Showing 63001 words to 66000 words out of 92932 words
Chapter 22 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt
su kai ma zabiya kenan, hakanne yasa suke ganin kamar k'abilar kirista sun fi musulmai yawan haifar zabiya, musamman ma Inyamurai." Dr ne ya ne mi ganina, ina hawaye na wuce su, sai zabga fad'a kawu ya ke yi, Yaya Kabiru na ta ya shi.
"Zauna madam"
Waje na samu na zauna, cikin k'arfafa guiwa da ya zama halayyar likitocin kwarai yace.
"Haidar kyakkyawa ne sosai, zan so ki kula da shi, da fatar shi, ta yanda ba zai samu kuraje da k'onewar fata dama, dabbara dabbaran bak'i ba. Ko dan ma guje ma Sankarar fata da ke addabar zabiya.
Duban shi nayi
"Dr in sha Allah in dai ina numfashi, kuma in dai akwai magangunam da zan yi ma Haidar amfani da shi ba tare da fatar shi ta k'one ba. Toh ni kuwa ko nawa ne zan jure siya mai. Amma Dr meye sababin da ke sa a haifi zabiya?
yace
"Good Albinism cuta ce da ake iya kamuwa da ita daga Iyaye, wanda abun ya shafi wasu kwayoyin halittar da ke d'auke da rashin daidaituwa ta hanyar samar da melaninn. za a iya yad'a shi ga yaro." Cikin fahimta nace
"Dr yaya zan yi in kare yarona daga kamuwa da sankarar fata?"
"Binciken ido da dermatological yana da mahimmanci, dan gyara lahani na gani da ke da alak'a da cutar zabiya.
mutanen da ke da albinism, riga kafin rana yana da mahimmanci don guje ma had'arin ciwon daji, sabida fatar su mai rauni ce sosai, kuma ta na kula da hasken UV. don haka kariya ga fata da idanu na da mahimmanci. ya kasance ko da yaushe ya na cikin inuwa, tare da sanya tufafi mai rufe jiki kirib. Sa tabarau dan kare ido daga hasken rana, sai shafa 50+index cream dan yana taka muhimmiyar rawa. Akwai mayuka da sabulan da zan rubuta miki. Da su za'a mishi amfani ko da yaushe.
B'angaren matsalar idanun shi kuwa, ku je zuwa nan da wata d'aya sai ku dawo dan a sake dubawa, xuwa kafin lokacin idanun zai iya bud'ewa ya soma gani ba tare da mun yi mishi komai ba." Godiya na yi mishi sosai. sannan na fito, Haidar na je na d'akko na fito.
Gida mu ka koma, abun mamaki sokotawa Allah ya yisu da canfi, nan fa labari ya karad'e k'auyan na haifi yaran k'azanta, babu wanda ya xo mun barka, har matan gida, Goggo Asabe da su Goggo Safiya ma, babu wanda ya zo. ranar suna daga ni Sai Goggo Hansatu sai matan Kamilu ne kad'ai. Kamilu ya yanka ma Haidar k'aton rago, haka mu ka yi sunan mu, daga mu sai mu. Bayan kwana biyu muka tattara ya namu ya namu, motar kayan da zata bi yanke cikin jeji, ita mu ka bi, babu wanda yai mun batun gadon Haidar, haka na yi musu sallama ina kukan tuno da Aliyu.
Kano state
Mama na zaune a tsakar gida, tana shirin had'ama Malam Kaka sob'o, mu ka shigo. Baki ta rik'e.
"Hansatu kaddai har ta sauka?" Dariya Goggo Hansatu tayi.
"Tun yaushe har an yi suna ma, an samu Aliyu Haidar. Hamdala Mama ta yi, a baya na ta sunto Haidar, wanda na rufe kirib, hular zata janye na yi maza na rik'e hannunta.
"Mama mu shiga daga ciki, Haidar ba ya son rana. Bata ce komai ba, mu ka shiga ciki. Goggo Hansatu ta labarta mata komai, sai da ta yi hawaye.
