Showing 15001 words to 18000 words out of 132173 words
Chapter 6 - JENNIFER COMPLETE BOOK BY Maimuna A.A Rano.pdf
da
Amma yanxu bama tare kwata kwata ...
Shiru bai dawo masa da amsa ba ya koma wajan ammar ibn Muhammad ya tura masa ....
ngd sosai bros amma ita din wacece haka ??
Yai sa'a shima yana online ya turo masa reply da ....
babbar shedaniya ce hatsabibiya Yar safarar kayan maye da fashi da makami kuma babbar yar
damfara nayi mmkin ganinka da ita sbd nasan kai mutumin kirkine ganinka da hindu xai iya
jefaka cikin masifa dan mutumin arxiki baxai hada sabgarshi da itaba yanxu hk a Dubai wanted
ce .....
Shiru haisam yayi yarasa amsar bashi
Wani test din Muhammad ya kuma
turo mishi.....
Kaima ka shiga tarkonta?? Hindu tana da Kyau kyawunta ke fuskar maza kuma da kyawun nata
take amfani wajan yaudaran mutane kayi gaggawar cireta aranka
.......
Haisam ya tura masa reply da
...
ngd sosai bros naji dadin shawararka kuma zanyi aiki da ita amma ba Sonta nake ba munyi
karatu ne kawai da ita
...
bai ce komai ba Muhammad banda xare ido da yayi
...yana kokarin sauka test din Elmustafha ya shigo da sauri haisam ya duba
..... Dole Ku rabu dan yarinyar ba ta da hali fitsararriya ce
......
Da sauri haisam ya tura mishi da
.....
Hakane wannan kam shine halinta na rashin kunya....
Ya dawo masa amsa .... Neman yarinyar nan nake ruwa a jallo duk lokacin dana ganta sai na
lalata mata fuska kowa ya huta tana amfani da kyawun nan nata tana ciwa kowa xarafi
...... Shi dai haisam mmk ne sosai ya cikashi ....
Dame xaka lalata mata fuska?....
Da acid ....
Wanne laifi tai maka ??...
Ta ciwa ubangidana zarafi har ta mareshi sanadiyyar hk na rasa aikina shi kuma tundaga
wannan lokacin yake bakin ciki zanyi hakanne dan nasashi cikin farin ciki ....
bata kyauta ba ...
Nayi alkawarin kudi mai yawa ga duk Wanda ya kawomin ita in dai xaka iya kofa abude take ga
numb dina nan +9......
Ya karewa number kallo yayi ajiyar xuciya
Sulthana asaudiyya
Hindu a Dubai
Jennifer a 9jaa
Wacece ita ??
Hannu yasa ya dafe kansa wannan al'amari da daure kai yakai Sam yakasa fahimtar komai
xame masa dole ya gano wacece ita ?? Me ya kawota gidansu ??? Lallai ya yadda shedaniya
ce tunda tana nuna msa shedancinta tanayin abu kamar bai taba haduwa da ita a katsashen
nan biyu ba dan karamin tsaki yaja cike da jin haushi xakiyi Dana Sani dan sai na tona mki asiri
awajan mutanen da suka yadda dake suka amince miki
Tana kwance adaki suwaiba na karatun kur'ani duk tabi ta rude tana saurarenta hnklinta
amatukar tashe jikinta har rawa yakeyi wayarta tai kara tana dubawa taga sunan Momy
aladabce ta daga ....Jennifer xo ina son ganinki ....
