Showing 24001 words to 27000 words out of 92932 words
Chapter 9 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt
a gidan Kamilu. Gida ya wuce da Sauri, kuma cikin k'arfin guiwar da Kamilu ya aro ya yafa mishi.
Sadiya
Ina zaune a saman kujera. ina karanta wasik'ar jaki. tare da yin lissafin dokin rano. Sallamar Aliyu ce ta katsemun tunanin da na ke yi. Idanamu muka zuba ma juna, murmushi ya sakar mun.
"Anty ki shirya za mu d'an fita yanzu. Bari na sake kaya."
uwar d'aki ya shiga. Take zuchiyata ta shiga bugawa da k'arfi. Harya fito ina zaune a wajan cikin muryar kuka nace.
"Aliyu ka sake ni ko. Amma me nayi maka toh?" lumshe idanu yayi yace da ni.
"Ban sake ki ba Anty, babu wanda zai iya kwace mun ke. gidan Iya mai Tubani zan kai ki ki d'an zauna acan zuwa wani lokacin. ki yi hak'uri da yanayin da muka riski kan mu a ciki. amma ki sani Ni bazan iya sakin ki ba." jikina a mace na shiga cikin d'aki tare da tattare 'yan suturu na nasa a k'aramar jaka. mayafi na yafa na fito. kallona yayi da kyau yace.
"Baki da hijab ne?" Da mamaki nadubeshi sannan nace.
Ina da na yin Sallah."
" Ki je ki saka shi. Daga yau karna kuma ganin kinsa mayafi. Ni namiji ne mai tsananin kishi sosai." mamaki Aliyu ya bani. Yanda ya b'ata rai bai ko ji nauyi na ba. Yake bani umarni. Bani da yanda zanyi haka na koma na zumbulo hijab har kusan k'asa.
Bai ce komai ba. Jakar hannuna ya karb'a ya shige gaba. ni kuma ina biye dashi a baya
Ta k'ofar baya mu ka fita. Kamilu ya na tsaye a gindin bishiya yana jiranmu. Da isowarmu muka wuce. Babur muka hau har zuwa bustop. Daga nan kuma mu ka hau motar da zata kaimu Mafara k'aramar hukuma.
Ina zaune a kusa da Aliyu jikina yana gugan nashi. musamman in an shiga kwazazzabo. wani irin yanayi nake shiga in jikina ya manne da nashi. Duk da suna d'an jefa hira shi da kamilu Amma kuma hankalinshi yana kaina. Ina kallon irin satar kallona da ya ke yi. Ni kuma tunane tunane duk ya cika mun kaina. A haka har muka iso mafara.
Babur muka sake hawa har zuwa cikin anguwar su Iya. Sukam naga suna da makarantun gwamnati da ma babban Asibitin gwamnati, ga wutar lantarki.
sai kalle kalle na ke yi. Ina ganin mata da k'ananun yara. ga 'yan makaranta an tasosu su na tafe suna wasanninsu. wasu ko takalmi babu, wasu kuma kayan makarantar duk datti. wasu nasu a yage, Abun gwanin tausayi. Ta ya ma yaro zai yi karatu mai kyau. Jikinshi duk tsami da datti, makarantar duk a rub'e ajujuwan ko bencin zama babu dana hango,ga wani zarni dake tashi na bayan gidan makarantar, wanda kab rabin anguwar zarnin ya damesu, ina ga malamai da d'aliban cikin makarantar? Shi yasa manyan masu muk'amin k'asar suke sanya yaransu a makarantun kud'i,domun sunfi kowa sanin me suka shuga a makarantun gwamnatin nasu. Ya ilayi ka tab'a zukata shuwagabanninmu su dube mu. a kofar wani gida muka sauka. ni dai ina biye da su har cikin gidan, sai kalle kalle nake yi. Kai kallo na k'auye."
mrs Bukhari
ANAN NA KAWO K'ARSHEN FREE PAGE. KI BIYA KUD'INKI DANJIN YADDA ZATA KASANCE. WANNAN TAFIYAR TA
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
21~22
Da sallama a bakinmu dukkanmu mu ka shiga.
Iya ta tsakar gida ta na k'wad'a zogale da rama. sai da yawuna ya tsinke da ganin wannan k'wad'on.
" A ahhhh Aure yau igiya goma sha biyu. Yaushe a gari inji mak'i bak'o. masu kwalli a ido Ai sun san da dawowarka, amma ni da yake ba'a auran dani ai saida ka yi kwantai." Dariya Aliyu yayi ya ce.
"Da surutu dama nasan zaki tarbeni ke irin auran naki kenan. Kinga kishiyarki magana bata fiye damunta ba, amma ke magana ta yi miki yawa." Dariya Iya ta yi. Tabarma ta nuna mana.
