Showing 87001 words to 90000 words out of 92932 words

Chapter 30 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt

laifin da na kasa rungumar ƙaddarata, kuma banso Innah ta sa Safwan ya sake ni ba, naso dai a dawo mun da Jaririnane kawai. Haƙiƙa, abunda haƙuri bai baka ba rashin shi bazai baka ba, ko ba komai da zan rayu da ɗana, ina kallonshi ina jin sanyi, amma haka na tsallake na barshi a tsunman goyo, da na zauna ko babu komai kullum da zan ganshi, tunda ba gida daban daban muke ba.
Zuchiya kenan mai ingiza mutum a cikin kogin aikin dana sani, kaita nutson da baka da wata madafa balle ka dafa ka fito, daga ƙarshe ciwon zuchiya ko hawan jini yai sanadinka.
Take hankalina ya karkata wajan Safwan da ɗana, tare da kwaɗayin son ganinsu ko da sau ɗaya ne, dan yanzu kam nasan na yi ma Safwan tsufa. A haka na kwana cur a cikin tunani, har zuwa washe gari da na tashi sukuku, ina ta so Goggo Hansatu ta sake yi mun zancan Safwan, ko zan samu damar jin labarin Jaririna, amma Goggo bata sake yi mun ba sam.
Wata ranar asabar, ina tsakar gida, ina wanke kayan Mama, kamar daga sama na jiyo sallama da zazzaƙar muryar da bazata taɓa gogewa a kaina ba, ƙamshin turerenshi na asali ya kaima hancina ziyara, ƙwabƙwab na jiyo takun takalman shi sau ciki, a hankali na saki wankin da na ke, na ɗago kaina, daidai Safwan yana leƙen fuskata dan son tabbatar da wacece ɗin a zahiri, wani irin nunfashi ya zuƙa tare da kafe ni da dattijan idanunshi masu burge wanda ake kallo. Safwan ya zama babban mutum, girma ya kamashi, ya zama wani irin wayayyen ɗan gaye, mai cike da haiba da kamala irinta dattijan asali, har wani haske ya kuma yi, ga key ɗin mota yana reto a yatsan hannunshi. Shima idanu ya kafa mini tamkar zai cinyeni, sai ajjiyar zuchiya ya ke ta saukewa a jere, sai dai fuskarshi a tamke babu walwala, hakanne ya kashe mun jiki sosai. Sallamar Badiyya, da wani kyakkyawan yaro ne ya dawo dani daga kallon Safwan da na ke yi, basarwa na yi, har ina wani yamutse fuska. Duban Badiyya na yi, wacce ta yi kyau farinta da kyanta ya kuma fitowa, tana sanye da tsadaddun kaya na mutunci, hannunta riƙe da Adam, wanda shima kallo guda na yi mishi na watsar, wankina na ci gaba dayi, amma a baɗini, zuchiyata sai tsalle ta ke yi, a ƙoƙarinta na son tona mun asirin tsohon son Safwan daya tashi a zuchiyata, wani kishinshi ne ya tokari zuchiyata, a yanzu na gane kuskuren barin Safwan da na yi tsawon shekaru.
"Sadiya, Maman ta na ciki kuwa?. Safwan ne yai magana da dattijuwar muryarshi. " kafin in ce wani abun, Goggo Hansatu ta fito, ganinsu Safwan yasa ta shiga washe baki, tare da tsokanar Adam.
" Ga mai gidana oyoyo, kazo duba matar taka ko? " Shigewa ciki Safwan yayi kamar gidansu, Badiyya kuma a ɗarare tace.
" Sadiya barka da zuwa mutanen jibia, kwana da yawa" Banko ɗago na dubeta ba nace
Yauwa barkan ku da zuwa" Daga haka na tsame hannuna a wankin na shige daki, Badiyya kuma ta shige ɗakin Mama. " Kuka na rushe da shi a tsakiyar ɗakina, ciwon son Safwan na taɓa duk wani rassa na jikina, son kasancewa da Yarona ya shigeni, yaron farat ɗaya ya shiga raina, abunka da Ɗa da Uwa. Zama na yi a bakin gadona, na dafe kaina kawai, na rasa shin wanne irin tunani ya dace ace na yi ne ma, dan na shiga wani irin damuwa ainun, ga Safwan ko a fuska bai nuna ya damu da ganina ba, ko fara'a ya kasa. Kiran da Goggo ta shiga kwaɗamun ne ya dawo da ni daga tunanin da na ke, labulen ɗakin nawa ta yaye, sannan ta shigo, zama ta yi a kusa da ni.
