Showing 39001 words to 42000 words out of 92932 words
Chapter 14 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt
wani asibiti ba. Gargajiyar mu ta ishe mu. mutane nawa ne su ka kasa warkewa a asibiti, kuma su ka
warke a gargajiya."
SOKOTO GENERAL HOSPITAL
ba mu sha wata wahala ba, aka ba su Aliyu gado. shi ya na b'angaren maza, ita kuma tana b'angaren mata. Likocine a kansu duka, ana kan binciken gano kan matsalar dan maganceta. Ni kuma na kasa zaune na kasa tsaye. Ni ce a b'angaren mata, ni ce a b'angaren maza. Haka nai ta zurga zurga. likitan dake duba khadija ne ya soma fitowa. Binshi nayi, nace da Kamilu.
"Ka tsaya a k'ofar d'akin da Aliyu ya ke ciki, ko likitan zai buk'aci ganinka kafin in dawo.
A office na samu Dr yana rubuta wasu allurai da magunguna.
mik'o mun takaddar yayi.
"A gurguje, ga Allurai da magani ki je kantin maganin dake cikin asibitinnan sai ki siyo. ana buk'atarsu da gaggawa." Amsa nayi na fita. Ban samu magungunan a cikin asibitin ba, sai da nai doguwar tafiya. bayan na kawo ma Dr magungunan, da alluran, sai kuma na je na bud'e ma su fail a asibitin." Dawowata kenan. Dr ya fito daga d'akin da aka shiga da Aliyu. yace.
"D'aya ya biyo ni, d'aya ya zauna da shi.
Ni na bi Dr dan inaso sanin meke damun Aliyu.
"Madam da me k'aninki ya k'one, ruwan zafi ko mai? shiru na yi na wasu mintuna. Bayani na yi mishi Dalla dalla kan abinda ya haddasa wannan ciwon. Kai ya girgiza yace.
"Wala Allah ta yi cushe cushen magungunan da mata su ka saba yi da sunan maganin mata ne, shine ya haifar musu da wannan matsalar. Ya samu rauni da kyailewar fatar wajan, fatar da take ba abun kariya ta sab'ule, abune mai wahala ace, ko zai iya gamsar da mace, ko da zai yi d'in, zai zama very wick. But za mu d'aurashi akan magunguna na sha da shafawa. Sannan kuskurene, wannan garin maganin da aka barbad'a mishi, domun da ba dan kunyi sauri ba. infection zai iya shiga ciwon, ya iya haifar mai da daji. Zan baki ki je phamacy a siyo Allurai da magunguna, ki same ni a d'akin." Jikina a mace na fita, na sake shiga cikin gari na siyo magungunan da alluran na dawo.
Aliyu ya na kwance, amma idanunshi biyu. d'akine da ba'a cika barin mace ta shigo ba. domun maza ne a d'akin, yawanci masu d'auke da lalurar ciwon gaba ne, da masu infection, wasu ma harda robar fitsari a jikinsu. Naga Aliyu ma an sa mishi robar fitsari. Dr na kanshi.
ledar hannuna na mik'ama Dr.
gefen Aliyu na dawo. Hannuna ya rik'e dam a cikin nashi, bai ce komai ba sai ido da ya kafamun.
"Sannu da d'awainiya Sadiya, Allah ya saka miki da aikhairi." Kamilu ke magana. da ameen kawai na bishi.
Allurai aka ma Aliyu, sai magani da aka bashi na had'iya, kana Dr ya shafa mishi tobe.
"A lemo mishi Abinci, domun zuwa nan da wasu mintuna zai samu bacci." Kamilu ne ya mik'e ya ce.
"Bari in nemo maka abunda zaka ci ko" Na yi saurin cewa.
Bari in nemo mishi, zan dubo Khadija daga nan." Fita na yi daga d'akin na lek'a dakin da khadija take, a zaune na tarad da ita. Nose na d'aura mata ruwa na biyu.
"Sannu yaya jikin? Kau da kai ta yi tace.
