Showing 72001 words to 75000 words out of 92932 words

Chapter 25 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt

sa Mudi a idanuna ai bana ce ga ranar ba. Sai dai iyalan na shi na zuwa wajan ita gyatumar taku. Murmushi Safwan ya yi ya ce.
"Dama gidan Anty Saliha zai raka ni can Bauchi in gaishe ta, na jima ban je ba, sai in lek'a gidan Kawu Tanko, da gidan Goggo Ta sallah. Innah tace.
"Ka kuwa kyauta sosai, ka je ya na ta faman jiranka. Fita ya yi a d'akin tare da yi musu sallama, su kai mai fatan dawowa lafiya.
Yana fita tsakar gidan na su, matan yayyunshi maza su ka shiga tsokanar shi.
Ango ka sha k'amshi Angon Sadiya ba da kan ka a sare ka je gida ka ce ya fad'i. Dariya ya bi su da shi kawai ya dubi matar Babban wansu ya ce.
"Anty Jamila wai har da ke?" Dariyar dattijuwar ta yi tace.
"Ai dole a yi da ni Safwan, mu dai fatanmu Allah yasa Sadiya ta shekara da d'anta a gidannan" Baisan sanda ya ce da ita "Ameen" Ba. Sallama yai musu akan zai je Bauchi ya na dubo Anty Saliha.
Yana fita ya ci karo da Mudi a cikin motar shi k'irar ( Beetil ) Hajiya ba 🤭.. Tsaki ya ja ya ce.
"Kai tsiyata da kai ka fiye nawa, tun yaushe na ke jiranka a nan wajan. Dariya Safwan ya yi, motar ya bud'e ya shiga gidan gaba, Mudi ya ja motar su hau titi.
"Amma fa Safwan na yi farin cikin dawowarka Azare wallahi, kuma ina ta ya ka murnar wannan Aure da za ka yi, Allah ya sa ka na da rabon ganin d'anka kaima a duniya."
"Ameen Mudi, amma ni lafiyata k'alau Badiyya ce ba ta da lafiya, itace ba za ta haihu ba, gudun kar ta shiga tashin hankali. Sai na boye takaddar da likita ya ba mu, na sanar da'ita dukkanmu lafiya muke lokacine kawai." Mudi ya dubi Safwan ya ce.
"Aboki a gaskiya ka ko yi halacci sosai, ka kuma rufa mata asiri da ka rufe mata lalurarta. Gashi itama ta yi k'ok'ari wajan goyon bayanka dan ganin ka samu Sadiya"
"Kuma na yi alk'awarin Sadiya in ta haihu zan ba Badiyya yaron kyauta ya zama d'anta." Mudi ya dube shi ya ce.
"Nan fa d'aya kuma Safwan. kar ka raba uwa da mahaifiyarshi mana, yaranka dai kowa ya san na Badiyya ne, ai ba sai ka bata ba, gidanku fa d'aya." Idanu ya lumshe domun shi kan shi ya san ba lallai Sadiya ta bashi wannan goyon bayan ba, duba da yanda ya ga ta na da son yara, amma ya na son jarraba hakan. Dan ya warkar da mikin da ke cikin zuchiyar Badiyya na rashin haihuwa. Da wad'annan tunane tunanen su ka isa garin Bauchi. Da gidan Anty Saliha su ka soma.
"Ohh Mudi idanka kenan, kuma an shaida mun a garin Bauchi kamfanin da kake aiki ya ke, ai ko abinci ka rik'a zuwa ci." Kai Mudi ya sosa. Anty ayi hak'uri, da ke ba ko da yaushe na ke shigowa Bauchin ba, a Azare kamfanin ya ke, kamfanin shinkafa ne, toh store d'insu kuma a Bauchi ya ke, lokaci zuwa lokaci na ke b'ullowa Bauchi. Dariya ta yi ta ce.
"Ina Sabuwa matarka yaranta nawa yanxu?"
"Bakwai Anty. Babban yaron na mu ya na karatu a makarantar kwana ta takanikal sayins J s s 2.
"Ahh masha Allah shima Safwan Allah ya nu na mana lokacin da zai ga na shi jinin."
Da ameen su ka amsa dukka, sai yanzu ne hankalin Safwan ya koma kan son yara da zumud'in samun su. Bayan sun huta sun ci abinci ne Safwan ya ce.
"Anty na ji abun arziki na gudun mawarki, na gode sosai Allah ya k'ara bud'i. Anty tace
"Ameen babu komai sati mai zuwa ma zan tawo gidan ayi komai ina nan, Allah ya baka ikon zama adali a gare su."
Bayan sun tab'a hira kuma, sai su kai mata sallama, gidan kawu Tanko da Goggo Ta sallah, duk yayyen mahaifiyarsu ne suka wuce akayi zumunci."


