Showing 84001 words to 87000 words out of 92932 words
Chapter 29 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt
Rannan na shi a mugun b'ace.
Gado aka ba ni, sauran abun da ya kamata a yi Safwan duk ya yi shi.
Ya na gefe na a zaune ya na mun sannu, wata nose na matse mun ruwan mamana, ni bana ma cikin haiyacina sam.
Tuni Safwan ya dena fishi da ni ya shiga yi mun sannu cikin tausayawa. Sannun Innah kawai na ke amsawa.
Magunguna aka ba ni da allurai, da yamma a ka sallame ni.
Mu na zuwa gida na tarad Goggo Hansatu ta zo. Duk hankalin Safwan ya bi ya tashi ainun.
"Sadiya ni na zo banga jaririn ma da ki ka haifa ba, ciwon nonon nan ya sa na sha'afa."
Cikin juyayin me zan ce ma Goggo Hansatu na ke, ina ganin kamar za mu daidaita da Safwan ya mai do mun da d'ana. Dabara ta fad'o mun na ce mata."
"Sabida maman nawa ya gurb'ace ga ciwo kuma, shine Badiyya ta taimaka mun da shayar da Jaririn, mu je ki ganshi ya na wajanta." Duk wannan maganganun da na ke yi cikin dariyar yak'e nake yi.
Idanu Goggo Hansatu ta zuba mun kawai ta yi murmushi.
"Sadiya ta yaro kyau ta ke yi ba ta k'arko. Ni uwarki ce, bazaki tab'a ninkeni bai_bai ba. Ki sanar da ni kawai me ke faruwa?"
Safwan
"Innah ki dena maganar saki dan Allah ni fa ina son matata gaskiya."
"Sai in tsine maka wallahi akan Sadiya. Ka rubuta mata takaddarta yanzu kafin ka bar d'akinnan, ka je can ka zauna da matarka Badiyya wacce ta nifi daraja, da k'arfin fad'a ka ji. In ka yi wata magana anan falon Allah ya isa nonona da ka sha, ka rubuta mata takaddarta."
Safwan gigicewa ya yi sai ambaton Allah kawai ya ke yi, yanason yai ma Innah magana, amma ta riga da ta d'aure shi da jijiyoyin jikinshi, ta kafa mai dokar da ko hauka ya ke yi bai isa ya tsallake ba."
_"Ni Safwan na saki matata Sadiya saki d'aya."_
Abunda ya rubuta a takaddar kenan mai kunshe da rubutu rabin layi. Sai sa hannu daga k'asa."
A gaban Innah ya ajjiye takaddar ya fita fuuuu, Turakar shi ya shige ya kulle k'ofar shi. Yana tunanin fuskar Sadiya, tare da auna sonta a sikelilin zuchiyarshi, tana da babban keji mai girma a rayuwarshi. Ta ya zai ko yi rayuwa kuma ba tare da Sadiya ba, sannan ya zai yi da nauyin sonta. Cikin dakiyar zuchiya ya busar da iskar bakin shi, tare da zama a bakin gadonshi."
"Itama ba sona ta ke yi ba. Tunda da Aure na a kanta ta na beken mijinta na da matacce ma." K'ut ya had'ye wani curi mai zafi daga mak'ogorinshi zuwa cikin shi. Gani ya ke yi abun kamar almara, wai shine ya saki Sadiya yau, da hannunshi ya rubuta takaddar sakin nata"
kwanciya ya yi a kan gado tare da lumshe idanunshi. Zazzab'ine ya saukar mishi bai mugun zafi, take ya soma jin d'ari. Bargo ya jawo ya lullub'a, hak'oranshi sai kakkarwa su ke yi."
Sadiya
Da hawaye shab'e_shab'e a kumatuka na kamar wata k'aramar yarinya, na ba Goggo Hansatu labarin abunda ke faruwa."
"Hmmm Sadiya rayuwarki cike da ke da k'addarori masu girma da tayar da hankali. Amma shawarata a gareki shine in za ki iya zaman hak'uri da Safwan toh, in kuma ba zaki iya ba, sai ki sanar da shi ya sauwak'e miki.
