Showing 54001 words to 57000 words out of 132173 words

Chapter 19 - JENNIFER COMPLETE BOOK BY Maimuna A.A Rano.pdf

12 Apr 2025

6871

tana ja dady yace
Subhanallah sulthana me ya faru ?
A kufule tace dady Dan kawai bamu san iyayen mu ba sai a tsanemu ? Waccen banxan zahran
tunda mukaxo gidan nan take mana kallon raini shine yanxu take xagin Anty jannat wai Mara
asali shegiya wllh dady banda sulthana y'arka ce kaida Momy dana koya mata hnkl, girgixa kai
dady yayi to shikenan muje sama ya sata agaba had'e da galla wa zahra harara, sakin baki
umma tayi cikin d'aga murya tace yaya bashir ina son mgn dakai bai waiwayo ba yace anjima
xamuyi mgnr yanxu zan rarrashi sulthana, salati umma ta saka
Momy ma hararar zahra tayi had'e da k'wafa tai sama
Nashiga uku ni hadiza xama tayi akan kujerar dining had'e da cire d'an kwalinta cikin tashin
hnkl tabbi jam ! Wannan masifar har ina ga y'arka data sha mari katafi lallashin wata cen
futsararriya, way'an nan yara basu bar yaya bashir haka ba dole akwai k'ullalliya, xonan zahra
kiyi hkr na fuskanci yanxu dadynku ta way'ancen shegun y'ay'an yake kaf sun juyar masa da
hnkl wllh munsa k'afar wando d'aya dasu baxan bar gidannan ba har sai na karya wannan asirin
ina xama bai kamani ba,


Daki suka shiga dukansu, jannat tace sulthana meya Sa kika mari zahra ? Haba sulthana ana
barin halak dan kunya kada ki manta tarin alkairan iyayenta akanmu,
Tsaki sulthana tayi Anty jannat baxan iya jure cin mutunci ba kawai ina xauna ina breakfast ta

hau xaginki tunaninta ko kece dama haka suke miki wannan cin mutuncin ?
To idanke kin jure kin San ni ba xan iya jurewa ba,
Hindu tace abinda yafi damuna sulthana ki xage kina fada da babbar mace bafa sa'arki bace
ki k'yaleta ko Dan girmanta,
Baxan iya bane kun San halina kun San yanda nake idan ina cikin wannan halin bana iya
tantance babba da k'arami hkr ne kawai banda shi amma bana Neman rigima muddin kuwa ka
tab'ani sai kayi Dana sani, jannat tace Allah ya kyauta suka amsa da amin

***********
Da yamma suna xaune a falo dukansu bayan sungama dinner umma cikin ya tsina tace
Ibrahim, yad'ago kai ya kalleta, meya had'aka da y'ar'uwarka ? Kana son nuna banbanci
tsakaninta da Jennifer ? Kasani fa xaka iya rabuwa da Jennifer jidda kuwa har abada
yar'uwarka ce, katseta yayi, umma plx kidaina min fad'a agaban yara ? Ya kallesu fuskar shi a d'aure Ku tashi kuba
mutane waje, kowacce tashi tayi tabar wajan,
Ya dawo da kansa wajan umma, ta cigaba da fad'anta haba Ibrahim kafin kasamu Jennifer
wa ka fara samu kashe wayarshi yayi daya ke dannata, umma ya kira sunanta, jannah matata
ce jidda kuma k'anwatace baxaiyi yu nak'i kowaccensu ba sbd d'aya sannan abaya na fad'a miki
kuma kin Sani yanxu ba Jennifer bace sunan Momy gareta ta musulunta, ya mik'e tsaye ni
bana son mgn akan abu d'aya me jiddan tace na mata ? Ko ma menene bai kamata kina min
fad'a agabansu ba ya fice ta bishi da kallo cike da mmki, innalillahi wa inna ilaihi raji'un ta kalli
momy, Firdausi ki biya malaminki, momy murmushi tayi ta mik'e ta bar mata falon gaba daya
hnklinta yai mummunan b'aci kai ta dafe dole tai musu gagarimin aiki Dan idan tayi sake
wataran khaleel xai iya mata cin mutuncin da batayi tsammani ba

