Showing 18001 words to 21000 words out of 132173 words

Chapter 7 - JENNIFER COMPLETE BOOK BY Maimuna A.A Rano.pdf

12 Apr 2025

6846

PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍

31&32



Gaba dayansu rikicewa sukayi musamman Momy da ta dora hannu aka cikin wani mugun
yanayi narashin tabbas Yar mutane ta mutu a dalilina rubayyace ta turesu daga jikin jennifer ta
kamota sbd nauyi ta kasa sai da ta nemi temakon su sa'a suka kama mata ita suwaiba kuwa
aikin rusa kuka take cike da jimamin faruwar abun da kyar suka iya dagata saboda mutuwar da
jikinsu yayi suka sata a mota Rubayya taja motar suwaiba ta shiga sbd rudewar da sukayi bame
me gyale asalima sun mance yanda suka fice Momy kasa xuwa tayi gani take babu wani sauki
Jennifer ta riga mu gidan gsky hawaye ke bin fuskarta da tarin Dana Sani na rashin kula da
yarinyar har wuta ta jata haduwa sukai ababban falo bamai cewa kowa uffan inbanda jimami da
raddadi zahra ma arikice take hnklinta yai masifar tashi damuwa da fargaba suka taran mata
tagumi tayi cike da danasani tana ta jera duk adduar da taxo bakinta akan Allah ya Sa Jennifer
ba mutuwa tayiba Jidda ma tagumin tayi cike da mutuwar jiki tana mmkin ganinta yanxu yanxu
amma har rai yayi hnlinsa tuni xuciyarta ta tsorata da hukuncin ubangiji cikin damuwa da jimami
tacewa Momy yaakayi ta taba soket din har wuta ta jata kasa bata amsa Momy tayi dan ita
kadai tasan me takeji aranta girgixa mata kai kawai tayi jin tmbyr da Jidda tayi yasa zahra kara
rudewa dan itace ummul aba'isin wannan bala'in da ayanxu take matukar Dana sanin aikata
hakan






Cikin asibitin suka shiga gadon daukar marasa lafiya nos sukaxo dashi suka dauki Jennifer cikin
gaggawa suka shigar da ita dakin duba marasa lafiya agagguce likitocin suka rufu akanta suna
iya bakin kokarinsu safa da marwa ruby take yi suwaiba na gefe adurkushe tana xubda hawaye
a xuciyarta kuwa xabga addua takeyi na Allah ya tashi kafadar Jennifer lallai sai yanxu ta
tabbatarwa da kanta tayi mugun sabo da ita sun dauki dogon lokaci suna cikin damuwa hade da
fargabar halin da Jennifer take ciki bayan dogon lokaci Dr ya fito yace su kwantar da hnklinsu ta
farfado xasuyi mata duk abinda ya dace ya wuce office dan ya rubuta musu abubuwan da suke
so abata da magungunan daya dace da lalurarta hamdala dukansu sukayi cike da murna na sai
alokacin suka gane yanayin da sukabar gida bayan Dr ya basu list din yace yanxu yanxu akeso
ta karba ta fito akan suwaiba ta kula da ita xataje ta siyo sannan xata koma gida ta sanar da
Momy sbd ta mance wayarta agida

A yadda ta barsu haka tashigo gidan ta samesu da sauri Momy ta kalleta tana son jin Karin
bayani Momy ta farka numfashi taja mai karfi hade da ajiyar xuciya gumi ya karyo mata cike da
murna tace alhamdulillah itama zahra hamdalar tayi aranta na jin dadin bata kashe rai ba bana
tausayin halin da Jennifern take ciki ba ta mike xata hau sama ruby ta dakatar da ita zahra ! Ta
tsaya tana kallonta kinsan ke kika jefa mu cikin wannan yanayin ?? Rai fa duk raine bata rai tayi
kinga nifa bansan xata jata da yawa haka ba toma menene abinda yadace ta itane tunda jininta
ya halatta ta karasa mgnr hade da yatsine fuska da murguda baki injiwa yace jininta halattacce
ne ?? Ki ka kuskura kika dauki rai koda na kafurine in dai baya cikin sharuddan kisa a addini kin
aikata babban kuskure kuma wutar Allah sai ta ciki tsaki zahra tayi to yanxu tunda bata
mutunba sai asakar min Mara nai fitsari taja tsaki ta haye sama Momy da Jidda kasa mgn
sukayi sbd mmkin da xahra ta basu hmmm Allah ya shirya min ke zahra ruby ta fada cike da
damuwa da kuma mmkin kiyayyar zahra akan Jennifer