Amma gaskiya abunda ya aikata zalunci ne, kuma zan fad'a miki gaskiya ba sonki ya ke yi ba. Bazan so in ganki a cikin damuwa ba, kuma bazan saki a cikin damuwa da kaina ba. Amma ki san meye matsayinki taka mai_mai a wajan Safwan mata, ko Baby Mama? Domun duk wanda zai kalli wannan lamarin dole kan shi ya d'aure sosai." Ni dai kuka kawai na ke yi, kuma na fi gamsuwa da Baby mama Safwan ya d'auke ni, ba sona ya ke yi ba tun farko."
Innah ce tai sallama tare da shigowa hannunta rik'e da takaddar da ganinta ya fad'armun da gaba, jiki a mace ta ce."
"Hansatu, ke da Sadiya ku yi hak'uri da abunda na zo muku da shi, a nawa ganin hakan shine maslaha. Wannan takaddar sakin Sadiya ce, da na tursasa Safwan ya sake ta, bisa sharad'in in bai sake ta ba, saina tsine mishi. Ga takadda ya rubuta. Hansatu inaso Sadiya tai nisa sosai, ta yanda Safwan ba zai ganta ba sai nan da wasu shekaru, inaso ya san mahimmancin Sadiya a rayuwarshine, inaso ya san amfaninta, ya kuma reni sonta, yayi begenta, har da damuwar rashinta kusa da shi."
Sadiya ki yi hak'uri inason in kwatar miki 'yancinki ne a wajan Safwan."
Mrs Bukhari ce
MRS BUKHARI
79/80
KATSINA/JIBIYA:
(Asalin Jibia ya samo asaline tun lokacin yaƙin cin nasara da Sarakunan Katsinq su ka yi, inda su ka yi hijirar maraɗi da Katsina kan yanki da addini, musamman bayan jihadin Usman Bin Fodiyo)
Gari ne mai cuɗanyar ƙabulu, Fulani da buzayen da yunwa ke fito da su daga Niger, da ma hausawa mazauna wajan. A garin jibia babbar budar da ta raba Niger da Najeria take.
Da misalin ƙarfe shida na yamma mu ka shiga cikin garin jibiya, sau uku na taɓa biyo Mama mu ka tawo ziyarar danginta da su ka kasance Fulani mazauna Jibia.
Da sallama mu ka shiga Family House ɗin su Mama.
Gidan gandu ne tabkeken gaske mai ɗauke da sashe daban daban, Dangine masu matuƙar son zumunci da soyayyar juna a tsakani.
Jama'ar gidan sai murna su ke yi da ganinmu, a ɓarayin matan asalin mai gidan mu ka sauka, Kakan su Mama, shi ya haifi mahaifiyarsu. wanda ya jima da rasuwa, ya bar mata huɗu da tarin yara maza da mata wanda za su kai arba'in. Daga baya matan da ya bari duk suma su ka shuɗe. Yaran mazan gidan su ke riƙe da gida, suna zaune tare da iyalansu.
D'akin Kawu Shafi'i mu sauka, wanda ya kasance wa ga su Mama na huɗu. Matanshi uku, yara kuma yanzu ba na ce ga yawan su ba.
Da fara'a uwar gidan Kawu Shafi'i ta tarbemu, dawo ta kawo mana da ruwa.
Kafin ta dawo ta zauna.
"Hansatu saduwa ta yi wuya, zumunci sai ja baya ya ke yi, dama kawun naku kuwa ya ke magana akan zai tura Saminu ya bi kan dangi duk a harhad'o zuwa babbar sallah za'ayi taro kamar yanda ake gudanarwa a baya. Dan gudun sake taɓarɓarewar zumunci. Ina su Aisha, har yanzu Aisha ta na zaune ba aure ko? Ke ma Hansatu kin ƙi aure, shi fa rayuwar duniya ɗan haƙurine, gashi mu muna ta turawa, da daɗi ba daɗi ana ta tafiya, kafin mu tunkuyi ƙasa kuma. " Hawayen da ya taru a gurbin idanunta ta sharce tace.
" wacece wannan kuma Hansatu?" kafin Goggo ta bata amsa, Kishiyoyin Goggo Kulu su ka shigo.
"Hansatu yau a gari in ji maƙi baƙo? In ji daya daga cikin matan da na ji Goggo Hansatu ta kirata da suna Goggo Fatima.
Nan aka shiga gaisuwa tare da hirarrakin yaushe gamo. Da ɗaya da ɗaya sai da matan gidan su ka cika falon Goggo Kulu tab, sai gaisuwar yaushe gamo su ke yi, ni dai da ido na ke bin kowa, domun wasu na gane su wasu kuma ban gane su ba sam.