"Sadiya, ki saki jikinki da Safwan, har yanzu yana sonki, baki ga wata fara'a da ya ke ta yi ba. In ya buƙaci yana son magana da ke, karki musa, ki je ki saurareshi, in bai nema ba ki riƙe kanki karki bari ya gane kin damu da shi, tashi kije ku gaisa, kar matarshi ta ga kamar kishi kike yi. " Bance komai ba, na miƙe na bi bayanta zuwa ɗakin Mama.
Da idanu ya bini harna nemi waje na zauna, kallon Adam na yi na ce.
" Zo ubana taho" Bai yi musu ba ya taso daga cinyar Safwan zuwa tawa cinyar, lumshe idanu na yi ina jin son yarona na daɗa shigata, a halin yanzu ji na ke yi mai raba ni da ɗana sai dai Allah.
Safwan ina yini, ya bayan rabuwa, ina su Innah da su Anty Jamila da Anty Zulai? " murmushi ya sakarmun mai birgewa yace.
" Lafiya lau Sadiya, ina Haidar ɗina ya girma ko, yanzu ajinshi nawa? " na nisa nace
Ajin farko a sakandare, yana malunfashi makarantar kwana, gobe ma zan je in dawo dashi za su yi hutu." Kai ya girgiza yace.
"Na yi kewar Haidar sosai, goben zan zo sai mu je tare mu dawo da shi, sai mu je da Adam, shima ya miki hutu tunda kina nan. Satar kallon Badiyya nayi ko zan ga sauyin fuskarta. Amma ina sai murmushinta data sake fad'ad'awa" Na ji daɗi sosai da zai bar mun Adam yai mun hutu a wajena, gashi hutune mai dogon zango na karshen shekara. Badiyya tace
" Ina yini Sadiya, ya jikin Mama kuma? " Daurewa na yi na dubeta ina jin kishinta na taso mun nace.
" Lafiya lau Badiyya ya gidan, sannu da ƙoƙarin raino fa an gode, Adam ya girma. " murmushi kawai ta yi mun, abinci da ruwa aka kawo musu, ni kuma na ja Adam zuwa ɗakina, sai hira ya ke yi mun, Adam yarone mai ɗan karen surutu da kuma saurin sabo, Nima jiki na sake da shi inata biye ma surutan shi, ina ta dariya. Sai da yamma lis su ka fito, fitowa na yi cikin kwalliya da ƙamshi, kwalliyar da na tabbatar zata tafi da hankalin Safwan dan nasan abunda ya ke so. Bina da ido kawai ya ke ta yi.
Da Adam ɗin za ku tafi, sai goben ku dawo ko zaku barshi anan ne? "Safwan ya ce, zai zauna anan, ai dole a garin Kano za mu kwana, Zanje in kai Badiyya gidan ƙawarta ne, acan zata kwana, ni kuma zan kwana a zangon baƙi, da daddare zan zo sai mu tsara yanda za mu yi tafiyar." Cikin kashe murya na ce da shi.
Toh babu damuwa, sai ka dawo, Badiyya sai anjima. Sallama mu ka yi su ka fice, Safwan ya waigo ya sake dubana ya sakarmun tattausan murmushi, bai dai ce mun komai ba.
Adam kuwa ya saki jiki sosai, dama ya saba da ganin su Mama, duk inda ya wulga da ido nake kallonshi kawai. Bayan sallar isha, Goggo Hansatu tace.
"Sadiya ki tashi ki je ki sabunta wanka, ƙila Safwan ya na hanyar zuwa, wannan damace kika samu, ki tabbatar kun sasanta kan ku a kan hanyar tafiyarku, tunda kun samu keɓewa. Nace.
"Mu da za mu bi motar haya Goggo wani hirane? " sororo Goggo ta dube ni tace.