"likitoci tun d'azu su ka ce a nemo mun abinda zan ci, sannan likita yace ya na son ganinku.
juyawa na yi na fita. tea da biredi kawai na iya samo musu. Akwai jerin masu sai da abinci ta waje, amma ban gamsu da tsabtar abuncin ba. Aliyu na soma kaima, na tsuguno daidai kunnenshi nace
"Zan je in zauna da khadija, ba daidai bane a barta ita d'aya, kuma likitanta ya na jirana. Sannan inaso in ta samu bacci zan d'an shiga cikin gari dan Allah." Hanuna ya rik'e gam yana girgiza mun kai.
"No Sadiya kasancewarki na k'aramun lafiya, ki je dai ki ga Dr ki dawo. Baxan jure rashin naki ba.
kan shi na shafa cikin sigar lallashi.
Toh na ji, bari in je in ga Dr din zan dawo.
Ahankali nake tafiya, harna fice a d'akin, dan na gaji sosai. wajan Dr'n khadija na isa.
"Dr gani, na shiga d'azu take fad'amun sak'onka. d'agowa yayi ya kalleni.
"Eh hakane, inaso in san meye abunda ya faru da ita? dan nasha samun ire iren casses d'innan. Yanzu haka a d'akin da take, akwai mata fin goma, masu d'auke da lalurarta. Sakamakon wata masifa da ta b'ullo na magungunan mata da ake ba ku ku dinga cusawa a gabanku, kuna kashe kanku da mazajen ku da magungunan da dayawa ba'asanma dame ake had'asu ba. wata baiwar Allah na ta ke d'akin jinyar take sanar dani, wai kashin raqumi ne ta cusa a al'aurarta ya haifar mata da mummunan matsala kwananta talatin a cikin asibitinnan tana jinye. Shima kuma mijin nata, yasha jinyarshi, dan gabanshi tsattsagewa yayi. Ya kamata fa ku hankalta da kyau mata.
Ajjiyar zuchiya na sauke, domun na gamsu da maganganun Dr, kuma ina tunanin abunda ya faru kenan da su Aliyun, dan ni a daren lafiya lau muka rabu.
Dr ayi ha'kuri, Amarya ce, wata k'ila tasha abunda yai mata yawa ne. yanzu haka mai gidan nata yana d'akin jinya a wannan asibitin. Amma wanne magunguna za'a d'aurata akai?
"mu na ta k'ok'arinmu dai a kwai tesses da mu ka yi, basu fito ba tukunna. An d'aurata akan magani, da mayukan shafawa, yanzu jinyar raunin da taji zata yi, dan raunin da yawa."
godiya nai ma likita. na koma wajan Aliyu.
Kawu da Anas na gani a d'akin, sunyi tsaye akan Aliyu sun balbaleshi da fad'a. Isowa ta wajan yasa, fad'an da kawu ya ke yi, ya dawo kaina. Har marina sai da kawu yayi, ya zageni ta uwa ta uba. Gefe na koma kaina a 'kasa ina shirgar Hawaye. Ala tilas su ka tursasama Aliyu sai ya tashi sun koma gida. Aliyu shi kuma yana ta k'ok'arin fahimtar da su Amma fur Kawu ya ki. Dole muka ne mi sallama, mu ka koma gida.
Goggo ta balbaleni da ruwan fad'a, ta uwa ta uba itama tai mun.
D'akinta ta buk'aci Aliyu ya koma da zama, khadija kuma mai dambu ta tafi da'ita jinya gida.
Magunguna kala kala na gargajiya ake ta d'irkama Aliyu. jama'ar k'auyannan sai tururuwar zuwa duba Aliyu su ke yi. Ni da Aliyu sai kallo, dan Goggo ta kafa ta tsare. Kullum wanzan yana zuwa duba lafiyar Aliyu. magunguna dai yana shansu sosai.
*BAYAN WATA D'AYA*
har zuwa lokacin Aliyu jinya ya ke yi, amma dai jiki da sauk'i ya na ta warkewa.
kamar kullum yauma ina zaune a gaban Aliyu Goggo bata nan, ta je dubo khadija. hannuna ya na cikin na Aliyu ina wasa da shi, shi kuma sai jawo ni jikinshi ya ke yi.
Ka yi hakankali, kar ka fama ciwonka fa." murmushi yai mun yace
"Ina kewarki ne sosai, kuma na yi na yi da Baba ta barni in koma d'akin ki, amma fur tak'i amincewa."
