Showing 60001 words to 63000 words out of 132173 words
Chapter 21 - JENNIFER COMPLETE BOOK BY Maimuna A.A Rano.pdf
take sawa ta kai masa dake bai fiya yin dinner a
cikin gida ba yauma har kusan 10:40pm bai shigo ba tana kallon jidda tana ta shiga da fice
ganin haka yasa Momy ta kira jannat dan har ta fara bacci tace ta dauki abinci Ibrahim ta kai
mishi da bacci a idonta ta nufi dakinshi Dan jiya batayi baccin kirki ba sallama tayi ya amsa
yana aiki da laptop dinshi ganinta yasa ya rufe laptop din ta karaso kusa da shi ta cire hijab
dinta ta xuba masa coffee tana kokarin xuba avincin ya dakatar da ita,
" banajin wunya
Ta kalleshi kamar xatayi magana sai kuma ta fasa ta sunkyar da kanta sbd wani irin kallo taga
yana mata,
Da kyar ya iya shanye coffee din ya matsar da kayan abincin ya janyota jikinshi, da sauri tace "
kayi hkr ya khaleel bacci nakeji,
Matseta yayi ajikinsa, muryar shi asanyaye yace " plx beautyna ina son jin jikinki ajikina kiyi
kwanciyar anan, shiru tayi hnklinta atashe,
Lumshe ido yayi yana jin wani mugun sonta na karuwa aransa, yana jin dadin yanda take masa
Sam bata iya Musa mishi duk abinda yace tana da biyayya sosai, tunanin shi xata wahalar
dashi, sai gashi yasamu abinda ya keso, mace mai biyayya mara tsiwa da rashin kunya wacce
tasan darajar aure, tana jinta ajikinshi takasa mgn da kyar tace, nabar Momy a falo tana jiran da
wowata, da sauri ya tari numfashinta,
" beautyna ke fa matata ce menene dan taga baki dawo ba baxata damu ba Dan tasan dakin
mijinki kikaxo ya dago fuskarta suka hada ido da sauri ta rufe idon, xame jikinta tayi,
tayi xugum tana son tayi mgn ta kasa ya kalleta da kulawa kina jin bacci ko ? Kai ta daga masa
ya dauketa cak yashiga cikin bed room dinshi da ita ta shaki kamshin air freshner mai dadi ya
ajjiye ta kan gadonshi ya juya tana kallon shi ya nufi inda manyan ledojin kayan da suka siya
jiya a store ya dauko sleeping dress mai Kyau ya ajjiye kusa da ita" tashi kisaka kayan bacci,
yana fada ya mike ya fice daukan rigar tayi tashiga toilet ta saka ganin rigar tafiya sharara
iyakarta kasan gwiwa yasa ta tarasa yadda xatayi gashi hijab dinta na falonshi shigowa dakin
yayi batanan ya xauna xaman jiran ta fito shiru kunya ta hana ta fitowa, ya gaji da jiranta ya
tashi ya bude toilet din a sunkuye ya ganta ta rufe kanta da hannunta, yai murmushi soyayyar ta
na karuwa aransa beautyna akwai kunya ya dago da ita ya kalli rigar yanda ta xauna mata
ilahirin surar jikinta abayyane murmushi ya kumayi Dan yagane abinda ya hanata fitowa
daukota yayi ya ajjiyeta kan gadon ya hawo ya janyota jikinshi yana shafa gashin kanta daya ke
matukar so a hnkl kamshinta na rikitashi ya fara mata wani xafafan kiss tun tanajin na hnkl har
taji abinda yana kokarin wuce xatonta don gaba daya ya hargitsata tsoro ya bata ta fashe da
kuka jin tana kuka sosai yasashi sassautawa ya rarrasheta ya hade ta da jikinshi gam a haka
sukai bacci motsi kadan intayi yakara riketa cikin jikinshi
**********
Da asuba ya tasheta tai sallar asuba tana laxumi bacci ya kuma a won gaba da ita yana
dawowa daga masallaci yaga ta jingina jikin bed dinshi tana bacci a hnkl ya xame hijab din ya
kwantar da ita shima ya kwanta gefenta yana kallon kyakkyawar fuskarta yana jin kamar ya
hadeta
Da safe ta tashi tashiga toilet din shi tana brush mgnr jidda taji kamar tana kuka... Ya khaleel ka
tausaya min ka duba halin dana ke ciki kasan ina sonka tunda kayi aure ka juya min baya har
gobe ina jin takaicin wai da Jennifer xanyi kishi,tsawa taji ya kwatsa mata.... Kada na kuma jin
kince mata Jennifer bakisan sunanta ba ? Ya khaleel ta fada da kuka nima fa macece kasan irin bakin cikin Dana ke sha kuwa ?
