Showing 90001 words to 93000 words out of 132173 words

Chapter 31 - JENNIFER COMPLETE BOOK BY Maimuna A.A Rano.pdf

12 Apr 2025

6927

tayi, ina murna ta hanashi kula,
"Alhmdllh naji dad'i sosai da wannan rakiya" dai dai lokacin da driver yaja motar su hjy suna
musu addu'ar Allah ya tsare,
suna fita daga gidan ya janyota jikinsa yana kallonta itama kallonshi take da murmushi a
fuskarta
"harna fara tunanin halin da zan kasance na rashinki kusa dani"
far tayi da ido,
"ni kaina na shiga wani yanayi na rashinka da zanyi"
"wow!"
ya rungomata sosai yana murmushi mai sauti,
da sauri ta kufce jikinta had'e da xare ido kallonta yayi da rashin fahimta da ido ta nuna masa
bafa suka d'ai bane a motar tab'e baki yayi ya janyo ta jikinshi a kunnanta ya rad'a mata,
"ina ruwa na dashi babu wanda xai hanani shak'ar k'amshin matata mai dad'i"
marairaicewa tayi shafa lip dinta yayi ya girgixama mata kai
"kiyi hkr baxan iya xama kusa dake ban jiki ajikina ba"
ta kalleshi ya kashe mata ido d'aya

a haka sukaje airport basu b'ata lokaci ba suka hau jirgi yana rungume da ita har suka isa Abuja
tare da security d'in da aka had'asu kai tsaye gidan Abba na cen suka tafi dan anan yace su
xauna shi kanshi gidan xagaye yake da security jinjina kai khaleel yayi yana tausayin Abba
gaba d'ayan shi arikice yake axxaluman mutanen nan sun rikita shi bashi da kwanciyar hnkl ko
kad'an

suna shiga cikin gidan alwala suka d'auro sukayi sallar la'asar suna idarwa ya mik'e yana
kallonta,
"taso muje muyi wanka"
kwab'e fuska tayi kamar xatayi kuka
"kaje kafara yi in ka fito ni sai nayi"
zaro ido yayi yana kallonta,
"tashi muje"
nuk'u nuk'u ta tsaya yi da kanshi ya mik'ar da ita yana k'ok'arin cire mata kaya rik'e hannunshi
tayi tana dariyar dole
"tsaya tsaya ya khaleel bari na cire da kaina"
sakin ta yayi yana dariya ta cire kayan tsab ta d'aura towel suka shiga toilet kallonshi ta tsaya yi
tana tunanin cire towel d'in ganin haka yasa ya janyo hand shower ya jik'ata da shi tana dariya
da kanshi towel d'in ya sub'uce ya fad'o kamar wasu yara haka su ka d'inka wasa da hand
shower d'in daga hannun wannan xuwa hannun wannan sun dad'e suna wasan ruwan sannan
sukayi wanka shi kanshi wankan haka suka d'inka facin facin da kumfa sun b'ata lokaci mai
yawan gaske sannan suka fito kowanne jikinsa d'aure da towel yana rungume da ita suka
k'araso wajan mirror ya janyo wani towel d'in na daban ya tsane mata ruwan jikinta sannan ya
mik'a mata ta tsane na jikinsa suka shafa mai suna tsokanan junansa da man shafawar,
bayan sun gama shafa man ya kalleta,
" kwalliya xan miki da kaina"
ware ido tayi had'e da dariya tana kallonshi,
ya d'auko powder ya shafa mata tana kallon mudubi tana mmk ya d'auko lip stick ya shafa mata
a leb'e xata gyra ya tsayar da hannunta,
"no ! ban yadda ba ni zan gyra komai na hutar da ke "
haka ya bar fuskar yana kallonta ta jikin mudubi silent makeup yai mata kyau sosai ta tashi
tsaye,
"gsky ya khaleel ka iya makeup zan bud'e maka waje na musamman ka dink'a yiwa amare
mskeup dan kaxama babbn arties"
dariya yayi shima yana kallon bayanta da ta juya tana tafiya wajan inda kayansu yake,
"matata kawai na iya yiwa banda ita baxan iya a fuskar kowa ba"
ta d'auko musu kaya su ka shirya,
"zan tafi meeting da bak'on Abba inaga baxan wuce 2 hours to 3 ba"
ya rik'o hannunta suka isa k'ofa ya janyota jikinsa suna kallon juna ya shafa lip dinta da yake so
"kinyi kyau da wannan kwalliyar"
itama lip d'inshi ta shafa tace,
"kayi kyau da wannan shigar"
dariya yayi,

