Showing 42001 words to 45000 words out of 132173 words
Chapter 15 - JENNIFER COMPLETE BOOK BY Maimuna A.A Rano.pdf
ya nuna mata kusa dashi a darare ta xaune tana noke noke, ya waiwayo ya
kalleta tana rufe rufe jiki da hannunta yai murmushi yarinta kamar ba daxu nagama wanketa ba
sai wani nuku nuku take ko me xata boye?
ajjiye cuf din yayi ya tashi,
xo muje ki gyaramin bed room dina, tabi bayanshi tana hararar shi duk yabi yasata jin kunya
yana shiga ya kwanta akan gadonshi,
dai dai lokacin data karasa shigowa dakin,
mmk abin yabata yanda taga dakin tsab agyare,
oh ! jannah kin san aikin da xakimin ?
girgixa kai tayi tana satar kallon gefen gadonshi,
tausa xakimin nagaji !
da sauri ta kalleshi tana jinjina mgnr,
karaso ki fara,
asanyaye takara so dai dai kusa da gadonshi tai turus tarasa ya xatayi batasan ta inda zata
fara,
ya khaleel plx kayi hkr, ta fada kamar xatai kuka
dago kai yayi yana kallonta takusa bashi dry yadda yaga ta koma lokaci daya kanta akasa,
hannu yasa ya janyota kusa dashi ya xaunar da ita kan gadon,
hkrin me kike bani ?
da kyar tace ina son zan koma daki,
nan inane ?
shiru tayi, tausa nace kimin nagaji bana son musu,
ranta bai so fa ta fara masa a hnkl
lumshe ido taga yanayi kana gani kasan dadin tausar yakeji, waje daya takeyi sbd ta kasa hawa
kan bed din, idonshi alumshe yaji waje daya kawai akeyin tausar ya bude ido yaga a tsorace
take dan bata motsa daga inda take ba, hannu yasa ya fusgota ta xube ajikinshi kamshin
turaren ta ya shaka me kamshi kanshi ya tusa dai dai wuyanta yana shakar kamshin xuwa
gashin kanta hannunshi rike da nata ta mau yakasa saki saboda laushin da hannun nata yake
dashi, hnklinta ya tashi jikinta ya hau rawa, shikam kamar ana turashi ko ina na jikinta sa kanshi
yakeyi, da sauri ta zame kanta, kam ya riketa cikin wani yanayi, idonshi cikin nata, hawaye ya
gani tab cikin kwayar idon ta kadan ya rage su fito ya dago fuskarta ya manna mata kiss a chick
dinta ya saketa, da sauri ta mike daga jikinshi ta dauki hijab dinta ta fice,
a wahalce ya juya yana sakin numfashi yana mmkin yarinya karama ta iya gyara kanta ko ina
najikinta na fidda sihirtaccen kamshi fatarta sumul da laushi kamar ta jarirai nan gaba in ta waye
bai son yadda xata koma ba murmushi yayi jannah dinshi ta hadu xai mata kyakkyawan raino,
hannun yasa zai shafo sajansa ya ji kamshin jikinta a hannun yakara shakarsa sosai yana fadin
ina sonki jannah !
*****************
da sauri ta koma daki tana mmkin abinda ya khaleel yai mata dakinta ta nufa tana shiga ta
tadda hindu da sulthana, wani irin kallo sukai mata hade dayin dariya bata tanka musu ba ta
cire hijab dinta tana kokarin kwanciya sulthana tace anty jannat ba acen xaki kwana bane ?
bata ta kan mata ba,
wllh anty jannat Allah yana fishi da matar da take juyawa mijinta baya,
hindu tana dariya tace yauwa sulthana tunasar da ita,
waiwayowa jannat tayi ta hararesu jarababbu yau kam duk jarabarku baxan tanka muku cikin
daren nan ba in kun gaji da neman fdan sai ku kwanta, ta juya musu baya
sulthana tace sorry anty jannat plx tashi ki bani shawarar na matsu naji kin san fa ina son
ya haisam,
hindu ta katseta,
wai je bakya jin kunya ?? ki budi baki kice kina son wani ?
dan Allah ki dinka abu da tsari,
hararta sulthana tayi akufule tace idan ana mgnr kunya hindu kina da bakin da xaki ce kina
da ita ?
