gidanka, da baka zo ba sai dai ka ganni kwatsam." Dariya ya yi mun kawai."
"Jikin ya yi sauk'i musamman da na zo na ci karo da kyakkyawar fuskarki, sai na dawo dai dai. Badiyya ta ce in gaisheki da kyau." Kallon tuhuma na yi mishi.
" Ka na nufin matarka ta san da zama na kenan?" mik'ewa ya yi tsaye.
"Sosai ma, tare mu ke gudanar da duk wani abu da ya shafi junanmu, kuma ta na farin cikin shigowarki rayuwata. Madam zan gudu, ban tashi a makaranta ba, ga shi lokacin tashin har ya kusa, kafin in koma makaranta an tashi."
Agogon hannuna na duba, hud'u saura.
Ka jirani kawai mu ta fi tare k'arfe hud'u zan tashi."
Kai ya d'aga mun halamar toh.
A wajan na barshi, na sanya aka kawo mishi ruwa, ni kuma na ci gaba da aikina har zuwa lokacin tashi.
Tafe mu ke mu na hira irin hirar da bamu tab'a yin irinta ba. Safwan ya bani labarin matar shi da irin son da ta ke yi mishi, da irin tsananin son haihuwa da su ke yi dukka, amma bai bani labarin asalinshi ba, maganar matarshi ya gundureni sosai, dan ina jin kishinta.
Mun iso k'ofar gidanmu mu na zaune akan dakali na dube shi na ce.
"Baka bani labarin ahalinka ba, da musabbabin da ya kawo ka Kano, ka baro azare."
"Sadiya zan baki wannan labarin amma sai mun yi aure tukunna, duk wani bincike da za ku gudanar a kaina kuna da dama, musulunci ya yarda da hakan. Dariya na yi.
"Tuni su Mama su ka gama duk wani bincikensu a kan ka ai, shi yasa hankalina ya sake nutsuwa, duk da ko da an samo matsala ni dai na ji na gani." Dariya na ba shi sosai.
"Sadiya kina burgeni kin iya tsara magana. Toh kin amince za ki zauna da mijinki a k'auye kuwa?"
Sosai ma, sai dai ina naiman alfarmar ka barni in ci gaba da aikina" Gintsewa ya yi, zunbur ya mik'e yace."
" Da daddare zan zo sai mu yi magana Sadiya, zan ta fi, ki shiga ki huta kema, ki gaishe da Haidar da Mama" Sallama mu ka yi, ya nufi gida, ni kuma na shige ciki da sallamata.
Haka kwanaki su ka ci gaba da tafiya shirye shirye ya ci gaba da kankama ta ko wanne b'angare, yanzu haka ma Safwan sun tafi Azare shi da Badiyya matar shi."
mrs Bukhari ce
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
Instagram links👇
https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Facbook group
https://facebook.com/groups/463653111781414/
Telegram links
https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
MRS BUKHARI
63-64
Azare
Safwan ne gurfane a gaban Innaj da Baffan shi, suna ta tattauna al'amuran biki.
"Safwan ga kud'i da aka tara nera dubu d'ari da sittin, daga wajan yayyunka maza da mata. Yayarku Saliha kuma ta d'auke nauyin duk abincin da za'aci a biki, ka ga har rago ta siya. Kawu malam k'anin mahaifinka kuma zai gyara maka b'arayin da zaka zauna, har an soma gyaran ma." Innah ta ce.
"Ya maganar Akwati kuma?" Safwan yace.
"Mun had'a akwati biyu ni da Badiyya, kugunmawar ta kenan, ita ta sai komai da komai da kud'in sark'ar zinarenta da azurfarta data gada." Innah ta yi tsalle ta dira akan Safwan da fad'a.
"Akan me za ta sai da kadarorinta data zo da shi daga gidansu, kalan ta dinga gorantama Sadiya a gaba cewar ita ta yi lefen bikinta? Ita kanta Sadiyan ai ba dad'i zata ji ba."
"Haba Rakiya haba Rakiya, wannan ai fad'an rashin gaskiya ne. Yarinya ta yi abin yabawar da ya kamata ki yabeta. Kayan gadonta fa ta siyar danta taimaka ma mijinta, Safwan Allah yai muku albarka dukka" Safwan ya amsa da.
"Ameen Baffa" Innah tace
"Ina kayan su ke, ko da su ta tafi gidan nasu? Yarinya fur ta k'i ta sauka a gidan mijinta sai gidan iyayenta, kai kuma ka amince mata, wai sai bayan biki da sati d'aya ma zata tare" Safwan yace.
"Innah na ga hakan ba laifi bane. Ta fi shekara biyu ba ta zo gida ba, ko zan tawo sabida rashin kud'i, sai dai in tawo ni kad'ai, kuma ba ta tab'a yi mun magiya ba. Yanzu kuma ta ne mi alfarmar hakan bai dace a ce na tauye ta ba, duba da yanda ta shige gaba a cikin hidimar bikina." Baffa ya ce."
"Hakan da ka yi na nuna kai adaline Safwan, amma ka sallameta da kayan fad'ar kishiya dai ko?" Kai Safwan ya sosa."
"A'a tukunna dai Baffa amma tunda kud'i sun samu zan yi mata. Sai dai ina so in yi mata d'inkunan biki ita da Innah kafin lokacin." Baffa yace.
"Allah yai ma Albarka, tashi ka je, Mudi ya na ta jewa a gidannan, rabon da in