"duk abinda nai miki sai kin min ko?
itama dariya tayi had'e da yin far da manyan idanuwanta daya k'ara mata kyau,
"kai ka koyamin"
tafad'a idonsu cikin idon juna,
shafa cikinta yayi yana kallonta yana dariya k'asa k'asa,
sunkuyar da kanta tayi had'e da jin kunya ,
dariya ta bashi sosai,
"ki rama mana"
girgixa kai tayi kanta ak'asa,
birgesa tayi ya kalli kanta data sunkuyar dashi,
yasa hannu ya d'ago fuskarta da sauri ta rufe idonta
fuskarta d'auke da murmushi,
har yanxu hannunshi d'aya na cikinta yana shafawa,
"bud'e idonki beautyna"
a hnkl ta bud'e idon suka kalli juna da sauri ta rufe harda sa hannu,
"d'ago kanki plx"
ya fad'a muryar shi asanyaye,
ta bud'e idonta don bata son yi masa jayayya,
" ina sonki "ya fad'a had'e da yiwa hancinta kiss ta lumshe ido,
tana k'ok'arin janye jikinta ya kuma rik'ota
"ina xaki tafi ?
"katafi wajan meeting d'in karka b'ata lokaci"
d'age kafad'a yayi,
dariya ya bata yanda ya d'age kafad'ar,
"zantafi ammaa....
"amma me ?
bakinta taji cikin nashi yana tsotsarsu kamar me shan mint mai xak'i
yadad'e yana tsotsar bakin nanta sannan ya saketa yana fidda numfashi a hnkl itama munfashin
take a hnkl kanta ak'asa
muryarshi a tausashe yace,
"amma sai naji lafiyar lip d'ina"
ya shafa cikinta yana mata wani irin murmushi
"ajiyata tana nan tafe very soon"
xaro ido tayi ya fice yana dariya,
yana jin sassanyar muryarta tana masa addu'ar Allah ya dawo mata dashi lfy,


yana tafe driver na janshi yana tunanin jannat d'insa yana jin tamkar ana k'ara mishi sonta ajiyar
xuciya yayi yana nuna farin cikinsa da gdy ga Allah da ya bashi mace mai biyayya dan shi
rayuwar sa yana son biyayya a haka yaje wajan meeting d'in sama sama yake jinsu sai da suka
kusan kwashe 4 hours suna tattaunawa hnklinsa na kan ya koma gida ya shak'i kamshin jannat
d'insa mai sanyaya masa rai
basu gama ba sai gaf da sallar isha'i duk hnklin sa ya tashi baiyi tunanin meeting d'in xai kai su

wannan lokacin ba sai da ya tsaya yai sallah sannan suka taho akan hanya ya tsaya yai musu
siyayya mai yawan gsk suka taho