"Hansatu amma za ki bar mun Sadiya da Haidar a nan ko? Domun a zaga da ita cikin dangi tasan lallai ita ƴar gatan dangi ce." Goggo Hansatu ta ce.
"Ai Goggo Kulu zaman Sadiya ya dawo Jibiya ina fatan ta samu wani daga cikin dangi, ayi tuwona maina da shi, Allah ya kawo mutuwar aurenta, Mijinta na farko ɗan Asabe ta aura, Yar mahaifinta, sai Allah yai mashi rasuwa, sai kuma ta yi wani auren dai na rashin soyayya a Azare, kina ji ko Goggo Kulu? " Goggo Kulu tace.
" Uhm ina jinki Hansatuwa.
"Yaronnan rimi rimi kamar abun arziki ya nuna ya na son yarinyar nan, ashe in faɗa miki shigo_shigo ba zurfi yai mata, ba sonta ya ke yi ba. Aure shekara guda bai cika ba. Auranta ya yi dan ta dinga haihuwar mishi yara, yana ƙwacewa yana ba uwar gidan shi. Kinganta nan yanzu haka jego take yi, kwananta uku da haihuwa, ya ƙwace Jaririn ya ba uwar gidan wai ta shayar da shi, gashi ita ciwon mama ya rabke ta. " Goggo Kulu sai girgiza kai ta ke yi ta na faɗin" Ashsha" Sannan ta ce.
"Bayan duk wannan zalunci da yaima marainiyar yarinyar nan shine ya biyo ta da saki, yanzu Jaririn a Azare ku ka baro shi? " Kuka ne ya ci ƙarfina, dan ba na ko ƙaunar in ji ana batun Jaririna, ni ƙaɗai na san halin da na ke sake faɗawa in aka yi maganar Safwan da Jaririna. Ni dai bazan yafe cutarwar da Safwan yai mun ba. Goggo Hansatu tace.
"gyatumarshi ita ta ƙarɓo ma Sadiya takaddarta, dan ta lura amfani da Sadiya kawai ɗanta zai yi. Tana so Safwan ɗin ya san mahimmancin Sadiya, da kuma iriyar asarar daya tabka wajan rabuwa da itan, har kuɗi ta ɗauko ta ba Sadiyan dan dai duk ta rage mata zafin zuchiyar da ɗanta ya haddasa mata. Na ga ƙoƙarinta kuma rabuwar auren shine maslaha, dan zaman ba zai sake yin kyau ba. " Goggo Kulu ta dube ni tace.
" Sadiya ki dena kuka, rayuwarmu mu mata cike take da tarin ƙalubale da karakaina, abunda zan jaddada miki kuwa shine ki tsare mutumcinki da kimar ki, kinsan al'ummarmu su nai ma Zawara wani kallo wanda bai dace ba, amma in ki ka riƙe darajarki ta ƴa mace sai ki fi budurwar da bata taɓayin aure ba daraja. Ɗauki jakarki ku shiga ɗaki ke da Haidar, ƴar uwarki ta na wajan aiki, itama auren ya ƙare kusan shekara biyu kenan mace macen auren yai yawa, ki rasa ta ina ake samun ɓarakar, tunda za ki ga ko wanne ɓangaren da na shi irin laifin.
Da sallama ya shigo cikin ɗakin, cike da fara, a ya ce.
"Goggo aka ce mun kun zo, wallahi ni na zaci wasa ne. Zama yayi a ƙasa kusa da ƙafar Goggo.
"Ina wuni Goggo, ya hanya, ya kuma aka baro mutanen kano? Goggo cikin fara'a tace
"Iko sai Allah Sauban ka na duniya, kai dai sai in an zo Jibiya ake iya ganinka, sam baka sada zumunci. Goggo Kulu tace.
"Mutanen Katsina da dutsen ma, suma kullum ƙarafinsu akan shi su ke yi, baya son zumunci, ga shi yaƙi aure Hansatu, duk matar da aka kawo mishi sai ya ce bai so, an taɓa yin haka? Dan matarka Allah ya yi mata rasuwa, shikenan sai ba za ka ƙara aure ba. " kai ya so sa, yace.
" Komai lokacine Iya da zaran lokacin yayi za'ayine. Akwai wata yarinya da na soma ne ma, amma ba mu gama daidaita kan mu bane tukunna. Goggo Hansatu tace.