"Ki yi hak'uri Sadiya komai mai wuce wa ne, yau ina Aliyu, baya kwanta dama ba? Toh haka za a k'are a duniyar ma. ki kula da yaronki, ki samu nutsuwar shayarwa Babu komai. Hansatu kin yi zumunci Allah ya biya ki."
Cikin kwanciyar hankali na ke shayar da Haidar, ya yi b'ulb'ul abun shi, gwanin sha'awa da shi, kullum a k'unshe a cikin suturar da zata rufe mai jiki yake. K'awayena da basu samu damar zuwa mun ta'aziyya ba, sun zazzo, har da abokan aiki na duk sun zo. cikin shekara guda Haidar ya zama kamar yaron turawa, babu ko sofane a jikin shi, kuma yana gani da idanunshi, sosai Haidar ke samun kulawa, sai da ya cika shekara biyu cib na cire shi a mama, yana gudun shi ko ina, baki kuwa rairai. tsawon wannan lokacin babu wanda ya tab'a zuwa duba Haidar daga cikin dangin mahaifinshi. Na koma bakin aiki na, a nan ne fa manaima su ka soma yi mun yawa, amma ni kula da Haidar da aiki na ya fi mun komai. Couse gwamnati ta d'auki nauyin tura mu 'kasar India, bayan 'yan setin farko sun dawo. Tare da Haidar na tafi, couse ne da zai d'auke mu tsawon shekaru biyu. Da hakan na samu damar jefa Haidar makaranta, tunda shekarun shi uku a lokacin, muna gama couse d'inmu mu ka dawo najeria, a lokacin Haidar na da shekara biyar a duniya. Ya sake yin mugun kyau, duk in da na shiga da Haidar sai ya samu masoya, fatar shi ta yi kyau, dan acan k'asar India na samu wasu mayuka ba irin namu na gida najaria ba, kuma sun amshi fatar tashi sosai.
Na murje na sake yin wani irin kyau, fatata ta murje sosai, na k'aro ilimi na kuma sake wayewa sosai. Mama ta ji dad'in ganinmu dukkan mu, bayan mun nutsa ne sai na jefa Haidar a makarantar firamare, da kuma islamiyya.
"Sadiya na zuba miki idanu in ga gudun ruwan ki amma fur kin k'i yin batun aure, sai hidima da Haidar kawai kike yi, kinga kar mu zama abun zagi a anguwa ke ba aure ni ba aure, kinsan yanzu kiwon mutane ake yi ba dabba ba. Ajjiyar zuchiya na sauke
Mama ba aure na k'i yi ba, ina tunanin yanda Haidar zai soma agolanci ne, amma da na yi auren, akwai wani Dr Saminu da ya jima ya na biyiyata, tare kuma mu ka tafi da shi wannan couse d'in, bayan shi akwai su da dama, Mama ba kowa ke iya auran bazawara me d'a ba, kuma ya iya rik'esu dukka, ba tare da ya nu na ma wannan agolan banbanci ba, ni kuma akan Haidar zan iya hak'ura da auran."
"Dallah rufa mun baki, shashasha, akan ki aka soma yin aure a tafi da agola ne,ko so ki ke yi sai bakin jama'a yai ma rayuwarki illah? tun wuri ki fito da mijin aure. wata d'aya na baki, in ba haka ba za ki ga hukuncin da zan d'auka akan ki, shekarunki sama da arba'in " A zaune mama ta barni ina tunani, Haidar na tuno da lokacin tashin su a makaranta yayi, ai ba shiri na fita da sauri zuwa makarantar.
Da gudu Haidar ya iso wajena na, rungumeshi, mu na dariya.
"umma zo ku gaisa da Abbana, kullum ya na gaisheki. Shafa kan shi na yi.