Sadiya
wasa wasa yau saura sati guda bikina da Safwan. Yau sati biyu rabon da in sa shi a idanuna, yana Azare.
Na yi wani kyau wanda ko a aurena na fari banyi ba, dan na sha gyara sosai, magungunna kayan mata kuwa Goggo sai d'irka mun ta ke yi, da na yi magana sai ta ce wai kishiya gare ni, dole in gyara kaina.
Biki ya rage saura kwana biyu, bak'i fal gidanmu daga gari gari, daga dangin mahaifina Kawu da Anas ne kad'ai su ka samu halartar bikina, k'awayena 'yan amana sun zo daga gari gari suma, Hadiza 'yar mutan katsinawa tace."
"Toh Allah ya kawo mu a karo na biyu kuma na k'arshe da izinin Allah.
Haka dai k'awayena su kai ta zaulayata suna dariya, ni tsabar farin ciki fal zuchiyata ba na ko iya magana ma.
washe gari da misalin k'arfe biyun rana, bayan an sakko daga masallaci. aka d'aura aurena da Safwan. Dubban jama'a ne su ka shaida.
Da misalin hud'un yamma kuma dangin Safwan su ka shigo gidanmu da akwatunan lefe guda biyu, bayan an musu tarbar arziki sun ci abinci sun sha lemo, sai kuma aka d'au haramar tafiya da ni.
Abun mamaki neman hawaye na na yi na rasa saima farin ciki da ya mamayeni. Ni ba yarinya bace an dai yi mun nasiha a gurguje, k'awayena da su Goggo Hansatu su ka mara mun baya, ina hannun dangin Safwan.
Mota d'aya na shiga da dangin Safwan, ina jiyo ihun Haidar da na barshi a wajan Mama zuwa wani lokaci, in zo in tafi da shi.
Motocinmu sun harba kan titi sai lula gudu su ke yi.
Su Amina da mamanta kuwa tun safe su ka wuce Azare tare da motar kaya."
Tafiya mabud'in ilimi kenan. Tunda na ke ban tab'a zuwa Bauchi ba. Amma ga Aure zai kaini Azare.


Azare
D'akin amarya ya tsaru sai k'amshin d'akin amare ya ke zubawa, komai na cikin falon bak'ine da ash, cikin uwar d'akin kuma komai ash and red ne, iya tsaruwa d'akin yai kyau. Kuma 'yan danki sun samu tarba me kyau. kaji da lemon kwalba da masar Bauchi a ka tarbesu da shi, kuma dangin Safwan su suka ta ya su suka jera komai ras, musamman Anty Jamila da tai ruwa tai tsaki a cikin lamarin. Abun dai gwanin sha'awa.
A ranar kuma suma dangin Badiyya su ka zo na su jeren, komai sabo Safwan yai mata a mazaunin dannar k'irjinta, ya yi bajinta sosai, 'yan uwanta kuma su kai mata karo karo aka siya mata kayan aikace aikacen gida suma sababbi dal. Ko wanne d'aki ya yi kyau ainun. Shima Safwan ya gyara turakarshi sosai, ya saka gado Babba, da sib, sai doguwar kujera a falo, da labulaye kyawawa.
Badiyya ta na gida zazzab'i ya ka da ita, sai rawar d'ari ta ke yi, wani irin duhu take gani tsabar kishin Safwan da ya ke cin k'asan zuchiyarta.
Misalin k'arfe goma sha d'ayan dare, motocin amarya suka iso garin Azare. Masha Allah sun iso lafiya.