Tsoro take kar mu keb'e mu famo ciwon da rashin hak'uri. Inka warke ai shikenan. Amma ya kake jin jikin naka? yamutse fuska yayi, tare da yaye mun tsumman da Anas yake rufa mai. Babu laifi ciwon na warkewa, har ya soma b'awo b'awo. Kuma nima akwai had'i na musamman da na yi mishi, dan farfad'o mai da kuzarinshi, a islamic kemist na harhad'o gasu kamar haka.
man zaitun
man habbatus sauda
man tafarnuwa
man kwakwa
man rid'i
zuma farar sak'a
garin hulba
da man shi
sai garin b'aure
da
garin ruman
dukka na cak'ud'a waje guda, nake bashi babban cokali uku da safe kafin ya ci komai
maganine sadidan, wanda yake farfad'o da sha'awar d'a namiji, kuma ya ke k'ara masa lafiyar wajan, har da ma k'arfi.
masha Allah dan muna ganin canji, dan in ina tare da Aliyu, yana jin feelings, kuma yana nunawa, amma ba sosai ba. Babu wanda yasan wannan batun, wannan tsakaninmu ne kawai."
Gidan su Khadija
Goggo ce a zaune a falon mai dambu.
"Sai yaushe wai yarinyar nan zata koma d'akinta ne mai dambu? naga ai jikin fa da sauk'i, yaci ace ta koma ai ko? amma kin mun shiru sabida Allah fa."
mai dambu ta b'ata fuska tace.
"Toh Asabe, ki bari wannan yaro ya samu ya warke mana, ba gara tana gabana ina ganin komai ba. Kofa ta koma gidannan sai dai kawai ta yi zaman hak'uri, sabida yaronnan fanko ne."
wannan magana ta daki Goggo Asabe sosai, cikin zafi tace.
"Fanko fa ki ka ce mai dambu, har Aliyu ya kai matakin a soma yi mishi gori, sabida asirin jikin naki 'yar ya karye ko? Da kyau, ai na jima da gane duk take taken ki, nason ganin kin hana khadija komawa d'akinta. Da kyau Mai dambu, kuma kin ban mamaki, bayan da duk shawararki nayi amfani har kika jefa mu a cikin wannan halin shine yanzu kike son zuk'ewa .
mai dambu tace
"Amma Asabe ni kin ban mamaki ma da har kike tunanin wai khadija za ta komawa Aliyu. Tsakani da Allah auransu bazai ci gaba ba, mahaifinta ma haka yace. Babu fa iyayen da zasu amince akai 'yarsu, wajan mijin da bazai iya gamsar da ita ba. Ai aure baya yiwu ne sai da lafiya. Ina fatan Allah ya bashi lafiya, ita kuma Allah ya b'ullo mata da wani mijin, tunda itama tace bazata koma ba, babu mai yi mata dole kuma ehe"
"mai dambu kin cuceni, bazan fasa maimaita tsinuwa akan ki ba. kuma zaku gani, shi alhaki kuikuyo ne, sharri kuma d'an aike ne, duk daren dad'ewa zai dawo maka. Za'a aiko ma da khadija takaddarta."
"Asabe kenan har ya fad'amun sharri d'an aike ne? Ai ko yanzun ma aikenshi kika yi ya dawo miki, itama Sadiyan ai rai gareta. 'yar d'an uwanki baki ji kunyar cutar da'ita ba, sai khadija ce bazai cutar ba nan gaba, ai mugu shi yasan makwancin mugu.
Aranar dai saida Goggo Asabe su ka yi dambe da Mai dambu, suka tarama kansu jama'a da k'yar mak'ota da kishiyoyin mai dambu suka raba wannan dambe na aminai.
Fita Goggo ta yi ta na kuka, a b'arayin Goggo Safiya ta ya da zango.
Sadiya
ina jikin Aliyu mu na ta hirar mu abun sha'awa, kamar kar Goggo ta shigo haka mu ke ji.
Bakinshi ya danna a cikin nawa. tsotsa ya ke yi tamkar ya samu Alawa, gam ya rik'eni, kamar za'a kwace ni. Munfi minti goma a haka ni da Aliyu, sannan na samu na kwaci kaina da kyar.