Haidar ka bari sai wani lokacin mana. Fur Haidar yak'i, hannuna ya rik'e har cikin ofishin malaman makarantar. Da sallama mu ka shiga. D'ago kai yayi mu ka had'a idanu, saurin kawar da kaina na yi, dan ban cika son had'a ido da maza ba.
"Angle ga umma na."
Murmushi malamin yayi.
"Sannu da zuwa umman mu." Dariya na yi kad'an nace.
"yauwa sannu malam da k'ak'arin aiki. Ina jin labarinka a bakin Haidar, kuma na yi farin ciki sosai da kake kula dashi, ya fad'a mun baka barinshi wasa a cikin rana. Ina godiya sosai da kulawarka ga Haidar."
Kallona ya ke yi. Ba yaro bane dan zai iya ba ni shekaru fin goma ma.
"Babu damuwa umman mu, ai d'a na kowa ne, kuma na yaba da k'ok'arin ki dan inganta rayuwar Haidar, zan zo gidan in sha Allah." Godiya na yi mishi, na kama hannun Haidar mu ka tafi.
wasa wasa malam Safwan kusan kullum sai ya zo wajan Haidar, tare da hidimomin da ya ke yi ma Haidar, Ahmad ma ya dawo waje na, kamar zai mai da ni ciki tsabar so, amma na kasa ba kowa Fuska, Kamilu ma yayi halacci, dan yana zuwa duba Haidar sannan ya na bashi kulawa dai dai da yanda zai iya. Ya nuna ya na son aure na, amma na nuna mishi yayi hak'uri, kuma na gode da kulawarshi gare mu.
Amina ce ta haihu yau suna, daga wajan aiki na wuce" K'awayenmu na makaranta duk sun zazzo, mu na zaune ana hira kawai sai ga Fatima, da k'aton cikinta ta shigo, sai tsokanarta ake yi, Fatima ta ji kunyar ganina dan tunda Ahmad ya aureta ba mu sake had'uwa ba."
"Sadiya ke ce kika zama haka? Hmmm manyan mata. zama ta yi, na ce.
"Fatima ai fishi na ke yi dake, ace duk a cikin k'awayenmu babu wacce bata zo mun ta'aziyya ba, sai ke." kai ta sosa.
"Wallahi ni kunyar abunda na yi miki ne ya sa na kasa zuwa. Dariya na yi.
"Haba.Fatima ai matar mutum kabarinshi, yaranki fa hud'u ga na biyar a cikin ki, da ya za'ayi da rabon yarannan? komai ki ka ga ya faru, ubangiji shi ya tsara faruwar shi. Dad'i Fatima ta ji, ta sake mu kai ta hirar mu abun sha'awa. Da na tashi tafiya ma ita ta yi mun ta yin mu je Ahmad ya rage mun hanya.
"Ahmad ka ga fa mutuniyar mun shirya, kuma ta fahimce ni sosai, shi dai Ahmad ta mirror ya ke kashe ni da mayyar soyayyar shi, dan shi d'in gwanine fagen iya soyayya. yace
"Na ji dad'in wannan had'in kan na ku sosai. Hira mu kai ta tab'awa, Fatima ya soma ajjiyewa sannan ya kaini k'ofar gida.
"Sadiya so ki ke yi son ki yai mun illah ko me? Sai bani wahala sonki ya ke yi, ke kuwa sai k'ara kyau ki ke yi abunki, ni ne fa Ahmad mai yawan sonki da k'aunarki, kuma na yi miki bayanin ba laifi na bane fasa auranki da na yi ba. Hannu na d'aga mishi.
"Dakata Ahmad kar ma ka soma cewa haka, dan in ba da sanin ka hakan ta faru ba, ba zaka auri Fatima a ranar da ka fasa aure na ba, wannan abun a shirye yake, kai da ita duk munafurtata ku kayi, bazan iya baka wata dama ba." Fitowa na yi daga cikin motar. Da Safwan mu ka had'a idanu, ashe ya na zaune a k'ofar gida yana jira na, kishi 'karara na gani a idanun shi, har ruwa ruwa k'wayar idanun shi ta yi. Sai na ji jikina ya mutu, a hankali na iso in da yake, zama na yi a dakalin da yake zaune. Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya sanya idanun shi a cikin nawa.