" Motar Haya kuma? Ai Safwan ya jima da siyan mota, aikin kamfani ya ke yi fa, kuma ya samu ƙarin girma, a Azaren ma ba a family House yanzu su ke da zama ba. " Kai na jijjiga kawai, na wuce wanka. Abun mamaki nafi minti talatin a bakin madubi ina kwalliya, in shafa wancan in lakata wannan, sai tashin ƙamshi na ke yi. Fakistan ne a jikina riga da wando, mai kalar jinin kare, rigar ta shige guiwata sosai, sai burgujejen wandon daya ɗan leƙo ta ƙasa, adone a jikin kayan faca faca, gyalen kayan na yafa, ina sake fesa turare na jiyo maganar Safwan da Goggo. Murmushi na saki, zuchiyata na mun wani irin daɗi, wanda nake ta mamakin tsintar kaina a ciki da na yi. ji nake yi tamkar an sabunta xuchiyata ne, salon son Safwan daya motsa mun, ya yi mun sak da irin soyayyar da sabuwar zuchiyar da babu kowa acikinta ta shiga.
MRS BUKHARI CE
83/84






Tabarma Goggo ta shinfid'a mishi a tsakar gida. Nafi minti goma sha biyar ban fito ba, sabida jan aji irin namu na mata, amma zuchiyata a cike take tab da son kasancewa da shi, in ji d'uminshi a gefena, tare da tattausan k'amshin turarenshi na Tony Mantana.
A yangance na fito da kofin silver d'auke da ruwan sanyi, a gabanshi na ajjiye kofin sannan na nemi waje a gefenshi na zauna.
Idanu kawai ya ke bina da shi, ni kuma sai wani basarwa na ke yi, harda cin maganin.
"Sadiya, ganinki ya yi mun wuya sosai, tsawon shekaru baki sake waiwayar kowa ba." Dubanshi na yi, cikin had'e fuska nace."
Tunda kana zuwa nasan ba zaka kasa samun labarin ina Jibiya ba, tunda har Gimbiya Badiyya mai sarautar birnin xuchiyarka ta san garin da nike. Ni kake nufin in waiwayeka? Ai in kaga an waiwayi baya toh gaba ba ta yi kyau bane, me zan waiwaya dan kuma wa zan waiwayo?." Murmushi ya yi mun yana wani kashe ni da kallo da mayun idanunshi, ni kuwa fur na k'i yarda mu had'a idanu, dan gudun kar asirin son shi da nake dannewa ya tonu."
"Ba abunda na ke nufi ba kenan, da nace baki waiwaye mu ba. Na zaci za ki dinga waiwayar Adam, kina duba lafiyarshi.
A matsayina ta wa a wajanshi, yaron da ba'aso yasan wacece asalin mahaifiyarshi, sai Badiyya, in ina yawan zuwa ai da kun jima da koroni, ni da ka nuna ma baka buk'atar in shayar da gudan jinina. K'ila ko tarbiyyata ce bataima ba shiyasa ka kwace d'a a hannuna ba tare da ka yi tunanin komai ba, kaba matar da ba ta san zafin haihuwarshi ba." Rai na ga ya had'e, ni kaina saida maganar ta fito daga bakina na gane ban kyauta ba, domun nima ba ni naba kaina haihuwa ba, sai sai ina cikin b'acin rai da zafin zuchiya ne, ni kad'ai nasan irin azabtuwar da xuchiyata take yi."
"Abun naki har ya kai ki yi ma Matata gorin haihuwa a gaban idanuna Sadiya, bakiji nauyi na ba? Amma baki kyauta ba" Cikin dakiyar zuchiyar da take son wanke kanta nace.
"Ni ya dace aji kunya, ni da ka raba ni da gudan jinina tun yana tsunman goyo, ka zuba sona a faranti ka d'agama duniya shi, a matsayin bora, ka nuna mun daka dawo mun da d'ana gara ka rabu dani." Hawayene su ka silalo mun a kumatuna. Nan take ya wani rikirkice mun, hankici ya ciro a aljihunshi ya bani, karb'a na yi ina goge hawayena.