" Ku zauna. Kamilu baka da mutumci Ace rabon da in sanya ka a ido. shekara sama da hud'u. Tunda mai gidan ya tafi madina karatu ka d'auke k'afarka a gidannan sabida Allah dai_dai kenan?. Dubana ta yi tace.
" uhmm baiwar Allah sannu da zuwa. ganin mazajennan nawa ne yaimun dad'i sosai. Kamilu wannan itace Amaryar da aka ce ka yi? Sai yau Allah yayi n ganta. Kai amma kuwa ka mori mace, ji mace a dire. Kamilu yace.
"Ki bari mu gaisa tukunna. Nina soma gaisheta dubana take yi da kod'addun idanunta da baza kai zaton tana gani ba ma, gasu fici_fici kamar k'wark'wata.
"Ai wannan kamar Sadiya ta wajan Adamu ko? Nayi matu'kar mamaki data kama sunana. Aliyu ya ce itace.
Kuka Iya ta fashe da shi, tana yi tana sharce majina, ta ce.
"Allah ya jik'an Adamu d'an boko mai mata 'yar boko. yaro mai hakuri da yakana. kai Adamu ya sha wahala a Hannun dangi da suka sashi a gaba. Dan kawai ya auri 'yar boko, musamman Asabe. Ni banga laifin Aisha ba. Tunda mahaifinta shi ya d'aga darajar Adamu har ya shiga gwamnati, Amma dangi sun d'aura ma Aisha wata iriyar jahilar tsana. Ke Sadiya taho in ji d'umin Adamu a jikin ki, ko na ji sanyi, haihuwa mai rana kenan.
Hawaye ne su ka soma xubo mun. A karon farko da na ji yabo daga dangin Babana kenan akan mahaifiyata, Aliyu ne ya girgizamun kanshi cikin sigar lallashi. Idanuna na lumshe. Ina isa inda take na rungumeta mu ka ci gaba da kuka.Kuka nake rerawa mai tab'a zuchiyar mai sauraro. Iya kuwa har da fyace majina. Mun jima a haka sannan ta d'agoni tace.
"Yaushe ki ka zo Sadiya? rabona da ke tun kina 'yar shekara goma, nayi mamaki dana ganeki ma. Ni kin sanni?" kai na girgiza mata. Wannan shine karo na farko da na soma ganinta a rayuwata.
"Assha wannan illar ta rashin zumunci ce. zumuncinnan inma ba'ayi anan gidan duniya ba, ayi a k'iyamar Allah. An hura wata iriyar muguwar gabar da tasa 'yan uwa suka mance da Adamu, balle su waiwayi abunda ya bari. Yaron.arxiki mai kunya. Adamu shine mutum na farko da yayi karatun boko a Raquma, dama na addinin mai zurfi. k'arfi da ya ji Sulaiman ya hana kowa zumunci da iyalan Adamu. Shi na d'aurama laifin tunda shine babban banza. Asabe ita ba kai bane da ita. shegen taurin kai da kafiya shiya sa ta auri ubanka ta k'are a wahale a gidan haya. Sai da ubanta mai hula ya mutu ta samu matsuguni na kai."
Aliyu yace.
"yanzu ma fa Iya sabida ita mu ka zo wajanki. Wani al'amarine ya faru ina madina lokacin." Nan ya kwashe komai da komai ya sanar mata.
Kuka ta kuma fashewa da shi har ta na bubbuga k'afa. cikin kuka tace.
"Amma Sulaimanu da Asabe sun yi Asara, sunyi fad'uwar bak'ar tasa, zan kuma b'ata musu tura takai bango zan nuna musu ni uwarsu ce. Dan k'asa ta rufe idan Adamu iyalanshi har sun kai ai musu wannan wulak'ancin saki fa? da data amince fa. akan bare Asabe zata sa a saki d'iyar k'aninta? Jahilci masu gari, yau saina sa Asabe ta shiga hankalinta. Aliyu yace.
"yanzu haka Yaya Fatima ta na gida. Wai dole sai mijinta ya sake ta. Yau za su je gaban me gari ma.
Nan ta mik'e tsaye tace.
"Haka asabe ta sake lalacewa? ta zama me kashe kashen Aure kenan, ko hauka tayi ne?. Ku barni da su wallahi sai sun yi dana sanin zuwana gidan dan yau wallahi sai kowa ya zubar da hawaye. Kai bacci ma sai naga dama za'ayi a gidan. Dauda da matarshi kuwa duka zansa jama'ar gari su yi musu, Bansan yaushe Dauds ya zama sallamamme ba. Me gari ko ya baka Dijangala ko kar ya baka duk d'aya. ga mata dirarriya mai k'ira mai kyau ka samu. Ni bazan so a had'ata zama da kishiya bak'auya ba ma. Bazan yadda da wani k'arin Aure nan kusa ba.
