Showing 6001 words to 9000 words out of 132173 words

Chapter 3 - JENNIFER COMPLETE BOOK BY Maimuna A.A Rano.pdf

12 Apr 2025

6845


nan kalau suntafi skul nayi missing dinku mama ta fada ashagwabe sorry Jennifer muma duk
mun damu darashin ki kusa damu ranar Sunday kixo nan gida mutafi Church tare da brothers
dinki damm ! Gaban Jennifer ya fadi rabon ta da xuwa Church har ta manta to mama zanxo
yawwa kina dai aikin ki akan kari ko ? Eh tafada jikinta duk yai sanyi baki da wata damuwa ko ?
Babu mama haka ake so sai xuwa anjima zan xubawa customers abinci ltr yata tayi mata addua
takashe wayan wulli Jennifer tayi da wayan ta dafe kanta Sam ! Xuciyarta bata son xuwa
Church kishingida tayi tana tuna abubuwa masu yawa da suke damunta takasa fadawa kowa
kuma tana tsoron yankewa kanta hukunci asalima tarasa da inda xata fara warware matsalarta
amincewarta aiki a gidan nan yana daya daga cikin warwarewar tunkushashshiyar matsalar ta
takuma rasa ta ina xata fara mikewa tayi jikinta asanyaye ta fito daga dakinta tayi hanyar
kitchen dan yau baxata ci abinci da mutanen gidan nan ba kicibus sukayi da zahra ta zabgawa
Jennifer wani kallo na raini cikin isa da izza ta bude baki da kyar kamar bata son maganar kije ki
gyaramin daki ta wuce tana rufe hanci Jennifer ta bita da kallo ta dawo baya tai hanyar dakin
zahra ta bude kamshi me dadin shaka ya bigi hancinta wannan shine karon farko da ta taba
shigowa dakin nata ko ina tsab haka dai ta karkade ta share da wanke toilet ta fesa air
freshener ta sauko down stairs a falo ta gansu ita da ya haisam gabanta ya fadi taxo xata wuce
atsorace hade da faduwar gaba kee! Taji muryar ya haisam jikinta na rawa ta xo maza da Allah
ya fada cikin tsawa ubanwa ya baki ixinin cin abinci damu tayi shiru kanta akasa mgn nake miki
! Da sauri tace ya haisam zahra da take kallo tace na fuskanci ya mahboob yana da feelings

akan yarinyar nan tsaki haisam yaja cikin jin haushi shi ya Sani amma baxa a kara cin abinci da
itaba inyaso yabita dakinta suci tare hmm zahra tayi mmkin dayake bani da baya iyajin warinta
ta fada tana done hanci wari ?? Jennifer ta maimaita aranta zahran ta waiwayo ta kalli jennifer
tun xuwanta gun sai yanxu ta kalleta hnklinta na kan tv da take kallo shishshigin naki yanaso
yayi yawa kitsaya iya matsayinki tashi ki bawa mutane guri kazama kawai ya haisam yafada
yana jefa mata mugun kallo na kiyayya da tsana da sauri ta mike tayi bangarenta ranta bace
abincin daba taciba kenan ta kwana da yunwa da bacin rai 






6:00am ta tashi ta gama komai da wuri dan batasan su dinka haduwa da mahboob taga ma tayi
wanka ta bar daki ta yi can bayan gida inda babu Wanda xaiyi tunanin xuwanta wajan ta jinkina
hade da sakanta jikin ginin wajan tasan tabbas mahboob ya ganta damunta xaiyi da tmbyoyi
koma yace taxo suyi break fast itakam yanxu kome xai mata baxata kara xuwa wajan cin
abincinsu koda kuwa xata yini da yunwa tana nan zauna har gyangyadi ya kamata abinka ga
Wanda baisamu ishashshan bacci ba hk tayi baccin axauna 




9:32am ta farka a gigice sbd rana ta daki fuskarta da sauri ta mike tayi dakinta tasa mukulli ta
rufe tayi kwanciyarta tasan basu gama break fast dinba tayi baccinta me isarta dan safiya ne
kadai time din hutunta duk inda 12:00pm ba ita ba sauran Hutu 