Ta amsa da toh ganinan Momy da sauri ta mike tai bangren momyn ababban falo ta sameta a
xaune Jidda tayi matashi ta cinyar ta tana kallon tv tashigo falon suka gaisa yauwa Jennifer
xakuje kasuwa tundaxu na aiki danjuma shiru bai dawo ba ga yamma xatayi kuma ba kowa sai
haisam da khaleel nasan bakwa shiri da haisam khaleel xai kaiki da sauri Jidda ta daga kanta
daga cinyar Momy Momy nima xani murmushi momy tayi svd kinji nace khaleel ne xai kaita
sarkin kishi tayi dariya aa Momy bana son ya dinka kallon wasu yanmatan ne a kasuwa ko su
su gane minshi kwara na bi abina rike haba Momy tayi oh ! To sai kibishi kiyi ganinsa ta mike
bari naje na shirya ta ayangance take tafiya kamar batason taka kasa bakin ciki ya dami
Jennifer bata maraba da wannan tafiyar Sam ! Koka dan batayi farin ciki da itaba Momy ta kalli
Jennifer kije ki shirya nai masa mgn toh tace ta mike tai bangarensu ranta abace ta koma daki
ta canza kaya gown tasa ta atamfa blue da adon yellow ajikinta daura dankwali na bata wuya
dan bata saba sakashi ba karamin gyale yellow tasa tai rollin din kanta dashi powder kawai
tashafa a fuskarta ta fito ranta abace xata hada tafiya da Jidda da kuma ya khaleel ta runtse ido
tasan yau kam sai sun sata takaici babban falo ta koma ta taddashi xaune shida Momy yana
sanye da 3 quarter blue black da Riga maroon wacce ta kamashi me kajeran hannu ta fuskanci
yana matukar San 3 quarter dan in dai ba wajan da xashi me matukar muhimmanci bane tofa
shigar shikenan kwas kwas sukaji da takalmi ta sakko itama sanye cikin wando pencil da riga
brown ta Dora kimono gown asamansu sai dan karamin gyale da ta yafa tayi Kyau sosai runtse
ido Jennifer tayi cikin tashin hnkl musamman kallon dataga ya khaleel yana mata ga mmkinta
sai taji yace Jidda kije kisa hijab ta turo baki tana diren diren kafafu tana shagwaba wanne irin
hijab ya khaleel nida ba sallah zanyi ba OK toh babu inda xaki cikin kukan shagwaba ta kwabe
baki Momy í ½í¸«í ½í¸«kinga ya khaleel ko ?? Wai baxai je dani ba ni wllh sai naje Momy tace haba
khaleel ka kyaleta mana tunda ta riga ta shirya mikewa yayi baice komai ba yafita Jidda tabi
bayanshi tana cigaba da kukan shagwaba da dire diren kafafu murmushi Momy tayi ta mikawa
Jennifer jakar kudin da xatai siyayya da list din abinda take bukata ta amsa ta fito fuskarta a
damke haushin Jidda ya kamata tana kallon lokacin da ta budewa ya khaleel mota sannan ta
xagayo ta shiga gaba jikin Jennifer asanyaye ta bude baya tashiga ta rufo mator tana dai daita
zamanta cikin motar list din abinda xata siya ya fadi ta sunkuyar da kanta xata dauko dai dai
lokacin da Jidda ta Dora kafarta aka taya khaleel da sauri Jennifer ta dago ta jingina da kujerar
motar dama tasan kawai yau cinikin bacin ranta xaayi yaja motar suka fice daga gidan Jidda
tana xuba masa hira kala kala shi dai yana binta da uhhim ko um ko yace himm a haka sukaje
kasuwar a mota Jennifer ta barsu ta shiga ciki bata bata lokaci ba ta gama ta hangosu tsaye
ajikin mota taxo gab dasu ya bude mata but taxuba kayan kwala mata kira taji anyi kafin ta