2days ago

***********
Da rana sulthana tana gardin dayake bayan babban kitchen tana xaune tana tuna
rayuwar ta mai dad'i wanda ayanxu komai ya cab'e ta koma kamar ba ita ba tagumi tayi, duk irin
gatan da umminta ta nuna mata ba ita ta haifeta ba hawaye ya sauko mata ta samu gata duk da
kasancewar ta cikakkiyar Mara kunya umminta bata taba nuna mata wata alama ba, motsi taji a
kitchen ta tashi ta lek'a ta jikin k'ofar baya ta hango jidda ta d'auko flast din abinci ta xuba
sulthana na hangenta ta jikin wata Yar mitsitsiyar k'ofa da akayita dan lek'e, gani tayi ta fito da
leda a hannunta ta xaxxge magani akan abincin, xaro ido sulthana tayi tana mmk ta rufe flast
din ta bude loka ta ajjiye ta fito daga kitchen din tai b'angarenta da sauri sulthana tabi bayanta
da niyyar ta nuna mata ta ga abinda tayi kafin ta k'arasa ta shige d'aki ta fad'a toilet
Cije yatsa sulthana tayi, dabara ta xo mata da sauri ta koma ta juye abincin acikin wani plate na
daban ta ta wanke flast din ta xuba wani abinci ta mayar lokar da ta ajjiye ta fito tana mmk
jikinta har rawa yake direct dakin momy ta wuce ta sameta xaune tana laxumi kusa da ita taje ta
xauna tayi ta gumi, Momy ta kalleta cike da kulawa, sulthana meyasa meki? Hawaye ya sauko mata, cikin kuka
tace momy halin da muke ciki na masifa ma ya ishemu way'an cen mutane suna k'okarin kara

jefamu cikin wata sabuwar masifar,
Atsorace momy tace wacce masifa sulthana ta share hawayenta ta kwashe abinda taga
jidda tayi da yanda ta sauya abincin, tagumi momy tayi jikinta asanyaye,
Momy irin wad'an nan abubuwan sai dai nagani a novel ko a film yau na gani da idona, ina
tsoran kada wani abu ya samu Anty jannat ita da ya khaleel kiyi wani abu momy,
Kwantar da hnklinki sulthana Allah ya fisu babu abinda xai faru bi'ixnillah zan kuma d'au
gagarumin mataki abinda nakeso dake kada kifad'awa kowa sbd xaki d'aga musu hnkl zan Sa
musu ido sosai daga ita har mahaifiyar tata kedai abinda nakeso dake ki cigaba da shan
maganinki akan kari ki dage da addu'a kinji ko ? Ta mik'e naji Momyna inshaa Allah xan kiyaye
asanyaye ta fice tana mmkin abinda ta gani ita kanta xata sawa jidda ido sosai tunda ta fuskanci
inda suka sa gaba

**********
da safe bayan sungama breakfast jidda ta kalli momy,
mom banga ya khaleel yaxo yin breakfast dinshi ba,
da sauri momy tace eh jannat tashi ki kaiwa yayanki breakfast, had'a rai tayi dan ba haka
taso ba ranta ya b'aci ta mike tai b'angaren d'akinta sulthana ta bita da kallo tana murmushin
k'eta
a kunyace jannat ta shi ta d'auka tai b'angarensa sallama tai masa ya amsa hannunshi rik'e
da laptop yana amfani da ita tana shigowa ta b'ata rai ta turo baki ita a dole fishi take dashi,
yaji dadin ganinta bata ran datayi yasashi murmushi ya xuba mata ido kusa dashi ta ajjiye flst
din ta gaishe shi ya amsa yana murmushi ta cire hijab dinta ta xuba masa tea a cup ta mik'a
masa ya amsa ta hada masa komai ta mike xata ta fi
" ina xaki tafi ?
bata waiwayo ba tace zan koma cikin gida ajjiye cup dinshi yayi ya janyo hannunta ya xaunar
da ita,tana ta fusge fusge dariya ta bashi ya tallo bo fuskarta, fushin me kikeyi ?
ta juya ido ni ba fushi nakeyi ba,
haka kawai yaji yana son tsokanarta dan kawai tai masa yarinta any'a kuwa wannan jannat ce ?
ya k'ura mata ido cikin wasa kodai sulthana ce ?
jannat din dana sani bata da tsiwa matsoraciya ce bata iya fada ba,
kallonshi tayi da sauri niba matsoraciya bace ta fada tana murguda baki, yayi murmushi me
fidda sauti yana shan tea din ya ce idan jannat ce me ya sameki kwana biyu ?
ta kalli cup din hannunshi ta kara hada rai ni babu abinda ya sameni
hada ranshi yayi ya kalleta , ki fadamin meya ke damunki ?
kwana biyun nan narasa gane damuwarki, tun ranar da nai miki mgn akan ki fadi abinda kikeso
ki huta da boye boye shine kike fushi,
ranta ya baci bata son wannan magnr ko kadan,
xuba mata ido yayi yana kallonta, ta dago kai ta kalleshi, kana son jin wanda nakeso ?
ajjiye cup din daya ke shan tea yayi yana gyada kai akufule tace,wanda nakeso ba shi na aura
ba
kallonta yayi da mmk ta marairaice, ban aure shi ba kuma ina sonshi sosai,
kishi mai xafin gsk ya taso masa ya fincikota agabana kike fadamin kina son wani ?
xaro ido tayi tana kokarin kwace kanta,