Bugun kofar dataji ne yasa ta mike zumbur akuma tsorace ta bude kofar karaf suka hada ido
yana murmushi sannu sarkin baccin safe ta daure fuska dan tana son yakiceshi ya shigo dakin
daxu ina kika shiga naita nemanki da safe ? Tayi shiru kanta akasa sbd ya tsareta da idanuwa
nayi wani aikine OK ya fada zanje unguwa sai yamma xan dawo me kikeso na taho miki dashi
?? Tayi shiru taji dadi sosai ta girgixa kai bana son komai ya bata rai baxaiyiyu ba zanyi fushi
muddin kika ki fadamin shirun ta kumayi sbd batason me xatace tana so ba ya juya ya fice
ranshi abace tabi bayanshi da kallo tana jin haushin kanta tayi rashin hnkl bai kamata tayiwa
Wanda ya damu da ita haka ta shi taje dining ta kwashe kayan da sukaci abinci ta gyara wajan
ta Dora na rana telephone tayi ring Momy ta gani ta amsa jennifer in kin gama kixo toh Momy ta
amsa aladabce 

Sauri tayi ta gama tana adduar Allah yasa ba laifi tayi ba a falo ta taddasu ita dasu Rubayya da
zahra suna hira suna kuma kallo kin gama jennifer ? Momy ta tmbyeta tana kallonta eh Momy
na gama OK yayi Kyau sannu da aiki Allah yasaka amin Jennifer tafada tana jin dadin adduar
Momy xakuje kasuwa ne keda Rubayya yau dadyn su xai dawo xuwa yamma tayi murmushi
Allah ya dawo dashi lfy amin Jennifer kije ki shirya to tamike da sauri tayi dakinta a gaggauce ta
shirya doguwar riga tasa baka arabiyan gown wacce rubayya ta bata tayi rolling din kanta da
gyalen rigar ta fito tsaye ta tadda rubayyan kusa da motarta tana waya gefe taja ta tsaya tana
kallon bayanta Jennifer ta lumshe ido Rubayya tana matukar birgeta sbd tana bata darajta dan
adam duk kaskancin Sa ta waiwayo tana kallon jennifer fuskarta dauke da murmushi muje ko
jennifer ta bude mota tashiga suka fice 




3:27pm dai dai suka dawo daga kasuwa gaba dayansu suka fada kitchen sbd 7 dady xai dawo
girki sosai akayi kala kala basu gama ba sai wajan 5:00pm da wani abun alokacin hjy uwani me
kawowa Momy yan aiki ta kawo yanmata su biyu wayanda xasu yi aiki tare da jennifer dukkansu
hausawa ne daki jennifer ta shige tana adduar Allah yasa kada su dinka nuna mata wariyar
launin fata wanka ta shiga toilet tayi ta fito tana shafa mai bayan tagama ta xo kitchen ta Debi
abincinta ta koma daki ta ci ta xo mayar da plate din kitchen Momy ta kirata falo cikin fara a
Jennifer ga mataimaka kin samu jennifer ta kallesu sannunku da xuwa suka bude hkr suna
dariya yawwa sannun ina yini ? Suka gaishe ta ta amsa da lfy lau xuwa gobe Jennifer sai ki
nuna musu kan aikin yau gidan namune duk muna busy inyaso na raba muku aikin da kowacce
xatayi toh Momy ki kaisu dakin kusa dake nan xasu xauna ta mikawa jennifer mukullin dakin ta
amsa sannan tace su taso su biyota da jakar kayansu ta kaisu dakin nasu ta nuna musu yadda
xasuyi amfani da komai na dakin sannan ta koma kitchen ta gyarashi tsab takwaso girke girken
ta Jere a dining ta gyara gidan tasss ko ina ya dau sheki ta kunna turaren wuta ta koma dakinta 



7:35pm taji motoci na shigowa gabanta ya fadi dady ya dawo itakam bata sanshi ba sai photon
shi kawai take gani taji hayaniya na tashi daga babban falo tasan farin ciki sukeyi da murnar
dawowar dadyn nasu oh inama itama rayuwarta irin tasu ce? Da sauri ta kauda tunanin da yake
tunxurota 