****************

Ta bude ido ta gansu akanta ta lumshe ido hawaye ya sauko mata ganin ta bude ido yasa suka
fara mata sannu sannu kai ta daga musu ta riko hannun suwaiba muryar ta na rawa tace
suwaiba naji dadi da Allah yasa ban mutu ba batare da na karbi addinin musulinci ba tabbas
Allah na sona tunda har na rayu kuma ina Sa ran samun gafararsa da rahamarsa hawaye ya
sauko mata in shaa Allah da lokaci yayi zan dawo kamarku nima xuciyta ta Dade da yadda da
addinin musulunci tun ina yarinya karbane kawai banyi ba amma yanxu lokaci ya kusa gaba
dayansu mmk ta basu da kuma tsananin tausayi Momy ta karaso kusa da ita inshaa Allah xaki
rayu xaki karbi addinin Allah ki mutu acikinsa ki kwantar da hnklinki komai yana da time banko
kofa akayi haisam tsaye bakin kofa cikin tashin hnklin yayo wajanta yasalam Jennifer sannu
yanxu nakoma gida danjuma yake bani lbr ban baro gida ba sai da nakira office na nefa akan
suxo su gyara wajan sannu my Jennifer kusa da ita yakara so fuskarshi cike da tausayinta da
kuma tashin hnkl




******************

Cikin hukuncin Allah cikin kwanaki uku ta warware sbd yanda doctors din asibitin suke kula da
ita lallai tasha gata awajan yan gidan tmkr yarsu haka suka maida ita komai na jin dadi sun
ajjiye mata xahra ce kawai taxo hospital din sau 1 sukam kullum anan suke yini haka Momy ta
kafa ta tsare akan bataso iyayenta suji zancen dan kada hnklinsu ya tashi su dauki matakin
rabata da gidan ita kanta Jennifer batai karanbanin tunanin sanar dasu ba dan muddin suka

Sani to dukkan plan dinta ya rushe kulawar da suka nuna mata yasa takara sakankacewa ta
kuma dauki damarar duk rintsi tana tare dasu har burinta ya cike suka daine mutanen da tai
mu'amala dasu ta kuma yi sabo dasu sabanin iyayenta dan mamanta bata barinta mu'amala da
musulmai dan tsoron karta musulunta tunda sunfuskanci Sam addininsu bai damu Jennifern ba

Yau aka salla mota suka dawo gida ta murmure sai rashin karbin jiki shima sai a hnkl xata koma
nrml Momy canza mata daki tayi ta dawo da ita bangaren yanmatan gidan Jennifer taji dadin
hakan sosai zahra kam taji haushi dan kiri kiri ta nuna bata so hakan ta faru ba da yamma suna
babban falon gidan kamar yadda suka saba ya haisam ya shigo hira sukeyi banda Jennifer da
tayi shiru tana tunanin wasu abubuwa da ita kadai tasansu ya xauna kusa da Momy ya dan kalli
Jennifer yace ya jiki ? Kanta asunkuye cikin jin nauyi da kunya ta amsa da sauki Momy yaufa
12: jirginsu khaleel xai sauka Jidda cike da jin dadi ta mike tana rawa oyoyo my heart yau xai
dawo dariya dukansu sukayi haisam yace ke kam kinfiya dauki ko irin Jan class din nan da
kuma kunya tai far da ido wa zanjiwa kunya ?? Ya nuna Momy da ido tabbi momyn tawa ta taho
da sauri ta rungume Momy momyn ta tallabota tana dariya wai fa kinji Momy ke xanji kunya
Murmushi kawai momyn tayi ruby tace ai Anty Jidda bata hada kowa da ya khaleel dinta ba
inkaga tana rawar kafa to tana kusa dashi far Jidda tayi da ido sbd shi na musamman ne
shiyasa nake rawar jiki akansa kada wata ta kwace min shi haisam yace ba mmk a tafiyar nan
tashi yasamu wata girlfriend a can zaro ido tayi hade da bata rai ya haisam xamu bata fa ta
shagwabe fuska Momy kina jin yaya haisam ko Momy ta jijjiga ta sorry shareshi kin San
halinsa dan tsokana haisam yace to shagwabatu da anyi mgn kice Momy kamar ke kadaice
me ita