Ta inda Iya ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba. Iya irin mafad'atan jinin sakkwatawannan ne. Har wani hunguna hancinta ya ke yi tsabar fad'a. Aliyu da Kamilu sai farin ciki su ke yi da goyon bayan da su ka samu a wajan Iya. Ni kaina banso maganar Saki ba har ga Allah. Ashe furucim saki masiface ga duk macen da tasan darajar kanta ? Sai yanxu ne na soma shak'ar iskar duniya. Kwad'on zogalennan Iya ta sa jikarta ta zuzzuba mana tare da kawo mana Dawo bako sukari dan su a haka su ke sha, kuma sun saba.
" ku ci abinci sai mu hanzarta tafiya. Jikina bazai daina rawa ba har sai na ga Asabe a cikin damuwar da ta fi damuwar da ta sanya ku a ciki, domun walahi sai hawayen Asabe ya k'afe yau. Ba wanda ya ce mata wani abun. Ni dai zogalen na ci. na kasa sabawa da dawonnan na sokotawa. Ba mu b'ata lokaciba muka kammala. Iya ta kwad'ama jikarta Hafsatu kira ta yi. da sauri ta fito tare da tsugunnawa. cikin ladabi ta gaida mu. Iya tace.
" ki ciro mun kaya kala biyu a akwati ki sa a leda maza. Idan Ramatu ta dawo daga asibiti ki ce mata na tafi RAQUMA ta kula da ku sosai. ko da Jikar Iya ta shiga ciki bata jima ba ta dawo da leda a hannunta. Ni na amshi ledar. mu ka fita.
"iya Yaya Ramatu har yanzu ba.aga mijin nata ba ko? Iya tace.
"kaidai ka bari. wannan yaro kwai tsinanne ba wani b'ata da yayi fa. wallahi talauci ne da jahilci su kai mai yawa, jahilin mutum, wallahi yafi mahaukaci ban haushi, ai duk wani sauk'i da wayewa ya k'are a wajan mutum mai ilimi, wanda yasan kanshi, dama 'yancinshi. Meye ba'a fad'ama Ramatu ba? Fur tsuntsun soyayyaya d'ebeta ta fad'a hannun jahilin namiji, ya dinga gasata, daga k'arshe yaci biredi ya yaga leda. Ni in mun je RAQUMA ma za'a yi har da maganar tata. ace a cikin su Sulaimanu an rasa wanda zai taimaki rayuwar Ramatu. Yara goma ace miji ya tsallake ya barka da su. Ai akwai tashin hankali. A asibitin gwamnati take shara da wanke kewaye. yaran nata kuma na ce su zo mu zauna. Tunda dangin uban nasu sunki d'aukar ko d'aya, sabida suma jahilanne. dukka suna zuwa makarantar gwamnati, suna tsinto karatun a haka. sai makarantar allo da suke zuwa. Ai mu mu ka yi karatu a cikin gata. a lokacin turawa ke koyar damu,har gida suke bi suna kwasar yara, free education, kuma karatu nagartacce. Allah sarki k'awata Zainaba, bana mantawa har gidan wak'afi aka kai mahaifinta, dan ya hanata karatun boko, wani alk'ali ne a lokacin mr Bensin, shi ya taimaka mata. A sanadiyyar Zainabu karkararsu ta samu hasken ilimi yake haskawa har yanxu, har gwamnati ta gina musu katafariyar makaranta a lokacin 'yar gaske. Iya ta shiga fece majina ta na hawaye.
Ni kaina da bansan kan labarin ba. Amma na tausaya ma Anty Ramatu gaya. Kuma naji dad'in labarin da iya ta bamu, dan ni inason sauraron tariihi, musamman na manyan matan da suka sha gwagwarmaya a rayuwa. Aliyu yace.
"tunda aka dena taron da ake yi na duk shekara. Shikenan zumuncin ya sake lalacewa. Iya kin tuna mun ma. makaranta na ke so in bud'e a raquma makarantar addini. Dan ina tausayama rayuwar jama'ar k'auyan raquma yanda su ke rayuwarsu da ka. Ba sani a tare da su ba kuma ba sa buk'atar saninma. Amma nasan Baba za ta iya hanani cikar burina. wallahi sabida al'ummar Raquma na dage na yi zurfin ilimin muhammadiyya ko Allah zai sa ta dalilina haske ya bayyana a cikin garin. Ta yanda nan gaba zan bud'e musu makarantar boko ma. A wannan zamanin baza'ace mun saki hannayenmu suna bin cinyoyinmu ba, da sunan muna jiran gwamnati ta yi mana ba. Bana ko ji. Gwamnatin jirar Sokoto bata san da zaman jama'ar Raquma ba. K'ila da sun kawo mana tallafi. ba mu da makarantar boko, Bamu da ta islamiyya, ba mu da kwalta, ba wutar lantarki, ba asibiti. Ba d'in ta yi mana yawan da sai dai mu ce ni 'yasu. ki duba fa."