Wajan goma taji tsit jikinta asanyaye ta shigo falon ba kowa yayi kaca kaca ta kwashe kayan
wajan ta kai kitchen ta share ko ina nan da nan wajan yai Kyau ta koma kitchen ta gyarashi ring

taji na telephone da mmk ta daga muryar ya khaleel taji kixo ki gyaramin daki taxaro ido cikin
Daren nan ina tuni ya kashe waya takalli agogan kitchen din 11 saura 






                


             BY   *UMMEEEEY*
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍




          15%16


Hon yayi me gadi ya bude musu get ya shige gidan sai yanxu ya samu nutsuwa tun haduwarsu
da yan fashi shikam haisam xuciyarshi ta tafi kololuwar tunanin ya akayi Jennifer taxo Dubai
sata ?? Wacece ita ? Me takeyi a gidansu Sam hankalinshi baya tare dashi bude kofa yusuf
yayi ya fito daga motar yana yiwa haisam wani irin kallo kafito mana haisam koda yake kaika
Sani inma anan xaka kwana cikin motar ya wuce cikin gida yana mitar halin da haisam ya sashi
bin Yusuf din yai da ido yana girgixa kanshi baka San mmkin dana ke cikiba nafika tashin hnklin
da kashiga baikai Wanda nashiga ba yanxun nan kwakwalwarshi ta rude yarasa wanne irin
tunani xaiyi waya ya janyo daga aljihu ya kira zahra ba ta dade tana ringing ba ta daga muryarta
adashe da alama bacci takeyi kiran wayar ya tasheta arikice yake tambayarta ........zahra ina
jennifer da mmk ta amsa da bansani ba ya haisam me ya faru ??? No ! No ! Dubomin tana cikin
gidan ta mike daga kwamciyar da tayi araxane menene wai ya haisam kafa dagamin hnkl da
sauri ya canza voice dayin dariyar yake oh ! Zahra bakomai ina son sata wani aikine tayi ajiyar
xuciya hade da yin dariya haba da katashi hankalina ta fito daga dakinta tai bangaren su
jennifer a hanya ta ci karo da Sa,a ke xo ta kira ta a ladabce Sa,an taxo hade da sunkuyawa ina
jennifer ? BATANAN TUN JIYA kaninta ne ba lfy ok ta katse Sa,an jeki kawai shima haisam din
kashe wayar yayi dan yaji amsar da Sa,a ta bawa zahra batanan tun jiya baiji karashen zancen
ba gumi me xafi ya rufeshi jikin shi ya fara rawa me ya ke shirin faruwa ?? Meyasa tahana
akashe shi ?? Tabbas yasan ya kuntata mata dafe kai yayi arikice yarasa wani irin tunani xaiyi
munafuka !! ya fada axuciye Allah ya Toni asirinki ya jingina jikin kujera xuciyarshi na ingaixashi
Allah Allah ya keyi gobe tayi ya dawo 9ja yaji dalilin zamanta gidansu 

Daren ranar baiyi baccin kirkiba gaba dayanshi arikice yake haka yaje meeting din batare da ya
fahimci me aka tattauna ba da kyar ya saita nutsuwarshi ya fahimci kadan suna gama meeting
din ya fito da gaggawa yai airport dan ya kagu yaxo gida ya tahumi munafukar yarinyar nan
azzaluma macuciya barauniya 




10:00pm ya iso 9jaa sai wajan 11 ya isa gida dare yayi haka yaita sintiri da ga bangarensu xuwa
cikin gida da kyar bacci ya kwashe shi 