"Sadiya sannu da dawowa." Kasa amsawa na yi, shi kuma sai bina da kallo ya ke yi. Mik'ewa yayi, tare da ajjiye mun ledar da ke hannunshi yace.
"Ki tashi ki shiga ciki, ni zan wuce gida, dama duba ki kawai na zo yi, ki gaishe da Haidar duk da shi yai ta taya ni hira."
A wajen ya tafi ya barni. idanunnan nashi sun yi jawur da su, Nasan Safwan yana sona, amma nauyi da kunya sun hana shi furta wa, gashi yau ya tafi cikin ciwon zuchiya. a sanyaye na shiga cikin gida."
mrs Bukari ce
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
Instagram links👇
https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Facbook group
https://facebook.com/groups/463653111781414/
Telegram links
https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
55~56
Mama da Haidar su na tsakar gida, shi yana aikin da aka basu na makaranta, ita kuma ta na karanta mujalla. Haidar ya tawo da gudu, tsugunnawa na yi na rungumeshi ina dariya. Mama ta zuba mun idanu.
"Sadiya zo ki zauna, Haidar k'arbi kayan hannunta ka shiga ciki.
Xama na yi kamar yanda mama ta umarce ni, Haidar kuma ya shiga ciki.
"Sadiya yaronnan Safwan meye matsayar maganar ku? Na ga ya na hidima da yawa a kan ki da Haidar, me yasa ba zaki bashi dama ba? Bana son in yi aure in barki a gidannan, domun hakan ba mutuncin bane. Ko ba kya son Safwan d'in shima? Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
"Mama bawai bai yi mun bane, ni halin da Haidar zai shiga ne damuwata. Duk da dai Safwan ya na son Haidar, amma mama bai tab'a mun maganar soyayya ba gaskiya, iyakata da shi mutunci."
"Sadiya ho, duk wannan jewar da Safwan ya ke yi, kin fi so sai ya furta miki yana sonki? Toh ki mai maganar turo magabatanshi, sai su je can Raquma a d'aura auran ke ma ki huta.
Toh mama in yazo zan sanar mishi."
D'aki na shiga, bayan na rage kayan jikina, wanka na yo, nazo na samu Haidar ya barbaje kayan da Safwan ya kawo mana.
mayukan Haidar ne, da sabulan wankan shi, lallai Safwan ya cancanci in bashi dukkan wata dama. Amma ta ina zan soma rarrashin shi ma? dan da fishi ya tafi.
Tun daga wannan lokacin Safwan bai sake zuwa gidanmu ba, sai dai ya aiko mun da sak'on gaisuwa. Da dai naga tafiyar ta mik'e har wata guda, ranar na taso aiki da safe, kai tsaye makarantar su Haidar na wuce. Aike nayi a kira mun Safwan.
Yana sanye cikin wani yadi da ya sake fito da kamalar shi. Shima sai kallona ya ke yi da mamaki, take kunya ta lullub'eni. Nama rasa in ya k'araso me zan ce mishi.
"Malama Sadiya barka da wannan yanayin, idanki kenan?" Tausayi ya ba ni sosai
Safwan kwana biyu me ya faru ka dena.zuwa zance gida? Hannayenshi ya zura a aljihun shi yace.