Wannan ke kikasa aranki look ! Jidda bana son mgn daya idan xaki iya fine idan baxaki iyaba ki
kyaleni nagaji, kasa jurewa jannat tayi sam ta manta rigar da take jikinta kai tsaye falon ta shigo
kishi na cinta,
Nesa da juna suke kanshi na kan waya yana danne danne ya dago kai ya kalleta da murmushi
a fuskarshi yace beautyna kin tashi ? Ta karaso kusa dashi, da mmk jidda ta dago kai tana mata
wani mugun kallo ganin rigar jikinta yasa ta runtse ido ta mike da sauri tabar dakin,
Tausayinta ya kama jannat, plx ya khaleel kaji tausayin ta mana,
Kura mata ido yayi da alama mmkin mgnrta yaji ya tabe vaki hade da murmushi kadan ya janyo
kayan breakfast sakko ki yi breakfast dinki ganin irin kallon daya ke mata yasa ta tuna rigar
dake jikinta da sauri ta janyo hijab dinta ta saka murmushi ya kumayi ya bude laptop dinshi
Da kyar ta iya shiga falo ga mmkinta ba kowa kamar mai sanda ta lallava ta hau sama ta shiga
dakinta ta kwanta tayi lamo momy ce ta shigo dakin itada su sulthana da hindu, "jannat xamu
fita dasu hindu ki kula da gidan Dan duk sauran suma basa nan, da kyar ta ce to Momy adawo
lfy Dan kunyar ta takeji murmushi Momy tayi ta fice Ajiyar xuciya tayi ta sakko kasa farfajiyar gidan ta xauna tana xama ta hango wata tsuhuwa
suna mgn da danjuma ya bude mata get ta shigo tunda jannat ta kalli tsohuwar taji batai mata
ba kusa da jannat taxo tai mata sallama ta amsa "Yar nan ina hajiyar take ? Bata nan sunfita
"Fitsari nakeji zan wuce nace bari naxo nan gidan nayi kuma hjyn bata nan
Jannat tace eh ta fita,
Nuna min inda bandakin yake jannat ta nuna mata na tsakar gidan Wanda anan driver da
danjuma suke amfani dashi kwata kwata jitayi hnklinta bai kwanta da matar ba, ta ajjiye jakarta
jannat ta kalli agogon tsohuwar na gwal ta xaro ido sosai ta bi tsohuwar da kallo har tashiga
toilet din bata jima ba ta fito ita kam jannat jikinta tuni ya fara rawa Dan tsoro damma ta hango
danjuma yana sallah nesa dasu kadan, takara so kusa da jannat," Yar nan nace Ku yan biyu ne
agidan nan ? Da sauri jannat ta girgixa kai a'a ni kadaice tana ganin lokacin da tsohuwar tai
ajiyar xuciya da alama taji dadin amsar da ta bata, "to ngd na tafi
Da kyar jannat tace mata to ! Gaba daya ta rude
By
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍
71&72
a tsorace take kallon matar xuciyarta na cikin firgici har matar ta fice daga gidan kasa komawa
cikin gidan tayi sbd firgicin da ta ke ciki meyasa wannan tsohuwar ta tambayeta su yan biyu ne
? tunda take bata tab'aganin wannan tsohuwar ba,gabanta yai mummunan fad'uwa da ta tuno
gargad'in sadik osasa akan su kiyaye yawo barkatai sbd har yanxu ba'a daina bibiyar rayuwar
su, xumbur ta mike xuciyar ta cike da firgici safa da marwa da farayi a cikin harabar gidan tana
jin takaicin kyale matar da tayi da bata cakumeta ba, bacin rai mai tsanani ta tsinci kanta da shi,
da sauri ta nufi danjuma axaune ta sameshi yana laxumi tak'arasa muryarta na rawa ta gaishe
shi ya amsa yana kallonta dan yaga hnklinta atashe,
danjuma kasan wannan tsohuwar ?