Tunda wuri yadda ta saba ta fito dora musu break fast sbd kwananta 3 ba agidan ba tana wajan
jinyar David suwaiba ta tarar a kitchen din suka yiwa juna murmushi suka gaisa suna girkin
suna hira kwatsam suka ganshi akansu daga shi sai dan gajeran wando dama al,adar mazan
kenan yawo da kana nan kaya kowanne irine da sauri ta kalleshi atsorace take gaishe shi ya
kura mata ido yarasa tana ina xai fara tambayarta sbd xuciyrshi da take akufule miko min tee ya
fada yana huci da sauri ta bude flask ta xubo masa a cup ta mika masa ya kalli tee din yana
jujjuyashi ahannunsa ya watso mata shi cikin zafin nama ta goce duk da haka sai da ya samu
gefen kafadarta ta kwalla kara sbd xafin da taji ya nuna ta da yatsa sai dai yakasa cewa komai
sai girgiza kai kawai yake yakaiwa iska naushi da hannunsa yai tsaki me karfi ya bar wajan da
sauri hade da ajjiye cup din hannunshi nesa da kitchen din su ya xauna yana tunanin hanyar da
xai bullo mata abinda yabashi mmk dakiyar daya ga tayi cikin gwaninta da yaudara kamar basu
hadu da ita a Dubai ba duk yadda akayi yarinyar nan bakar shedaniya ce bai kamata kai tsaye
ya damketa ba kamun kazar kuku ya kamata yai mata xaibar wannan a cikinshi cikin lokaci
kalilan zai mata mugun kamu binciken wacece ita xai farayi ya alkawarta sai yago dalilin
zamanta cikin gidansu 



Kuka takeyi sosai suwaiba na bata hkr kiyi hkr Jennifer wayeshi ? Cikin kuka take bata amsa
dan gidan nan kanin ya mahboob ranar da aka kawoki ya tafi Dubai dama tuntuni baya kaunata
suwaiba dan kawai addininmu ba daya ba ta kuma fashewa da kuka kiyi hkr Jennifer kin San
kowanne kalan mutun da halinsa nikaina naga kiyayyarki sosai a kwayar idonsa kuma na
fuskamci bashi da tausayi ko imani dan me imani baxaiyi abinda yayi ba bakomai suwaiba
komai yana da lokaci addua suwaiba tacigaba dayiwa jennifer tana tofawa a inda ta kone
inshaa Allah wajan bai tashiba kiyi hkr ki koma daki daki zan karasa girkin kai jennifer ta girgixa
kibari mu karasa tunda kin min addua Allah ya saka miki suwaiba na fuskanci kina da adalci da
daraja dan Adam in sha Allah xakiyi albarka arayuwarki dan mamana tana fadamin mutane

masu kyawawan hali da daraja muatane yanuwansu masu adalci da biyayya ga ubangijinsu
suna albarka arayuwarsi kin dace dan wannan halin mamana ta fadamin baiwace Wanda sai
mai rabo ubangiji yake bashi murmushi suwaiba tayi hade da kura mata ido cikin xuciyarta tana
adduar Allah yasa kina da rabon musulunci Jennifer kalanki da nutsuwarki da kamanninki irin
namune Allah mai iko tana mamakin kasancewarta cikin wannan halin Allah y shiryaki Jennifer
shirin addinin musulunci bayan sun gama suka jeresu a dining sannan suka koma daki sukayi
nasu break fast din suna hira jefi Jefi Jennifer na duba konewar da tayi abinda ya bata mmk
kokadan koniyar bata tashi ba ta kalli suwaiba tana murmushi suwaiba kinga ikon Allah
tafashash shan ruwan xafine fa amma kinga koniyar bata tashi ba suwaiba ta saki fuska baxata
tashiba jennifer na miki adduar annabi Ibrahim alaihis salam lokacin da aka jefashi cikin wuta
duk irin wutar da ta tabaki kowacce irice in kikai saurin yinta kika tofa ta tofa yanda bata illata
annabi Ibrahim alaihis salam babu abinda xatai miki ko da yarone ya kone shiru Jennifer tayi
tana tunanin wani abu Wanda babu Wanda yasan menene ciki kuwa har da ni ummee