Aliyu na ke ta bi da kallo domun tunaninshi ya burgeni. Lallai Aliyu jarumi ne tunda ya ke so da k'arfinshi da lokacinshi ya k'wato k'auyan Raquma daga halakar da su ke ciki. a karon farko da Aliyu ya burge ni fiye da tunani kenan. Harna k'udurce a raina zan bashi taimako d'ari bisa d'ari, da dukkan k'arfina.
"kai Aliyu gaskiya tunaninka da kyau. Amma yin makaranta ya na buk'atar kud'i dan gudanar da komai yanda ya dace. Allah Sarki mai hula. da irin k'udirinka a ranshi ya amsa kiran ubangiji. ya so ace ko Adamu ko Sulaimanu su kasance masu cire jama'ar k'auyan Raquma daga cikin duhun jahilci. wanda a lokacin maggi su ke siya a matsayin maganin kashin hak'ori tsabar duhun kai. amma in kana buk'atar taimako daga gareni zan taimaka. nima lada zan samu. Ke Sadiya ki taya mijinki wannan yak'in dan watak'il sai sun yi gangamin zuwa k'one gidan mai hula. Dan ba k'aunar karatu suke ba. Dariya mu ka sa duka har da ita. Babur mu ka hau. suka fita damu daga layin su Iya. Daga nan kuma, mota muka shiga zuwa bustop. mu na sauka a nan kuma mu ka sake hawa Babur xuwa cikin Raquma.
Goggo
Goggo Asabe ta na tsakar gida sai kuka ta ke yi tana fad'a. Domun da kanta ta je b'arayin su Aliyu , bata same su ba. ihu take yi kan Sadiya ta shanye mata yaro ya zama bita zai_zai.
Sadiya
Iya ta girgiza kai ta dubi Aliyu da ni tace.
"ku soma shiga inga uban da za tai muku. duk wannan fad'an ni ta gado. Amma wallahi banayin fad'an rashin gaskiya, sabida ni ina da ilimina."
wucewa muka yi zuwa cikin babban tsakar gida. Goggo Asabe ta na ganinmu ta nufo mu da gudu, A gaban Aliyu ta tsaya. mari ta sakar mishi, wanda sai da marin ya shafi idanunshi. take idanunshi su ka rufe ya dena ganin komai.
"Ka sake ta ko in tsine maka albarka. ka sake ta na ce.
Ke kuma gayyar asiri. tunda nake da k'usar ya'ki bai tab'a jinkirta bin umarnina ba, sai da ki ka zo kika juya mai kwakwalwa da asiri, kece harda fita tare da shi? zaki rabashi da Raquma kenan, kamar yanda uwarki ta raba Adamu da Raquma dama danginshi ko?." Kaina na k'asa ina tsiyaya hawaye, ni abun ya isheni har ga Allah, hak'urina ya kusan gazawa. Iya ce ta shigo. Aliyu kuwa sai kallonshi na ke yi. dan naga ya kasa bud'e idanunshi d'aya kuma sai ruwa idan yake zubarwa.
Goggo Asabe juyowar da za ta yi, su ka had'a idanu da Iya.
"Yayi kyau. Asabe ashe haka kike d'ibar albarka a cikin gidannan. Ke kin isa kisa ya saki matarshi bacin yana son abunshi. Ashe zaki iya ja da hukuncin ubangiji kenan" Ko da ya ke. Ance mun kin zama mai dalilin kashe aure, Fatima gata a gabanki za ki kashe mata aure. Asabe kin yi k'arkon kifi daga ruwa izuwa wuta. kuma wallahi sai na d'auki mummunan mataki akan kowacce mace a gidannan. Har da baren da kika basu dama su wulak'anta Sadiya. Dan haka ko wacce shegiya ta bar duk abunda ta ke yi, ta same ni a b'arayin na god'i sulaimanu babban banza. yau sai an saki duk sirikan gidannan ko da uwayensu su ke tafe."
tana kaiwa nan, ta juya izuwa b'arayin Kawu sulaiman. Wanda tunda ta soma magana hankalinshi ya tashi, dan yasan a wuyanshi zata sauke alhakin komai, surukan gidan kuwa kowa tasha jinin jikinta.
mrs Bukhari ce
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
Instagram links👇
https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Facbook group
https://facebook.com/groups/463653111781414/
Telegram links
https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z