tambayata kayi na baka amsa plx ka cikani sakin ta yayi, yana jin ba dadi aransa ta mike xata
fice ya kuma fincikota, ya xare mata ido,kikace kina sonshi sosai ? kai ta daga masa atsorace
matseta yayi da jikinshi har sai da tayi kara ? dolene ki cireshi aranki baxaiyiyu ina aurenki kina
son wani ba, ya saketa ta fice da sauri,
sai bayan ta fita yake jin haushin abinda yai mata kamar wani karamin yaro yake mata fadan ta
cire wani aranta, tsaki yai shi sam bai son yayi hakan ba sbd kishin daya ta so masa, anya
kuwa da gaske take masa ? idan kuwa har haka dinne xai san matakin da xau dauka dan yana
matukar sonta yna kishinta
tana fita daga dakinshi ta waiwayo tana kallon kofar murmushi tayi ya khaleel kenan
abinda kakeson ji baxaka ka taba jinshi ba idan har bakai kafara fada ba ta wuce tana jin dadin
yanda lokaci daya tai nasarar cire masa wancen tunanin ta hau sama tai alwala tayi sallar
walaha ta dade tana addu'a akan Allah ya kawo musu mafita na halin da suke ciki


************
da daddre momy ta fito daga dakinta xataje dakin dady giftawar mutun ta hango a
k'asa taji tsoro ta dake da kyar ta lek'a abinda ta gani ya bata mmk ta kalli agogo 11:38pm da
sauri ta shiga dakin dady tace ya xo yaga wani abu ya biyo bayanta suka sauko kasa da mmk
yake kallon umman jidda magani ne a hannunta tana barbade falon dashi tsawa ya kwatsa
mata ranshi ab'ace hadiza !! menene haka kikeyi ??



by
*Ummee Garkuwa*
[2/28, 6:43 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍



67&68

a raxane ta dago kai ta kalleshi yana sauka daga stairs momy na biye da bayansa, menene
haka hadiza ?
cikin yadda da abinda xata ce masa ta kalleshi ta marairaice yaya bashir akwai matsala,daxu
naje wajan malamina yake fadamin yaran nan ba banxa suka barka ba sun maka asiri sosai
kuma yayi tasiri ajikinka,ya fadamin ma xamansu cikin gidan nan babu alkairi ka koresu wannan
maganin danake barbadawa shine makarin asirin da suka maka dan yace gidan nan xagaye
yake da layun da sukai maka binne, kallon takaici yake mata kamar ya rufeta da duka yace,
meyake damunki hadiza ? meyasa kika bata kanki da wannan banxar rayuwar ? wannan wacce
gurbatacciyar rayuwa ce kika dora kanki akai ? wanne irin asiri kuma ? yaran nan nina janyo su
jikina basu suka kawomin kansu ba, ki dinka abu da tunanin me jibi xata haifar, kina da yaya

xaki samu jikoki idan suka fada irin wannan rayuwar xakiso su hadu da hannu nagari shi alheri
dankone mai shi yake bibiya,
da mmk take kallonsa, yaya bashir ka yadda da abinda nake fada maka kasan baxan cutar da
kaiba ba xanso wani ya cuceka ba, tsawa ya kwatsa mata haushinta ya kamashi cike da
kuluwa yake girgixa kai dan mmkinta yagama kureshi, bansan a inda kika samu wannan
tarbiyyar ba dan iyayenmu ba irinta suka dora ki akaiba, wannan yaxama shine last kada
kikuma shigomin da irin wannan karerakin ni ba mutumin banxa bane nasan me nakeyi kije ki
tubarwa Allah muddin kina son xaman lafiya ki kiyaye, bana son karajin wayannan xantukan na
karyar banxa da wofi, ya kalli momy ki fdawa yaran nan su wanke wajan nan gaba daya, ya hau
sama momy ta tsaya kan stairs din tana neman nimbers din ma'aikatan gidan, ran umma abace
tacewa momy idan kin hanashi karya tsubbinki anan baki isa ki hana wanda xanyi a bayan
idonki ba ta gallawa momy harara tai bangarenta momy takira yaran cikin daren suka wanke
falon


