Showing 75001 words to 78000 words out of 92932 words
Chapter 26 - GISHIRIN ZAMAN DUNIYA Book Complete by Badi'at Ibrahim mrs Bukhari.txt
ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
MRS BUKHARI
67-68
Anty Bilkisu ta ce.
"Safwan ya na da sauk'i, ga shi da d'aukar shawara. kuma ya na da kafiya da taurin kai a bisa abun da ya sanya a gaba dan gudanarwa. Ya na da hak'uri, amma kuma akwai zafi musamman in ki ka tab'a dangin shi, Akwai biyayya da jin maganar na gaba. Ya na wani irin murd'add'en hali wanda in ya birkice babu mai iya gano kanshi. Abincin da ya fi so shine. Tuwon shinkafa miyar kub'ewa d'anya da bushasshen kifi da man shanu, Baya shan shayi sai kunu, kuma ya fi son mai tsami. Ya na da tsabta wanda a lokacin da yake yaro mu kai tunanin ko aljanune su ka shafe shi. Matar shi Badiyya kuma ni bansan wani halinta ba. Gare ki Anty Saliha an zo wajan ku. Dariya Anty Saliha ta yi ta ce.
"Badiyya dai ta na kirki da kawaici sosai dan ta shanye abubbuwa da yawa a cikin dangin mu, kuma ta ba Safwan goyon baya d'ari bisa d'ari a rayuwar shi ma ba ki d'aya. Ba mu santa da mummunan hali ba. Mu na fatan ke ma ki zama kamarta ko fin ta ma. Allah ya baku zaman hak'uri ya kawo 'yan biyu sau hudu." Dariya mu ka yi dukka.
Ina zaune a falon Innah surukan gidan su ka rik'a shigowa gaisheta d'aya bayan d'aya. Sai a yanzu ne na ke kallonsu da kyau tare da k'ok'arin rik'e sunayensu.
Na jima a d'akin Innah ina jiran Safwan ganin bai shirya dawowa yanxu ba, na mik'e tare da yi musu sallama.
Tare da Madina muka fito, yarinyar wajan Anty Saliha ce, tana rik'e da kwanukan abincinmu har zuwa b'arayinmu.
Ina zaune kwalam tamkar wata mara gata, agogon dake kafe a bangon d'akin na ke ta kallo, sai sha d'ayan rana Safwan ya shigo d'akin."
"Amarya bakya laifi, aimun afuwa Yayarki ce ta d'auke mun hankali. amma a yi hak'uri dan Allah."
Zama ya yi a kusa da ni, tare da hamo hannaye na dukka biyun ya na murzasu. Lumshe idanuna kawai na yi amma na kasa cewa da shi komai.
"Kin ta shi lafiya?" Sai lokacin na dube shi, fuskarshi da bakinshi duk janbaki yayi jawur. Ajjiyar zuchiya na sauke, ahankali na zame hannayena.
Ina kwana, ya gajiyar hanya?"
Jawo ni ya yi na fad'a jikin shi a hankali, k'amshin turaren shi da k'amshin turaren Badiyya ya cakud'e a jikinshi ya ba da wani kalar k'amshi na da ban."
"Sadiya kamar fishi ki ke yi da Angon na ki ko, ko akwai wani abun da na aikata wanda bai miki ba? Ki sanar da ni in baki hak'uri, yanayin tamkar horo kike mun." Cikin cijewa na aro dauriya da juriya na dangana ma kaina. Da murmushi na d'ago fuskata na dube shi. murmushi mu ka sakar ma juna, Hannu nasa na goge mishi bakin shi da fuskar shi.
Babu laifin da kai mun, sam gajiyar biki ce ba ta sake ni ba. Kuma ka sake d'aura mun wata gajiyar....
Ban rufe baki ba, Safwan ya rufe mun da na shi, kusan minti 30 ya na muzata yanda ya ga dama, ga ciki na babu komai.