waiwayo taji an rungumeta tana waiwayowa taga Janata kawarta a skul cikin murna ta
kankameta Jennifer kina nan ?? Ta tmbayeta cike da murna tunda muka gama skul ba'ajin
lbrinku wani ne ya karaso kusa dasu sanye cikin coat ash colour ya dafa kafadar Janata yana
murmushi Jennifer wannan shine Emanuel yayana da yace karatu a England ya mikowa
Jennifer hannu su gaisa da sauri ya khaleel ya mika nashi suka gaisa hade da jifan Jennifer da
harara mmk ya kamat ita jidda mmk tayi suka gama gaisawa hade da musayar numbers sukayi
sallama suka shiga mota
Bayan sun dawo gida ta koma wajan Momy tana falo ita dasu zahra suka shigo tabar Jidda
acen wajan ya khaleel tana zama ta shigo ta xauna akan kujera hade da fadin wash ! Momy
mun dawo Jennifer ta mike tana shirin tafiya Jidda tqce ta hau sama ta wanke mata toilet Momy
tace a a bari sa'a taxo ta wanke miki zahra tace no mom kibari ta wanke tunda itace a nan ta
nufi upstairs xata hau Jidda tace kinga kada kiyi wahalar wanke pants din ki hada har pad din ki
xubar kai kawai Jennifer ta daga mata ta wuce cike da takaici tana bude toilet din ta ganshi faca
faca ga karnin jini haka ta gyara toilet din pants me hade da pad Wanda tai amfani dasu gasu
nan xube ta hade su ta xubar xuciyarta na tashi dan tatsani karjin jini tagama xata fito Jidda
tashigo dakin cikin fara'a kin gama ko ? Ngd ta miko mata turare Jennifer ta amsa hade da
godiya ta fita tana komawa dakinsu ta wuce toilet ta kwara amai tana jinjina wannan kaxantar ta
fuskanci Jidda na da kirki kamar Rubayya
Da daddare suka shigo itada suwaiba dan debe kayan da masu gidan suka ci abinci a dining
suna jin hirarsu kamar ko yaushe cikin nishadi da jin dadi dady yace haisam gobe fa xamu tafi
Dubai tare dakai da tare da khaleel xamu tafi kasan yanxu yayi bakuwa ba shi ba barinta dariya
dukansu sukayi tana jin muryar zahra harda kyalkyalawa da sauri Jennifer ta kwashe sauran
kayan ta fice ranta bace
Washe gari da yamma suna babban falo dady da haisam sun shirya xasu tafi Jennifer ta shigo
falon tana hawaye lafiya Jennifer ?? Momy ta tambayeta cikin muryar kuka tace rashin lafiyar
David ce ta tashi suna asibitin nassarawa zanje nagansu dady yace ayya ! Sorry Allah ya bashi
lfy dukansu suka amsa da amin banda haisam da mmkinta yasashi cikin bahagon tunani dady
ya xaro kudi masu yawa yabawa Jennifer ta amsa tai gdy ta fito daga falon suma suka fito suka
shiga mota driver yaja me gadi ya bude gate dai dai lokacin da xasu fita haisam ya ganta
tashiga adaidaita sahu ya runtse ido cikin fargaba dan yasan inda xata shin idan sun hadu da
ita acen me xatai musu ? Kasheku xatai xuciyarshi ta bashi amsa kan wane dalili ? Abinda
yakasa Sani kenan
By
*UMMEEEYY*
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: âœâœâœJENNIFERâœâœâœ
25&26
Al'amarinta ya daina bashi mmk sai ta'ajjubi kansa ya daure sosai ya rasa kalan tunanin da xaiyi
ya samu mafita ya kwantar da kanshi jikin kujerar mota ranshi na suya shin me xatai musu in
sunje cen ?? Meyesa anan take boye muguwar akidarta a can take bayyanawa ?? Oh rabbi !