arud'e ya amsamata, a a madan wllh ban santa ba me ya faru ??
a tsorace ta kalleshi hnklinta ya kuma tashi,
meyasa kabarta ta shigo ?
mikewa tsaye yayi yana xare ido,
cemin tayi wajan hjy taxo nace sunfita shine ta ce min waccen ba Jennifer bace nace eh
shine tace bari ta baki sako wajan hjyr intaxo a fada mata,
girgixa kai kawai tayi dan bacin rai ya hanata mgn cikin gidan ta wuce ta dafe kai hade da xama
akan tyles na harabar gidan cikin wani mugun yanayi ? bataraba dayan biyu tabbas matar nan
taxo bincikarsu aikota akayi , su kuwa wanne irin laifi sukayi ake bibiyar rayuwarsa ?
wani axababban hawaye ya sauko mata haka ta dinka jin xubar hawayen kamar fanfo sam
takasa tsaida hawayen, daga kanta tayi ta kalli sama cikin xuciyar ta tana addu'a akan Allah ya
kawo musu sauki, ya Allah ka tsare bayinka ya Allah ka karemu daga sharrin makiyan mu
wayanda muka sani da wanda ba mu sani ba gareka na dogara kuma gareka nake neman
taimako ya Allah ka kara tsaremu daga dukkan abinki Allah kada kabawa makiya nasara ya
Allah ka rushe mummunan nufinsu akanmu, haka ta dinka jero addu'o'i kala kala tanayi tana
xubar da hawaye sam tarasa gane laifin da sukai da ba'ason haduwarsu da iyayensu, tanayi
tana girgixa kai sbd abun ya matukar dauri mata kai, haka su momy suka dawo suka tadda ita
cikin wannan yanayin, arud'e suke tambayarta, ta kwashe labari ta fad'a musu xama sukai
awajan suna mmk da ta ujjibi kansu gaba daya ya daure, kowacce tagumi tayi tana mmkin
yadda alamarin yake tafiya arikice da kyar momy tace wai ni way'an nan mutanen way'anne irin
axxalumai ne ? dole musa matakan tsaro sosai a gidan nan salati kawai take nanatawa da
kanta tashi taje wajan danjuma tai masa gargadi kada ya kuma barin wata tashigo gidannan
sannan duk wanda ya tambayeshi jannat yan biyune yace ita kadaice agidan a tsorace ya amsa
mata dan shi gani yake kamar ya tafka wani babban kuskure na barin matar ta shigo yai wa
momy rantsuwar baxai kuma barin wani ko wata tashigo sai da ixininsa balle ya basu lbrn jannat
su ukune, ta dawo ta samesu suna kuka sun rungume juna tausayinsu ya kamata ta dade
akansu ba su san taxoba surutai sukeyi na jimamin halin da suke ciki da kyar ta lallashesu
sukayi shiru suka koma falo babu wanda ya iya yin lunch aranar duk a tsorace suke, sai yamma
dady ya dawo ganinsu cikin jimami yasa ko d'akin shi baije ba ya xauna ya na naxarinsu yasan
akwai bak'on al'amarin daya shigo cikin gidan, da kyar momy tace,
alhaji narasa gane laifin daya rannan sukai akeson wulakanta su akeson tarwatsa
rayuwarsu,hawaye ya xubo mata koma waye Allah ya isa,
ta kwashe lbr ta fad'a masa xura mata ido yayi cikin mmkin xancen nata,
ya girgixa kai, wannan abin yana matuk'ar bani mmk wannan somin tab'in tonuwar asirin koma
waye tabbas asirinsu ya kusa tonuwa, karfin addu'a ne yake fito da wayannan misalan, firdausi
makiya basai ka musu komai ba wasu ma basu da dalili xasu ji kawai sun tsaneka bakuma xasu
barka haka ba har sai sundinka jifan ka da sharurruka iri iri dana baki dana karkashin kasa kai