A cikin satikan amarcin mu na murzu a hannun Safwan. ga tsaiwar dare da ya ke yi kullum kan Allah ya dube shi ya ba shi magaji.
Ranar da na cika sati guda a gidan Safwan, har da kwana ukun da Badiyya ta k'aramun a kai. Ranar Badiyya ta tare a d'akinta. Na ga zumud'i da rawar kai sosai a wajan Safwan, dan tun magriba ban kuma sa shi a idanuna ba."
A shashen Innah na ke kusan rabin wuni na, kullum inai mata wanki, shara, gyaran d'aki, har kitso da tsifa duk ni na ke yi mata. Hakanne ya d'aga darajata a idanun Yayyen Safwan maza da mata da ma shi kan shi Safwan d'in."
Yau dai na ta shi jikina babu wani ishasshen k'arfi, ga amai da duk ya addabe ni sai ta so mun ya ke yi, Safwan a d'akina ya ke. bayan na sallameshi ya ta fi wajan aikin da Mudi ya ne ma mai a kamfanin shinkafar da ya ke aiki. Safwan ya na 'daya daga cikin masu d'ura shinkafa a buhu su sa a inji ya rufe bakinta, sannan in za'a sa a mota a tafi da shinkafar zuwa store d'insu a Bauchi. su za su yi dakon shinkafar.
Lallab'awa na yi na shiga d'akin Badiyya dan muna zaune lafiya kan mu a had'e ya ke sosai, dan duk zuk'e jikina da na ke yi, Badiyya tak'i yarda fur, a jiki ta dinga jana, kuma na ga Safwan na k'aunar hakan dole na saki jiki da Badiyya.
"Ah Sadiya ya dai yau na ganki haka lafiya dai ko?" Sai da na zauna tukunna na ce."
Ke dai bari Badiyya rai dangin goro, yau jikin dai sai lallab'awa kawai na ke yi. Amma ya maganar mu, dan Allah kin yi mai maganar kuwa? Na ga ya shigo nan kafin ya fita."
Dariya ta sakar mun
"Wallahi Sadiya na yi mishi magana, kuma cikin yardar ubangiji ya amince da hakan, ya ce mun zai karb'i takaddun naki, zai je asibitin da kan shi zuwa gobe akwai abokinshi likita zai kai mishi, ya ne ma miki gurbi, dama mu na da k'arancin mata a harkar kiwon lafiya, ni kaina sai na ji dama na yi boko, ko dan in ba da tawa gudunmawar ga d'umbun lada da zan samu." Ajjiyar zuchiya na sauke na dinga yi mata godiya, ita dai sai dariya ta ke yi mun.
"Amma fa ya kwab'eni kan cewar kar in fad'a miki. Sai ki ja bakin ki ki yi shiru." Magana na bud'e bakina zan yi, wani tari me had'e da amai ya tunk'uro mun. A guje na isa madugana na dinga shek'a amai Badiyya na kaina ta na mun sannu, na yi amai sosai a wajan. Da taimakon Badiyya na gyara bakina da jikina da na soma b'atawa. Ita ta kaini har kan gado na.
"Alhamdulullahi abun naima fa ya samu, yau zan mallaki k'aton goron albishir kenan."
Hannunta na rik'e ina haki na ce.
Badiyya dan Allah kar ki sanar da shi komai, ki bari takaddar samun aikina ta zo hannuna, na baki dama ya ji a bakin ki."
"Toh babu damuwa, amma na yi farin ciki matuk'a. tsawon shekaru sama da goma sha muna neman d'a amma sai yanxu Allah ya amshi rok'onmu. Sadiya ko akwai wani abun da ki ke sha'awar ci?" Kai na girgiza mata na ce.
"Zan lallab'a in je wajan Innah akwai kunun tsamiya shi kad'ai na ke sha'awar sha." Ta ce
"Amma za ki iya zuwan? Ki huta mana" Dariya na yi mata.