mikewa Jennifer tayi dan tagaji da jin hirarsu mai bata haushi dakinta sabo ta koma ta kwanta ta
rufe kanta da bargo hawaye ya sauko mata


*****************

Tun 11: sukaje airport tarar shi Jennifer ma ta bisu dan yanxu sun maida ita tamkar tasu janta
sukeyi sosai ajiki sbd sunji tana muradin addinin musulunci itakam taji dadin wannan mugunta
ta xahra tunda gashi ta dalilin haka tana samun kulawa da kuma tausayawa tana ganin ta haka
ne babban burinta xai ciki 12:10 jirginsu ya khaleel ya sauka suna tsaye wajan masu jira suka
hangoshi hannunsa dauke da jakar shi dayan hannun kuma rike da iphat cikin kasaita da isa
yake jefa kafarsa Jennifer na hangoshi gabanta ya fadi yayi Kyau yayi haske ya danyi kiba yana
karaso wa Jidda tasa kukan shagwaba ta fada jikinshi yayi murmushi ya dan ture ta kadan hade
da rike mata hannu yan uwan ma rungumeshi sukayi suna fadin oyoyo 1 week kawai amma
kowa yayi missing dinka bai kula da itaba sai da ya kusa shiga mota ya ganta arakube ya kura
mata ido bai San lokacin da yace kinyi rashin lfy ne ?? Turus sukayi gaba dayansu cike da
mmkin tambayar da yai mata ganin jikinsu yayi sanyi yasa yace kin koma gefe kin rakube kamar
Mara lfy oya Ku shigo mota mutafi nagaji ina son hutawa suka shiga mota dukansu suka bar
wajan

*******************

Bayan kwna 2 da dawowarsa daga Singapore suna xaune basu Dade da gama yin breakfast va
duk da yaga sauye sauye akan Jennifer bai nuna ya lura da hakan ba sbd miskilanci Jidda sai
shishshige masa takeyi duk inda ya xauna tana kusa da shi Jennifer tun tana damuwa har tafa
ra hkr ta xuba musu ido yauma tana kusa dashi tace sweeter ina tsaraba oh ! Ya fada na manta
ke ! Yacewa Jennifer ta kalleshi ya miko mata key din dakinsa kije ki daukomin wata karamar
jaka ta amsa tafice haushin shi duk ya kamata ta dauko ta kawo masa ya ciro wayoyi masu
Kyau da tsada iPhone last ta wannan year din ya raba musu suka hau murna dukansu abin
mmk ya dauko irinta sak ya mikawa Jennifer sororo sukayi dukansu ita kanta Jennifer mmk abin
ya bata ciki kuwa har da Momy Jidda kasa boye kishinta tayi ya xakayi hk khaleel ka hada
bamu kyauta da Yar aiki zahra ma mugun kallo tabi Jennifer ta shi ita kanta Momy da Rubayya
wani rikitaccen kallo sukewa Jennifer ta sunkuyar da kanta kamar ta fashe da kuka tsawa Jidda
tayi masa ganin bashi da niyyar amsa mata tmbyrta me kake nufi !? Ya dago kai hnkl kwance ni
kikewa tsawa ? Sbd kin maidani danki ko ? Abinda kikeso xanyi ? Xaki iya hidimta min kamar
yadda takemin gyaren daki girkina duk itace kifada min kintaba min daya daga ciki?? cikin jin
haushi tace ai biyanta akeyi afusace yace ke kike biyanta abinda naga dama shinakeyi bakuma
Wanda ya isa yace min danme idan kina so mushirya kibi tsarina idan kuwa ba haka ba ki kuka
da kanki ya mike yabar falon tasa kuka ta mike tana sane ta takwa Jennifer hannu harda
murxawa tai sama tana kuka