Sadiya
Ni dai sai rarraba idanu na ke yi a cikin mayafi, muryar Safwan na jiyo, ashe zugar motocin abokan ango na biye da mu a baya.
"Goggo ku rik'eta a hankali kar kui mun asara man." Goggo Ta sallah ta yi mai dak'uwa.
"Ungo na ka d'an nema" Murmushi na yi kawai. D'akin Innah a ka wuce da ni, ta sanya mun albarka da auran ma, sannan ta ce.
"Yaya Ta sallah ku kai d'iyata d'aki ta huta, zuwa gobe a zaga da'ita dan gidan akwai girma, kowa ya yi bacci an gaji." D'akko ni su ka yi zuwa b'arayina. Sai da na yi adda'a sannan na shiga, cikin sallama mu ka shiga d'akin, Goggo Ta sallah ta dank'ani a hannun Goggo Hansatu, su kai mana a huta gajiya.


Safwan
labarin rashin lafiyar Badiyya ya isar ma Safwan, babu shiri a daren ya nufi gidan su Badiyya, ana cikin cecekucen Safwan bai ma Badiyya adalciba ya fad'o tsakar gidan. Mata ya gani tuli guda a tsakar gidan, tsugunnawa ya yi ya gaishesu, sannan ya ce.
"Na zo duba jikin Badiyya ne, yanzu dawowarmu kenan na ji labarin rashin lafiyar tata, zan ga jikin nata, sai mu ta fi asibiti tun wuri."
Da hannu Maman Badiyya ta nuna mishi d'akin da ta ke a kwance, k'awayenta sai lallashinta su ke yi.
Da sallama ya kutsa kai cikin d'akin, idanu su ka had'a shi da Badiyya."






Mrs Bukhari ce
MRS BUKHARI
65-66










Idanu ya lumshe ganin yanda lokaci d'aya ta fige ta fad'a. Zama ya yi a bakin gadon da ta ke kwance. Bai ko kula da 'kawayenta da ke wajan ba, hannu ya sa ya jawota jikinshi. K'amshin turarenshi ta shak'a, a hankali ta shiga rera kukan da ya rasa ina zai tsoma ta, da d'aya da d'aya k'awayenta su ka watse tas, d'akin ya rage da ga Safwan sai Badiyya" Jikinta ya ji ya d'auki zafi rau.
"Ya salam haba Badiyya. yanzu abunda za ki yi mun kenan? kin sa k'afa kin shure alk'awarin da ki ka d'aukar mun, kan Aure na bazai zama abun d'aga hankalinki ba. Gashi ba'aje ko'ina ba kin yi ta kuka, har zazzab'i ya sauka miki." Hannu tasa ta k'ank'ameshi gam a jikinta, ahankali ta soma sassauta kukan na ta, shi kuma ya na ta aikin rarrashinta, tare da shafa bayanta, cikin shigar rarrashi, sai magana ya ke bata. Sai da ta tabbatar nutsuwarta ta dawo mata ta d'ago kanta hawaye cab'e cab'e.
"Safwan rayuwata amana ta ke a hannunka, ka yi k'ok'arin zamewa namiji d'an goyo da zani. Kar ka wulak'antani, kar ka ba da k'ofar da za'a wulakanta ni. Zuchiyata jaririyar zuchiyace, tattali da lallab'a kawai ta sani. Na san kai mun halacci da ka zauna da ni fin shekaru goma babu haihuwa, duk da irin gori da danginka su ke yi mun." Hannunshi ya sa ya rufe mata bakinta da shi, cikin mutuwar jiki ya ce.
"Badiyya kishi ne ya saki subda hawaye ko? Iya k'ok'ari kin yi, kuma na yaba. Ki sani k'arin auren da na yi ba ya nufin kin gaza ta ko ina. Wallahi na yi aure ne, dan buk'atar hakan ta taso mun, amma ki sani ke macece tamkar da dubu. Baki rageni da komai ba. Ba na son uwar gidana ta sake yin kuka, ki ta shi mu je asibiti."
"A'a Safwan Na warke, dama fargaba ce kawai ta haifar da zazzab'in Amma yanzu ka k'arfafa mun guiwata. Je kai kwamciyarka ka huta."
Cikin soyayya su kai sallama, kai tsaye d'akin zaure ya nufa. Mudi ne ya shiga da sallama, hannunshi rik'e da ledar kaji da shayi mai kauri a cikin k'aramar robar fenti.
"Safwan ga shi a kai ma amarya da k'awayenta." Ya na dariya ya amsa. A kunyace yai sallama b'arayin su Sadiya ya mik'a musu kajin. Hadiza ce ta amsa tace.
"Bari a kirawo ma Sadiyan."


