Showing 60001 words to 63000 words out of 92932 words

Chapter 21 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt

yau da kullum.
Rayuwa kenan. matar Yaya kabiru, da matar Anas sun samu juna biyu, yayin da Hasiya ita kuma kullum jaraba ita da abokiyar zaman nata, sun haddasama Dauda deeprecion, domun kullum a cikin tashin hankali da tunani yake, ko wacce yai mata saki guda guda, ya korasu gidan tsofaffinsu.
cikina na kwata takwas da kwana goma sha biyu, na tashi da safe, sai na soma jin halamun nak'uda na ke yi, da kad'an kad'an, ni anguwar zoma ce, na tabbatar wannan haihuwace, Goggo Hansatu wacce yau kwananta uku da zuwa na sanar ma, babu shiri ta had'a kayan Babyn da na bata kud'i ta shiga kasuwar Zamfara ta harhad'o mana. Ina rik'e a hannun Goggo Hansatu ina d'an cijawa, Goggo Asabe tace."
"Hansatu Lafiya kuwa, ina zaku je da kaya a cikin riyo da jaka?" Goggo Hansatu tace."
"Nak'uda ta soma ji, shine za mu yi hanzarin zuwa asibiti, dan a can zata haihu." Nan fa Goggo Asabe ta dirar mata.
"Ai mu a gidannan bama xuwa asibiti, canjan yara su ke yi, ko kuma su kashe muku d'a, tun daga kan margayiya Zainab matar wannan yaron aka dena zuwa Asibiti a gidannan, kasheta su ka yi, abunda ta haifa ma su ka kashe, ranar munga tashin hankali." Goggo Hansatu tace.
"Hak'uri za ki yi Asabe, akwai had'ari babba a ce mace zata haihu an barta a gida, musamman haihuwar fari,yanda akeso ma, ko a gidan ka haihu sai ka tafi asibiti, dan a duba lafiyarki data jaririnki, ki yi hak'uri, a samu wacce zata raka mu kawai." Fur Goggo Asabe ta k'i, da k'arfin tsiya Goggo Hansatu ta fige ni a hannun Goggo, kamar za su yi dambe, ta tasa k'eyata muka fice. Ni dai ba bakin ma magana. kafin mu isa asibiti, nak'uda zanga zanga, dan da k'yar na iya k'arasawa cikin harabar Asibitin, a harabar na kakare. wai ashe haka haihuwar take?


Goggo
sai raraka fad'a ta ke yi, har zuwa shashen Goggo Safiya tace.
"Safiya ki xo mu je, mu gani da idanunmu dan kar su yi mun canjan jika, Hansatu ta figi hannun Sadiya zuwa Asibiti, ki fito muje." Goggo Safiya tace
"Ba mu ci ta zama ba, muje kinji" mik'ewa ta yi, ta sa mayafi su ka fice. A wajan hawa babur ne suka had'u da Kamilu yace.
"Baaba gari zaku shiga? Goggo Safiya tace.
"Matar aminin naka ne haihuwar taxo. Cikin gigicewa yace.
"Yaushe? ko d'azu naje na duba lafiyarta fa. Goggo tace
"Ai kasan nak'uda, yanzu haka suna asibitin birni. kamilu yanke uxirin da ke gabanshi yayi, ya ma manta matarshi ce kwance ba lafiya, daga lamba yake, ya siyo mata kwayar bature. Tare da shi su ka wuce zuwa asibitin.