By
*UMMEEYY*
[2/28, 6:41 PM] Nana Zee: ✍✍✍JENNIFER✍✍✍




27&28


Tun xuwanshi saudiyya ya dage da addu'a sosai kullum yana masallaci yana adduar samun
falala da kuma rahma awajan ubangiji xuciyar shi tafara haske damuwar dayake ji akan sanin
wacece Jennifer ta taragu fiye da da dan da wani irin abu yakeji ya tsaya masa arai kansa ya
kulle tunani ma rasa wanne iri xaiyi yanxu kam xuciyarshi tayi tass yasamu kwarin gwiwar da
xaiyi binciken asalinta da kuma manufarta na munafuntarsu sai dai tunda yaje basu haduba
daya idar da ibadarsa aikin nemanta yake tafiya haryanxu basu haduba

Kwanakin daya kesonyi sun kusa karewa xuciyarshi ta fara taradda din ko shareef al Hussain y
samu nasarar kasheta ?? Dam gabanshi ya buga ya salam ! Dukkan mai rai mamacine amma
baxaiji dadin mutuwar ta ba yaso ace ta musulunta ta tuba sannan yana son jin lbrinta dafa
kanshi yayi shikam baita ba cin karo da wannan al'amarin ba koda kuwa a films tashi yai ya
koma masallaci yai addu'a sosai sai dare ya dawo gida ya shirya kayansa a jaka dan gobe yake
son wucewa ranso bai soba tunaninshi Jennifer bata raye ya kwanta ranshi abace



Washegari ya shirya ya fito ya hau motar daxata kaishi airport ya sauka daga motar ya shiga
ciki

Bayan sungama masa komai ya xauna jiran time dan sai 1 jirginsu xai tashi wata mota ya
hango mai Kyau sosai ta shigo tai parking ya kalli motar tai masa Kyau a ido ya kauda kansa ya
cigaba da kallon shuke shuken da ke wajan dai dai lokacin daya ji sanarwar passengers
wayanda suka da wo daga Egypt sun sauka ya sunkuyar da kansa kasa yana dagowa yaga
wata mace mai kiba fara irin farin 9ja ya kuma kallonta yana son tunu inda ya santa wata ya
hango sanye cikin riga da wando Pakistan ta yafa kyalen kayan akanta bayanta ya hango baiga
fuskarba rungume juna sukayi suna dariya kana ganinsu kaga jin dadi da kwanciyar hnkl
waiwayor daxatayi gabansa yai mummunan faduwa da sauri ya mike hade dayin Hamdala ya
nufo su yana jin dadin sake ganinta kafin ya karaso har ta budewa babbar macen nan mota ta
shiga itakuma ta xagayo tana kokarin budewa ta shiga Jennifer ! Ya kira sunanta ta waiwayo
sbd yaxo gab da ita ta galla mishi harara tana mishi kallon raini fuskarta cike da tsiwa meyasa
kike wasa da hankalina ? Dakata tace mishi baka da hnkl ya xaro ido yana mata kallon mmk ko
kana da shi ?? Ta tambayeshi da rainin wayo shiru yayi yakasa bata amsa dan yasan da rainin
wayo murmushi tayi ta bude mota kadan kaji ka kuma gani ta fada mota driver yaja ya wuce
mmkinsa ya karo me yarinyar nan take nufi da kadan kaji kadan kuma ka gani ?? Tana nufin
xata kuma cigaba da wahalar masa da tunani ?? Girgixa kai yayi zaiyi watsi da son sanin ko ita
wacece koma metake son yi musu Allah ya fita hk time yayi ya hau jirgi ransa abace