***********
washegari da safe momy xama tayi a kitcean tana kallon jidda da ummanta suna ta
xirga xirga taki barin kitcean din har sai su suwaiba suka gama hada musu breakfast aka jeresu
a dining suka hadu nan kowa ya karya banda khaleel dan tun xuwansu jidda bai fiya xama aci
abinci da shi ba, bayan sungama tacewa jannat ta dauki nashi ta kai mishi tana kallon irin kallon
takaicin da umma da jidda suke yiwa jannat a kunyace ta ratsa ta gabansu ta dauka tai
bangarensa sallama tai masa ya amsa ya fito daga wanka jikinshi daure da farin towel dan
karamin a hannunsa yana goge ruwan kanshi dashi, kallo daya tai masa ta kauda kanta ta ajjiye
kayan ya karaso kusa da ita ya xauna ta gaishe shi ba tare da ta kalli inda yake ba ya amsa
yana kallonta ta mike xata fita ya dakatar da ita,
"ina xaki tafi baki xuba min ba,
ta kalleshi kunya ta kamata sbd ba riga jikinshi ta sunkuyar da kai naga baka shirya ba, dawo ki
xauna xanje na shirya tunda naga kina jin kunyar kallona, ya tashi ya shiga bed room dinshi tayi
ajiyar xuciya ta cire hijab din ta xuba masa tea a cup da soyayyan dankali ta hada masa da
plantains ya shigo falon nasa ya saka wando 3 quarter da riga me gajeran hannu ya xauna ta
miko masa cup din ya amsa dayan hannun nashi rike da remote xai kunna tv shiru sukayi
dukansu suna sauraron lbaran bbc a hankali ta mike xata fita ya riko hannunta ta fixge hannun
ya kalleta yaga ta hada rai,
"fushin me kikeyi ?
ni ba fushi nakeba,
kallonta ya cigaba dayi ta juya ta fice daga dakin ya jinginar da kansa jikin kujera yana jin
kansa wani iri,

falo ta koma ta tarar da sulthana kwance kan kujera umma da jidda na gefe dukansu harar
junansu suke tana shiga suka bita da mugun kallo,
ganin yadda sukeyi yasa tace, sulthana tashi mu tafi daki akwai aikin da xaki tayani ta mike tayi
tsaki muje anty jannat mubar marasa aikinyi,
suna shiga daki jannat ta rufeta da fada,

sulthana meyake damunki ? kiyi hkr ki sharesu mana anty jannat nifa idan baxasu dainaba
nimafa baxan fasa ba ki kyalesu zanyi magaminsu kima daina wahalar da kanki dan baxan
daina ba tagumi jannat tayi tana kallon sulthanan dan da gaske takeyi,hmm Allah ya kyauta,
murguda baki sulthana tayi hade da cewa amin

***********
da rana ma momy tattaro su jannat tayi da sulthana suka shiga kitcean suna aiki tare
da ma'aikatan momy tana xaune a kitcean din ana ko mai akan idonta jidda tashigo ganinsu
duka yasa tayi sororo jikinta asanyaye tace momy kina nan na duba cikin gidan ban ganki ba
murmushi momy tayi tace eh jidda muna nan ana aikin tare damu, gyada kai jiddan tayi hnklinta
atashe ta juya tabar kitcean din murmushi momy ta kumayi dan tasan akwai abinda ya kawo ta
ganin su yasa jikinta yin sanyi, kiran sallar da akayine yasa momy ta dakatar da su akan suje
suyi sallah jannat kawai suka bari sbd tana fashin sallah kafin momy ta tafi sai da tace kada ta
kuskura tabar kitcean d'in,suna fita ta hau tattara kayan ta suka b'ata xata gyara wajan rungumo
bayanta taji anyi a tsorace ta waiwayo tana kokarin yin ihu rufe mata baki yayi yana murmushi,
fusge jikinta tayi ya k'ara janyota jikinshi ya rungumeta k'am a hankali ya furta I extremely love u
jannat i love u too ina sonki ina sonki sosai, tun ranar dana fara ganinki nasan kece uwar
yayana tundaga lokacin nake dawainiya da soyayyarki, ina son na rayu dake,
mmk tayi dan jin xancen nashi tayi kamar saukar aradu ta lumshe ido tana jin dad'in mgnr
daya mata xamota yayi daga jikinsa ya kura mata ido cikin matuk'ar jin kunya ta sunkuyar da
kanta ya sa hannunshi biyu ya tallabo fuskar ta runtse idonta, cikin wata iriyar murya taji yace,
plx jannat bude idonki kiga soyayyarki cikin kwayar idona, ki kalleni ki tabbar da baxan iya
rayuwa babu ke ba plx jannat, maganganunshi sun kashe mata jiki ta bude idonta da kyar ta
kalleshi ta xame jikinta ta juya xata bar kitcean din ya riko hannunta a rikice,
ta waiwayo a hnkl tace masa ngd da soyayyarka ta xare hannunta ta fice,
xaro ido yayi yana mmkin amsar ta baiyi tunanin irinta xata bashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login