Ai ba na jin ciwon komai, dama amanne ya dame ni, kuma da na yi sai na samu sauk'i, zan lallab'a"
B'arayin Innah na wuce, a can na wuni cur, har abincin dare a can na ci, kasancewar Safwan a d'akin Badiyya ya ke yau.
Ina zaune ina matsa ma Innah k'afa, mu ka jiyo sallamar Safwan, hannunshi rik'e da jaka, ga Haidar na biye da shi a baya."
Na yi farin cikin ganin Haidar sosai, shima yaron ya yi farin cikin ganina, sai tumurmusata ya ke yi. Innah ta dinga jan Haidar da wasa, shi kuwa da ya ke mai d'an banzan surutune, sai ya sake da'ita kamar sun saba sosai.
Bayan mun tafi b'angarenmu, a falon Badiyya mu ka ya da zango, kamar yanda ya ke a tsarin Safwan, duk d'akin da ya ke, toh anan za'aci abinci ayi hira kafin a watse. Muna shiga Badiyya ta soma murnar ganin Haidar, na ji dad'i yanda kowa ya amshi Haidar hannu Bibbiyu ba kyama."
Dama Kano ka ta fi Safwan shine ko Labari? Dariya kawai ya mun ya na kallona.
"Uhm ai d'aurin Auran Mama na je, an d'aura auran, shine na tawo da Haidar, ta yi mana k'ok'ari ai." Kunya ce duk ta lullub'eni a wajan har na kasa cewa komai." Abinci mu ke ci, da ya ke miyar ganye ce sai na ji dad'in abincin sosai, ina gamawa na rik'e hannun Haidar na ce.
Toh mu kam za mu ta fi, bacci na ke ji sosai."
Safwan ne ya mik'e.
"Mu je in ra ka ku."
Sallama mu ka yi da Badiyya, mu ka fice, Haidar na saman kafad'ar Safwan a kwance"
A kan gadona ya shinfid'eshi, har ya yi bacci abunshi, rumgune ni ya yi a jikinshi yace."
"Ya a ka yi ne uwar 'ya'yana, plz ki yi ma Haidar k'anwa mana." Dariya maganar ta shi ta ba ni, kanshi na shafa na ce.
Lokacine kwanannan za ka ji kyakkyawan labarin da zai dadad'a rayuwarka, ya zama sanyin idaniyarka."
Cikina ya shafo idanu a lumshe ya ce.
"Allah yasa Uwar 'ya'yana."
Ameen
Saman sib d'ina ya zarce ya d'anyi bincike a wajan, takaddun makarantata ya d'auka ya fice. Da ido kawai na bi shi, kaya na tub'e, wanka na je na yo, na zura rigar bacci mai sauk'i. Ina kwanciya sai bacci.
Asuba ta gari
mrs Bukhari ce
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
Instagram links👇
https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Facbook group
https://facebook.com/groups/463653111781414/
Telegram links
https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
MRS BUKHARI
69-70
Washe gari ma, haka wunin ya k'are mun a daddafe na ke yin komai, dan laulayi na ke yi sosai. Yau a d'aki na wuni a kwance, Innah da sauran matan gidan sun tafi Bauchi ana bikin Madina d'iyar Anty Saliha, Badiyya ma ta tafi, ganin ba na jin dad'ine Innah ta ce in zauna a gida kawai. Na dai ga ta fita ta na d'aga hannayen ta sama halamar ta na godiya ga Allah. Murmushi na yi dan na fahimci Innah ta ga ne a wanne halin na ke.
Da daddare mu na zaune ni da Haidar, na gama amai kenan na shigo ina nishi, na jiyo dawowar su Badiyya.
Innah ce ta soma shigowa ta same ni sai ni shi na ke yi, duk na galabaita.
" Sadiya, laulayin ne ya ke baki wahala haka? kai Allah ya raba lafiya.Allah na gode ma in da rabo ashe zanga jinin Safwan."