ai babu me sauki a cikinmu irin jenny, ta kama baki sbd hararar da jannat tai mata sorry na
manta jannat zance, cikin daure fuska tace ki kiyaye gaba plx bana son wannan sunan
hindu tace rashin kunyar da kikeyi sulthana bazan taba yin irintaba
tsaki sulthanan tayi tanawa hindu kallan sama da kasa ke abinda kikeyi waxai iya shi ? ko
mazan ma da sukeyi ba kowanne namiji ne xai iya ba balle ke mace,
cikin fada hindu tace zan wanka miki mari fitsararriya,
farr sulthana tayi da ido ta ya b'una fuska ke kuma fandararriya
jannah ce ta katsesu haba dan Allah gsky ku kyaleni ko kowacce ta tafi dakinta kullum sai
kun biyoni sannan baxa a xauna lafiya ba,
hindu tace sai dai ke kifita ba inda zani,
sulthana tace shareta anty jidda bani shawarar yanda zan shawo hnklinsa kin san ita ba
abinda ta iya sai rike bindiga da baraxana da ita,
dariya hindu tayi sbd rashin kunyar ki yasa keda kika iya soyayyar kina so ba'a sonki
shiru sulthanan tayi hmm anty hindu kenan baki san ni bane na wahalar da samari banta ba
son kowa araina inba haisam ba karkiso kiga tulin samarin dana ke dasu larabawa yayan
sarakai da na attajirai
soyayya daban take bata daukar matsayi ko mulki na yadda haduwar jini ce kawai,
anty jannat ina jinki,
ajiyar xuciya jannat tayi idan xaki kiyaye ki jure,
tsaki tayi kinga anty jannat ke shari'ah ce da xaki dinka kafamin sharadi ?? kawai ki bani
shawara dan ma kin ga ina lallabaki?
girgixa kai tayi zan bk ne sbd ke macece ciwon ya mace na ya mace ne ba dan halinki ba,
soyayya ba hauka bane dan kina son mutun ba hauka xaki tayi kina babatu har raini ya
shiga tsakaninku, muddin kina shishshigewa namiji da nuna masa mahaukaciyar soyayya dole
ya tsaneki ko da kuwa yana sonki burin namiji yasamu mace me aji, aji bawai wulakanci ba sbd
yanmata basa tantance aji da wulakanci, wulakanta mutun bashi da kyau duk kaskancin sa,
koyaya ansan mace da kunya idan baki da ita kina da kawaici ko baki iya kauda kai ba dole ki
koya kibawa kanki kima da daraja ki canza wannan dabi,un da kike nuna masa agabansa ki
shareshi, ba gaba ba, sama yake dake gaisuwa kawai xata dinka hadaku itama bawai ki saki
fuska kina kwasar dariya ba, a a ba yabo ba fallasa daga gaisuwa kada ki yadda wata mgn ta
hadaku dashi, jim sulthana tayi tana jinta,
sai ki janyo hnklin shi ta abinda yakeso bawai yadda xai gane ba cikin rashin sanin baki son
yana so ba, da sauri ta kalleta anty jannat ta yaya ban gane ba ?
kinga ya haisam yana da son kwalliya da nutsuwa sannan yana da son cin abinci kusan
duk mazan yanxu suna da son wayan nan abubuwan,
misali kiyi girki ki xubawa kowa shi kuma ki tura masa plate din kice ya xuba kinga yasan ke
kikayi idan yana waje yi kokari ki kama kanki koda xakiyi surutun kiyi shi me ma'ana xaki ga shi
kanshi ya fara shayinki,
jikinta asanyaye tace idan kuma baya sona fa ?
dariya jannat tayi kin san wani abu ? duk wanda kikejin soyayyarsa aranki shima yana ji xaiyi
wuya kisamu wanda bayajin hakan ko yaya idan kika ga ya kyaleki kin nuna xakewa shine
xaisa yaji ya tsaneki, kada ki kuskura ki nunawa namiji xakewa da rashin nuna kimarki ki nuna
kina da kima da daraja kada ki nuna masa soyayyarki afili kija ra'ayinsa ta hanya mai kyau
wacce xata kara miki kima awajansa, yasan lallai ke ta mutunci ce, ba namijin daya keson
ballagaza, ki kyale ya haisam kiyi kamar ba sulthanan da cen ba dariya tayi cikin jin dadi ngd
sosai anty jannah
*********************
washe gari bayan ta idar da sallar asubah gari nayin shaa ta koma bacci bata tashi ba sai 11:00
tayi mmkin baccin datayi ta shi tayi ta shiga toilet tai wanka hade dayin brush ta fito kenan taji
karar test murmushi tayi dan tasan mr coffee ne dauko wayar tayi ta duba ....nashigo daxu kina
bacci munta fi abuja da dady yau ko gobe xamu da wo ki kula da kanki....