1:30pm suka gama lunch suka kai musu dining sannan suka dawo daki suwaiba ta wuce toilet
tayo alwala ta tada sallah Jennifer na satar kallonta ta fuskanci suwaiba tana da ilmin addini
daidai gwargwado sannan tana aiki dashi dan akwai son yin ibada akan lokaci tanayin komai
nata anutsu sabanin sauran yan aikin su Sa a da hadiza da ko shiga harkarta basayi tunda suka
San wacece ita novel ta janyo na Hausa tana dubawa na suwaiba ne tagane tana son karance
karancen litattafan Hausa in dai sungama ayyukamsu ta idar da sallar ta dauko musu nasu
abincin Jennifer ta sakko tasa hannu tana kallon suwaiba tai addua sannan ta fara cin nata
bayan sun gama ma sai da tayi abin ya birge Jennifer sallamr hadiza sukaji sannunku yanmata
masu hadin kai to kuxo masu gida suna nemanmu a babban falo da murmushi suwaiba ta
mayar mata da to yanmata marasa hadin kai muna xuwa dariya Jennifer sukayi ita da hadizan
sannan ta bar dakin tana mitar wai suwaiba ta fiya mai da kurji ciwo 





Gaba dayansu ma aikatan gidan suka taro a babban falo dady da Momy ne a ciki kusa da shi
ya khaleel ne hnklinshi akan waya yana danne dannenshi Jennifer tarasa me yake dannowa da
kullum baya gajiya tun xuwansu wajan babu wacce ya dago kai ya kalla cen gefe zahra ce rike
da lpad itama tana game Rubayya hnklinta na kan tv sarkin kallon series films 


Yayana sunnunku da xuwa daddy ya fada da sauri dukansu suka kalleshi cike da mmkin kiransu

da yayi da yayanshi ya aiki ? Ya tambayesu cikin hadin baki suka amsa da alhamdulillah babu
wata damuwa dai ko ya kuma tmbyr su babu damuwa dady to masha Allah na tarakune sbd jibi
dukanmu nida iyalina xamuje umara saudiyya kowacce xata koma gidansu ajibin sai mundawo
dan 2 weeks kadai xamuyi ma aikatan mu maza su zasu kula da gidan banda Ku mata yaxaro
kudi masu yawa yararraba musu sukayi godiya sosai sannan ya sallamesu kowacce acikinsu
murna take banda jennifer da take cikin damuwar rabuwa da yan gidan suna fitowa sukai karo
da mahboob ya harareta suwaiba tasaki hannunta tai gaba ita kuma ta tsaya tana kallanshi
itama ..kinsan fushi nake dake ?? Ya tambayeta tayi dariya a a Yaya mahboob bansani ba
shiyasa na fda miki dan na fuskanci bakisan ina fushin dakeba xo muje garden hira xamuyi ta
xaro ido aikinfa ? Baxa kiyi ba ya bata amsa yana kallonta ta kwabe fuska kar nabar suwaiba
shiittt ! Ya katse ta hade da Sa yatsansa daya abakinshi muje aikinta ne itama tabi bayanshi
bata soba akan dadduma suka xauna cikin grass idon shi akanta Jennifer menene yake
damunki kwana 2 dinnan naga kamar kina cikin damuwa ?? Shiru tayi tana tunanin amsar bashi
dan tasansa da bin kokwkwafi hakane David ne bashi da lfy yana fama da sicler idan ta tayar
masa hnklinmu na tashi duka sbd muna son yaron rashin lfyr nasa yana takura masa Ayya! Ya
fada cikin tausaya kuyi hkr kuyi masa addua Allah ya bashi lfy amin ta fada jibi xamu tafi umara
naso ace tare muka tafi wani daliline me karfi yasa baxa mu tafi tareba amma next in shaa Allah
tare xamu tafi murmushi tayi dan tasan dalilin shine kasancewarta Kristan ne hira sosai yai
mata cike da tsari kasancewar Sa dan tsara zance ya dauko wayarsa sukayi photo tare kala
kala dakyar ya bar ta tashiga gida yna fadin shi baigaji da hirar ba tana shiga cikin gidan taci
karo da ya khaleel a tsaye hannuwansa cikin aljihu ya jefa da kallon da ya saba yimata Wanda
takasa fassarashi 





          Saudiyya 


Sun sauka lfy kwanansu 3 da xuwa haisam yana masallaci yna dawafi bayan an idar da sallar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login