"Sadiya, ina sonki son da ya fi na Badiyya wallahi bazan yi miki k'arya dan kiji dad'i ba. Badiyya uwar gidana ce, ina kuma girmamata domun ta aure ni tun bani da aikin komai, tasha wuya da ni, kuma likitoci sun tabbatarmun ba zata tab'a haihuwaba, tausayinta ne yasa na yi mata kyautar Adam. Kuma ta na yi mishi rik'on da ko ke ba lalle ki yi mishi ba, ta na yi mishi son da bazai misaltuba, ko ni da na kasance Uba ga Adam, kuma wanda ya jima bai haihu ba, Ba na yi ma Adam irin son da take yi mishi, yaci a yabeta Sadiya. Kuma ta rik'e danginki tana zumunci da su, Amma tsantsar so ke na ke yi ma. Ko kinsan halin da na shiga a sakamakon rashinki kuwa? Ita kanta Badiyya ta yarda na fi sonki fiye da ita, kuma ta rungumi hakan a matsayin k'addararta, babu irin kuka da tashin hankalin da bata shiga ba. Babu yanda za'ayi dama son da na ke muku ya zama daidai, amma dai_dai da rana d'aya Badiyya bata tab'a canja mun ba." Shiru na yi ina saurarenshi, domun ni kaina na san Badiyya jaruma ce, kuma a zaman da na yi da ita bata tab'a canja mun fuska ba a matsayina na kishiyarta ba, ta rungumeni tamkar yaya da k'anwa, in ban yabe ta ba, ba na kushe ta ba, babu irin hidimar da ba tai mun ba a lokacin da na ke da juna biyu, babu irin abunda bata shanye ba, domun har rabon kwana denawa aka yi, tana ji tana gani dole ta sallamamun Safwan. A gaskiya juriyar da Badiyya ta yi a zamantakewarmu bazan ma iya irinshi ba sam, har mamaki take bani in ta yi wani abun, kuma wallahi da zuchiya d'aya take yi. Na yi imani da Badiyya ce ta haihu Safwan ya bani jaririn, ba za ta tanka ba, ko da kuwa ranta bai so ba. Kawaici da karamcinta ya cika, a hakan ta ci gaba da bin dangina tana zumunci da su. A take kunya duk ta lullub'eni, a baya duk wannan tunane_tunanen ba su zo mun ba sam. Ni kawai abunda na d'auka an zalunceni kawai. Na yarda Badiyya ta fi ni son Safwan nesa ba kusa ba."
"Baki ce komai ba Sadiya, baki yarda da ni ba ko? wallahil azim nafi sonki fiye da Badiyya. Badiyya da zan aureki ita taimun kayan lefenki kab, zinarenta na gado ta siyar ta yi wannan bajintar.Ni dai na ma rasa me zance mishi, gaskiya na tabka abun kunya gaskiya.
Na yarda da kai Safwan, sai mu yafi juna duka itama Badiyya ka bata hak'uri." Ajjiyar zuchiya ya sauke, ni kaina ji na ke yi tamkar an sauke mini wani nannauyan dutse a k'irjina.
Nan kuma hirar soyayya ta b'alle kowa na fallasama d'an uwanshi halin da ya shiga a sakamakon rashin juna. A daren Safwan ji ya yi tamkar ya kwana yana hira da ni, nima a nawa b'angaren hakan na ke ji. Da k'yar muka yi sallama da juna. Sawai na ke jin zuchiyata a daren.
D'akin Mama na shiga, ta samu bacci Goggo Hansatu na samu a zaune ta na kallon labarai a tashar NTA.
"Ah ya tafi ne? A kunyace na ce mata
Eh ya tafi"
"In ce dai kun sasanta kan ku tunda ku ba yara bane kuma ba sabuwar soyayya bace?" Cikin kunya na ce mata
Eh mun sasanta, duk rashin hak'uri ya haifar da komai, da kuma kasa bashi dama da na yi in saurari jawabin da zai mun. Amma a yanxu ni da kaina na bar ma Badiyya Adam. Kuma bana so har abada yasan ba ita ta haifeshi ba." Goggo Hansatu tace.
"Gaskiya ne Sadiya kinyi aikin hankali, dan Badiyya ta yi k'ok'ari ainun, mahaifiyarki za ta ji dad'in labarinnan, amman ni ina ganin, daga Malunfashi in kuka d'auko Haidar, Sadiya ku daure ki kai Haidar wajan dangin mahaifinshi. Kar ki biye musu duk tsiya sune gatanshi, kuma ko aure zai yi sune za su shige mishi gaba." Kuka na soma yi ma Goggo ta na ta aikin lallashina.