Kanshi ya daure tamau ahaka suka isa airport xuciyar na suya basu dade ba jirginsu ya tashi
fargabarshi ta karu sbd rashin sanin matakin da xata dauka akanshi musamman shi dayake
kuntata mata
Cikin dare suka isa direct gidansu na cen suka wuce dakinshi ya zarce yai wanka ya sauya
kaya ya bude jakar shi ya dauko laptop din mahboob dan bai mayar mishi ba sbd baya son ya
San komai akan Jennifer yafison sai ya ganota Kafin ya tona mata asiri yagama danne
dannenshi ya ajjiye laptop din ya kwanta yana kallon rufin dakin girgixa kai yayi hade da futar da
iska daga bakinshi ya gyara kwamciyar da yayi ahaka barawo bacci ya kwashe shi
Washe gari suka shirya dady ya wuce wajan meeting shi kuma ya tafi wani company dan cen
dady ya turashi yaje sugana da masu companyn kan wani aiki da xasuyi musu a darare yaje
atunaninshi kowanne lokaci xata iya kawo masa farmaki yagama duk abinda xaiyi sai yamma
ya dawo ya tadda dady agida shima ya dawo
Kwnansu 3 a Dubai har yanxu fargabar Sa bata yankeba dan ko alama basu hadu da ita ba
tunaninshi yarinyar ta Sa musu ido tana kallon duk abinda sukeyi tunda duk inda sukaje sai sun
ganta tun yana fargabar haduwarsu har ya dake so yake su hadu yasan wacece ita ?? Da
daddare suna falo shida dady suna kallon news dady yana yanka lemon bawo yana sha cikin
kulawa ya kalli haisam da hnklinshi ke kan tv tunaninshi kuma na cen yadda xasu kare da
Jennifer haisam ya waiwayo ya kalli dady naam dady kana lafiya kuwa ? Naga kwana biyu kana
yawan tunani kamar kana cikin damuwa gyara xama haisam yayi akan kujera ya kishingida
dady bakomai ina lfy katabbata ?? Dady ya tmbyeshi na tabbata dady ya fada yana Sosa
gashin kansa OK to haka akeso gobe nake son wucewa Singapore sbd aikin da nafara ina son
naje agama shi akan idona kaikuma sai ka tsaya idan companyn cen sungama kaduba kayan
ka gani sai ka tura su 9ja xuwa jibi sai ka koma gida to dady Allah ya kaika lafiya amma dady
yayi shiru yana kallon wta talla da akeyi a chanal din da suke kallo ina jinka dady ya fda yana
kallonshi kallo na kulawa ina son zanje umara zan wuce cen daganan OK to Allah ya kaimu ngd
dady murmushi yayi ya cigaba da shan lemon shi yana jin soyayyar yayanshi tamkar hancin
cikinsa Wanda inbashi ba rayuwa
Washe gari yaraka dady airport bai bar nan ba sai da jirginsu ya tashi ya dawo kan hanya
takaici fal ranshi jibi yake son barin Dubai gashi basu hadu da Jennifer ba yaja tsaki natakaici
sosai ya koma gida ya shiga daki yai wanka yasauya kaya ya fito falo turus yayi sai da yaji
gabansa ya fadi duk da yana namiji wasu manyan garada ya gani marasa kyan kamanni
fuskokinsu atamke hannayensu dauke da manyan bindigo lafiya ?? Ya fada da mmk yana
kallonsu suwa ye Ku daxaku shigomin gida haka ? Kafin ya gama magana suka rufu akanshi
suka daure masa hannu da idanu suka ingixa keyarshi suka fice daga gidan cikin mota suka
turashi sannan suka ja motar suka bar gidan
Yana cikin mota yayi jigum hnklinshi amatukar tashe yarasa inda xasu kaishi tafiya sukai mai
nisa sannan yaji alamun xasu tsaya suna tsaya suka fito dashi suka ingixa keyarshi cikin wani
waje Wanda baisan ko inane ba suka tsayar dashi hade da bude masa ido ya bude idon shi da
sauri ya rufe sbd hasken wajan da yaiwa idonshi yawa ahankali ahankali ya bude idonshi ya
sauka a tamfatsetsen falo me dauke da kujeru jajaye da labulaye ja komai na falon jaa ne babu
sirki da sauri ya mike yana kallon garadan dasuka kawoshi nan wajan cikin daga murya yai
magana me yasa kuka daukoni kuka kawo ni nan ?? Me nai muku suwaye Ku ?? Ko kallonshi