Sadiya
Muna ta zabga hirar mu kamar ba dare ba, Hadiza ta shigo da ledar kaji da shayi. Da ta ajjiye tace.
"Sadiya ki je Safwan na son ganinki."
Duban ta na yi na ce
Ni wallahi Hadiza kunyar su Goggo na ke ji, kawai sai in wuce su?
"Munafuka, duk sun yi bacci tuni, ki tsallake su ki fice kawai.
Ahankali cikin sand'a na fice a d'akin.
A jingine na same shi a garu, da ganina ya zuba mun idanunshi masu karya mun kuzarina. Kallon da Safwan ya ke jifa na da shi na musamman ne, ni na fahimci in da kallon ya dosa."
Barka da dare angon Sadiya" Murmushi ya mun, yai k'asa da muryarshi kamar mai jin bacci yace."
"Barka da shigowa rayuwata Sadiya, barka da sabunta mun jini da kike k'ok'arin yi gobe uwar haka, ina miki barka da shigowa familyn Safwan Sales Gwarzo." murmushi kawai na bishi da shi.
Matsowa ya yi daf da ni, take numfashina na ji ya na katsewa, soma jawo shi da kyar na yi kamar wata mai ciwon asma. Hannayena ya kamo yana murzawa a hankali_ a hankali. D'umi da taushin hannunshi su ka sanya ni bisa wani yanayi na daban.
"Sadiya ki shirya amsar Baby na gobe, ki shirya jiyar da ni dad'inki, ina mararinki Sadiya. ki je ki kwanta, dan ki samu bacci har da na gobe."
Hannuna ya saki, ya soma ja da baya da baya. Ni kuma ina tsaye a wajan ya maishe ni tamkar poster, har sai da na ga k'ulewarshi, na sauke numfashin da na ja. Idanu na lumshe tare da shigewa ciki."
Washe gari aka shiga bud'ar kai. Eh lallai nasan na auri d'an dangi. Kuma abun sha'awar duk k'anne da yayyun Safwan kamanninsu d'aya, har da wad'anda ba ciki d'aya su ka fito ba. Anty Salaha ce ta shigo d'akina tare da Badiyya. Ina uwar d'aki da k'awayena su ka yo sallama.
"Anty Saliha kin dawo?" Murmushi ta yi mun
"Uwar gidan Safwan ce ta dawo da ni, ta na son ganinki tun jiya amma cunkoso ya hanata ganin naki.
Da kallo na bita, iya mace Badiyya ta kai mace, tsaiwar diri da cikar k'irji kawai zan nuna mata,farace sol. gata doguwa siririya. Ta sha kwalliya har da jan k'unshi ta yi shar tamkar amarya. Yak'en dole na yi mata.
"Barka da isowa uwar gida."
"Ke zan yi ma barka da zuwa, da fatan ba ki yi fishi da ni ba ko?" Da sauri na girgixa kai na, jikina ya mutu lakwas. dan ba haka na yi tsammanin ganin Badiyya ba. Katse mun tunani ta yi da cewa.
"Ga wannan babu yawa, tawa gudunmawar kenan" Laida ta mik'o mun cike. Hadiza ce ta amsa tare da yi mata godiya. Anty Saliha tace.
"Abincin k'awaye da aka aiko da shi, ita ta yi komai da komai." Godiya su Hadiza su ka shiga yi mata. Har suka juya ni dai na kasa d'auke idanuna akan Badiyya. Fargabace ta tasan mun. Gani nake Safwan ya Aure ni ne, kawai dan in haihu mishi, kuma sabida tausayin Haidar. Nan take damuwa ta shigeni.
Ina gani su Hadiza da su Goggo su ka had'a yana su yana su, Su ka wuce, Bayan sun zagaya da ni wajan matan yayyen Safwan maza, da ma sauran dangin nashi, Anty Saliha ita ta dinga yi mun bayanai dalla dalla. Ni ba gane komai da kowa na ke yi ba. Bayan tafiyar su Goggo. ina k'unshe a d'aki. Yayyen Safwan suna falo dank'am Har dare.
Da misalin k'arfe goman dare na jiyo Sallamar Safwan. Ajjiyar zuchiya na sauke. Amma abun mamaki sai na ji na shak'i k'amshin turaren da ban san Safwan da shi ba." Badiyya ce ashe, hannuna ta kamo, ni kuwa na biyota tamkar rak'umi da akala har zuwa falo.
Ita ce 'yar rakiyar Ango. Doguwar nasiha tai mana, tare da yi mana sallama.
Ta na fita Safwan ya matso jikina cikin zumud'i. Manna ni yayi a yalwataccen k'irjinshi. Idanu na lumshe hawaye su ka kwaranyo mun, bansan na fashe da kuka ba sai da na ji, labb'an Safwan a kan nawa, yana lallashina.