"Ai ya kamata ayi a gama komai, kaiba yaro ba, ka doshi shekaru hamsin fa. Goggo Kulu tace.
"Hamsin ɗin zai cika zuwa jibinnan fa. Ka shiga ciki ƴar uwarka na ciki, Sadiya yarinyar Babarku Aisha. Baki ya washe yace.
"Allah sarki da'ita aka zo kenan? An soma kiran sallah bari in na fito masallaci zan zo mu yi hirar zumunci. Baba ma ya dawo, ya na ƙofar gida. "
A tsanake ya fita a cikin ɗakin, mu ma muka shiga yin alwala dan gabatar da sallar magriba.
Abinci kuwa haka a kai ta shigo da shi, har daga maƙota, k'auye akwaisu da karamci da girmama baƙo. Sai da na yi sallar isha sannan na fito falon inda na jiyo muryar Kawu Shafi'u suna ta hira da Goggo Hansatu. Tsugunnawa na yi a gefe na gaishe shi kaina a sunkuye. Cikin kulawa da washe baki mu ka gaisa, Haidar kuma ya je ya ɗale ƙafarshi kamar ya san shi.
"Sadiya na ji duk abinda ya faru, Hansatu ta yi mun bayanin komai, ki yi haƙuri ki kuma cire damuwa a ranki, ki shinfiɗa sabuwar rayuwa, gobe Sauban zai kai ki asibiti a sake duba lafiyar mamanki da ya ke yi miki ciwo, in kika samu lafiya kuma, saina nemo miki aiki, me kika karanta a kiwon lafiyan? Kaina na sunne nace.
Ɓangaren Anguwar zoma na karanta Baba.
"Toh babu damuwa akwai asibitin gwamnati zan nema miki gurbi, ƴar uwar ta ki ma Mai sunan kyatumarki Aisha, ita ma a asibitin take aiki, amma ita tana ɓangaren masu ba da kati ne. " Da sallama ta shigo, da gani a gajiye take. Kawu ya ce.
" Kinga ƴar halak, Aisha kin dawo?" murnar ganimu ce ta hana ta amsa maganar Kawu, rungumeni ta yi, ta na dariya, sannan ta koma wajan Goggo ta rungumeta.
"Goggo kune a Jibiya da Sadiya? Ikon Allah, rabona da Sadiya ya jima sosai. Sauban ne ya shigo da sallama, ɗagowa na yi mu ka haɗa idanu, dariya na yi mishi, shima fuskarshi ƙunshe da murmushi yace.
"Sadiya idanunki kenan, kin maƙale a Kano abunki. Kunzo lafiya? "
Lafiya lau Yaya, mun same ku lafiya?
" Lafiya lau Sadiya, wannan baturen sojan na wajenki ne? " murmushi kawai na yi, Goggo ce ta amsa mishi.
Aisha ta ce
" Sadiya ta so mu shiga daga ciki mu sha hirarmu. Sauban yace.
"Kaji ƴar son kai ko Baba, wai su shige daga ciki. Ina ta zauna mu yi hirarmu anan dukka.
Kawu dai sai dariya ya ke binmu da shi, ficewa ya yi abunshi, Goggo Kulu ta bishi zuwa turakar shi. Goggo Hansatu kuma ta shige cikin ɗakin da ya ke kallon inda na shiga ɗazu.
Nan hira ta ɓalle a tsakanimu, tare muka ci abinci a kwano ɗaya ma, mun jima muna hira kafin mu ka tafi kwanciya.
Ni da Aisha sabuwar hira mu ka ɓalle, har bacci yai awon gaba da ita. Ni kuwa sai juye juye kawai na ke yi, tunanin Jaririna wanda naima kallo ɗaya na ke ta faman yi, duk yanda na kai da son yakice tunanin amma ina abun ya ci tura. Sai da na yi kuka ma'ishina sannan na yi bacci?