Aliyu, tun jiya na ke son mu yi magana da kai, Amma ban samu damar hakan ba."
sake gyara mun zama yayi a gefenshi, muka sark'e hannayen mu a cikin na juna.
"Ina sauraron ki Sadiya ta, menene?"
Dama uhm juna biyu gareni. wata zabura Aliyu yayi, tare da sake damk'e hannuna.
"Da gaske ki ke yi Sadiya?"
Eh da gaske na ke yi, duk wani halamu sun nuna hakan, ga kasala, da yawan yin amai, kuma abu kad'an da na yi sai in ji duk na gaji."
Rumgumeni tsam Aliyu yayi a k'irjina, yana wani murna mara misaltuwa
"Sadiya nagode, Allah yai miki Albarka, yanzu nine na kusa zama Abba? Allah na gode ma daka azurta ni da samun rabo.
ni dai kaina na sunne a k'irjinshi, kunya na ta kamani.
d'agoni yayi, yana kallona.
"Me ki ke so in miki Sadiya?" Dubanshi nayi da kyau, duk ya wani rud'e sai lallab'ani ya ke yi."
Aliyu, so na ke yi, in dinga zuwa asibiti awo, sannan inaso in haihu a asibiti. Aliyu sannan dan Allah kar a kai yarona almajirci dan Allah.
hawaye na soma zubarwa, dan bazan iya haifar d'a a cikina akai mun wata uwa duniyar ba. bani da wannan juriyar d'a yafi gaban ai wasa da rayuwarshi. Sake rungumeni yayi yana rarrashina.
"ya isa Sadiya ki dena kukan haka. na miki alk'awarin zaki je asibiti, kuma zaki haihu a asibiti, dake da Babyn bazan so wani abun ya same ku ba. maganar Almajirci kuma, zan iya iya k'ok'arina, dan ganin yaranmu sun rayu a gabanmu. Sadiya ina samun lafiya zan bud'e makaranta. yarana a tsangaya ta za su yi karatun arabic d'insu. Kuma ina da tabbacin za ki koyar da su boko. uhm haba maman twins." Dariya muka yi. na sake mak'alk'ale mijina
mrs Bukhari ce
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
Instagram links👇
https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Facbook group
https://facebook.com/groups/463653111781414/
Telegram links
https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
[8/14, 8:36 PM] Badiat Ibrahim: G Z D
MRS BUKHARI
35~36
"Wai yaya Asabe, lafiya? tunda kika shigo ki ke ta runtuma kuka. Kuma naga jikin Aliyu ai da sauk'i sosai. Goggo Asabe tace.
"hmmm Safiya bari, mai dambu ce take so a raba Auran Aliyu da khadija, ki duba duk irin hidimta musu da Aliyu yayi, wanne irin so ne ban nuna ma khadija ba, dama ita kanta mai dambun? Har gori take yi, wai Aliyu bai da kuzarin iya gamsar da mace, Bacin duk khadijan ita ta jefa shi a cikin wannan kaddarar." mamaki ne ya kama Goggo Safiya ainun, domun in ba dan a bakin Goggo ta ji wannan labarin ba, toh da k'aryatawa za ta yi tsab."
"Yaya ita mai dambun ce ta ce hakan, ko kuwa har da mai gari?" majina Goggo ta share tace.
" mai dambu ta sanar dani, shima kanshi mai garin yace, Aba khadija takaddarta. duk irin kud'in da Aliyu ya narka ma khadija a lefenta. Sannan kuma fa, sun kwashe adakar baki d'aya." Goggo Safiya tace.
"Tunda haka su ka zaba, Yaya ni ina ganin a basu takaddar, tun kafin a yi rikici, kinsan mai dambu ba mutunci gareta ba."
"Ni babbar damuwata shine, Aliyu zai rayu ne a cikin damuwar rashin magaji, ko dad'in Aure d'and'anashi yayi kawai na d'an lokaci. Abun yana damuna Safiya. Duk da wanzan yana ta k'arfafa mana guiwa akan hakan"
Sun jima su na tattaunawa, sannan Goggo ta koma b'arayinta.