basuyi ba bare su bashi amsa haushi ya kamashi yai musu ashar ko xai tunxirasu su kulashi
daga karshe ma GAM suka Sa suka rufe mishi baki suka kuma daure masa ido suka ingixa
keyarshi cikin wani waje suka rufe
Yana cikin wannan halin xuwa wasu awanni sannan yaji alamar bude kofa suka shigo suka
bude masa idanu da bakinshi hade da tura masa plate dankaren da abinci wani mugun kallo
yake binsu da shi hade da yiwa abincin kallon ko inkula dam Sam bayajin yunwa asalima halin
daya ke ciki baxai barshi ya iya cin wani abinciba xugum yayi yana son tuna wanne irin laifi yai
aka kawoshi nan ?? Shigowa suka kuma yi hade da ingixa keyarshi xuwa inda suka fara kaishi
da farko maza ne manyan garada xagaye da ita dukkansu suna dauke da muggan bindigu tana
sanye cikin wando jeans blue black da riga baka gashinta asake ta Dora kafa daya kan daya
kana kallonta xaka hango bindigun dake sarkafe jikin aljihunan wandonta fuskarta amurtuke
tana masa kallon tuhuma ya wurga mata harara hade da fadin ke wcece ?? Me kike nufi da
rayuwarmu ?? Wanne laifi mu ka aikata miki kike kokarin ganin bayanmu ?? Magana nake miki
jennifer meyasa kike wasa da hankalina ki fadamin wacece ke ?? Meyasa kika yaudari
yangidan mu kika je musu a matsayin Yar aiki ?? Jennifer meyasa kike bibiyarmu duk inda
mukaje ?? Ya fada cikin tsawa da daga murya bata ce komai ba in banda mugun kallo da take
binshi da shi nakasa gane miki Hindu a Dubai Jennifer a 9ja Sul........... Yayi shiru hade da rufe
kunnanshi sakomakon karar harbi me karfin gaske da sukaji a guje wani katon mutn ya shigo
madan da matsala fa shareef al Hussain ya kawo mana hari mikewa tayi adake kowa ya shirya
ta nuna daya daga cikin garadan duk rintsi ka maida guy din nan gida ta nuna haisam muje
taxaro bindigunta tai waje suka bita haisam ya mike katon nan ya tura shi suka fita ta baruniyar
hanya yana jin karar fitar harsashi hnklinshi ya tashi sosai katon yasashi a mota sai da sukai
nisa da wajan sannan ya cillo haisam daga mota yatafi ya barshi cikin mutuwar jiki da fargaba
ya tari taxi ya maidashi gida da kyar ya shiga gida ya xarce toilet yai wanka ya dauro alwala yai
sallolin da baiyiba ya baje a gado yana maida numfashi lallai babu komai afashi face rayuwar
wahala da fargabar harin makiya sai yanxu yakejin tausayinta xaiso dalilin dayasa take wannan
rayuwar xaiso kuma dalilin dayasa bata cutarda shi ba tabbas da tana son cutar dasu da tuni
tayi to meyasa ? Kansa ya daure meyasa bata bashi amsar tmbyoyinsa ba xuwan da su shareef
all hussani sukayi ne ya dunkule hannunshi hade da kaiwa iska naushi daren nan da kyar yai
barci
Shiru shiru yana jiran ko xata dawo yaji babu alamunsu har ya gama avinda xaiyi baiji dadi ba
Sam yaso ace sun kuma haduwa karo na biyu ko dai su shareef al Hussain sun sami nasarar
kasheta ?? Gabansa yai mummunan faduwa nan da nan ya tsinci kansa cikin mugun yanayi no
! No ! No ! Baxaki mutuba Jennifer ina bukatar jin ke wacece ?? Yana xaune a airport hnklinshi
atashe jikinsa asanyaye dolene yaje yai addu'a sosai a dakin Allah kafin wannan tunanin yafara
yi masa illah ahaka ya shiga jirgi yana addu'ar Allah yasa Jennifer tana cikin kwanciyar hnkl
muddin tana lfy dole ta sake nemanshi lumshe ido yayi ranshi na suya idan har tana cikin
mugun yanayi bai xama lallai ya taradda da ita a saudiyya ba shi dai babban fatansa Jennifer
tana nan araye dan yana jin sautin fitar karar bindigar su shareef al Hussain mai ban tsoro da
firgici
By
*UMMEEYY*
[2/28, 6:41