suna shiga ya fito daga motar dan sauri bai bari sun k'arasa parking ba kai tsaye cikin gidan ya
shiga had'e da sallama tana xaune a takure da ganinta kasan cikin damuwa take da sauri ta
d'ago manyan idanuwanta tana kallon shi had'e da yin ajiyar xuciya siyayyar ya ajjiye akan
center table d'in falon ya k'arasa kusa da ita ya xauna ya janyota jikinsa, hawaye ya gani
kwance kan fuskarta xaro ido yayi yana jin ba dad'i yasan dole ta damu,
"kaina bisa wuya beautyna!
kiyi hkr meeting d'inne yaja mu tsawon wannan lokacin ni kaina banyi tunanin xai kai mu haka
ba bazan kuma ba plx plx plx ina jin ba dad'i araina sbd na saki xubar da hawaye akan
kyakkyawar fuskarki ban so ba yasalam !"
ajiyar xuciya tayi tana kallonshi duk ya rikice sbd ganin hawayenta lumshe ido tayi tana jin
dad'in irin yanda yakeji da ita,
"ban xubar da hawaye na dan kadad'e ba nayi ne sbd ban san halin da kake cikiba"
k'ank'ameta yayi sbd yaji dad'in maganarta
"ina nan k'alau sai azabar tunaninki da nai tayi hnklina bai kwanta ba sai da najiki kwance cikin
jikina"
k'asa k'asa yai da muryar sa
"ina sonki jannah !"
ta xame daga jikinsa
"ka gaji muje kayi wanka kaci abinci"
baiyi musu ba ya mik'e hannunshi rik'e dana ta yana murxawa taraka shi bakin toilet d'in ya
shiga yai wanka ya fito da taimakonta ya sauya kaya ya kalli agogo 9:49pm
"ya khaleel taso muje kaci abinci"
wani irin kallo yake mata ya girgixa kai
"d'auko ledar dana ajjiye a falo"
ta juya ta fita ya bi bayanta da kallo had'e da lumshe ido bata dad'e ba ta dawo hannunta rik'e
da manyan ledojin ta xaune ya bud'e manyan gasassun kajine da kuma siyayya kala kala
"zo muci"
girgixa kai tayi,
"naci abincifa"
kallon da yai mata ne yasa ta marairaice ta matso tana ci kamar tana shan magani kad'an taci,
"ya khaleel na k'oshi fa dan bai bana son jayayya da kai"
jinjina kansa yayi
bayan ya gama ci ya mik'e yana kallonta fuskarshi d'auke da murmushi
"taso muje muyi alwalar nafilar da xamuyi"
jikinta asanyaye ta mik'e suka d'auro alwala sukayi sallah ya dad'e yana addu'a sannan ya
waiwayo yai addu'a tuni gabanta ya fara luguden fad'uwa dan tsoro bayan ya idar ya tsura mata
ido yana tunanin abubuwa da yawa jikinta na rawa ta mik'e xata fita gaba d'aya ta rikice jikinta
har ya fara rawa, da mmk ya kalleta,
"ina xaki jannah !?

hanjin cikinta sai da yaka d'a dan tsoro
"dawo nan ki xauna ba inda xaki "
[2/28, 6:44 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍



95&96

*Ummee Garkuwa*
yana gama fad'an ya kashe wayar,
shiru ya khaleel yayi jikinsa asanyaye ya mik'e ya nufi cikin gidan b'angaren sa ya nufa ya
shiga d'akinsa a xaune ya sameta ta had'a kai da gwiwa, xumb'ur ta mik'e tana kallonsa yanayin
da taga ya shigo ne yasa ta marairaice hawayen da yarage a idonta ya k'arasa xubowa,
"dan Allah ya khaleel kayi hkr wllh ban fad'awa dady ka hanani xuwa da wata manufa ba
baxan iya yi masa k'arya bane"
kallonta kawai yake tana xubda hawaye tausayinta ya kamashi ya jinjina kai lallai jannat d'insa
ta dabance da wata ce fishi xata yi dashi amma ita hkr take bashi haushin kansa yaka masa
meyasa ma ya hanata alhali tana gudun b'acin ransa ? meyasa yadda take son faranta masa
shima baxaiyi k'ok'arin faranta mata ba ? k'ara sowa kusa da ita yayi still hak'urin take kuma bashi sbd taga baiyi mgn ba,
kusa da ita ya tsaya numfashin su na karo da juna da kyar ya iya d'aga hannunsa dan jikinsa
nauyi yai masa yasa hannunshi a wuyanta ya cire mata sark'a ya d'ago hannunta ya cire
awarwaronta da xobunan ta kallonshi kawai take cike da mmkin sa ya d'auko hankacif ya goge
janbakin da ke leb'enta tass sannan ya goge eyebrow d'inta sai da ya goge kwalliyar fuskarta
tass sannan yace,
"je ki wanke fuskarki"
jikinta asanyaye ta shiga toilet ta wanke fuskarta ta fito ya d'auko wani hankacif d'in daban ya
goge ruwan fuskarta ga mmkinsa sai yaga kamar ma tafi kyau babu makeup,
jinjina kai yayi,
" ke ta dabance ina jin kishin ki fita da wannan kwalliyar wasu mazan su ganki da ita, na goge
ma duk da hakan ina ganin kinyi kyau ya d'anyi shiru yana tunani
"kiyi hkr nasan na b'ata miki rai banyi hakan dan ranki ya b'aci ba nayi ne sbd bana son kowa
yasan kyawun da matata take dashi ina tsananin sonki sonda nake mikine yasa nake matuk'ar
kishinki"
idontane ya cicciko da bawaye kamar xata fashe da kuka ta rik'o hannunsa,
"ni ya kamata na baka hkr dan ni nayi kuskure wajan nunawa wasu kwalliyata wanda hakan
yake haramun tunda ni matar aure ce kayi hkr ya khaleel hidima ta sani manta hakan ngd daka
tunasar dani tak'arasa da kuka,
rungumota jikinsa yayi ,
"no ! no ! beautyna kada kiyi kuka kiyi hkr mu tafi a hakan ina mmkin yarinya k'arama dake kin
san hak'k'in aure ubangiji Allah yai miki albarka"
ta amsa da "amin,
yaja hannunta ta nok'e tana girgixa kai sororo yayi yana kallonta,