jim tayi xuciyarta ba dadi asanyaye tace Allah ya dawo da ku lfy ta shirya cikin riga da siket na
less mara nauyi kalan brown da kwalliyar golden yellow ajikinshi falo tayi breakfast ta sakko
babban falo ta same su dukansu ta xauna kusa da hindu tana gaishe da momy cikin kulawa da
fara'a momy ta amsa, karar motoci sukaji, wasu mata suka shigo tare da jidda datake kuka,
ganinsu yasa gaban jannat ya fadi tana kallon matan tagane dayar kanwar dady ce wacce ta
xageta lokacin sa ranar jidda, da fara'a momy tace sannunku da xuwa,
dayarce tace dakata hajiya fiddausi " ba gaisuwa ce ta kawo mu ba, jidda na kwance jikin
ummanta tana kuka lallai bashir ya nunamin ban isa da yayanshi ba tunda har xa a daura auren
danshi yakasa sanardani sbd munafunci irin naki, dayar matar da jannat bata santa ba cikin
fada tace hjy fiddausi burinki ya cika kin mallake mana dan'uwa sai abinda kikace sai abinda
kikeso shi akeyi ke ishashshiya a daura auren waccen arniyar ta nuna sulthana atunaninta itace
jannat da ibraheem bamu sani ba sbd tsabar munafunci irin naki, a kufule sulthana tace wllh ni
ba arniya bace kije cen kinemi arniya inda take to wai ma suwaye ku da xaku xo kuna yi mana
haushi cikin gida ?? da sauri momy ta toshe bakin sulthana idan na isa dake sulthana kar na
kuma jin bakinki, sakin baki sukayi hade da yiwa sulthanan wulakantaccen kallo, da kyau
dangin agumi yar masu sai da garar garau akan titi, sulthana ta zaburo momy ta riketa na miki
mgn ba ruwanki dani sukeyi kiyi shiru,
hjy amina kiyi hkr ba a kyauta ba amma dadynsu da shi khaleel din sunta fi gidanki ta nuna
daya matar cen abuja su fada miki yadda abun yake da niyyar in xasu dawo xasu biya wajan hjy
hadiza, hjy hadizan ce momyn jidda cikin tsawa ta katseta rufemin baki munafuka, ran momy
abace tace ku sani kufa kannan mijine ba yayyansa ba ba kowacce mgn ya dace ko yabamin ita
ba, sulthana ta fashe da kukan takaici momy me yasa kika hanani mgn ? ki kyaleni na nuna
musu jarabar sabon jini rikota momy tayi a a sulthana,
haka suka kare musu tas xagi nacin mutunci sannan suka tafi zigum kowa yayi a falon
sulthana ce kawai take mitar jarabar an hanata kwatawa momy yanci jikin jannat asanyaye ta
hau sama hawaye sosai takeyi tana kukan bakin cikin cin mutuncin da kannan dady sukaiwa
momy duk a dalilinta gsky momy da dady mutane ne nagari baxata gushe ba har abada xata
cigaba da yi musu addu'a har karshen rayuwar ta ranar kam gidan kwanan bacin rai kowa yayi
*****************
washegari da safe tana tashi test din ya khaleel ta gani na suna hanya sun kusa isowa hindu ta
shigo fuskarta ba walwala jannat ta kira sunanta,ina son xuwa gidana nida sulthana zamu
kwaso kayanmu masu amfani kin san tunda muka baro cen bamu koma ba,
da murna jannat tace nima zan biku ina son naje naga mamana da su david,
xaro ido hindu tayi waya ce miki yanxu irin da kike ? shari'a bata yadda ki fita ko nan da nan sai
da ixinin mijinki,
a sanyaye tace yaushe xaku tafi ?
hindu tace sai yamma,
da murna tace yauwa time din ya dawo sai na nemi ixininsa,
********************
kitchen ta shiga ta shirya masa abinci kala kala wanda tasan yana so karfe biyu da rabi na rana
ya dawo ya bar dady acan shi sai gobe xai dawo sbd yana da mittin,
tana shiga dakinsa ta tadda ya fito daga wanka ya xauna kusa da ita hade da kunna tv yana
kallon tashar world sinima ta janyo flask xata fara xuba masa coffee dan tasan shiyake fara sha
kafin yaci komai,
dakatar da ita yayi kinga " tashi ki cire wannan hijab din na jikinki a shagwabe ta kalleshi ya
kau da kai yana kallon tv ganin ba wasa afuskarsa yasa ta cire ta ajjiye akan kujerar kusa dashi,
ta dauko cup ta xuba masa coffee ta mika masa ya waiwayo xai amsa ya kalli kayan jikinta sun
mata kyau sosai kamshin turarenta mai dadi ya cika dakin shi ya amsa yana sha kadan kadan
ta xuba masa abincin ta ajjiye ta mike xata fita,
ina xaki tafi ? tayi shiru dawo ki xauna anan sai nagama cin abincin ya nuna mata kusa da shi a
darare ta xauna tana jin kunya sosai ya kalleta yaga tayi nesa dashi daure fuska yayi ya nuna
kusa dashi sosai, nan nace ki xauna, turo baki tayi ya yi murmushi sbd turo bakin yai mata kyau
ta dawo kusa dashi ta xauna tana bata rai itama girgixa kai yayi yace yarinta ko meye na bata
ran ?