washe gari
Da asuba na shirya kamar yanda mu ka yi da Safwan, cewar a masallacin unguwarmu zai yi sallar asuba. Ai kuwa hakan aka yi, ana idar da sallah sai ga shi, sallama mu kai ma su Mama, Safwan ya rungume Adam wanda bacci bai isheshi ba, mu ka d'auki hanya a motar Safwan k'irar civic.
Tafiya ce wacce ta kasance ta shiga tarihin rayuwata. Domun cikin shauk'in soyayya mu ke ta cin hanya. Ji na ke yi Safwan ya dawo fil a xuchiyata, ban sha wuya ba har muka isa malunfashi.
Cikin makarantar mu ka shiga, ga d'alibai sai fita suke yi da akwatunan kwano,.wasu a motar gida, wasu a motar haya, wasu kuma da k'afa suke fita zuwa titi dan tarar abun hawa, ba mamaki k'ila su 'yan cikin garinne ko k'auyukan da suke makwabtaka.
Haidar na hango yana tafe a guje ashe harya hango mu. Hannayena na ware ina jiran isowarshi. Wuce ni yayi ya fad'a jikin Safwan, duk girman da Haidar yayi bai hana Safwan d'agashi ba, tare da jujjuyawa kamar yanda ya ke yi mishi a da.
Hawayene suka sintiri a kumatu na, ina jin k'aunar Safwan ta na hudani."
Haidar ne ya rungumeni, yana share mun hawayen fuskata. K'ank'ameshi na yi a k'irjina ina rok'on Allah ya gafartama mahaifinshi.
Mota mu ka shige, tare da barin harabar makarantar.
Jibiya mu ka nufa, nan na zazzaga da Safwan dangina. Kawu Shafi'e ne ya mayar da aurena da Safwan, a masallacin gidan, sai shigowa ya yi kawai ya mik'a mun sadakina. Yaya Sauban kuwa ya ji zafin rasani, amma yayi mun fatan alkhairi, tare da yi mun kyauta.
Kwanan mu biyu a Jibiya, mu ka wuce kai tsaye sai Raquma.
k'auyan Raquma ya na nan inda na baroshi, babu wani ci gaba daya shiga cikin k'auyan, yana nan a inda na san shi. Ina kan babur, ina tuno kyakkyawar rayuwar da na yi a cikin k'auyan ni da Aliyu, da irin abubbuwan da suka faru. A k'ofar gidansu Aliyu mu ka tsaya. Gidan ya kuma tsufa da ragwab'ewa sosai. Safwan a waje ya tsaya, ni kuma na rik'e hannun Haidar da Adam mu ka shiga cikin gidan da sallama."
Tsakar gidan duk shara da tarkace, ko'ina ya kwarab'e. Ga wata mai mugun zafi data k'walle, k'irjina sai duka ya ke yi, ta maza na yi, nai ta kutsa kaina ina ta sallama, Amma sai na ji shiru, daidai k'ofar d'akin Goggo Asabe, sai ga Bilkisu matar Anas ta fito da kwano a hannunta. Duk ta tsofe ta wani yankwane, ga duhu data sake yi. Dubana ta yi ta kuma.
"Sadiya kece haka ki ka waiwayemu, baki yi fishi da mu ba, wannan Aliyu ne ya girma haka?
Ajere ta yi mun wannan tambayar, ni kuma murmushi na yi mata nace.
"Malama Bilkisu nice, Allah yayi na waiwayo ku, ga Haidar nan. Goggo fa suna ciki?
"Dukka suna ciki suna tattaunawa" Murmushi na yi mata nace.
"Ina Hasiya mutuniyar fad'ana?"
"Hmmmm rayuwa kenan, Hasiya ta rasu shekaru biyu kenan da su ka wuce, sakamakon..
Fitowar Kawu ne ya katse mata maganarta.
"Ahh Aliyu ne ya dawo bature haka? Sadiyana kice ki ka zo. Murmushi na yi cikin ladabi na ce
"Nice Kawu, tare ma da Baban Adam muke yana waje."
"Shiga daga ciki iyayen naki na ciki, bari in sa Kabiru ya shigo dashi d'akin zaure ya hutu. Kun shawo hanya."
Haidar dai sai gaishesu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login