A daren babu wata hira data gudana a tsakanina da Safwan, bayan gabatar da nafila bisa koyarwar addini, sai kaza da madara da Safwan ya baje mana, ni tsabar sanyi jiki, madarar kawai na sha.
A cikin darennan Safwan ya raya sunna da ni, sai dai fa lallai na san na auri jarumi, awa guda Safwan ya yi a kaina. Sannan da komai ya lafa ya murgina yai bacci. Sambatun kalmar da Safwan ya dinga nanata mun ita ce ta sa ni na kwana cur ina kuka.
"Ki sama mun d'a Sadiya, zan baki Baby a cikin darennan, ki haifa mun kyawawan 'ya'ya." Sune kalmar da Safwan yai ta nanata mun, sai hud'un asuba bacci ya fisgeni, idanuna duk a kumbure. Sai ajjiyar zuchiya na ke saukewa a cikin baccin kamar k'aramar yarinyar da ta wuni kukan rigima.
"Sadiya Sadiya, uwar 'ya'yana, ki tashi ki yi sallah, shidda har da rabi."
A cikin mafarki nake jiyo sautin muryar Safwan ya na dukan dodon kunnena. A hankali na bud'e idanuna, banko kalli in da ya ke ba, sauka na yi akan gadon, tare da fita zuwa kitchen. Risho na kunna na d'aura ruwan zafi, wankan sallah na yi, tare da gargasa jikina.
Da sallama a bakina na shigo, ya na tsaye a gaban madubi, yana gyara tsaiwar hular shi."
"Kin fito uwar 'ya'yana?"
Eh. Kawai na iya ce mai.
"Bari in je in duba ya Badiyya ta kwana da jiki, ki jira ni kar ki yi kumallo, Innah zata aiko da shi." Fuskata ya shafa, ya fice.
Yuuu na bishi da idanuna da suka cika tab da hawaye, ina zubar da hawaye na yi sallah, bayan na idar zama na, na yi akan sallayar ina ta ragargazo adda'a tare da neman dacewar Aure.
Gidan na gyara ko ta ina, turaren wuta d'an tsinke 999 na kunna, ko ina ya d'auki k'amshi.
'yar kwalliya na yi a fuskata mara hayaniya. Shadda ce a jikina d'inkin doguwar riga ruwan goro. Mayafi na yafa, na fice zuwa cikin gidan."
d'akin Innah kawai na shiga, su Anty Saliha, da su Anty Murja duk su na nan, amma da halama shirin tafiya ma su ke yi. Farin cikinsu ya kasa b'oyuwa har akan fuskarsu, musamman Innah wacce ta rasa inda za ta tsoma ni. A kunyace na gaishe su dukka, kaina a k'asa. Cikin fara'a da zaulaya su ka amsa mun, Innah ta ce.
" 'Yannan na ji dad'in ganinki sosai, inai miki maraba da zuwa gidannan, dama yanzu mu ke shirin zuwa wajan na ki da su Murja da su ke shirin tafiya. Tunda kin shigo mu yi komai a nan, Bilkisu ga Sadiya, a yi mata nasiha, sannan ki fayyace mata waye mijinta a sauk'ak'e dan ta ji dad'in zama da shi cikin sauk'i, da ma abokiyar zaman na ta"




mrs Bukhari ce.


*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*








1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_


5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_




Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300


*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇


0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.


Domin tura shaidar biya👇


0810 433 5144


Masu tura katin MTN👇


0814 179 9224


Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇


0817 952 3215


Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f


*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨




Instagram links👇


https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=




Facbook group


https://facebook.com/groups/463653111781414/




Telegram links


https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk




*YADDA AKE BUƊE

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login