Daki ta shiga ta xauna kusa da suwaiba tana kokarin kishingida suwaiba hnklinta nakan novel
tana karantawa hannu Jennifer tasa ta warce buk din da sauri suwaiba ta kalleta tana murmushi
dan Allah bani Jennifer in karasa haba a tsurawa buk ido ba'aji ba'a gani karatun novel kawai
hmmm baxaki gane bane bakisan dadin da yake cikin karanta novel ba far Jennifer tayi da ido
hade da tungura mata buk din gashi nan ki cigaba da aikin kurawa buk ido da sauri suwaiba ta
dauka ta dago kai takalli Jennifer gobe Mr coffee xaiyi tafiya dariya Jennifer tayi hade da
gyarama xama ya khaleel ba ina xaije xaibi dadi Singapore daxu ina babban falo zan kunna
turaren wuta naji suna hirar Jidda tana ta zabga shagwaba Momy tana lallashinta kinsan abin

ban haushi ? Jennifer ta girgixa kai kanshi na kan waya yana danne danne baice cikanki ba
abin ban haushi tsaki Jennifer taja su suka Sani suwaiba ta cigaba da mgn nafuskanci khaleel
din nan miskiline na karshe ace budurwarka na kukan missing dinka sbd xakayi tafiya ka kasa
ce mata komai hmmm tabbijam ina son miskilin namiji amma na Mr coffee yayi yawa ajiyar
xuciya Jennifer tayi tana jinjina xancen wayar hannunta ta duba kinga lokaci yayi tashi muje mu
fara aiki mikewa suwaiba tayi ta cigaba da mgn duk cikinsu mahboob yafi sauki amma kinga Mr
pepper karshe kenan haisam tunda ya dawo dai naga kamar yarage wulakanci Jennifer tai
dariya watakil inda yaje ne suka Konya masa daraja dan adam sukayi dariya dukansu suka
shiga kitchen dan fara aikin abincin dare



Washegari bayan yan gidan sungama cin abincin rana Jennifer ta fito tana kwashe kayan tana
kaisu kitchen dukansu yan gidan suna babban falo kamar ko yaushe suna hirarsu ke ! Taji
muryar ya khaleel yana kiranta ta tsaya cak zonan da sauri tai cikin falon ba wanda ya kalleta
sai Momy key ya mika mata shiga dakina ki dauko min jakar akwatina ta amshi key din ta fara
tafiya taji Momy nace mishi time fa ya kusayi katashi mana tafice dakinsa ta nufa a hargitse ta
tadda dakin ta sunkuya ta sunkuci jakar tafito ta taddasu atsaye jikin motocinsu ta ajjiye jakar
tana miko masa key din nop ki koma ki daukomin dayar guda biyu juyawa tayi ta koma ta dauko
dayar har ya shiga mota shida Jidda suna baya driver na gaba dayar motar kuma Rubayya ce
zahra na kusa da ita Momy ta kalli Jennifer ko xaki bisu shiru tayi tana murmushi jeki ki dauko
gyalenki kiyi musu rakiya jiknta asanyaye ta je daki ta dauko gyale ta shiga bayan motar da
Rubayya take ja suka bi bayan motar su ya khaleel


Bayan sun je airport din Jidda na zuba masa shagwaba ta rike masa hannu har time din da akai
kiransu tasa kuka ya tsaya yana kallon fuskarta yasa hannu ya goge hawayen da ke xarya a
fuskarta kiyi hkr plx 1 week kawai zanyi zan dawo tarike masa hannu biyun duka zanyi missing
dinka sosai a wannan week din sannan tasaki hannun kallon Jennifer yayi ke ! Xo ki dauki jakar
nan kibiyo ni da ita turuss gaba dayansu sukayi suna mmk da sauri Jidda tace bari na daukar
maka a a ajjiyeta tamiki nauyi ganin ba wasa a fuskarshi yasa ta ajjiye jakar da tai saurin dauka
sbd yace na dauka hannun Jennifer na rawa ta dauka tabi bayanshi yayin da suka rakata da
muguwar harara sunyi tafiya sai da suka xo dai dai wajan da ba dama Jennifer ta shiga ya tsaya
yana kallonta murmushin mugunta ya watsa mata da sauri ta sunkuyar da idonta tana son gane
fassarar murmushin ke ! Yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login