dai babban burinka Allah yai maka tsari daga sharrinsu, kuyi hkr yayana jarabawa ce bakusan
irin baiwar da Allah yai muku ba nan gaba, Allah baya jarabtar mutanen banxa sai na arxiki
koma wanda Allah xaiwa wata gagarumar baiwa duk wani k'usa kowani shahararre baya xama
haka banxa sai Allah ya jarabceshi ya gwada imaninka gwargwadon imaninka gwargwadon
jarabawarka da kuma shahararka,
kuyi hkr kuxuba wa sarautar Allah ido shiru sukayi suna jinshi suka d'ai suka san irin bakin cikin
dake cikin rayuwarsu da kyar ya rarrashesu da nasiha suci abinci, cin abincin suke tamkar suna
xuba wa cikinsu mgn kowacce ta kagu tasan kanta takuma san wanne irin abu taiwa mutanen
nan da suka jefa rayuwarsu a wahala suka hanasu jin dadin duniya,
************
da daddare tana kwance bayan ta idar da sallah shafa'i da wutr tayi lamo kan gadonta
xuciyar tana jinta wata iri tmk mad'aci sam bata san shigowarshi ba sbd dogon tunanin da ta
tsinci kanta aciki jitayi an rungumota asanyaye ta kalleshi yai mata murmushi kad'an ta kauda
kanta hade da ajiyar xuciya da ita kadai tasan tayi ta kwantar da kanta yayi ajikinsa, cikin
muryar lallashi yake mata nasiha had'e da lallashi tayi lamo ajikinsa dan dai dai kunnanta yake
mata mgnr tana jinshi kuma nasihar tana ratsata sun kai kusan 11:00 na dare yana lallasarta
har sai da yaga ta gamsu da nasiharsa dan jikinta yai matuk'ar sanyi haka ya kwantar da ita
ajikinsa tamkar yar baby a hnkl a hnkl bacci mai nauyi ya fusgeta,
***********
ganinta tayi cikin wani rami ita dasu sulthana da hindu suna gudu xasu fita daga ramin
kag da xasu fita suka ga wannan matar da tagani a mota ta taho da gudu itama daga wani gefe
na jikin ramin tana ce musu koxo yayana kuxo na ganku kada a rabani daku saura kiris taxo
kusa dasu wasu mutane suka xo wajan fuskokinsu a daure basa iya ganinsu suka biyo su, suka
rirrik'esu wasu suka rik'e matar wasu suka rik'e su tana ihu ga mutane birjik amma sunki suxo
su cetosu firgit ta farka da sauri ya rungumeta gam ajikinsa tuni gumi ya jiketa fincike jikinta tayi
daga nasa tana nishi da ajiyar xuciya wani irin kallo yake mata, beautyna menene? kallonshi
tayi idonta cike da hawaye ta girgixa masa kai muryarta na rawa tace, nayi mummunan mafarki,
mik'ar da ita yayi shima ya mik'e ya nuna mata agogo 3:59 muje muyi alwala mu fad'awa Allah
bukatarmu kiyi addu'a sosai dan haka annabinmu ya koya mana duk lokacin dakayi mummunan
mafarkin anfison katashi kayi sallah raka'a biyu kayi addu'a sosai akan Allah yai maka tsari da
abin ki na cikin mafarkin ya kuma sadaka da alherinsa dan shi mafarki bushara ce babba,
alwala suka d'auro sukayi nafilfili har asuba sannan yabar d'akin nata,
************
washegari misalin 1:0 tana daki hannunta rik'e da kur'anin mai ixfi takwas dan shi ake
koya mata karatu tana ta hadda dan tayi nisa sosai hayaniya taji sosai a falo ta k'arasa karatun
ta ajjiye kur'anin ta sakko falon abinda tagani yasa gabanta fad'uwa umman jidda ce da d'ayar
matar nan da suka xo kwanaki da kuma wata daban amma tana kama dasu dady sun sa momy