"menene beautyna?
far tayi da ido,
"tunda baka so ba inda xani "
murmushi yayi kad'an had'e da manna mata kiss,
"ina sonki jannah ! kiyi hkr muje"
yaja hannunta suka fice daga d'akinsa ya bud'e mata mota ta shiga ya shiga shima ya fice daga
gidan



suna isa wajan hjy murja tak'ara so wajansu da sauri taja hannun jannat sukaje wajan da aka
tanadar musu ta xaunar da ita kusa da y'an'uwanta haka akayi ta musu addu'o'i da kuma basu
kyautuka tagani ta fad'a sannan aka fara ciye ciye
hjy murja ita da hjy Nabila da dady da wani matashin saurayi sukayo wajansu matashin
saurayin ne ya k'ura musu ido cikin fara'a da murna
"anty murja nuna min hishma ta acikinsu Allah nagode maka da ka dawo mun da hishma gida
alhmdllh,
hindu ta turo baki dan tasan ita yake nema,
cikin fara'a hjy murja tace,
"lallai hafiz wato hishma kawai ga Afrah nan da jasra baka ambace su ba sai ita kad'ai wannan
ai son kaine"
murmushi yayi
"nasan duk gasunan ni dai ina son sake kallon fuskar hishma ta rabona da ita shekara nawa
Abba nuna min hishma acikinsu"
da sauri hjy murja tace
"Abban jannat karka nuna mishi kyaleshi ya nunata da kansa"
rik'e kansa yayi da hannu,
"oh anty murja kina wahalar dani kuma na matsu naganta anty nabila plx nuna min ita"
tana murmushi hjy Nabila ta nuna hindu,
"yanda ka matsu a nuna maka ai kwara ka ganta kaga yanda hishman ka ta koma"
zare ido yayi,
"wow ! hishma ! kece kika xama haka ?
alhmdllh Abba kaga hishma ko ?
bata sanni ba plx anty murja ki bata labarina"
"kwantar da hnklinka hafiz zan bata labari sai mun koma gida"
idonshi ya kai kan su sulthana,
"ina Afrah ina jasra ?
murgud'a baki sulthana tayi babu su anan"
dariya yayi cikin wasa yace,
"toh suwaye ?
"jannat ce da sulthana
rangwabar da kansa yayi toh,
"k'anne na kuna lfy ?

yab'una fuska sulthana tayi,
"sai yanxu zaka kulamu?
ba hishma kawai ka sani ba ?
dariya sukayi dukansu hjy murja tace,
"sarkin kishi ai masa afuwa ya rud'e ne da yawa baya k'asar kuka dawo na bashi mmk ne bai
san da dawowar ku ba sai jiya da yaxo"
ya kallesu ya d'age kafad'a
"sai mun koma gida zansha lbr ko hishma?
b'ata rai tayi,
"nifa sunana hindu"
kama bakin shi yayi,
"sorry hindu baxan kuma ba kinji aimin afuwa ban san komai ba sai yanxu bari na barku xuwa
yau da daddare zamu had'u zaki fahimci koni waye awajanki"
dady yace
"ai yau bamu da sakewa hishman hafiz ta dawo " yana mgnr suna tafiya hannunshi rik'e dana
hafiz d'in dagani kasan sun shak'u da juna bayan angama ciye ciye akai addu'o'i akan Allah ya
tsaresu ya kuma tona asirin way'anda suka sacesu taro ya watse kowa yana cike da murna da
annushuwa