Sadiya
Ina cikin labour room na had'a mugun zufa, idanuna duk sun firfito waje, sai cije baki da rik'e baya na ke yi. Adda'a kam duk wacce tazo yin ta kawai nake, Nafi awa biyu ina abu d'aya. tun ina iya nishin har ma na dena, marata kuwa ta d'auki d'umi tamkar zata tarwatse. ruwa da allurai sunyi mun babu adadi, a hankali nace da wata anguwar zoma.
"Ku yi mun tiyata k'arfina ya k'are bazan iya haihuwa ba." tace
"Gaskiya ne madam, bari in samu mijinki yasa hannu sai ayi miki tiyatar kema ki huta, ga matan da su ka zo su ka same ki a d'akin duk sun haihu, har sun tafi 'dakin hutu."
Tana fita su Goggo na isowa.
"waye mijin Sadiya, ya biyo ni." Kamilu bai tsaya kwana kwana ba ya bita. Goggo Asabe ta harari Goggo Hansatu tace
"Bata haihu ba har yanzu?
"Eh wallahi tukunna dai, amma in sha Allah ta kusa. Goggo Asabe tace.
"Allah yasa yarinyarnan ta haifi abunda ke cikinta lafiya, yaronnan yazo duniya ko zanji sanyi, in ina kallon Aliyu a fuskar jaririn."
"Malam Hannu zaka saka mana, dan baza ta iya haihuwa da kanta ba, bayan dubawa da mu ka yi, sai mu ka gano kamar 'yan biyu ne a cikin nata, zuwa wani d'an lokaci in bata haihu ba, zamu shiga da ita tiyata" inda zai sa hannun aka nuna mishi ya saka, cikin tashin hankali ya dawo wajan su Goggo"


Sadiya
wani nishi ne naji yanayin kan shi da kanshi, k'arfen gadon da nake na rik'e, kamar yanda muke ce ma mata su yi, jaririne ya sunb'ulo, amma kafin in kai dubana ga abunda na haifa, sai na ji sabuwar nak'uda zanga zanga, amma ba tai tsawo ba, na sunkuto yarinyata. Numfashi na shiga saukewa a hankali, hawaye sai zubo mun suke yi, ana yanke musu cibi aka manna mun su a jikina. Sai lokacin na bud'e idanuna na dubesu.
Kau idanuna ya d'auka, gabana yai mummunar Fad'uwa da ganin irin abun dana haifa. Runtse idanu na yi na sake bud'ewa. Tabbas zahiri idanuna suka nuna mun, rungumesu na yi sai na fashe da kuka, aduk yanda suke sai naji son su na bubbud'e mun k'ofofin jinina. ina son su, kamar yanda ko wacce uwa take son abunda ta haifa. Amma ina mai cike da tausaya musu, a yanda na haifesu, ga kuma maraici, ko ya za'a amshesu a matsayin 'ya'ya oho, dan al'umma mugun kyamarsu da tsangwamarsu suke yi, ni kuma bazan iya juran ganin marayun yarana a irin wannan halin ba. Nose ce ta zare su a jikina, ta fita da su, ina kwance ana kwashe mun jini, mutuwar Aliyu ta dawo mun d'anya, yaranshi sun fama mun mikin dake zuchiyata. Kuka na ke yi sosai.


mrs Bukhari ce


*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*








1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_


5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_




Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300


*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇


0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.


Domin tura shaidar biya👇


0810 433 5144


Masu tura katin MTN👇


0814 179 9224


Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇


0817 952 3215


Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f


*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨




Instagram links👇


https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=




Facbook group


https://facebook.com/groups/463653111781414/




Telegram links


https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk




*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -


*Enter your name:* (Cikakken sunanki)


*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)


*Enter your password:* ( misali 12341234)


*Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


Masu iPhone


Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
51~52








"Baiwar Allah ki dena kuka akan abunda kika haifa su ma fa mutanene kamar kowa, kuma suna rayuwa mai tsayi kamar kowa, ki taso in raka ki d'akin hutu." Bance da ita komai ba, ni ba kukan kyautar da Allah yayi mun nake yi ba, in na yi hakan ai tamkar na butulcema kyautar da Allah ya bani kenan, ga mata da yawa na neman haihuwa Allah bai basu ba. Aliyu ne ya dawo mun d'anye. Gado ta nuna mun, da dabara nahau kan gadon, ina ta kallon matan da muka haihu a d'aki 'daya da su, ko wacce ga mijinta a kusa da ita, ana basu kula amma banda ni. Allah ya jik'an ka Aliyu, Allah ya isar da haske kabarinka. Ga yaranka nan Aliyu, in sha Allah duniyar musulunci za su yi alfahari da su, ba zan bari su yi maraici ba. Hawaye na na share, dan na hango tahowar Su Goggo.
Sannu su ka shiga yi mun, na kasa amsa kowa, sai kuka na nake had'iyewa, amma ina. da kuka na fashe mai tsanani, kowa na wajan sai da ya tausaya, domun sun fahimci halin rashin Aliyu nake, dan an riga an sanar musu na sauka lafiya, Allah ya azurta ni da mace da namiji.
"Ki yi shiru Sadiya, tsakanin ki da Aliyu sai adda'a, dan ma Allah ya nufi zamu ga jininshi." Goggo Safiya ke rarrashina. kamilu yayi shiru daga gefe sai bina da idanu ya ke yi. wasu ma'aikatan kiwon lafiya ne, su ka shigo da yaran a hannunsu, daya an sa mai saiti fari, dayar kuma ovaroll mai kauri da hula aka saka mata, a cikin bargo d'aya aka nannad'esu, kasancewar kayan mutum d'aya mu ka tawo da shi. Goggo Asabe da murna ta amshi yaran a hannun wannan Nose d'in, dayar kuma ta nufo ni dan ta duba lafiyata."
"Wayyo Allah mutane ko aljanu? Goggo hannunta na rawa ta saki yaran a k'asa, su ka fad'i tum. Idanu na rintse, dan wani irin abu na ji a zuchiyata mara misaltuwa. Kuka na fashe da shi, da Sauri Goggo Safiya da Goggo H su ka nufi jariran da kukansu ya cika ward d'in da muke. Amma ganin yaran yasa Goggo Safiya ja da baya, Goggo Hansatu ce, ta yi k'arfin d'aukar yaran ta rungume a jikinta tare da aikin jijjigasu.
Suna kafad'ar Goggo H, Kamilu ya je ya lek'a fuskar yaran.
"Allahu akbar" shine kalmar da ta fito a bakin shi, mutanen d'akin sai bin mu da kallo su ke yi.
"Ke Hansatu, wad'annan yaran aljanu Sadiya ta haifa? Ji yara kamar yasan sarkin aljanu, tsabar fari" cikin zafin xuchiya Goggo.H tace.
"zabiya ne Allah ya bata, amma ai ko ba ku tab'a ganin zabiya ba, ai bai dace ki yar da jarirai haka a k'asa ba.
Goggo Asabe da muryarta har rawa take tace.
"Wallahi Allah ban tab'a ganin zabiya ido da ido ba, nasan dai 'ya'yan k'azanta ne, wanda aka haifa a k'azance." Kai Goggo H ta girgiza kawai, za ta yi magana, wata nose ta k'araso tace.
"Dan Allah a ara mana jariran za mu d'an k'arashe gwaje gwaje a kan su." Goggo H tace.
"Akwai wani damuwa ne a tattare da yaran?
"A'a Baaba, kinsan su irin wannan bayin Allah yawanci masu lalurar ido ce, ba su cika gani sosai ba, idanun nasu za'a duba dan a san a wanne matsayi suke." Goggo ta mik'asu, ni dai na yi shiru na zuba ma sarautar Allah idanu.
Bayan kamar awa guda da fita da jariran da aka yi, ina zaune ina shan tea da kamilu ya sawo mun a waje, Dr ya shigo, a gabana ya tsaya ya dube ni.
"Maman biyu ya jikin na ki?"
Da sauk'i. kawai na ce mishi, ruwan da ke d'aure a hannuna ya cire mun sannan yace.
"ke kam mun sallame ki, Amma twins mun basu gado a b'angaren yara, zuwa gobe zamu tura ku zuwa asibitin sokoto, dan acan za su fi samun kulawa." kwarewa da tea d'in nayi nan na shiga tari, aka shiga yi mun sannu.
Sai tsiyayar hawayen tausayin marayun zabiyan yarana nake yi, nan nace.
Allah ya jik'an ka Aliyu, da rabon ba zaka gana da kyawawan yaranka ba." Dr ya zuba mun idanu. su Goggo dukka kowa ya dubi Likita. Kamilu yace