Wuff Safwan ya shigo d'akin, Badiyya na biye da shi. Sai murmushi take yi.
"Innah na ji kamar kin ce laulayi ko?" Duk ya bi ya rud'e dan ji ya ke yi tamkar mafarki."
"Eh Safwan laulayi, juna biyu gareta, Allah ya amshi addu'o'inmu
Sujjada Safwan ya yi na godiya ga Allah, ya kusan minti goma a durkuse yana mai godiya ga Allah. Innah sai sharce hawayenta ta ke yi. Safwan d'ima da hawaye ya d'ago a fuskar shi.
Sannu kawai ya shiga jera mun ya ma rasa ina zai sani. Innah tace.
"Me ki ke son ci Sadiya?" Cikin munfashi sama sama na ce mata.
Tuwo zanji."
"Toh shikenan, Badiyya sai ki je wajan Jamila ta zubo mata tuwo, aiki ai ya same ki, dan ko tsinke Sadiya ta dena d'agawa a gidannan. Kai kuma dole Sadiya ta koma turakar ka kwata kwata. Haidar ma tafiya da shi zanyi, jibi zan tafi b'oto da shi zan ta fi."
Sallama ta yi mana, ta ja hannun Haidar su ka wuce.
k'ank'ame ni Safwan ya yi, ya na jin d'umina da na yaron shi a jikina. Sai shafar bayana ya ke yi kawai.
Badiyya ce ta yi sallama, Anty Jamila na biye da ita.
jikina na zame a hankali, ina jin kunyar wannan terere.
"Masha Allah sannu Sadiya, kai abun murna. An dad'e ba'a shiga murna irin ta yau ba a family, su Saliha da su Bilki ma duk dai sun ce a yi miki sannu.
Ni dai kaina na k'asa kunya duk ta tufe ni.
Badiyya ta dure mun tuwon a gabana, har sai da Anty Jamila ta fita sannan na soma cin tuwon."
"Badiyya" Safwan ya kira sunanta da
"Na'am" Ta amsa"
"Za ki yi hak'uri zan kasance tare da Sadiya har zuwa wasu 'yan watanni kafin jikinta ya warware. Ina ga hutu zan d'auka a wajan aiki ko na sati ne. Ki d'ebo mata kayanta a sib ki kai mun turakata. Gashi da har na sama mata aiki a Babban asibiti na nan, kuma Dr Jibril har ya d'auketa."
Ina jin haka zumbur na gyara zama na nace."
Zan iya amma ai Safwan, wallahi ina son aikina" Shafar cikina ya yi
"Ni ma haka ina son Baby na, hak'uri za ki yi kawai."
Badiyya dai, mik'ewa ta yi abunta ta yi abunda Safwan ya umarce ta.
Tun daga wannan ranar na zama sha lele a gidan su Safwan, dan ina samun kulawa ta musamman a wajan kowa da kowa. Innah ta na b'oto ita da Haidar. Sai rainon cikina na ke yi cikin k'oshin lafiya, Badiyya ma na ga k'ok'arinta a kaina, dan har mamaki take bani, ko tsinke ta hanani d'auka, hatta ruwan wanka in Safwan ya fita ita ke kai mun.
Su Anty Saliha kuwa duk sai da su ka zazzo ganina, ni kunya ma duk ta isheni.
cikina na da wata uku
Fitowa na yi da 'yar jakata a hannu, Haidar kuma ya na makaranta. Badiyya na yi ma sallama.
B'angaren Innah na nufa.
Innah na fito zan je asibiti. Baki Innah ta washe ta ce.
"Masha Allah, ko Jamila ta rakaki ne, Sadiya.?" Kai na girfiza na ce.
A'a Innah, Anty Jamila akwai k'ok'ari, kullum sai ta aiko mun da tuwo, ban da su goba da yalo."