Mrs Bukhari ce
MRS BUKHARI
81/82
Washe gari da safe, Aisha ce ta dinga zagaye da ni a cikin gidan, ɗaki ɗakin kawunan Mama manya da ƙanana, tare da iyalansu. Na ji zuchiyata ta yi mun sawai, kasancewar yanda dangin mahaifiyata su ke ta yin nan nan da ni, barin ba Yaya Sauban, da Yaya Saminu. Haidar ma ya samu gata a cikin dangina, dan babu wanda ya nuna mishi kyama a matsayinshi na zabiya. Kwanan Goggo Hansatu bakwai ta koma Kano. Goggo Kulu mata mai karamci, itace tsaye a kaina wajan ganin na gudanar da jego mai kyau da gata, Yaya Sauban kuma, kullum sai ya shigo mun da balango mai ruwa ruwa na ci. Haka na ci gaba da jegona cikin kulawa, mamana tuni ya warke, watsi na yi da tunanin Safwan da Jaririna da ban ma san sunanshi ba yanzu.
Cikin kwanciyar hankali na ke sosai, bayan na kammala jego na tas, Kawu ya sa Yaya Sauban zagayawa da ni danginmu na dutsen ma da manunfashi.
Munyi ziraya mun dawo, Kawu ya naima mun gurbin aiki a asibitin gwamnati, mu na tafiya tare da Aisha.
A yanzu ba ni da wata matsala, aikina kawai na ba ma hankalina, sai Haidar da na ke ba shi dukkan wani kulawa.
Makarantar gwamnati ya ci gaba da zuwa kamar yanda sauran yaran gidan su ke zuwa. Sai Islamiyya mai kyau da na sanyashi. Yaya Sauban yana ta nuna mun so, amma ni na yi kamar ma bansan me ya ke nufi ba, har yanzu dai ya kasa sanar mun, bana fatan ya fallasamun sirrin zuchiyarshi sam, domun ba zai samu so daga gare ni ba. A haka rayuwa tai ta garawa har tsawon shekaru.
A cikin shekaru biyar abubbuwa da dama sun faru, na asarar rayuka, da kuma samun ƙaruwar haife haife, aure aure, da ma mace macen aure.
A halin yanzu Mama ta san halin da na ke ciki, ta na yawan kawo mana ziyara.
Haidar yanzu ya na karatu a makarantar gwamnati ta bai ɗaya ta Unity dake malumfashi. Yana ajin farko a sakandare.
A lokacin manaima sun yi mun mugun ca, manya mutane masu ji da mulki da kuɗi, amma ni fur na kasa sakin jikima da su.
Shekaruna sun ja, kasancewata ƴar boko da gaye kuma, baza ka ce na manyanta ba, fatata ta sake wani murjewa da gogewa, na zama babbar mace sosai, kullum a cikin gyaran jiki da gashi na ke.
Mama na kwance ta na wata iriyar jinya mai tsananin gaske, haka dole na baro Jibiya na dawo Kano jinyar Mama, anan Goggo Hansatu ta ke sanar mun irin ɗawainiyoyin da Safwan ya dinga yi da Mama, da duba ta da ya ke zuwa yi a kai a kai, Innah ma ta yi ƙoƙari wajan yin zumunci da dangina.
Goggo da ma Safwan ya na zuwa, shine ba ku taɓa sanar da ni ba? " Goggo ta ce.
" Sadiya ho, mu sabida gudun fama miki ne yasa ba wanda ya sake yi miki zancan Safwan, amma har matar shi tana zuwa kawo ziyara danginki, da yaronsu Adam ɗan gayu. Da mamaki na ce.
"Haihuwa Badiyyan ta yi ne? " Goggo ta ce.
" Jaririnki dai da Safwan ya ƙwace ya bata, baki ga son da take yi ma yaron ba wallahi, yaro ɗan gata gaba da baya. Yanzu haka ba dan sabida yana jigilar kai Innarshi Asibiti ba lafiya itama, amma da yau juma'a za ki gansu sun zo a motarsu, tare da kayan tsaraba iri iri, Sadiya ya kamata ki yafe ma Safwan, sai daga baya ya soma bani tausayi, domun a halin yanzu Safwan ya na buƙatarki a cikin rayuwarshi, kuma ya gane mahimmancinki kamar yanda mahaifiyarshi ta so. Kuma ya ba yaronki Adam duk wani gata da kulawa, ita kanta Badiyyan ta yi matuƙar ƙoƙari gaskiya.
Ni dai na kasa cewa komai, zuchiyata ce tai wani irin duhu da na tuno Jaririna wanda bai san wacece ni ba, Ashe sunan Babane da shi. Safwan na shiga tunowa da irin rayuwar da mu ka yi a baya.
Ɗaki na shiga, nan na shiga zurfin tunani, ni kaina ina da nawa