agaba suna xabga mata ruwan masifa tayi tagumi tana kallonsu d'aya matar da bata tab'a
ganinta ba cikin masifa take mgn, kinga firdausi shiyasa bana xuwa gidannan yaya bashir wana
ne amma sbd ina bakin cikin naxo na ganki cikin gidan nan yasa bana xuwa duk girman
wannan gidan ace ke kadaice ? sbd mugun abu sannan kin kwasu wasu shegun yara kin kawo
su gidan nan da xummar wai taimako har an daura wa daya daga cikinsu aure da Ibrahim mu
bamu sani ba sai aka fake da auren gaggawa to bamu san da wannan yarinyar ba kuma har
avada bata cikin danginmu auren shi da jidda kawai muka sani, shiyasa muka had'u kanmu mu
nuna namu ikon, da sauri jannat takoma baya dan batasan d'orawa kanta wata damuwar wacce
take cikima ta isheta d'aki ta koma tasaki wani marayan kuka ta durk'ushe bakin kofa cikin wani
mugun yanayi kuka take sosai tana mmkin wannan wahalalliyar rayuwar data ke ciki su kam ai
abin tausayine lallai cikakken mai imani dole ya tausaya musu dan suna cikin wani mugun
yanayi wanda duk bai tausayawa rayuwar ba imaninshi ragaggene son xuciya ya hana
yan'uwan dady gane cewa su na buk'atar taimako, haka tai ta sambatu hindu ce ta shigo
hannunta rik'e da na sulthana tana ta haki da fusge fusgen hindu ta kyaleta taje taci mutuncin
matan da sauri jannat ta tashi ta rufe kofa tamau tana kuka, plx sulthana kiyi hkr ya xama dole a
goranta mana danmu abin gorine ki barmu da abu daya ki kyalesu Allah yana jinsu yana kuma
kallonsu ramuwarki sam bata da amfani, itama sulthanan fashewa tayi da kuka anty jannat na
fasa xuwa nikad'ai nasan me nakeji araina xuciyata kamar ana babbaka wuta haka nakeji
wayannan mutanen magangamin su nasa naji na tsani kaina na tsani rayuwata, karar wayar
hindu sukaji ta amsa wayar, osasa plx mu hadu dakai agidana na hotoro, araxane suke kallonta
kasa daurewa jannat tayi, idan kinh hadu dashi me xaki masa shiru tayi bata amsa mata ba, a
kufule sulthana tace malama mgn ake miki kina da kudin daxaki iya biyanshi banxa still ta kuma
yi musu, gidan ubanwa xakije ki samu kudin ? uban me xaki fad'a masa idan kun hadu?
ubanki xan fd'a masa ! tafad'awa sulthanan cikin tsawa da fad'a kina min mgn kamar wata
y'arki ta xaro ido cikin wani mugun yanayi ta koma da sak tana kallonsu tana nunasu da yatsa,
kada wacce ta kuma shiga rayuwata babu wacce nake tmbyr ta abinda bai shafeni ba kuyi
harkarku nayi tawa, dama kuna yi min kallon wata bare a cikinku kuyi rayuwarku kada ku shiga
tawa ta mik'e ta rab'e ta jikin jannat ta bud'e kofa ta fice da mmk suka kalli junansu, suna xubar
da hawaye,
***********
da daddare bayan sun gama dinner gaba d'ayansu sun koma falo, cikin isa matar da
jannat bata tab'a ganinta a gidan ba tafara mgn yaya bashir gamu munxo da tamu mgnr
muhimmiya akan sa ranar jidda da Ibrahim da ance sai bayanta gama nysc dinta to yanxu mgn
ta tashi mun dawo da sa ranar sati uku mai xuwa, kowannansu sai da gab'ansu ya fad'i, tunda
ta fara mgnr yake danne dannen waya jin ta ambaci bikinshi da jidda nan da 3 weeks ya mik'e
afusace ya fice daga