Sadiya
Da sauri na fita daga jikin Aliyu, zuwa can gefe in da na saba zama. Goggo ce ta shigo, duban Aliyu ta yi.
"Kai kuma lafiya kake dariya haka?" cewa yayi zauna Baba.
Xama Goggo ta yi kusanshi.
"Goggo Allah kenan mai k'arfin iko akan dukkan bawanshi, Allah ya k'addari zaki samu jika daga gareni." Sororo Goggo take kallonshi tace.
"Banfa gane komai ba." Hannunta ya kama yace
"Baba Allah ya axurta Sadiya da juna biyu." Da sauri nai k'asa da kaina. Ina sauraron shin wanne irin farin ciki Goggo zata bayyawa. Fashewar kukanta mu ka ji. Daga ni har Aliyu mun yi tunanin kukan farin ciki ne. Ashe sab'anin hakanne."Shikenan ta faru ta k'are, zamu sake cud'anya da Aisha ni Asabe, sai kuma yanda su ka yi da Aliyu." kuka ta ke yi sosai. mamakine ya cika ni, take wasu zafafan hawayen bak'in ciki su ka shiga sunturi a kumatuna, gashi na na kasa mik'ewa dan jikina har rawa ya ke yi, tsabar jin haushi. Aliyu kuwa ganin zubar hawayena, duk sai ya rud'e ya rasa wacce zai rarrasa a cikinmu, Yace"
"Baba mu fa muka yanke k'auna da samun rabon d'a, sakamakon abunda ya faru da ni, ni na zaci murna zaki yi Baba, a tunanina komai ya xo k'arshe." Tana kuka tace.
"Yanzu komai zai fara Aliyu, ita kanta Aisha sai da ta haifi Sadiya ne, boka ya bata nasarar raba mu da d'an uwanmu. Bazan zuba ido haka ta faru da ni ba. Bana farin ciki da samun juna biyun Sadiya, dan juna biyunnan barazana ce ta rasa gudan jinina." mik'ewa Goggo ta yi, tare da shiga cikin uwar d'aki, a bakin gado ta zauna, ta shiga tunanin meye mafita, mai dambu ce ta fad'o mata a rai, Amma sai ta tuna da irin yanda suka kashe baran baran, amma lallai ta k'udirin niyyar zubar ma da Sadiya cikin dake jikinta, ko kuma ta tilasta mishi ya sake ta. Tabawa k'awarta ce ta fad'o mata. wani murmushin mugunta ta saki."
Ni kuma, da kyar na samu na yunk'ura zuwa tsaye, dan duk wata lakar jikina, ta gaza ba ma jikina sapot d'in daya dace.
Aliyu ne ya kira sunana a hankali, sai da tsigar jikina ta tashi.
Ahankali na juyo ina kallonshi, shima a cikin tashin hankalin yake, idanuwanshi su na dab da su zubo da ruwa, sun kad'a sun yi jawur, tausayinshi ne ya kamani, duk ta dalilina ya kasa jituwa da mahaifiyarshi. Ina ganin barin gidannan shine A'ala a gareni.
"Sadiya ki yi hak'uri kinji, kar ki sama kanki wata damuwar kinga ba ke kad'ai bace." runtse idanuna na yi, nace.
Aliyu ka yi hak'uri bazan iya ci gaba da zama da kai a cikin wannan halin ba, Goggo bata sona, yau na sake gasgata cewar har abada baza ta soni ba, bazata amshi jika daga gare ni ba. tafiya zanyi."
A guje na fita a cikin d'akin. ina jiyo muryarshi da k'arfi yana kirana.
Da sauri Goggo ta fito daga d'aki, hawaye ta samu yana zubarwa. Tare da kung'urin tashi.
"Kar ka kuskura ka taka k'afarka daga cikin d'akinnan. Sabida k'anwar uwarka tana kuka shine kai ma kake ta ya ta ko shanyayye? Aliyu ka ji kunya wallahi. Ina saninka ya tafi ne? an gama birkita maka rayuwa da asiri, wama ya sani ko ba cikin ka bane ma, har kake wani b'are b'are. Toh babu inda zaka fita ka bita. Tafi ruwa gudu, ta kaima duk uban da zata kaima k'arata. Inji sammaci