"Dr me ya same su? bayan ya gama cire mun ruwan yace.
"Basa gani sam, kasan zabiya da ma da matsalar idanu, toh wad'annan ganin ma basa yi, amma zan tura ku zuwa babban asibiti, dan a yi musu bincike da kyau, tunda sunfi nan kayan aiki, nima ina aiki a can d'in." Kuka na fashe da shi sosai. Nan jikin kowa yayi sanyi kowa ya tausaya halin damuwar da nake ciki. D'unguma mu ka yi d'akin da 'yan biyu su ke kwance. D'akin yarana, ga sunan lalurori iri iri, jarirai da na'urar numfashi, wasu da roba ta hancinsu, ga wata yarinya itama a kusa damu abun tausayi, uwar sai kuka take yi. Dr na ke kallo yanda naga yana juya Husaina abun ya tsorata ni, bayan ya gama aune aunen shi. sai kawai ya juyo ya dube ni tamkar mai jin tsorona yace.
"Allah ya amshi rayuwarta ita kam." Sumewa ne kawai ban yi ba, amma duk mai tausayi saiya zubar mun da hawayen tausayi. inaji ina gani, Su Goggo Asabe, da Goggo Safiya su ka tafi da gawar Husaina, da k'yar su ka iya rik'eta.
Jikin Goggo H na fad'a na kuma sau kuka.
Goggo yanzu shikenan itama yarinyar mahaifinta ta bi kenan, itama rasata na yi? Allah na gode maka, ubangiji ka bani ikon cinye wannan jarabawar, shi kuma wannan bawa naka ka raya mun shi da imani." Hawaye na na share, na saki Goggo H wacce itama kukan ta ke yi, take wani dangana gami da juriya su ka saukar mun, ban sake yin kuka ba.
Da yamma Dr ya sake shigowa duba mu, duba na yayi.
"Yaron ya farka kuwa?"
A'a bai farka ba tukunna, kuma k'alau ya ke? murmushi ya yi mun.
"k'alau ya ke ba ya d'auke da wani ciwo in ba ciwon idanunnan ba. ki same ni a office zan rubuta miki allura a je a siyo." Juyawa yayi ya fice. Goggo H tace.
"Toh maza jeki, ko ni zani, sabida yanayin jego ga ba ruwan zafi. Murmushi na yi mata nace.
"Babu damuwa bari in je, zan iya.
Wuce wa na yi zuwa waje, dai dai ya b'ille wata kwana, ahankali na ke jan jikina, dan har jiri nake ji, babu abunda nake buk'ata face ruwan zafi. Ko da na b'uulla inda naga yabi, ban ganshi ba, gashi ni bansan sunan shi ba. haka na gama bukayi na, harna juya zan koma sai na ji yace.
"Gani nan Halima" Da sauri na juyo, yana tsaye a baya na, yace.
"Jikin ki baya miki dad'i ko? Nace
"Babu damuwa, akwai magungunan da zan siya dan kare lafiyar jikina, in sha. Da mamaki yace.
"Kina da ilimin hakan kenan? Bance mishi komai ba, takaddar allurar ya nuna mun, amma bai ba ni ba, yace
"Ki koma, zan kawo miki, shima wanda zaki sha d'in zan kawo miki, kije"
Wuce wa na yi, ina shiga na tadda Iya da Anty Ramatu sun iso, da ruwan zafi a flaks da abincinsu. Hassan yana hannun iya tana tofe shi da adda'a.
"Sadiya sannu da jiki, ayi hak'uri da yanda aka tsinci kai." murmushi kawai na yi, na gaishesu da ladabi, buta Goggo.H ta mik'a mun.
"Ungo je ki kama ruwa ki ji dadi, ga abinci mai nauyi kici, kafin yaronnan ya tashi, dan nono zai naima afujajan." Iya tacs.
"Ga zam zam da dabino ma, daya farka a tauna a cusa mai a baki, kuma a bashi zamzam ya sha." Na sa hannu na amshi butar a hannun Goggo.H, ina jin dad'in yanda Iya ta nuna kulawarta akan Hassan, Ni sai lokacin na tuna cewar ban yi musu adda'a ba. Lallai na tabka kuskure babb."
Dr ne ya isa wajan gadon da Sallama, Allura yai ma jaririn, sannan ya ba da sallahun magani na.
Dana fito ne Iya ke mik'a mun, karb'a na yi na sha, sai na ci tuwon da Iya ta kawo, amma ba dan inaso ba, so nake Hassan in ya farka ya samu abinda zai sha. Ina kwanciya Sai baccin gajiyar nak'uda ya kwashe ni. Su Iya sun tausaya mun a halin da na ke ciki.
Ina bacci su Anas su ka zo, Anas ne yai ma jaririn hud'uba da Sunan Aliyu.
"Iya sunan shi Aliyu Allah ya raya."
Iya ta sa hannu ta amshe shi ta na kuka.
Bani na farka ba sai jefin taran dare, rabona da irin baccinnan tun Aliyu na da ran shi"