dawowarta kusadashi yasa yaji kamshinta sosai sunkuyar da kanta tayi yasa hannu ya dago
mata da fuskar ta suna kallon juna taja baya ya danji haushi hakan yasa ya fisgota jikinshi yana
shinshinar kamshin ta yarasa gane wanne irin kamshine me fusgar sa da take sawa
dankwalinta ya xame ya kalli gashin kanta baki sidik gam ya riketa ajikinshi laushin fatarta na
fusgarshi da sauri ta tureshi hade da shagwabe fuska, plx ya khaleel sakin ta yayi ta matsa
nesa dashi lumshe ido yayi ta mike da sauri ta xira hijab dinta gab dazata fita tace,
zamuje mu kwaso kayanmu sannan zanje na gaishe da maman dadiv, kai kawai ya daga mata
cikin wani yanayi yarasa yadda akayi karamar yarinya take kokarin ta iya jan hnkl,
tana fita taci karo da sageer ya gaishe ta a kunyace ta amsa ya shiga dakin khaleel ya ganshi
wani iri , dariya sageer yayi hade da rike baki, cikin zolaya yace ango ango a haka xa'ai karatun
??
harara khaleel yai masa hade da janyo wata hirar
******************
da murna ta fada musu ya bata ixinin ta je, a shirye suke momy tace danjuma ya kaisu, suna
xuwa gidan yaran hindu suka tarar suka shiga ciki suna kwaso muhimman kayansu, da sauri
boy one ya shigo madan ya kira hindu kinyi bako, da mmk ta kalleshi waye ? sadik osasa ne, da
sauri ta mike a tsorace me yaxoyi ?? kwantar da hnklin ki madan yace wai yana son kuyi muhimmiyar mgn ne, afusace ta fito suka
biyo bayanta a falo suka taddasu ya dora kafa daya kan daya da murmushi yace hindu,
sulthana, Jennifer, gsky na tayaku murnan ganin juna kwantar da hnklinki hindu ba fada ko
tashin hnkline ya kawoni ba, taimakonki naxoyi tunda kin bar min dubai dama ke kadaice kika
fini a harkan nan tamu, kuma kin barmin shiyasa naxo nai miki tayin taimakona ko xaki iya siya,
ranta abace tace ina jinka , su kuwa su jannah da sulthana binshi sukayi da kallon mmk,
kin san ni aminin marikinki ne ?
yanxu haka kina neman iyayenki meya sa kika manta dani alhali kinsan nasan duk wani sirrinshi
?
asalima kina kwana arba'in aduniya aka kawo mishi ke tare dani dashi akai mana gargadin
komaarki gida daukan ranmu, nasan mahaifinki da mahaifiyarki xaki iya biyana na fada miki
suwaye iyayenki ? ajiyar xuciya hindu tayi kudin har nawa kakeso ? sulthana ce tayi tsaki kaga
malan kaxo kana yiwa mutane wani gadara gadara kawai inxaka fada ka fada, kallonta yayi da
murmushi yace kimsan ahmad al'mansoor ?
araxane da kuma mmk ta kalleshi hade da murguda baki,
ya taba bani aiki akan ki yana so na lalata miki fuska da acid ganin kece yasa na kyaleki, sbd
nasan ke wacece, da fada tace dakasan ni wacece sai akayi yaya ? nifa bana son gadara
kawani tara wani uban kasumba ko kyan gani baka dashi kanawa mutane dariyar mugunta wai
kai mai adalci kawai ka fada mana suwaye iyayenmu ? idan xaki iya biyana gashi ya miko
mata karamar takarda rubuce da adadin kudin dayake bukata hindu ce tai caraf ta mashe ta
duba xaro ido tayi tana kallonsa plx osasa baxan iya biyan wannan kudin ba aina zan samu,
dariya yayi haba hindu kece fa a yanxu in kikai niyya tsab xaki samu nin kinsu kin mata hikimar
ki ta damfara ? kinfi kowa kwarewa girgixa kai tayi sulthana ta warce takardar ta duba ta xaro
ido itama ta mikawa jannat itama xare ido tayi ya mike cike da ji da kansa kuje kuyi shawara
amma zan taimakeku da mgn daya ku kiyaye yawo barkatai dan har yanxun wanda suka
tarwatsa muku rayuwa sunana bibiyarku da mmk suka kalleshi ya fice ya barsu jigum sukayi
suna kallon juna cikin tashin hnkl ga koshi ga kwanan yunwa, kowacce tambayar kanta su kuwa
me sukayi ake bibiyar rayuwarsu haka ?
By