"Toh shikenan, ki d'an tattaka a k'afa tunda ba nisa, sabida tsinka jinin na da kyau a wajan mai juna biyu. Da
Toh" na bi Innah"
Ahankali na ke tafiya har na isa asibiti, kati na yanka, sannan na ja layi, mata ana zazzaune, masu tsohon ciki, da masu sabon ciki, sai hira su ke yi a tsakaninsu gwanin sha'awa. Zama na ke da wuya, wata baiwar Allah ta k'araso a galabaice, da k'yar ta zauna, sai da na taimaka mata ma.
"wash wannan ciki ya na bani wuya, ko fa bacci bana yi, Allah dai ya ba mu ma su jin k'anmu" wannan matar da ta zo yanzu ce ta yi magana, na ce
"Ameen, amma rainon ciki da rainon yaro bansan wanda ya fi wuya ba." Matar nan cikin cijewa ta ce.
"Kai rainon Yaro ya fi wuya, shifa ciki dududu, wuyarshi ka haihu wata tara zuwa goma. Shi Yaro kuma, sama da shekaru ashirin kana rainonshi da ceta shi, balle ni da Allah ya jarabceni da 'Ya'ya mata har bakwai. Maza uku, ga ciki kuma. Da idanu na bita ina jinjina ma Uwa, ba ya uwa a duk duniya. Ji wuyar da ta ke sha amma ga cikin na goma sha d'aya a jikinta.
Tabbb mu ma su na biyu kuma fa, ai ba ma tantance komai ba.
Tace
"Kinga baiwar Allah, duk ciki haka ya ke zuwa mun da laulayi, ga fitinar yara da hayaniyar su, ga hawan jini ina fama da shi, Duk k'ok'arinka kuma Namiji akan k'ank'anin abu sai ya ce ka ga za.
Da safe in ta ta shi kamar maukaciya haka na ke komawa, in sallami me gidan ya ta fi aiki, Yaran in sallami 'yan makaranta suma su ta fi, yungu yungun muna tare a gida, wallahi har 'yan makaranta su dawo ina aiki. Sai sun dawo ne na ke samu in sa d'uwawuna a k'asa, hayaniyarsu ba za ta barni in d'anyi k'ailulaba, ga makaranta ina zuwa ta adults education dan yak'i da jahilci, yanzu haka na kusa kammala sakandare, kuma zan fad'a tsangayar ilimin likitanci. Rayuwar mace bata tafiya da kyau sai da ilimi, yawan yara bazai hana ka karatuba, ko dan ka inganta tarbiyyar yaranka ai ka je makaranta kai ilimi. Mace uwar al'umma ce fa."
Mamakin wannan baiwar Allah duk ya bi ya cika ni, ga ta tsab da'ita kai ba ka ce ta hayayyafa har goma ba, ga karatu ta na yi, abunda ya fi komai burgeni kenan nace mata.
Sunana Sadiya, kuma kina da ra'ayin in kin kammala karatun likitancinki, ki yi aiki akan abunda ki ka karanta? Dariya ta yi, cikin hali irin na masu tsohon ciki tace.
"Sosai ma, ai amfanin karatun kenan, mata da yawa su na zaune basa neman ilimi, sai su fake da aure ko yara. Kuma dukka basa hana ilimi ko aiki. Shi yasa mu mata mu ka zama koma baya sosai, ko asibitocinmu ki ka shiga, sai ki ga maza sun fi yawa. Mazan da yawa suna k'alubalantar ilimin mace, sai ki ga mace ta dage ta ci karatu dan ta yi ma k'asarta hidima, amma daga k'arshe sai ta rasa mijin aure. Za ki ji wasu har d'an kira su ke yi mata da sunan karuwa ko 'yar bariki, ga masu cewa 'Yan boko basa zaman aure ga raini, Wannan ma ya na dak'ushe k'wazon mata kan neman ilmi." Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
"Abunda ke faruwa a Al'ummar mu kenan, matan da su