"Sadiya na lura kamar takura miki hakan ya ke, kuma bana son Bazawarin ki me mota da yake yawan suntiri a k'ofar gidan ku yayi tunanin ko akwai wani a tsakaninmu, kuma ni wajan Haidar Aliyu mai hula na ke zuwa. Gabana ya fad'i sosai, bansan son Safwan ya shige ni har haka ba. Jiki a sanyaye mu ka yi sallama da Safwan.
ko da na koma gida kasa nutsuwa na yi. da yamma lis yaro ya turo kira na. Da zumud'i na fita a tunanina Safwan ne, ina fita na ci karo da Ahmad. yana jingine a bakin motar tashi, raina bai so zuwa ba, dan dai na riga na fito ne. Ina zuwa in da ya ke, Safwan ya na shawo kwana Idanu muka had'a, a mugun zuciye ya koma. Ni kuwa sai lek'e na ke yi, ji na ke tamkar in bishi da gudu.
"Sadiya lafiya kuwa, naga hankalin ki baya tare da ni?" Harara na zabga mishi tare da jan tsaki na koma cikin gida na barshi a nan a tsaye."
Safwan yana tafe yana tunanin me yasa ma ya damu da Sadiya alhalin ita bata ma san yana yi ba? da tunane tunanen daya isa gida kenan.
Badiya ya samu ta na wanke wanke a tsakar gida, murmushi su ka sakarma juna, kujera ya jawo ya zauna a gaban wanke wanken, ya shiga d'auraye mata.
"Sannu da zuwa, yau baka je wajan su Haidar bane, naga ka dawo da wuri, kuma ranka a b'ace ?"
"Badiyya ni na hak'ura da Sadiya kawai, kamar ba sona ta ke yi ba Allah." murmushin danne kishinta ta yi tace."
"Gobe zan je ni da kaina dan yi ma yak'in nemo soyayyarta,burina shine inga ka samu magaji, ko ni ma na huta da gorin da 'yan uwanka su ke yi mun.
Inna ce ta bankad'o gidan ta shigo, salati ta shiga jerawa.
"Safwan bawan Badiyya ka zama? ka fita ka nemo abinci, aikin gidanma sai ka taya ta? Dama ta cika mun gidannan da jikoki ai duk da sauk'i, yarinya ta hana ka sak'at da makirci irin namu na mata." Da Sauri Badiyya ta mik'e, tare da rik'e jakar ledar Innah.
"Sannu da xuwa Innanmu.kawo jakar in shigar miki da'ita." Fisge jakarta Inna ta yi tace.
"Ke zan ma sannu da xuwa dan ke ce bak'uwa, nan gidan d'anane." Tana kaiwa nan ta shige ciki ta barsu a wajan, Safwan ya kalli Badiyya wacce take ta faman aikin tsilalar da hawaye. Rungumeta yayi yana shafan bayanta cikin sigar rarrashi. Hannunta ya kamo su ka shiga matsakaicin falon na su, da hanzari Badiyya ta zame hannunta a na shi, ita ta soma isa wajan Innah.
"Ina wuni Inna ya hanya, ya aka baro mutanen Azare?" Babu yabo Babu fallasa Inna ta amsa mata. Mik'ewa ta yi dan kawo ruwa da abinci. Safwan kuma yana gefen Inna a zaune, yana gaisheta ta yashe baki da fara'a ta amsa.
"Baffan ka yana godiya da irin hidima da kake yi da su, Safwan ni dai kwanciyar hankalina shine ka komo gida, sannan ka yi aure, anan d'in koyarwa kake yi, a can ma akwai koyarwar, ni nafison ina ganinku a kusa dani. Ya batun bazawarar da kai mun maganar ta, kwanaki dana zo? na tafi cike da murna wallahi." Kai ya sosa yace.
"Yanxu maganar da mu ke yi da Badiyya kenan, akan gobe zata je da kanta da shawo mun kan Sadiyan." Had'e fuska Innah ta yi tace.
"Ni na shiga uku na da zancen Badiyya, dama fa kakarta ance mayya ce, yarinyar nan dai ni na ja ma kaina, tunda ni na had'a wannan aure na jaraba. Ni da kaina zanje gidan su Sadiyar mu yi magana da gyatumarta, ayi komai a gama, amma fa a