mrs Bukari ce
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯‍♀️👎👇👇*








1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_


2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_


3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_


4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_


5, *AUREN WATA TARA*👩‍❤️‍👨
_Miss Hajo_




Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300


*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇


0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.


Domin tura shaidar biya👇


0810 433 5144


Masu tura katin MTN👇


0814 179 9224


Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇


0817 952 3215


Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f


*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩‍❤️‍👨




Instagram links👇


https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=




Facbook group


https://facebook.com/groups/463653111781414/




Telegram links


https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk




*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -


*Enter your name:* (Cikakken sunanki)


*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)


*Enter your password:* ( misali 12341234)


*Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.


Masu iPhone


Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
53~54






"Sadiya bashi nono bawan Allah tun d'azu ya tashi, ya d'an yi kuka kad'an" Kab'ar shi na yi a hannun Goggo.
man zaitun da muka tawo da shi na bud'e. na goggoga a kayikan nonon nawa. Sannan na zura mishi.
Addu'ar da d'axu ban samu nutsuwar yi musu ba, yanxu na yi mishi nashi. Goggo ta sanar dani Aliyu aka mayar mishi.
Goggo a rink'a kiran shi Haidar. Goggo Hansatu tace.
"Babu laifi Sadiya. ni ina zuwa. Fita ta yi ta barni da kallon Haidar, fari k'al da shi, gashin kan shi ja, haka bakinshi jawur da shi, a raina nace.
Ina ma zai tsaya a haka ba tare da yayi wannan kurajen da dabbara dabbaran ciwo a jikin shi ba, da zan yi farin ciki. Murmushi na yi na shafi fuskar Haidar bawan Allah kenan, sai mama ya ke sha, ni kuma zafin shan maman har can cikin raina na ke ji.
Washe gari da safe akai mana transpar zuwa asibitin cikin gari.
Dr ne ya amshi Haidar ya shiga da shi zuwa ciki.
waje mu ka samu ni da Goggo Hansatu mu ka zauna. Mu na wajan Sai ga Kawu ya tawo, shi da Yaya Kabiru. Babu yabo babu fallasa su ka amsa gaisuwata, kawar da kaina na yi daga gare su, dan k'iyayyar da su ke nuna mun ta yi mun yawa, kuma lokaci ma ya cika da zan bar musu gidansu, Ina ji Kawu na fad'an garin yaya na haifi 'ya'yan k'azanta, yaran da ake samun su ta hanyar, in mace na jinin al'ada aka sadu da ita shine ake haifar zabiya. Wannan a canfin da hausawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login