bayan sun koma gida sunyi wanka gajiya ta sauka wayar jidda tana ta ring tak'i d'agawa jannat
ta kalleta ta girgixa kai,
"wai anty jidda meyasa baxaki d'aga ba ?
ya mutsa fuska jiddan tayi had'e da kashewa wayan,
"mtssww anty jannat ko na d'aga takaici kamani xaiyi kun d'auki abun k'arami sam bakusan
girman shiba"
gaba d'ayansu kallonta suke,
zahra tace,
"anty jidda ke kika mai dashi babban abu tun farko kin maidashi mai girma "
jannat tace,
"anty jidda mai zai hana ki had'ashi da sarkin iya tsari ?
gaba d'ayansu suka kalli jannat
sulthana tace
"waye kuma sarkin tsari ?
sai da jannat tayi dariya tace,
"mahboob mana"
dariya dukansu sukayi Rubayya tace,
"la la laa anty jannat kin kawo shawara danjuma kam tabbas daya mahboob ya dace kun san
shine da tsara mgn musamman in yaga mace"
dukansu dariya suke har jiddan,
"wllh kam hakane anty jannat zan had'asu nasan mahboob bashi da wata matsala"
hjy murja ce ta shigo tana mgn;
"nifa narasa wacece anty a cikinku dukkanku kowa sai naji kuna kiranshi da anty wacece antyn

ta gsky ?
jannat da sulthana suka nuna jidda,
jidda da zahra da Rubayya suka nuna jannat,
dariya dukansu sukayi,
hjy murja ta ware ido
"tsakanin jannat da jidda waye anty ?
jidda tace,
"jannat ce anty dan tana auren babban yayanmu kinga umma dole itace anty"
sulthana tace,
"umma kinga itace babbarmu tun farko kinga dole muce mata anty "
rik'e hab'a hjy murja tayi,
"kowa yana da gsky dole ku dink'a kiran junanku da anty " ta kalli hindu datake akwance tana
kallonsu bata mgn,
"hindu ga hafiz cen yadamu sai ya ganki nace masa a'ah kin gaji kuma dare tayi sai gobe baku
san shi ba ko ?
kai suka d'aga mata suna kallonta,
"k'anina ne uwa da uba duka d'aya lokacin da suka mutu rik'onshi ya dawo hannuna dan shine
autanmu da aka bani ke tun kina jinjira kullum kina hannunsa yana sonki yana ji dake yana
fad'awa kowa kece matarsa in ya girma"
ya b'una fuska hindu tayi had'e da yak'e,
"bayan an sace ku kullum sai yayi kuka akan yana son ganin hishmar sa da kyar akeyi masa
dabara ace an kaiki makarantar jarirai"
tak'ara sa mgnr kamar zatayi kuka,
sulthana tace,
"dole ya damu yana son ganinta ashe matar shi xai gani "tak'ara sa mgnr da dariya k'asa k'asa,
hjy murja mik'ewa tayi,
"sannu sulthana kedai kishi kike tun d'axu dan baice yana son ganinki ba"
ta fice daga d'akin
rubayya tace
"oh hindu da saurayi,
kwafa hindun tayi,
"ni konaje ma ban san me zance masa ba danni wllh ban san abinda ake fad'a awajan zance da
namiji ba"
kwashewa sukayi da dariya,
sulthana tace,
"anty hindu dama fa ke ba abinda kika iya kada kidamu ga iyayen soyayya nan anty jannat zata
koya miki abinda ake fad'a,
girgixa kai jannat tayi "ke kika sani"


suna xaune a falo dukansu hira suke sosai hirar walimar yau had'e da murnan angama lafiya ya
khaleel sai raba ido yake yana kallon agogo ko xai ga fitowar ta shiru shiru har kusan 10;00
kasa jurewa yayi ya mik'e xaije b'angaren su hjy murja ta kalli Abba ta nuna masa da ido ya kalli

khaleel dayake gaf da xaifara hawan stairs,
dady ya kalleshi da mmk yace,
"khaleel ina xaka haka dare yayi ?
sosan kanshi ya keyi yana in ina,
"dama...dama.. ina ..son zan duba.. jannat ne..
zaro ido dady yayi,
"kabari sai gobe dare yayi,
Abba yace
"ah 'ah yaje ya ganta jeka khaleel"
juyawa yayi cike da jin kunya ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login